Sunday, 23 October 2016

HEEDAYAH!


                1⃣7⃣
   written by miemiebee👄

       Dr yakira nurses aka dagata itama aka kaita wata dakin, heedayah na ganin mummy'nta a sume ta sakar dawata irin ihu sanda aka fitar da ita daga asibitin kuka takeyi sosai kamar ba yarinya ba, immediate attention aka bama mummy within 20mins ta farfado ba abin da take furtawa face "habibi na don't go nd leave me" ahaka har tayi gaining back conciousness, kuka takeyi sosai heedayah da nanny ne suka shigo, heedayah ta karasa gun mummy'nta tayi huggung nata tightly tana kuka "mummy ina daddy? Muje mu daukosa mukoma gda mubar wannan asibitin eventually we will all fall sick dan Allah mutafi" tafashe dawata erin kuka me tsuma zuciya mummy ta taso da ita daga jikinta tace "look at me heedayah" da hannunta biyu rike a fuskarta "zamu tafi gda kinji dnt worry bari daddy yadan samu sauki kadan se mutafi stop crying kinji? Bansan inga princess dina na kuka, ure tears are way expensive, kinsan menakeso dake ynxu?" Heedayah ta girgiza kai da alaman a'a mummy tace "kuje gda da nanny kici abinci kiyi sallah, pray for daddy, do ur assignmnts seki kwanta ki huta kinji? Kina tashy nida daddy zamu dawo gda heedayah tace "inason inga daddy, mummy pls ko kadan inason inga daddy na" mummy tace "don't worry ynxu daddy na bacci anjima kadan ze tashy" heedayah tace "promise me mummy" baki na rawa mummy tace "i promise mumy's princess" tabata peck a goshi tace wa nanny "ku tafi" nanny bata ce komi ba takama hannun heedayah suka fice mal idi yayi dropping nasu sannan mumy ta kirasa yakuma dwowa asibitin. Bayan tashin mummy da like 15mins dr yashigo ya dubata yaga shes perfectly fine yace "ki huta madam, Allah bada lafya" mummy tace "ameen dr pls tell me meke damun mijina? How is he? Inason ganin mijina pls he need me by his side" dr yace "calm down ynxu ki huta" mummy ta ta rokon dr da yagayamata meke damun mijinta daga karshe ya karisa gaya mata bebar komi ba, salatin mummy kawai ke tashy a cikin dakin wai ace yau an wayi gary daddy is paralysed, bayida wani amfani kuma again, dashy da babu duk daya ne subhanallah ya Allah kaba ma mijina lafiya. Baki na rawa tace "dr pls kabarni inga mijina, pls" dr yace "muje" da kyar ta mike tabi bayansa suka shiga dakin daddy dr yabasu waje, jiki na kyarma takarasa gun daddy ta dauko hannunsa dake hade da drip ta rike bibbiyu da nata a hankali hawayenta ke sauqa kan hannun daddy se suratai take zubawa tana kuka tagama tayi addu'a ta kwantar da kanta gefen daddy ahaka har bacci me nauyi ya dauketa***
     Da maghrib ta farka tayi sallah tasa mal idi kwaso mata essential things da zatayi needing dan kwana a asibiti yazama dole cuz har ynxu daddy beyi gaining conciousness ba. Allah ya so time da mal idi yaje kwaso kayan heedayah na bacci da har nanny zata ta da ita sallah sekuma tace bari ta idar sannan ta tayarda ita yadda Allah yaso su knan, har aka gama diban kayan heedayah batasani ba. Mal idi na tafiya nanny ta kira mumy ta gaisheta da jiki take tambayarta ko ta dafo mata abinci ne? Mummy tace "a'a kibary kar heedayah tayi noticing wani abu zan sa idi ya siyi min" nanny tace "toh shiknan tunda haka kkace, ya jikin daddy'n heedayah?" Mummy tace toh da sauki amman kam har ynxu beyi gaining conciousness ba nanny, i dont know what to do" nanny tata bata hakuri amman wannan abu da abin dubawa aciki, mummy tace "kibary kawai sena dawo se anjima" ta katse wayar. Nanny ta manta da zancen ta da heedayah yin sallah ma gabadai. Se around 10:00pm heedayah ta tashi tayi brushing tayi alwala without anyone telling her to, tayi sallolinta tayi ma daddy addu'a sosai sannan ta zauna tana nazarin abinda tajiyo dazu kwata kwata ta kasa gane waye ke maganar ko alhj lawal ne ko alhj ismail amman dey jikinta yafi bata alhj ismail ahaka tabar tunanin ta sauko kasa tasami nanny a parlour ta karasa gunta tace "nanny ina mummy da daddy?" Kafin ta jira me nanny zatace ta dau hanyar dakin daddy tana kwala masu kira shida mummy

No comments: