Sunday, 23 October 2016
HEEDAYAH!
1⃣8⃣
written by miemiebee👄
Tagama yawonta bata ga masu kamannin daddy da mummy ba, ta sulale a kasan dakin tafara raira kukarta me tsuma zuciya, nanny ta taso ta daga ta, tana lalashinta heedayah taqi yin shiru kuka takeyi sosai har bacci yayi awon gaba da ita tana jan numfashy a hankali nanny ta kaita daki ta rufeta da bargo sannan tarufo mata kofar.
Washegary, around 7:00AM daddy yadan motsa yatsar sa daidai lokacin idan mummy yakai gun da saurin gaske taje ta kira dr suka shigo tare yadan dudduba daddy yace "ma'am mugodewa Allah ur husband has gained conciousness" mummy tana murmushi tace "alhamdulillah" dr ya fice. Mummy ta karso kusa da daddy ta riko hannunsa da hawaye sharkaf a fuskarta tace "welcome back habibi" ta masa murmushi, daddy ya gwada magana amman ina yakasa, anytime yace zeyi mgn its becoming hard, atake mummy tafara sabon hawaye tana sharewa suna zubowa, haka daddy ma hawaye yake da kyar ya mata murmushi, mummy tasa hannu ta goge masa yar hawayensa tareda gaya masa "everything is gonna be fine in shaa Allah, try not to talk" tabasa peck a goshi. Tashi tayi ta dauko wayarta dan kiran nanny bugun farko nanny ta daga suka gaisa mummy tace "princess dina fa, tatafi sch?" Nanny tace "da kyar" mummy tace "Allah sarki my poor heedayah, ki hado mana breakfast ga daddy nan ya farfado" nanny tace "toh toh alhamdulillah kiban hour daya" mummy tayi hanging. Kiran dr dinsu tayi na washington DC sanda tayi 2 missed calls sannan ya daga a na uku ta gaishesa yake bata hkr akan delayance din maganin bada ga wurinsa bane mummy tace "ba komai gbe ne ai" yace "ya jikin me gidan?" Nan mummy tabasa labarin komi ya mugun tausaya wa daddy da mummy matuka ya ce ta kwantar da hankalinta ze hado mata wasu maganin in shaa Allah mijinta will get better duda it will take long process ne, yagayamata tips dayawa mummy tayi godiya in return ahaka sukayi sallama (duk wannan zance da turanci sukeyi.)
A sch heedayah kuwa ba wanda take masa magana kullum tana cikin tunani abin ba karamin tama antinsu hankali yake ba ace yar yarinya kamar heedayah amman ta zauna se aukin tunani gashy anytime ta tambayeta meke damunta setace mata rashin lafyan daddynta ne kawai amman aunty kam tasan for sure there must be something, har don moha sanda anty ta tambaya amman shima yace mata besani ba cuz heedayah is avoiding him bata masa magna ynxu yayi yayi da ita amman ina taki so ze bata space, daga karshe anty tayanke hukuncin kiran mummy. Bayan an tashy frm sch mal idi ya zo daukan heedayah acikin mota tace masa ita karya kaita gda gun parents nata takeson zuwa tata masa bori sanda ya yarda daga karshe suka zarce asibiti mummy tayi mamakin zuwan heedayah da unifirm wato ko gda ma bataje ba balle taci abinci nan danan ta kira nanny, nanny tace ita batasan da zuwansu bama akadawo kan mal idi aka suburbudesa sosai. Heedayah ta fashe da kuka "mummy wato ure not happy to see me? Haka jiya kka min karya kkace zaku dawo gda da daddy nata jiranku bakuzo ba, ba damuwa mal idi take me home" tatashy mummy ta riko hannunta "not at all my dear, kema kinsan kanki mummy will not lie to u like that, inason in gaya miki wani abu nd inason kibany mind naki kijini da kyau. U see, daddy is in a critical condition, Heedayah! Daddy baya magana ynxu yayi paralysing" ta fashe da kuka, heedayah tace "mummy? Me paralysing? Kibar kuka pls mummy nima zanyi fa" Mummy ta share hawayenta "daddy baya iya magana, ko tafiya heedayah" hannu heedayah tasa a kunnenta "nooo mummy wasa kke min, my daddy can talk nd walk noooo" tabar gun a guje ko ya akayi bata manta dakin daddy ba oho dan heedayah batada mantuwa dakinsa ta wuce straight kafin su mummy suce pim. Tana shiga ta hango daddy'nta a kwance kan gado da hawaye na bin fuskarsa tasa lock a kofar takarasa kansa da gudu tafadi a kanshi "daddy nooo pls daddy u promise to always stand by my side, kace u'll never leave me, remember? I want my daddy, plss dady" kuka takeyi sosai daddy naganinta amman ba abinda ze iyayi se hawaye sanda tayi kuka sosai sannan ta dago jajayen idanunta ta share hawayenta, ta share na daddy tace "daddy listen to me I promise sena rama maka abinda baban muhammad yamaka, zanje in tambayi antinmu me mutum yake karantawa ya iya kama criminals nd I promise sena kamasu na kaisu prison har su mutu a can" (ji yadda heedayah ke magana kamar ba yarinya ba). Su mummy suna isowa dakin taga a rufe mal idi yafara kokarin budewa tace "let her be" suka nemi gu suka zauna se kuka takeyi a hankali.
Alhj lawal na zaune a parloun gdnsa da files na gdaje, filaye, companies, na alhj s.u agabansa ya sakar dawata dariyan mugunta sannan yadau wayarsa ya kira alhj ismail bugun farko ya daga ya gaishesa alhj lawal yace "bar duk abinda kakeyi kazo I need u now!" Baki na rawa alhj ismail yace "yes alhj gani nan zuwa yi hakuri pls." Kamar kyaftawan ido sega alhj ismail a gdan alhj lawal ya durqushe ya gaishesa alhj lawal yace "hau kujera ka zauna magana zamui nd inason kbani hnkalinka dan abu zansa kamin nd banason failure"
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment