Sunday, 23 October 2016

HEEDAYAH!


                1⃣9⃣
   written by miemie👄
 
       "Ko kana da labarin alhj s.u na asibiti?" Alhj ismail ya gyada kai, alhj lawal ya cigaba "toh kasani bara muje dubansa ba, daga mu har iyalan mu bawanda zeje dubansa, kaji ai?" Alhj ismail zeyi mgn knan alhj lawal yace "ko bakaji bane" alhj ismail yace naji, alhj lawal yayi yar murmushi sannan yace "zan baka files na gdan alhj s.u dayake ciki ynxu kaje ka siyar" Alhj ismail ya zaro ido sannan yace "kar mu masa haka pls mun kwato campany nasa da sauran filaye ai ya ishemu ba se mun sai masa da gdan dayake ciki ba, for goodnake sake su koma ina?" Alhj lawal ya buga table "ni nake ma magna kana kin ji?" A zuciya yace "lallai se malam ya dado min wanga magani" jiki na rawa alhj ismail yace "yi hakuri i'll do as you say" alhj lawal ya miko masa file din gdan yace "goodluck, you can go now" alhj ismail na ficewa alhj lawal ya zarce side na matarsa ya sameta kwance kan gado tana kallo suka gaisa yake ce mata ta shirya zasu je duban alhj s.u bai da lafya, tace "ayya ai banda labari barin kira mumyn heedayah" ya ce "toh kiyi sauri" yana fita takira mumy'n heedayah suka gaisa ta tambayeta ya jikin daddy? Mummy tace "da sauki" umman mustapha (matar alhj lawal) taba mummy hakuri kan rashin zuwan da tayi cuz bata san daddy baida lfya bane ynxu zata kira maman muhammad (matar alhj ismail) ta sanarda ita halan su shigo tare ma ahaka ta katse wayar. Ta kira maman don moha suka gaisa take fada mata, maman don moha ta tausaya wa mummy matuka tace itama zata shigo anjima sukayi sallama, alhj ismail mijinta taje tasamu yana zaune a garden take gaya masa kan zata fita anjima zataje gaishe da daddy'n heedayah da jiki ko zamuje tare ne?, alhj ismail yace "ba inda zakije" tamasa rokon duniya ya hanata haka takoma ciki amman de tasa a bayan mind nata se taje koda bada izininsa ba, ace duk yadda suke da mummy'n heedayah mijinta ba lafya yace barataje dubanta ba ai ba ta kyauta ba.
       Alhj lawal, dansa mustapha da matarsa na hango a asibitin da akayi admitting daddy da manya manyan ledoji guda 2 a hannun matarsa, yasa ta kira mummy, mummy ta musu kwatancan dakin suka kariso suka gaggaisa kowa yaga daddy seya tausaya masa harta alhj lawal dinma beji dadin ganin amininsa a condition haka ba amman ya ya iya da son zuciya, umman mustpha ta tambaya "ina heedayah ne banganta ba?" Mummy tace "ai bata jima da barin nan ba" umman mautapha tace "ayya ashafa min kanta" bayan like 15mins da zuwansu alhj lawal yace "zasu tafi" a daidai lokacin daddy ya tashy daga yar baccin da yakeyi yana ganin alhj lawal jikinsa ya soma rawa mummy suka rasa meke faruwa, shide alhj lawal yaja baki yayi kum dake yasan dalilin hakan, mummy duk ta kidime tarasa nayi can tace bari taje ta kira dr, alhj lawal yace "kar ta damu magana alhj ismail keson masa sesa jikinsa ke rawa" ya karasa gun alhj ismail da har ynxu jikinsa rawa yakeyi yace "dan uwa try not to talk nagane me kake nufi, Ina company dinka dake abuja neko? Nxt week zan shiga abuja in shaa allah in kula maka dashy kaide Allah baka lafya kawai, sannu" yadawo da kallonsa kan matarsa yace "mutafi ko?" suka aje wa mummy ledojin tayi godia sosai ta musu rakiya sannan ta dawo ciki. Data dawo ta karisa gun daddy tana nuna masa ledojin da alhj lawal yakawo se yaba hankalinsa take, shiko se kokarin magana yakeyi yace mata "karta amsa, alhj lawal munafiki ne" amman ya kasa, mummy kuwa tace "try not talk yace zeje maka company din ya duba ai nasan alhj lawal da kirki he won't let you down" Haka har dare yyi maman don moha batasamu daman zuwa ba dake alhj ismail a gda ya wuni ranan, can dare ta kira mummy ta gaishe ta sannan tabata hakuri kan bata samu daman fita yau ba amman in shaa Allah gbe zata zo, mummy tace "ba komai, Allah kaimu" maman don moha tace "ya jikin maigidan?" Mummy tace "toh da sauki nakega gobe ma za'a sallamemu cuz gbe maganinsa zasu iso" maman don moha tace "ahh alhamdulillah in shaa Allah zan shigo kamin ayi discharging naku din, Allah bashi lafya" mummy ta amsa da "ameen nagode se da safe" tayi hanging.
      Heedayah na zaune akan study table  nata da assignmnts nata a gabanta amman ko kadan hankalinta bai gun har nanny tashigo dakin bata sani ba, "heedayah!" Nanny takira sannan ta dawo hankalinta, nanny ta kariso kusa da ita tace "heedayah ki rage tunanin daddy'nki in shaa Allah ze samu lafya ba kina mishi addu'a ba?" Heedayah ta gyada kai can setace "nanny can I trust you?" Nanny tace "sure my heedayah wani abu ne?" Heedayah tace "nanny daddy'n don moha ne yasa daddy ya dena magana da motsi" nanny ta zaro ido waje "heedayah! Ya kke magana haka? Daddy'nki ba frnd na daddy'n don moha bane, mesa ze masa mugunta?" Heedayah tace "nanny believe me" tayi tayi da nanny ta saurareta amman ina nanny taki sauraronta dan ita kwata kwata maganan bekama kwakwalwarta ba ace yadda alhj ismail ke son daddy ne za'a ce ze masa haka? Gaskia karya ne. Ahaka ta taya hedayah tagama assignments nata tayi sallah sannan ta kwantar da ita.

No comments: