TANA TARE DA NI... PAGE 34
BY MIEMIEBEE
“Abuu dan Allah kayi hak’uri kaja baya da zancen nan, Abuu I’m not ready please”
“Ready? Wani irin ready ne bakayi ba Anas? Ko so kake kacemin duk cikin ‘yan matan ka ba wacce ta maka.” Take wajen Anas ya shak’e ya soma tari sanda Shettima ya taho masa da ruwa. “Eh Anas? Duk cikinsu ba wacce ta maka?”
“Abuu nifa I’m not seeing any girl, bani da wata budurwa kaga ko ba yadda za’ayi ace zanyi aure.”
“Akoi sosai Anas, dan ni na riga na maka mata wacce takeda degree a business admin wacce zata taimaka maka sosai wajen kula da Enterprise naka.”
Ido wuru-wuru Anas ya zaro. “Abuu mata? Mata mawa? Ummie dan Allah kisa baki ki hana sa, ni wallahi banasan yin aure I’m still young.”
Tausayin Anas ne ya kama Ummie “Ya Ibrahim kad’an sassauta masa dan Allah, yaro neshi har yanzu.”
“Nafeesa zamu b’ata dake fa yau, tashi ki koma d’akinki banasan zaman ki anan.”
“Kayi hak’uri Ya Ibrahim amman kar muyi rushing abun nan, ayi komi a hankali dan Allah, wace wannan matar da kace kayi masa?”
“Falmata ce, ‘yar Inna Suwaiba na yaba da tarbiyyar yarinyan kuma ina kyautata zaton barata k’i wannan had’in ba.”
“Falmata Abuu?” Anas ya zaro blue eyes nasa da suka kad’a. Kwata kwata ya manta da akoi wata Falmata a duniya, shi rabuwansa da ya sata a ido tun barin su Bama, shi me zeyi da Falmata? ta rik’e kwalin degreen ta baya buk’ata, shi ko kad’an ma yarinyar bata burgesa.
“Eh ita Anas, tana da tarbiyya.”
“A’a Abuu dan Allah karka min haka” take idanunsa suka soma tsiyayar da hawaye. “Wallahi banasan ta, ko kad’an bana santa dan Allah kayi hak’uri Abuu.”
“Anas yanzu kuka kake saboda nace zan had’a ka da ‘yar uwata? ‘yar uwarka?”
“Ni Abuu badan haka bane, ni koma da waye zaka had’ani banaso. Abuu koda zanyi aure ba a yanzu ba, ina ma ace nakai irin 28-30 d’innan, please Abuu.” se hawaye yake kan d’an yaro.
“Lallai fa Anas! Yanzu har so kake ka kai shekaru 30 a duniya bakai aure ba? Kasani kai daban kake da sauran sa’o’in ka you are a billonaire Anas not just any man, kasancewar ka billonaire yazamo dole rayuwarka ya bambanta da nasu. Anas zaka auri Falmata, ni na fad’a maka.”
Kuka sosai Anas yake daidai lokacin Amal tafito daga d’akinsa ko me takeyi tun d’azu se Allah, ganin yayanta na kuka ta nufa kansa da gudu “Ya Anas mesa kake kuka? Abuu meh kama Ya Anas d’ina yake kuka?” Hannu tasa ta share masa hawayen ko k’ala bece mata ba dan bak’in ciki da haushi da takaici.
“Ba abinda na masa Amal, shitirita ne kawai ke damunsa, dan nace yayi aure, ya auri Aunty Falmata shine yake wannan kuka.”
“Toh Abuu in bayaso abarshi mana.”
“Bara’a barshi ba Amal tashi ki wuce d’akin ki.” Zata sake magana ya bud’e mata ido “now!” Itama hawayen ta soma ta tashi a guje Ummie tabi bayanta tana kiranta ko k’ala Anas bece ba dukda yadda yakeson Amal.
“Zuwa next week su Falmata zasu shigo gari seku had’u ku sasanta a tsakaninku”
“Abuu please karka min haka karka aura min Falmata dan Allah.” Sosai Shettima ya tausaya wa wansa danko yasan yadda Anas ya tsani zancen aure. “Na yarda zanyi auren amman karka sa in auri Falmata.”
“Dalili Anas, kaifa anan kace bakada koda budurwa bale ace tsayayyiya.”
“Eh Abuu bani dashi amman kabani lokaci zan nemo in kawo ta gida muyi auren amman dan Allah karka sa in auri Falmata, dan Allah...” ya fad’i abin tausayi yana share hawayensa sekace ba Mr. Fauzin da muka sani ba.
“Har zuwa yaushe kuma zaka samu sabuwar budurwa har ku daidaita ka aureta?”
“Abuu just 2 years zaka bani-”
Katsesa Abuu yayi “2 years? Anas kanada hankali kuwa? Kai wai mesa baka tunanin lafiyar company’n ka ne?”
“Abuu toh shekara d’aya da rabi kasan halin mata yanzu abin duniya kawai suka sa a gaba, ya kamata in samu wacce zata soni tsakani da Allah badan kud’i na ba.”
“Shine har se nan da shekara biyu? Zan baka nan da wata shida.”
“Abuu wata shida? Wata shida yayi kad’an dan Allah kayi hak’uri ka k’ara min.”
“Anas in baraka d’au wata shidan dana baka ba seka auri Falmata dan ban tsammanin yarinyar da zaka kawo min zata kai Falmata tarbiyya da ilimin addini dana boko duka.”
“A’a Abuu na yarda da wata shidan.”
“Good na baka nan da wata shidan amman kasani barin k’ara maka koda second kai ba, in har baka kawo wacce ta maka in 6 months time ba zan aura maka Falmata na dole.”
Hawaye sosai Anas yake shi da ko tunanin aure baya yi yau shine aka basa wata shida yaje ya nemi macen da ze aura? A sanyaye ya mik’e daidai lokacin Amal da Ummie suka fito daga d’akin Amal da alama lalashinta Ummie tayi.
“Anas ina zakaje?” Ummie ta tambaya ganin yana nufan bakin k’ofa ga kuma yadda yake zubda hawaye. “Anas ka tsaya mana kaji Baba na.”
“Ya Anas ina zakaje?” Amal ta tambaya cike da damuwa. Be tankasu ba yafice tare da jan motarsa yabar gidan a 360. “Ummie ina Ya Anas zeje? Ummie kice ya dawo.”
“Ya Ibrahim yanzu me amfanin wannan abu? Kaga yadda kasa Anas kuka gaban k’annensa bayan haka ma Allah kad’ai yasan ina zeje yanzu kaga yadda yaja mota a fusace ya fita.”
“Duk inda yaje ze dawo, wannan shine son da zan iya nuna wa Anas” yana kaiwa nan ya tashi ya nufa d’akinsa. “Ummie mesa Abuu yake ma Ya Anas haka?” Amal ta tambayi Ummie kan wanda zatayi kuka.
Dafe kafad’arta tayi “nima bansani ba Amal karki damu ze dawo in shaa Allah”
****
Tuk’in ganganci Anas yake a fusace shi inda hatsari zeyi ya mutu ma da yafiye masa Allah ne kawai ya isar da shi paint house nasa chan ya fito daga motar tare da buga murfin sannan yashiga ciki, direct fridge nasa ya nufa tare da ciro mafi tsada cikin kwalaben, tunda ya kafa a bakinsa be cire ba sanda ya kurb’e fiye da rabi yamutsa fuska yayi sosai, tunaninsa se juyi suke.
Mesa Abuu zesa sa yin aure a d’an wannan shekaru dayake dashi daidai yana cikin cin duniyarsa da tsinke yana enjoying bachelor life nasa za’a masa ruining. Shi yanzu ina zesa kansa? Ina ze nemo macen da ze aura? Koda ya samun ma shi baya san auren, me zeyi da mace a rayuwarsa? Duk mata d’aya ne sak abinda Ummimi tama Abuu haka shima duk macen daya aura haka zata masa, ta gudu ta barshi da yaransa. Abinda baya so kenan bayasan yaransa suyi witnessing a day without a mother. Kwalban ya sake kafawa a bakinsa wannan karan sanda ya kurb’e tas sannan yacire tareda wurgi dashi kad’an ya rage be fashe ba.
Wayarsa dake aljihunsa ne ya soma ruri ko duba wake kira beyi ba ya kashe duka wayoyin take a wajen wani irin bugeggen bacci ya rufesa. Bashi ya tashi ba se chan k’arfe 11:50 na dare, da k’yar ya lallab’a bayi ya rage kayan jikinsa tare da sake shower a kansa, gashin kan sa me uban yawa ya kwanta jikin fuskarsa luf kota ina, ruwa na tsiyaya. Tunani yakeson yi amman ya kasa, yarasa me ke masa dad’i.
Bayan ya fito yad’anyi frying omalet yaci sannan yabiya sallolin da ake binsa. D’akinsa ya nufa ya mik’e kan gado baccin da yake son yin ma yakasa, tunanin da yake son yi ma ya kasa haka yadda yaga rana yaga dare ranan tsoron sake shanye wani kwalban yake gudun kar alcoholic level na jikinsa ya hau eventually Abuu ya gane yana shaye shaye. Haka ya hak’ura ya kwana ido biyu.
Asuban fari ya tashi ya idar sannan ya kunna wayoyinsa messages ba iyaka yaga daga Ummi, Shettima dakuma Amal se saura daga wajen aiki. Amal ya soma kira alokacin ma bacci take tak’i tashi tayi sallan Asubah ita atapir se Ya Anas nata ya dawo. Shi kansa Abuu yashiga damuwa danko yayi ta trying wayar Anas a kashe yakeji, haka de duk suka kwana cikin damuwa ranan. Rurin wayarta ne yasa ta tashin dole ganin Ya Anas ke kira ta daka tsalle “Ummie! Ummie!”
“Na’am Amal se yanzu kika ga daman tashi?” Ummie dake bayi ta bata amsa.
“Ya Anas yana kirana!” ai kamar kyaftawan ido Ummie tafito daga bayin “kawo nan.” Nan take d’aga “hello Babana dan Allah ina kashiga? Kadawo gida please.”
“Ummie ina kwana?” Ya gaishe ta a nitse.
“Nifa ba lafiya ba seka dawo gida hankali na ze kwanta.”
“Calm down Ummie sekace yau ne karo na farko dana soma kwana a waje? Karki damu zan dawo gida amman ba yau ba.” Zata sake magana ya katse ta “ina Angel?”
“Amman Ana-” katse ta ya kuma yi a nitse “kibata wayar please Ummie karki damu I’m fine” tana mik’a wa Amal wayar ta amshe da zumud’i “Ya Anas good morning.”
“Morning my Angel ya kike?”
“Ya Anas I’m not fine dan Allah ka dawo gida.”
“Zan dawo very soon don’t worry okay?”
“Okay” tace a hankali “toh bye take care” nan ya katse ya kira Shettima. Ba yadda beyi dashi ba ya fad’a masa ina yake Anas yak’i.
K’arfe 7:56AM ya shigo building nasa da bak’ar suit, bak’ar shirt dakuma bak’ar neck tie alaman za’a suburbud’a tsiya da rashin mutunci kenan yau. Duk ma’aikatan nasa sunyi noting wannan shiga dan haka suka maida hankalinsu gaisuwa suke binsa dashi duk corner’n daya shiga.
D’aya daga cikin staffs nasa ne yasha gabansa tare da gaishesa cike da girmamawa “good morning Boss, wannan files zakayi signing please zanyi sumbitting nasu ne, yanzu Manager’n ze tafi Ukraine, I’m sorry ban samu nakai maka jiya ba.”
Kallo me rai da lafiya Anas ya watsa masa wanda yasa sa had’iye miyau dakansa yaja da baya “I’m sorry Boss.”
“You are fired kaje kasamu Adam.” Anas yace dashi cike da nuna rashin damuwa.
“Boss I'm so sorry dan Allah kayi hak’uri...” ko sauraronsa Anas beyi ba ya nufa personal elevator’n sa. Kowa wajen sanda ya tausaya wa Abdallah da akayi firing.
Fannah kuwa se 8:05AM ta shigo building d’in kafin ta isa office na Anas kuwa har 8:10AM yayi knocking tayi a hankali tana sanye da abaya ne yau wanda ya mugun mata kyau. “Enter” yace almost kamar yana masifa. Tun daga nan zuciyarta ya hau bugu ita meya kawo ta office nasa ma bayan ya mata nata office d’in? Wata zuciyar tace mata saboda ki had’a masa coffee kinsan sarai inhar kika bari shi ya nemeki toh da akoi k’ara’i kuma bayan wannan ma jiya ba yace first thing tomorrow morning ze miki aike ba? Kishiga. Zuciyar nata tabi a hankali kanta sunkuye a k’asa ta bud’e k’ofar. Tunda ta shiga Anas yake kallonta yau shine karo na uku dayake ganin ta ba hijabi da ranan da taje paint house nasa, da shekaran jiya dayaje gidansu seda yau da take sake da abaya. Sosai abayan ya mata kyau irin me A shape d’innan ne tayi nad’in tarha da maroon colour be bar kallaonta ba har se lokacin da ta k’ariso gaban table nasa tare da gaishesa still kanta na k’asa ko sanin kalan kayan dake jikinsa batai ba gudun kar ta kallesa yace tafiye kallo amman de tana jin blue eyes nasa a kanta “Good morning Mr. Fauzi” ta gaishe dashi “jiya kace zaka min aika first thing in the morning” ta tunatar dashi ko incase ya manta se b’ari takeyi dan yadda takejin idanunsa a kanta.
“Ina sane ai, nafasa aiken just make me coffee before then ki mik’o min bottle d’aya acikin fridge. Kuma sau nawa zan fad’a miki kidena zuwa min office late? Mschww” Dudum! Taji zuciyarta ta buga bade shaye shaye yakeson yi ba, be kamata ta zuba masa ido tana ganinsa yana shaye shaye ba dukda kuwa bata da right na hanasa amman be kamata ba meyake nema a duniya ya rasa da ze na shaye shaye? Tatso ta yayi daga duniyar tunanin data fad’a ta hanyar daka mata tsawa “ba kaiji me nace bane?! Ko senayi firing naki?” Take ta d’ago idanunta ta kafasu kan Anas. Kallo d’aya ta masa ta gano yana cikin wani yanayi na damuwa yau, gashi nan karara rubuce a fuskarsa hala shiyasa yake san yayi shaye shaye dan kwantar da hankalinsa kamar yadda masu shaye shaye suke fad’i giya na gusar da problem.
“Mr. Fauzi ba seka sha wancan abin bane problems naka zasu tafi I’ll make you coffee kana istighifari trust me duk damuwar ka zakaji suna gushewa cikin ikon Allah.”
Kallon ta yatsayi yi. “Waya fad’a miki kinada right da zaki gayamin abinda zanyi? You are my PA abinda nace inaso shi zakimin saboda haka pass me the damn bottle!” ya sake daka mata tsawa b’ari sosai Fannah take amman ta rantse da Allanta barata basa ba, not anymore duk da yadda take tsoronsa tace yau sede yamata abinda zeyi amman barata bari yayi shaye shayen nan ba sede in a bayan idonta.
Wajen fridge d’in ta nufa ta bud’o murfin tare da irga kwalaben ko nawa ne, guda uku ta irga duk ya shanye sauran. Ukun duka ta ciro ta sake su k’asa “tas! Tas! Tatatas!” Duk suka fashe a k’asa ita kanta b’ari takeyi. Kallonta Anas yake cike da mamaki.
“Ke!!!” Ya fad’i cike da tsiwa. “What did you just do? Magana nake miki? Kinasan ki mutu ne?” Mik’ewa yayi daga kan kujerar sa a fusace yasoma nufan inda take tsaye da nufin kai mata bugi se kakkarwa take.
“Mr. Fauzi please calm down kayi hak’uri I’ll make you coffee dayawa cikin flasks biyar in kanaso, kayi hak’uri dan Allah kar ka tab’ani. Shaye shaye ba abin yi bane me ka nema ka rasa a duniya da za kana shaye shaye please stop it kodan darajan manzo SAW” ta fad’i murya na b’ari jiki na rawa duk tsoro yabi ya ratsa ta. Sauran befi inchi uku tsakaninsu ba chak Anas ya tsaya.
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment