Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 35
BY MIEMIEBEE


       A da yayi niyan kai mata bugi, a da yayi niyan ya illata ta a wajen danko bottles uku da ta fasa masa babban asara ne da bayasan ya tuna. Besan me ba kalamun ta duk yabi ya kamasa, alokacin yaji ya tsani giyan nasa coffeen tan yakeson sha. Kallonta yake se nishi take cike da tsoro da fargaba ko d’aga ido ta kallesa ma takasa. Shikuwa a hankali nishin zakin da yakeyi ya soma dawowa daidai dana mutane. Baya ya koma ya zauna kan d’aya daga cikin cushions na office nasan.
   
   Wani irin mumfashin godiya ga mahalicci Fannah ta saki. Idanunta ta d’ago tana kallon Anas daya d’aga kai sama tare da aza hannunsa a kai yana cize baki a zaune kan kujera. Da sauri ta juya ta soma neman cups dan had’a masa coffeen sede inda ta saba d’aukan cups d’in ta duba bata ga ko alamun su ba. Tashin hankali! nema sosai take cikin wajen babu. Alokacin da Anas ya sauk’o da kansa yana kallonta kuwa yaja wata doguwar tsuka. Bakinta rawa yake tace, “Sir please calm down cups d’inne ban gani ba.” Se yanzu ya tuna ashe jiya yasa an fita dasu duka aka kawo sabi wanda suke cikin wani kwali daga gefen table nasa. “IQ naki baya functioning ne? Kin duba nan baki gani ba, ba seki duba cikin office d’in duka ba. Mschww!” Mik’ewa tayi ta soma bin office d’in da kallo tana neman teacup duk tsoro ya rufeta, har ta wuce kwalin cups d’in batayi noticing ba.

    “Makauniyar ina ce ke? Bakida ido ne? Wancan meneh? Ki dena sani surutu do you get me?”
    Nan ne ta hango kwalin kasamcewar idanun Anas dataga akai da sauri sauri ta tsuguna ta bud’e tare da ciro cup d’aya da spoon sannan ta nufa wajen coffee machine d’in cikin mintuna k’alila ta gama had’awa amman Anas da rashin hak’uri yakasa hak’ura har takawo masa. Ta juya kenan zata kawo masa ya daka mata tsawa “wai har yanzu me ki-” be k’are maganar ba dan yadda ta tsorata copin ya sub’uce daga hannunta tatas! Kukeji a k’asa sabon copin ya faffashe, coffeen kuwa saura ya zube jikin ta saura a k’asa kuka ta soma take bata san sanda ta tsuguna ta soma tattarawa ba hak’urin ma takasa basa.

    Kafin Anas yayi kyakkyawar motsi inaaa aikin gama ya riga ya gama kiat! Glass d’in ya yanke ta a kumburarren hannunta data sha rubutu dashi jiya. K’ara sosai ta saki a yayinda kukanta ya tsananta. Take ya mik’e tare da mik’ar da ita da hannunta daga sama da zafin bala’i.
    “Kin huta ai yanzu da kika kuma yanka kanki, why are yo so clumsy? Yanzu me kikeson nasha? Kin min asaran beer (giya) na, kin had’a min coffee amman kin zubar, yanzu kuma kin yanka hannunki. Wace erin mutum ce ke? Ahaka ne Abuu yakeson yamin aure? Me zanyi da mace a rayuwa na mschww.” Hannunta yayi yunk’urin ja gam! ta rik’e kanta, kallo ya watsa mata “lets go” ya sanar da ita a tsawace.
 
   Tana hawaye tace, “no zan kula da kaina, let me go.” Tsuka yaja ba tare da ya saurareta ba yajata bayi dan se d’igan jini hannun nata yake famfo ya bud’e tare da forcing hannun ta k’ark’ashi ruwan na tab’awa ta sake sakin k’ara zafi kan zafi bayan daya wanke ciwon da ruwa ya zaunar da ita kan toilet sit tare da ciro first aid box daga cikin wata cupboard. Ganin haka Fannah ta sake rikicewa batasan spirit a ciwo Allah kad’ai yasan zafin da tasha last time daya sa mata.

      “Sir please kar ka samin spirit jinin ze tsaya da kansa please.” Ko sauraronta beyi ba ya d’iga spirit d’in kan audugar. Ya juya yana rufe kwalban kenan Fannah ta mik’e a hankali dan guduwa takai da bakin k’ofa kawai Anas ya cafko ta da hannu batasan tun d’azu ya ganta ba yana kuma sane da abinda takeyi. “Sir dan Allah kayi hakuri karka sam-” bata k’are maganar ba ya manna audugar kan yankar nata. “Wayyyyooooo Alllaaaahhhhh Mamii naaaa?!!? ya kasheni.” Zogi sosai hannun nata yake mata har wani kamar ba’a jikinta takeji ba. Kuka take sosai se daya tabbata ya kashe germs na ciwon ya cire tare da manna mata plaster. Be sake hannun nata ba yajata zuwa d’akinsa daidai kan gado yayi wurgi da ita b’ari sosai Fannah ta soma a yayinda kukanta ya tsananta. Meh Mr. Fauzi yake shirin mata? Innalillahi bade aika aikan da aka tab’a mata da a Bama ba za’a sake mata. “Ya Allah gani gareka, karka bar Mr. Fauzi yaci nasara a kaina kar k-” bata k’are maganar zucin da takeyi ba taji an wulla mata leather a fuska tana dubawa taga sabon abaya ne pil cikin ledan.
 
     “Ki canza cikin wannan” ya fad’i a yayinda yabar d’akin tare da bankad’o k’ofar. “Huhhhh!” Ta saki numfashi tana goge hawayenta. “Yakamata in dena wannan sak’e sak’en Mr. Fauzi ba kalan mazan da suke bibiyar mata bane, dukda bangane meyake nufi ba d’azu naji yace ahaka ne Abuu ne ko waye yakeson masa aure. Me zeyi da mace a rayuwarsa, amman mesa yace haka? Nide tunda nake ban tab’a jin na miji yace me zeyi da mace ba se Mr. Fauzi to mesa? Mesa akeson sasa aure?” Ganin batada amsa ga wad’annan tambayoyi kawai ta mik’e tare da locking k’ofar gudun kar Mr. Fauzi ya fad’o cikin d’akin yaganta ba kaya dukda kuwa tasan bareyi ma hakan ba dan a yadda ta karance sa baida interest a mata kawai yana amfani dasu ne yana breaking musu hearts wanda batasan dalilin hakan ba.

    Kayan jikinta tasoma ragewa a hankali. Anas kuwa tsuka yaja dayaji tayi locking k’ofar inde kallon mata half naked ne to ya riga yayi ba sau d’aya ba, ba sau biyu ba dayake London saboda haka ba abinda ze gani jikin Fannah (a tunaninsa.)
   Daidai kayan ya mata wanda hakan yabata mamaki sosai chan kuma ta tuna yadda yake da ‘yan mata kam ba abin mamaki bane, yanzu haka kayan daya siya zekai wa budurwasa ne ya bata tasa. Gaban madubi ta nufa ta sake rolling gyalenta daidai sannan tafito bayan ta ninke kayan data ciren. Koda tafito Anas be d’ago kai ya kalleta ba, rasa nayi tayi ta je ta kira cleaners ne kokuwa ta d’au tsintsiyar da take gani acan ta share b’arnan data masa ne?

     Daidai ta d’aga k’afa zata nufa wajen tsintsiya da parker’n kenan ya kira sunanta da “Miss Aleeyu.” Cak ta tsaya, tare da kewayo da kallonta garesa taga ko kallonta baiyi. “Get out of my office” yace.
   “Sir inason in sh-”
   “I said get out!” Ya fad’i a tsawace batasan sanda ta soma hawaye ba. A sanyaye ta nufa wajen da ta ajiye jakarta dan sa kayanta ciki ta fice kamar yadda ya buk’ace ta. Bata gama sanya kayan ciki ba ya fisge hannunta tare da fitar da ita daga office d’in yayi banging k’ofar. Har k’asa ta sauk’a tana kuka takasa sabo da masifan sa da k’yar ta tashi ta nufi office nata inda taje ta k’are kukanta.

     Ta kasa gane wani irin mutum ne Anas, daga abu ya tab’a lafiyarta ze nuna damuwa ya taimaka mata har ya bata sabon kaya amman kuma take wajen seya sake bunka mata rashin mutunci. Daidai nan knock yazo daga office nata “come in” tace tana share hawayenta. Yusuf ne ya bayyana, murmushi ta k’irk’iro masa “Yusuf” ta kira sunansa “bismillah come in.”
    Murmushin ya mayar mata tare da rufo k’ofar sannan yanemi waje ya zauna. “Wato Fannah kinyi office amma sede muji a bakin mutane koh?”
       “A’a wallahi Yusuf jiya ne Mr. Fauzi ya bani da aka tashi kuma na nemeka  dan sanar dakai ban ganka ba.”
   “Ayyah” yace yana admiring office natan. “Gaskia yayi kyau sosai congratulations.”
   “Thank you” tace masa.
   Fuskarta ya karanta seya gano kamar tayi kuka. “Fannah kuka kikayi ne?” Ya tambayeta cike da damuwa.

     “A’a” ta masa k'arya.
      “Eh Fannah keda waye ne? Mr. Fauzi ne?”
    Giving up k’aryan tayi ta fad’a masa gaskia. “Eh” tace tare da jan hanci.      
           “Fannah yaci ace kin dena kuka akan Boss, haka yake in ya bak’anta wa mutum rai ne yakejin dad’i. Kuma kisani duk rananda yayi shiri in black to ki kiyaye duk wani abinda ze had’aki dashi saboda ransa a b’ace yake a ranan.” Kai ta giad’a a hankali “thank you Yusuf zan kiyaye.”
    “Good” yace mata “ga wannan F&A ne suka kawo ana buk’atan sa hannun Boss akai zuwa gobe ko anjima zasu dawo su karb’i as his PA ke zaki kai masa ki tabbata yayi signing bayan nan seki ajiye zasu zo su karb’a.”

        “A’a Yusuf in kanayi wa Allah ka kai masa dakanka dan Allah, wallahi masifeni ze sakeyi please.”
    Dariya sosai ta bawa Yusuf. “Fannah sekace wajen mala’ika zan aikeki? In ke mace be sassauta miki ba ni na miji fah? Ai se yayi firing d’ina nima. Bare miki komi ba in shaa Allah.”
 
    “Yusuf please mana.” tace kan wacce za tayi kuka.
      “Fannah please mana” ya cofeta “toh ni na gama nawa bye”,kafin ta sake magana ya fice.
    Kallon files d’in take batasan ya zatayi ba, wallahi batayi shirin soma kuka again ba. Tafi minti ishirin tana nazarin abinyi ganin ba mahalicci se Allah ga kuma Yusuf yace ko zuwa anjima zasu zo su karb’a. Ba ita tabar office natan ba se kusan bayan awa d’aya da minti goma da tafiyan Yusuf dan ko seta kai bakin k’ofar office natan seta dawo ciki again. Da k’yar d’in k’yar tayi gathering confidence ta nufa office na Anas chan ma sanda ta tayin drama musamman ma da ta tuna yadda yace mata tafita masa daga office. Jiki na k’yarma tayi knocking bisa k’ofar nasan. Shiru taji be amsa ba. Tayi kusan sau uku duk ba amsa se kawai ta bud’e a hankali tana lek’awa har ta bud’e duka bayan ta k’ariso cikin office d’in taga office d’in kaca kaca banda kwalaben giyan da coffeen data fasa d’azu ga papers da akayi watsi dashi a k’asa sekace dagangan. A gefe guda tagansa zaune kan kujera da kwalban giya a hannunsa ya kishingid’ar da kansa jikin kujerar yana bacci hankalinsa kwance. Kai kawai ta kad’a wato sanda yasha giyan, abinda yasa ya korata waje kenan d’azu. Files data shigo dashin ta ajiye kan table nasa sannan ta soma tattara papers d’in tana sawa cikin dustbin. Bayan tagama ta share kwalaban tare da mopping k’asar tsatsaf ta mayar masa da office nasa.

      Table nasan ta koma ta soma arranging papers daya hargitsa kai sekace d’an yaro. Garin yin haka tayi coming across wani littafin dayake nan harda kwad’o. Ko ba’a fad’i ba za’a san littafin nada muhimmanci. Sede kwad’on tagani a bud’e haka kawai kuma taji tanasan ganin me aciki. Kallonsa ta sakeyi ta tabbatar eh bacci yakeyi sannan a hankali tana b’ari ta bud’e first page d’in family photo tagani mak’ale ajiki. Fuskoki biyu tagane ciki da na Anas seda na wani wanda tana da tabbacin k’aninsa ne dan kama, sede fuskar wanda take zaton mahaifiyar sun ne taga a kankare, an kankare da biro dagangan dukda hakan kuwa ta seda ta tantance kamannin Anas da wansa ga wacce take zaton mahaifiyar sun ne. Amman toh mesa ze kankare fuskar mahaifiyarsa? Yabar na kowa ya kankare na mahaifiyar, mesa? Ta rasu ne? Amman ai koda rasuwa tayi bare kankare ba, toh mesa? Zata juya next page d’in taji Anas yaja numfashi cikin bacci ai tana b’ari ta mayar da littafin k’asa inda ta d’auka.


*© miemiebee*

No comments: