TANA TARE DA NI... PAGE 33
BY MIEMIEBEE
Haka har k’arfe 4:00PM lokacin tashi yayi Fannah bata gama rubutun ba acikin d’ari tayi 77, daga k’arshe ma da gajiyan ya mata yawa bata san sanda bacci ya sace ta a wahalince ba. Anas kuwa tun 3:50PM awa d’ayan daya bata yayi ya kirata ba iyaka a telephone nata haka har call d’in ya tsinke bata d’agawa se baccinta takeyi daga k’arshe kam ma Fannah unplugging wayar tayi daga jikin bango dan distracting nata da yake, sannan takoma kan table d’in tare da aza kanta ta cigaba da bacci. Haushi ne ya cika Anas dam wato bayan yace mata kar tayi disconnecting wayan shine tayi ko? da kyau. A fusace ya mik’e daga office nasa ya nufa nata, yana isa yayi banging k’ofar bacci sosai Fannah take cike da gajiya ko noticing abinda yayi ma batayi ba.
Mamaki ne ya cikasa daya ga yadda ta bararraje tana bacci kan table lallai ma! Bece da ita komi ba, bayi ya nufa tare da d’ibo ruwa cikin mod’a yafito dashi sannan yayi kanta sanda ya k’are mata kallo sannan ya sa hannunsa cikin mod’an ya d’iba ruwan cikin hannunsa sanda ya tabbata ya matsar da papers d’in gefe guda sannan ya watsa mata a fuska a birkice ta tashi tana nishi da k’arfi razana tayi ganinsa a gabanta yaushe ya shigo? Yaushe ma tayi nisa a baccin? Na ‘yan mintuna fa tace zata d’an huta.
“Sannu da hutawa ko Fannah Aleeyu? Kin gama aikin dana saki kenan har kike bacci. Bayan haka kuma kikayi unplugging wayar daga jikin bango saboda kar a tada ke daga beautiful sleep naki koh? dukda kinsan na hanaki.” Se yanzu ta tuna lokacin data zare wayar daga bango ma, ita ta d’au duk a mafarki ne. Kasa fad’in komi tayi har yanzu mamakin ya akayi ta fad’a bacci take. “Baki amsani ba har yanzu, kin gama abinda na saki kokuwa in sake watsa miki ruwan ki gama tashi?”
“Ban gama ba da saura” ta basa amsa kanta sunkuye tana tsiyaye ruwan daya fesa mata a fuska da cikin hijabin ta.
“Sauran guda nawa?” Ya tambayeta.
“Saura 23.” Papers d’in ya tattaro gabanta “oya finish them.” Hijabin ta tasa ta sake share ragowan ruwan fuskartan sannan ta soma rubutun bayan ta gama d’aya ya amshi ya rik’e. Tambayar sa tayi “Sir k’arfe nawa ne please? Kar la’asar ya wuce ni.”
“Nima bansani ba da kika kwanta kina bacci ai baki tambayeni k’arfe nawa ba” yabata amsa takaicacce. A daidai lokacin ta d’aga kai ta sauk’e idanunta kan wall clock aiko taga 4:07PM “nashiga uku! banyi sallah ba” tana gwada yunk’urin tashi Anas ya zaunar da ita “sit! Ai ba inda zaki sekin gama sauran 22 d’in nan gaba in na saki aiki zakiyi bacci.”
“Sir Sallah fa na gaba da komai, 5 minutes kad’ai ya isheni in na idar se na cigaba.”
“Wa’azi zaki min? Toh banasan ji. Damuwanki ne dan bakiyi sallah on time ba da waya ce ki baje kiyi bacci?” zama yayi kan table d’in “get on with it, in kin ga kin tashi yin sallah toh se in kin gama rubuta sauran” Zata sake magana yace, “now!” A tsawace. A ranta tace ai wallahi zunubin na kanka. Haka yana zaune akanta har ta gama rubutawa tas sannan ya mik’e tare da tattara sauran ya had’a gu d’aya. “Kin gama aikin ki na yau zaki iya tafiya.” Dad’i sosai taji a cewarta ya manta da aiken dayace ze mata. “Gobe first thing in the morning zaki aiken da nayi niyan miki yau, karki zata ko na manta ne dan kar Mami tayi tunanin na rik’e ki a ranar farko ne yasa nayi hakan.” Yana kaiwa nan ya fice. “Allah raka taki gona” ta fad’i bayan da ta tabbata ya fice “mugu kawai, kuma Allah ze sak’a min” mik’ewa tayi ta shiga bayi chan tayi alwala tayi amfani da mirron ta giara fuskarta bayan tafito ta idda sallah nan ta tattara kayakinta ta fice, koda ta sauk’o bata ga Yusuf ba dad’i sosai taji dan gida takeson zuwa yanzu ba sauraron labaransa ba.
Kallo d’aya za’a mata asan tasha aiki yau ta kuma gaji. Mami ta soma tararwa a tsakar gida tana sirfen wake. “Sannu dazuwa Habibti.”
“Yawwa sannu Mami” ta k’irk’iro murmushi. “Ya aikin? Yau da alama agaje kike wuce ciki ki watsa ruwa ki kwanta kafin nan mun gama alalen.”
“A’a Mami zan tayaki sirfen.”
“A’a Fannah wannan aiki na da Afrah ne itan ma tashiga bayi ne yanzu zata fito karki damu.”
“Toh Mami sannu da aiki” tana kaiwa nan ta wuce d’akinsu, sosai taga d’akin ya canza kamanni duk an sake cikasa da kayakin da Mr. Fauzi ya kawo musu jiya tsuka taja wanda yasa Afrah fitowa daga bayan wardrobe inda ta lab’e tana chatting. “‘yar munafukai kinzo kina chatting kinbar Mami na aiki ita kad’ai ko?” Cewar Fannah ba alaman wasa tattare da ita.
“Ya Fannah dan Allah kiyi shiru kar Mami ta jiyoki bayi nace mata zan shiga.”
“Ai wallahi sena fad’a mata gaskia a mayi seizing wayar taki ai nima haka kika sa baki jiya nakoma wa Mr. Fauzi aiki.”
“Yi hak’uri Ya Fannah dan Allah ya office d’in?”
Baki Fannah ta murgud’a mata “bansani k’anwar shed’an kawai jibi yadda hannu na ya kumbura shafin paper guda d’ari na kwafe masa ai wallahi Allah ya isa kuma duk laifin ki ne. Mami! Mami!”
“Na’am Fannah wani abu ne?” cewar Mami da k’arfi yadda Fannah zata jiyota.
“Ya Fannah dan Allah karki fad’a mata.” Afrah tace k’asa k’asa.
“Ai wallahi se na fad’a.” nan ta d’aga muryarta “Mami ga Afrah nan ta mak’ale tana chatting ba bayin da ta shiga.”
“Mami wallahi k’arya take yanzu fitowa na” wayarta ta mayar cikin wardrobe d’in.
“Fito nan Afrah kinsan zan karb’e wayarki ko?” Gwalo Fannah tamata a yayinda Afrah tafice zuwa samin Mami tana bata hak’uri. Kayan jikinta ta rage ta fad’a bayi dan watsa ruwa.
****
“Oyoyo Ya Anas!” Amal tayi hugging Anas a wajen parking lot. “Oyoyo Angel.” Flasks biyun yaciro daga motarsa ya mik’a mata empty’n “ungo wannan rik’emin.” Bayan ta amshi tace, “Ya Anas me acikin na hannunka?”
“Coffee ne” ya amsata a takaice yana murmushi. “Toh shine har flask biyu.”
“A’a d’aya ne na riga na shanye d’ayan.” Ido wuru wuru ta zaro “ka shanye?? Duka wannan na hannun nawa?”
“Eh Amal yunwa a office.”
“Ayyah Ya Anas to ko zaka soma tafiya da lunch box ne?” Dariya ya d’anyi kad’an “karki damu I can take care of myself mu shiga daga ciki.”
“Toh Ya Anas.” A parlour suka tarar da Abuu da Ummie suna zauna se tattaunawa suke sannu da zuwa suka masa a yayinda ya mik’awa Amal flask na hannunsa me coffeen kan takai masa d’aki. Shettima kuwa na dining space yana d’iban abinci shima da alama yanzu ya dawo daga school. “Sannu dazuwa Ya Anas.”
“Sannu maza” ya amsa sa. “Abuu, Ummie sannunku da hutawa.”
“Yawwa Anas ga abinci can seka d’iba kaci ko akai maka d’aki ne?”
Shi da yakeda coffeen sa yau har cikin flask me zeyi da abinci? “A’a Ummie don’t worry bana jin yunwa munje meeting naci abinci a hotel d’azu.”
“Ai dama kullum haka kake cewa toh a huta gajiya.”
“Yawwa Ummie” ya juya ze nufa d’akinsa kenan Abuu ya kira sunan sa “Anas!” chak ya tsaya tare da juyowa “na’am” Abuu ya amsa cike da girmamawa. “D’an zo ka zauna magana nakeson muyi.”
Ba musu ya k’ariso cikin parlour’n tare da zama kan rug d’in.
Giaran murya Abuu yayi, “ni Anas shin baka da tsarin aure ne a rayuwar ka?”
Blue eyes nasa ya zaro tare da sake baki wangalau cike da mamaki. Bambarak’wai yajiyo maganar, dududu shekarunsa nawa ne? 24 nede da ‘yan wattani akai shine za’a masa maganar aure? Cikin mates nasa gabad’aya ba wanda yaji ance yayi aure ko Baana me san mata ma beyi ba se shi ne za’a ce yayi aure? Lallai kuwa! ai da fili kawai Abuu yafito yace masa ya gaji da basa abinci ya tattara kayakin sa yabar masa gida, da yafi mai akan yace wani baida tsarin aurene a rayuwarsa.
“kayi shiru Anas.” Abuu yasake tambayar sa.
Juyi kansa yaji yana masa da k’yar ya iya fad’in, “aure kuma Abuu?”
“Eh Anas aure” Abuu yasake jaddada masa.
“Abuu aure fa kace? Ko ka manta shekaruna ne? I’m just 24 fa, Ummie ki tuna masa mana.” Yadawo da kallonsa kan Ummie. Shiru Ummie tayi dan itama sanda ta fad’a wa yayan nata kan kar ya tinkari Anas da wannan zance na aure yayi yaro he is just 24 amman Abuu yak’i sauraranta saboda wasu k’wararun dalilun dayake dashi.
“Ya Ibrahim nakega abar maganan nan, Anas yaro ne” ta fad’a tana b’ari gudun kar wan nata ya masifeta. “Nafeesa munyi maganan nan dake d’azu inhar kinsan baraki bani goyin baya ba to kiyi shiru.” Kum taja bakinta tayi shiru, dawo da kallonsa yayi kan Anas da ransa ke tafasa, blue eyes nasa sun sake shiga jin an ambato masa kalman ‘aure’ abinda ya tsana fiye da komai. Haka kawai yau yana jin dad’insa Fannah ta dawo masa aiki za’a tinkare sa da zancen aure. Mschww!
“Aure Anas nakeson kayi, kai kanka kasan kalan kud’in da kake dashi, kalan arzikin da Babanka ya bar maka yaro ne kai har yanzu baka gama mallakan hankalin ka ba hanya d’aya ce kuma zata sa ka mallaki hankalin shine ta hanyan yin aure, yazamto kanada mace a gefenka wanda zata tayaka shawarwari da sauransu. Kuma ko ba dan haka bama kai bakasan ace d’an daka haifa ko ‘ya suyi gadon wannan company naka me albaraka? Sanin kanka ne kap a ‘yan gidan nan bame iya kula maka da wannan babban company koda ace yau kafad’i ka mutu, ga kuma yadda ake mutuwa, iyye Anas?” Shettima dake sauraronsu kai kawai yake kad’awa, ma’ana maganganun Abuu na shiga ta nan na fita tacan ne kawai dan ko za’a had’a sama da k’asa Anas bareyi aure ba inama ace yasamu yarinyan dayake neman ne, wacce ya amshi martabarta da se ace da sauk’i halan ya yarda yayi auren.
Ganin Anas baida niyan magana Abuu yace, “kayi shiru Anas ko bakada abin cewa ne?”
Giyansa kawai yakeson sha yanzu shi kad’ai ne ze daidaita masa tunaninsa gashi dama ya d’an kwan biyu be tab’a ba. “Abuu aure? Ni nayi aure? Ai in neman me shawara nake ga Ummie gaka ga Shettima. Ko Amal ma zata iya bani shawara gaskia Abuu ni banasan wannan shawara.”
“Kinji irin rashin hankalin danake fad’a mikin ba Nafeesa?” Abuu yafad’i yana kishingid’a bayansa jikin kujerar dayake zaune kai. “Anas yaro ne kai har yanzu bakasan ciwon kanka ba aure ne kawai zesa ka mallaki hankali, kasan ko kap Nigeria kaine youngest billonaire? Taya kakeson ka rik’e sunan nan in bawai kanada wanda zata na baka shawara ba? A yanzu a hakan ka tsab abokan banza zasu iya juya maka hankali kayi messing up rayuwar campany’n ka amman in kanada mata fah? Barata tab’a barin hakan ya faru ba. Kai yanzu tsakanin ka da Allah komi da kake ciki ne kake sanar dani ko Ummie’nku?”
Kai Anas ya kad’a a hankali. “Toh! Amman in mata kake dashi komi zakaji kanasan sanar da ita, in kuwa me hankali da tunani ne duk abinda kakeyi ba daidai ba zata jawo hankalinka, ko baka gane ba?” Ko giad’a kan da Abuu ke jiran Anas yayi beyi ba shifa bega abinda zesa yayi aure ba, shida aure sun raba hanun riga.
“Baraka fahimce abinda yasa nace kayi aure a yanzu ba se a nan gaba, se anan gaba zaka gano so ne yasa na keson kayi aure.”
“Abuu wai wani irin aure? Ni ban tab’a jin inda me shekaru 24 yayi aure yayi aure a wannan zamani ba, ko kaifa 27 kayi aure Abuu, a da ma kenan”
“Nonsense, taya zaka had’a kaina da kai? Kuma ai dama baraka ji ba Anas saboda yawancin masu irin shekarunka basuda aikinyi wasu yanzu suke kammala makarantar wasu kuwa sun kammala ba aiki har yanzu to taya zasuyi aure ba aikin yi? A da ne ko ba aiki mata suke yarda su auri maza amman banda yanzu da ‘yan mata suka sa kwad’ayin abin hannun mutum. Kaga ko dole kace baka tab’a jin me shekaru irin naka yayi aure ba. Amman kuwa in kayi la’akari kai naka case d’in daban ne kap cikin mates naka akoi wanda yakaika samu ne? Mu ajiye samu a gefe ma akoi wanda yake da aiki me kyau kamar naka ne? Ai dama abinda yasa ake delaying aure kenan, rashin samu da abinyi. Kaida Allah ya riga ya baka fa? Seka tsaya yin meh? Jira zakayi se sanda mates naka suka soma aure kaima kayi?”
“Eh Abuu” ya amsa ransa a b’ace.
“Toh Anas kayi k’arya dolenka kayi aure kodan mutuncin company’nka kai bakasan in kanada aure mutanen da kake alak’a dasu a sauran k’asashen duniya zasu fi baka mutunci da girmamawa bane? Sabida shi aure hankali yake k’arawa dakuma daraja a idan mutane. Ka ajiye k’ank’antan shekarunka a gefe kayi facing reality Anas, aure ne ya kamance ka kodan kare martaban company’n da Babanka yabar maka.”
“Abuu gaskia ni barin yi aure ba, my company is doing perfectly fine duk abinda nasan ya kamata inayi ba abinda muke lacking, aure ba abinda zemin inbanda raba min hankali.”
“Anas yau da ni kake yin che in che? Aure zakayi ko kanaso ko baka so, abinda babba ya hango yaro ko ya hau kan tudu bare gani ba wannan kenan.”
Kamar wanda zeyi kuka yace, “Abuu dan Allah karka min haka please, karka sani yin abinda banaso banida interest akan aure I’m not ready, wallahi kabi duk sauran investments da companies da muke aiki dasu kaji, komi ina kiyayewa ina running business d’ina perfectly, na yarda duk sanda kaji ance maka nayi wani abun da be kamata ba ka sani auren, in fact ka nemo min matar da zan auran ma da kanka amman banda yanzu please. Please Abu.”
“Anas taimakon,ka nakeson yi, trust me barakayi regretting wannan shawara na yin aure ba.”
“Abuu please fa nace dan Allah-”
Katse sa Abuu yayi “a’a ya isa Anas, na d’aga wannan shawara ya zamto umarni yanzu wanda dolenka ka amince ko kanaso ko bakaso, dolenka zakayi aure ko kanaso ko bakaso ni na fad’a maka.”
“Ya Ibrahim dan Allah kayi hak’uri take it easy on him, yaro ne.”
“Dakata Nafeesa wannan uban san da kike ma yaran nan ze zamo musu illa wataran, in gaskia tazo dole a fad’eta, ehe!”
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment