BY MIEMIEBEE
*ASSALAMU ALAIKUM MASU KARATU, INASON INYI AMFANI DA WANNAN DAMA IN FAHIMTAR DA MASU K’ORAFI KAN LITTAFI NA, NACEWA INA YAWAN SA TURANCI CIKI. RIGHT FROM THE START NASO DAMA IN YI MAKING IT CLEAR KAN ZA KUNA YAWAITA GANIN TURANCI CIKIN LITTAFIN NAN AMMAN KUMA SENA FASA. GANIN ANASON A MAIDA ABIN SUBJECT OF DISCUSSION YAZAMA DOLE INYI MAKING IT CLEAR YANZU. IN KUKA LURA BAWAI NA K’WARE A HAUSAN BANE, KOYO NAKE HAR YANZU, BA BAHAUSHIYA CE NIBA ‘YAR MAIDUGURI CENI, YOU GUYS KNOW RIGHT ‘YAN MAIDUGURI BA’A SASU CIKIN JERIN HAUSAWA. INDA NA K’WARAI A HAUSAN AI BARIN NA SIRKAWA DA TURANCI BA. KUGANE PLEASE KUNA MIN UZURI. MOREOVER, A CHAPTER’N BAYA CHAPTER 15 KENAN, NAGA SHINE NASA TURANCI SOSAI SABODA A OFFICE SUKE, SANIN KANKU NE MASU K’ORAFI BA’A CIKA YIN HAUSA A OFFICE BA, ENGLISH UNIVERSAL LANGUAGE AKE SPEAKING. INA FATAN DAGA YAU MUNYI SOLVING WANNAN ISSUE. THANK YOU SO MUCH, I LOVE YOU GUYS HAVE FUN READING!!!*
Ba tare da ya kalleta ko yace da ita komi ba yacigaba da abinda yakeyi cikin laptop dake gabansa. Tafi minti biyu tsaye sannan ya ciro wata paper daga drawer ya ajiye kan table d’in. “Here is the coffee description, sugar should be minimum.” K’arisowa tayi ta d’aga paper’n lallai ma d’an wannan order’n ne bare irga min ta waya ba seya sa nazo all the way here.
“Sir is that all? Naga ai irin wannan orders muna d’aukawa ta waya.”
Ba tare da ya kalleta ba daka tsawa “just shut up and leave please!” Har tsakiyar kanta tajiyo wannan tsawa rabuwanta da a daka mata tsawa haka tun barinsu Bama. Take tajiyo hawaye na ciko wa idanta daman ita ba me daure masifa bane, batare da tace komi ba tajuya ta kama tafiya tana share hawayenta nan ne ya d’ago kai yana kallon bayanta har ta bud’e k’ofar ta fice.
Da misalin k’arfe 3:50PM su Fannah suka iso conference hall d’in komai is in place. 4 on the dot su Anas suka hallaro hall d’in. Fannah na ganin sun shigo ta fice ko sa Anas a ido batai ba, bata masan wani kalan kaya yake sake da ba, se sanda za su soma serving coffee’n ne ta dawo kanta a k’asa take tafiya dan karta jawo attention, haka table by table take bi tana ajiye coffee’n. Table nasu Anas takai k’arshe a hankali ta d’aga kai dan sasa a ido saidai ba direction nata yake kallo ba ya juya yana magana da d’aya daga cikin mutanen kan table nasun. K’eyarsa kawai tagani yadda yayi styling gashin kansa me tsawo wane na bature.
Bayan ta gama ajiye musu tajuya zata tafi kenan taji familiar voice ya kirata da “waitress” gam ta rufe idanta a hankali ta juya “yes sir” lokacin kuma Anas ya juya yana magana da wasu, k’arisawa tayi ta tsaya daga gefensa “yes sir!” Ba tare da ya kalleta ba yace, “take this away I don’t take coffee.” Kallo ta k’are masa sannan ta d’aga ta fice. Mamaki ne yacika ta wai waye wannan Anas ne ko me sunan san yake feeling like.
Bayan taron ya watse suka raba kud’in da suka samu sannan ta dawo gida d’aki ta wuce direct. Afrah tasamu se faman chatting take bayan ta mata sannu dazuwa seta karinci kamar wani abu na damun Fannah. “Ya Fannah lafiya?”
“Wani irin lafiya? wallahi wannan d’an Alhj Muh’d d’in ji da kai ya masa yawa. Bakiji yadda yake ma mutum magana ba ke ko kallon mutum ba yayi.”
“Kina nufin Anas Ibrahim Fauzi?” Cewar Afrah.
“Eh wai haka naji sunan nasa amman ya akayi kika sani?”
“Yanzun nan aka nuna sa a NEWS nake gama meeting d’inda kuka jen ne. Yasa black suit da white shirt da black necktie ko?” Cike da mamaki Fannah ke kallon Afrah. “Eh haka” ta amsa ta.
“Ya Fannah baki ga kyansa ba wallahi kamar bature.”
“Toh ai kyansa be amfana sa ba tunda baida hali me kyau.”
“Ya Fannah waya keta hali? Ke bakiga fuskarsa bane?”
“Bangani ba kuma bansan gani, ni mubar maganarsa ma he is so arrogant. Barinje inyi wanki kafin Maghrib yayi.”
Wankin ta takeyi hankalinta kwance tajiyo kiran Afrah daga d’akinsu Baba. “Ya Fannah! Ya Fannah! kizo da sauri.” Nan ta bar abinda take ta ruga a guje ciki acewarta kowani abu ne yasami Afrar dan su Mami basu gida takai Baba asibiti Aiman ta rakata. “Afrah lafiya?” Ta bankad’o labulen d’akin zaune tasamu Afrah gaban TV “Ya Fannah gashi nan! Anas d’in” kafin Fannah ta kai dubanta kan TV’n har ya juya sede taga kamar ta ga fuskarsa kamar kuma bata gani ba. “Mstw tun d’azu nake kirar ki gashi ai har ya kau da kansa”
“Yanzu Afrah fisabilillahi akan ganin wannan Anas d’in kika kirani all the way here nafa d’au ko wani abu ne ya same-”
Bata k’are maganar ba Afrah da hankali ke kan TV tasomsa sabon ihun “gashi nan! gas-” karap NEPA suka d’auke wuta. “Oh damn it! NEPA bakuyi ba.” Tsuka Fannah taja sannan ta koma ta cigaba da aikin dake gabanta.
_Wattani da dama sun shud’e..._
Rayuwa ta cigaba da kasance wa Fannah daidai ba abinda ya sake had’ata da Anas. Tana zuwa gun aikinta kullum. Baba kuwa magunan da aka basa a asibiti cikin ikon Allah yana samun sauk’i sosai. Tsoron Fannah d’aya ne rananda magunan zasu k’are bata san ina zata samu kud’i asake sai masa ba. Kullum cikin add’ua take.
Ta b’angaren Anas kuwa abu sunan yadda suke shaye shaye dakuma breaking up da ‘yan mata kullum yana kan yi. Saidai ba kamar da ba, d’an watannin baya da suka wuce sam yadena mafarke mafarken daya saba na Ummimi da kuma yarinyar dayayi raping but kwanan nan sede be kwanta ba seyayi mafarkin yarinyan dayayi raping d’in wai ta dawo garesa. Syrup nasa yake kwankwad’a bayan kwana biyu yasake tashi da mafarkin ji yake yarinyan is somewhere close to him. To kode tana d’aya daga cikin ‘yan matan daya tab’a breaking up dasu ne? Kai! A’a da k’yar ai ita wancan a Bama take. To ina take??
Shettima dake tsaye a kansa ne yayi ihu dagangan dan tsoratar dashi. “OMG!” cewar Anas da hannu dafe kan k’irjinsa. “K’aniyanka kasan yadda kaban tsoro kuwa!” har yanzu nishinsa be dawo dadai ba. Dariya sosai Shettima ke “hahaha! Kaga fuskarka kuwa? Anyways tunanin me kake har na shigo d’akinka baka sani ba.”
“Kajima anan ne?” Anas ya tambaya yana k’ok’arin daidaita numfashinsa.
“Yup about 2 minutes ago” cewar Shettima.
“Babu, ba tunanin da nakeyi.”
“Oh common! Ya Anas kama dena min k’arya kasan ko lokacin da ka b’oye min lamarin abinda kama wancan yarinyar a Bama nagane so just tell me what is it now?”
Tasowa yayi ya zauna, shima Shettiman ya zauna kusa da wansa “tell me ina jinka.”
Nishi Anas yaja “kasan wani abu ne? Its been long banyi mafarkin wannan yarinya ba but yanzu anytime na kwanta tunanin ta kawai nake ji nake kamar *_TANA TARE DA NI_* I don’t know whats wrong kullum cikin tunaninta nake Shettima I can feel it yarinyar bata mutu ba.”
“Toh fahhhh” cewar Shettima dan ko besan me zaice ma wansa ba he is speechless.
“Fad’a min Shettima what are you thinking?”
“Well, Anas maganar gaskia bansan me zan ce maka ba. Yarinyar nan fa a Bama take theres no way zata dawo Maiduguri kuma kai da bakinka kace she was 15 time da abin yafaru who knows ko bata rayu bama an-”
Katse sa Anas yayi “No Shettima I can feel it, bata mutu ba” hannu yasa cikin gashinsa “I don’t know what to think anymore, inasan ganin yarinyar in nemi gafararta Shettima.”
Kafad’arsa Shettima ya dafa “komai will turn out perfect karka damu, wayasani ko ta kasance d’aya daga cikin ‘yan matan da kake wasa dasu. Saboda baka san fuskarta ba.”
“But I’m sure ita tasan nawa ai, in ta ganni zata gane ni tunda ita ba’a buge take ba time d’in.”
“Tsab ko zata iya mancewa da fuskarka Ya Anas, katuna da dare ne ranan kuma ruwa akeyi, in har ta rikice beyond imagination alokacin sosai tsab zata mance da kaman ninka. Allah desa bata kasance d’aya daga cikinsu ba.” “Ameen” Anas yace sannan ya koma ya kwanta tare da zura wa ceiling ido. Wayarsa ya soma k’ara yana kai dubansa yaga family doctor’nsu ne, ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga “Hello Dr Mansur?”
“Hello Anas kabar duk abinda kakeyi kazo gidan Babanka yanzu.” ya fad’i cike da tashin hankali sannan karap ya katse wayar.
“Hello..? Hello...?”
Zabura yayi yajawo jacket nasa yasa tare da d’auko key’n motarsa ya fice a 360. Bayan ‘yan mintuna ya iso gidan Mr. Muh’d. Sama ya haura direct zuwa d’akin Mr. Muh’d can yasamu Dr Mansur tsaye a bakin k’ofar. “Dr Mansur whats wrong? Meya samu Baba?”
“Anas is about time kasan gaskiya Babanka yata b’oye ma gaskia saboda bayasan ya saka cikin tashin hankali amman yanzu da lokaci yariga ya k’ure I have to tell you.”
Take idanun Anas ya cike da hawaye “meke faruwa Dr. Mansur? Meya samu Baba?” ya tambaya murya na rawa.
“Anas calm down tunba yau ba Baba ke suffering da cutar cancer.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Anas ya saki salati. “No thats not true please karka ce haka Baba baida cancer.” Kuka yasoma yi sosai.
“Anas thats why nace maka you need to calm down yanzu ba lokacin musu ko kuka bane addu’a zaka masa. Kasan shi matsalar cancer ba’a cika discovering na sa da wuri ba bale ayi maganinsa saboda bai da symptoms cin jiki yake sosai the moment ya kama mutum. Haka yasamu Baba ma, yau shekara kenan yana fama da cutar a iya sani na kenan. Duk sanda kaji Baba yace maka zeyi tafiya to ciwon nasa ne yatashi.”
“Dr Mansur niba wannan ba dan Allah” yasa hannu ya share hawayensa. “Do something to save him please.”
“I’m so sorry Anas but its too late, saisa nace maka addu’a zamu masa yanzu lokackin Baba yayi, be a man please, kai kad’ai Mr. Muh’d keda bayida wani family bayan kai, you have to be strong.”
Inaaa Anas se kuka sun shak’u da Baba sosai wane Abuu. Kuka yake sosai Dr. Mansur na basa hak’uri ganin ba mahillici se Allah yasa ya share hawayen sa a hankali ya bud’e k’ofar d’akin Mr. Muh’d. Kwance yagansa rai a hanun Allah wani kukan yasake faso masa jiki a sanyaye ya k’arisa gaban gadon nasa ya tsuguna tare da rik’o hannunsa yana kuka.
“Baba dan Allah kar ka tafi kabarni, kar ka tafi kabar Enterprise naka we need you.” Magana ciki ciki Baba yace, “shhh Anas, bar kuka ni zan tafi amman na bar musu kai. Kai na mallakawa Enterprise d’ina da duk wani abinda na mallaka”
“Noo... Nooo please Baba” Anas ya katse sa.
Baba yacigaba “na riga nayi signing komai under your name Anas, kamar yadda nasan ka da hankali da hardworking ka cigaba da kula da Enterprise d’in koda a bayan raina, naka ne yanzu banida ikon in fad’a maka abinda zakayi dashi, just do what is right. Ban samu naga su Abuu da Amal ba tell them am sorry.”
“Baba please kabar magana haka in shaa Allah zaka tashi baraka mutu ba please.”
Wani irin numfashi Baba yasoma yi da k’arfin gaske.
Gamgam Anas ya rik’e hannunsa yana ihu “No! No! Baba dan Allah karka tafi Dr. Mansur! Dr. Mansur!” a guje Dr. Mansur ya shigo saidai shima ba abinda ze iya tsayawa yayi daga gefe d’aya yana kallon yadda Baba ke nishi. “Dr. Mansur do something to save him please karka bari ya mutu.”
“Anas I'm so sorry amman ba abinda zan iya masa, lokacinsa ne yayi.”
“La ila ha illallah muhammadur-rasulillah salla-” be k’are ba numfashinsa ya yanke kap. Ihu Anas ya k’urma “Noooooo! Baba you can’t die please” hugging Baba yayi yana kuka yana jijjik’asa Dr. Mansur ne yazo yana k’ok’arin d’aga sa daga jikin gawan Baba amman ya kasa haka ya zuba wa Anas yana kukan cire rai yana basa hak’uri. Sun musan minti talatin sannan Anas ya tashi a garin yin haka wayarsa ta fad’i kasa “Ina zakaje Anas?” Cewar Dr. Mansur.
Idanunsa sunyi jazir wane barkono blue eyes nasa sun k’ara shiga. Batare da ya kalle sa koya ce dashi komi ba yafice be tsaya ko inaba se bar (gidan giya) inda yaje ya bugun buguwa. He can’t take it mesa Baba ze mutu ya barsa?
Wayarsa Dr. Mansur ya d’aga ya kira Abuu ya sanar dashi halin da ake ciki salati kawai kukeji. Bayan ya ajiye wayar ya rufe gawan Baba sannan ya fito a ranan aka ma Baba wanka aka sallace sa aka bisine sa. Kuka sosai kowa yake, ‘yan Maiduguri sun mugun jin mtuwan Mr. Muh’d. NEWS na ranan kap Mr. Muh’d aka yini ana nunawa.
Ba inda ba’a nemi Anas ba an rasa ina yashiga se Allah, gashi wayar sa bata gunsa. Ranar de ta kasance a very bad day wa mutanen Maiduguri all in all.
Se washegari da safe Anas ya dawo gida Allah yaso daya dawo Abuu da Ummie basu nan Shettima kad’ai a gida shi ya kula da Anas. Sosai Anas ya bugu ko d’aga k’afa bai iyawa Allah kad’ai yasan ya yadawo gida lafiya. Bayan Shettima ya tayasa rage kayan jikinsa ya kwantar dashi tare da rufe sa da bargo. Bacci sosai Anas yayi se shabiyun rana ya tashi. Shettima yagani zaune a gefensa yana karatu.
Kansa ya rik’e yana k’ok’arin zama. Nan ne Shettima ya jiyo ya kallesa cike da tausayi. “How are you feeling Ya Anas?”
Kallonsa kawai yayi ba tare da ya amsa sa ba.
“Ya Anas hak’uri zakayi Baba lokaci yayi, zuwa gidan giya ka bugu is not a solution. Ba abinda ze amfanar da Baba kamar yadda bare amfanar dakai ba kaima. Addu’a ya kamata ka masa.”
“No Shettima bara ka gane ba, baraka tab’a ganewa ba. Why is my life always like this? Se lokacin dana soma jin dad’i Baba ze tafi ya barni da burden na Enterprise nasa. Baran iya ba Shettima I can’t manage his company.” A hankali ya soma kuka kamar d’an yaro.
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment