Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 17
BY MIEMIEBEE


 
      “Oh common please Ya Anas, kowa yasan how you must be feeling, hak’uri zakayi ka d’au wannan ma wata k’addara ce.” Cewar Shettima yana shafa bayan Anas dake kuka. Daidai lokacin su Abuu da Ummie da Amal suka shigo kan gadon Anas Amal tayi. Ganin wanta na kuka itama tuni ta fara “Ya Anas bar kuka kaji? In shaa Allah Baba is in a better place yanzu.” Rungumosa tayi yana kuka ajikinta kamar d’an yaro.

          “Anas hak’uri zakayi, munsan yadda kaji mutuwan Alhj Muh’d amman yazama dole kayi tawakalli ga Allah kayi masa addu’a lokaci ne yayi. Yabar duk wani prperty’nsa maka inda hali zuwa anjima ‘yan jaridu sunasan magana dakai dangane da faruwar wannan abu.”

       “Noo Abuu please, ni baran iya kula da enterprise na Baba ba baran iya ba, kabawa ‘yan press hak’uri baran samu zuwa ba. Ni Enterprise nasan ma baran iya handling ba, I can’t.” Ya sake fashewa da kuka.

     Ummie ce ta k’ariso ta karb’esa a hannun Amal, “yes you can Anas, zaka iya. Babanka bare ji dad’i ba inda ze dawo yanzu yaji abinda kake cewa, ya bar maka company’nsa ne saboda ya yarda da kai da abilities naka, he is sure zaka iya cigaba da gudanar da lafiyar conpany’n saisa yabaka karka basa kunya Baba na. Kayi hak’uri kukan nan baida amfani gacan abinci na had’aka maka kaci kaje mutanen suna jiranka a TV station ko muce suzo ne?.”

     Kai ya kad’a yana kuka sosai. Bayi ya fad’a dan yin wanka amman wankan ma yakasa damuwa sun masa yawa shower kawai ya kunna ruwan nata zuba kansa kusan na minti ishirin sannan yafito yasa kaya yafice zuwa dining inda Amal ke zaune tana jiransa itama idanun nata sun kumbura sunyi ja. Serving nasu abincin tayi kamar yadda suka saba a plate d’aya sukeci. Sede ko kad’an yau Anas baici. “Ya Anas kayi hak’uri dan Allah kaci, karka zauna da yunwa.” cewar Anas.

        Hawaye taga na cikowa idanunsa, hannu tasa ta tare “Ya Anas kasan baran iya jure kukan kaba please kayi hak’uri.” Be iya yace mata komi ba hannu kawai ya aza kanta tare da mata murmushin dole sannan ya kai spoon d’aya baki bayasan jin Amal na had’asa da Allah kwata kwata spoon biyar yayi yace mata ya k’oshi. Yabari su Abuu su raka TV station d’inma yak’i yana isa wajen ‘yan press tunda ga waje suka soma binsa har sanda ya shiga ciki.

    Bayan an basa kujera ya zauna suka soka jero masa tambayoyi wanda kad’an daga ciki ya amsa sauran kuwa kuka suka sa sa haka fa kamar d’an yaro Anas ya bud’e dandalin kuka a TV station su kuwa se recording suke direct ana uploading a news *Nigeria’s most youngest billonaire.*
      Ba’a gama interview d’in bama yatashi yafice dan yadda kuka yafi k’arfin sa. He wanted to be strong amman ina bare iya ba, besan dawani damuwa ze fara handling ba, na Ummimi ne ko kuwa na ‘yar dayayi raping ko na mutuwan Baba kokuwa na managing babban enterprise da Baba ya bar masa. Yakasa tunani giya kawai ne in yasha ze warkar masa da wannan damuwa gidan giyan ya koma ya sake buguwa sannan yafito ya kwanta cikin motarsa har bacci me nauyin gaske ya iske sa.

    ******
        “Ya Fannah yi sauri kizo kiga abin tausayi, hurry!” Afrah ta danna wa Fannah dake kitchen kira. Wanke hannu tayi tafito da wuri.
      “Kiga yadda d’an Alhj Muh’d ke kuka, Allah sarki.” cewar Afrah. Fannah na kai dubanta kan TV’n taga Anas zaune kan kujera da hanky rik’e a hannayensa biyu ya rufe fuskar sa dashi se kuka yakeyi kamar d’an yaro se kace besan da camera kota ina a gaban sa ba. “Allah sarki!” tace “Allah jik’an Alhj Muh’d, yasa k’arshen wahalarsa kenan.”

     “Ameen” Afrah dake jin kamar tayi joining Anas suyi kukan tare. “Kinsan kuma me worse part d’in? Fannah ta kad’a kai. Akace a idan Anas d’in Baban nasa ya rasu, yana ji yana gani mutuwa ta musu katanga, Allah sarki!”

     Tausayi Fannah taji yabata jibi yadda yake kuka sekace bashine mara mutunci me gasa wa mutane magana ba, sekace ba shine me uban jijji dakai ba Allah sarki rashi. Dan yadda Anas ke kuka yasa ta fito daga d’akin ko fuskarsa yakasa bari agani tasan sarai ta k’ara minti d’aya a d’akin kuka zata soma dan hawaye bai bata wuya ga kuma uban tausayi...

        Haka fa tun daga ranan rayuwar Anas ya lalace yafi na da worse ba aikinsa se shaye shaye barin gida ma gabad’aya yayi ya kama hotel yadda yake shaye shayensa hankalinsa kwance.

       Safe, rana, yamma, dare Anas na rik’e da bottle na giya a hannu yana sha. Da rasuwan Baba yau sati biyu kenan amman Anas ji yake kamar yau yau d’innan Baba ya rasu sau kusan kullum yake kai ziyara gidan Baba, masu aiki ya nemo dasuna kula da gidan, a rana se anyi shara da mopping sau biyu wane akoi mutum ciki. Tun rasuwar Baba kuwa ya rufe company’n har yau ba’a bud’e ba masu aiki a wajen ba yadda basuyi dashi ba ya bud’e su koma aiki amman yak’i shi a tunaninsa bare iya handling ba bayasan ya b’atawa Baba koda k’wayan zarra ne cikin company’nsa. Allah kad’ai yasan wahalar dayasha kafin yasamu ya gina wannan sky scrapper saboda haka yake jin tsoro sosai kar yayi wani abu yayi ruining abu ciki.

Kusan sati uku ake nema yau Anas yak’i bud’e company ga on going projects dayawa nan barkate. Daga k’arshe sanda ‘yan manya manyan wajen suka je suka ma Abuu bayanin komai sannan ya ce musu zema Anas d’in magana. Bayan tafiyar mutanen, Ummie dake taya Amal tsifa tace, “Ya Ibrahim wallahi Anas tausayi yake ban, ba laifinsa bane yaro yake har yanzu dudu shekarunsa 24 nefa, he is still young.”
    “Saisa yakamata ya bud’e office  d’in, yayi hak’uri ya rungumi k’addara k’in bud’e company’nsa ba taimakasa masa zaiba kin deji abinda masu aikin nasa sukace akoi on going projects dayawa  kuma koba dan wannan bama yau ace Alhj Muh’d na raye ai bareyi farin ciki da abinda Anas keyi ba. Kowa ya tausaya masa shiima yayi hak’uri ya tausaya wa kansa.” Shiru Ummie tayi ta giad’a kai. Amal kuwa idanta tuni suka cike da hawaye rabuwanta da sa Ya Anas a ido har tamanta tun da yabar gidan kota kirasa wani sa’in ma bai d’ agawa yadda zakusan lallai Anas yashiga wani erin yanayi kenan. Ace Amal ma gabad’aya yak’i picking call nata. Allah sarki!

 
         Anas na zaune k’asan carpet a hotel room nasa da giya hannunsa se sha yake ba makawa, gashin kansa ya tarwatse wane na mahaukaci, d’akin duk warin giya yake. Ko ina kwalb’an giya kuke gani ko masu giara sunzoyi bai barinsu su shiga. Kan gadon ne kawai kenan tsatsaf shima d’in saboda ya k’aurace wa kwanciya kai ne a k’asa yake kwanciyarsa yanzu. Wayarsa dake kan gado ya soma ringing haka yana ji amman yakasa koda d’aga k’afa bale yaga kowaye. Haka ya d’aga giyan hannun san yakai baki sanda ya kurb’e tas sannan ya wurgar a k’asa kamar yadda ya saba. Bajewa kawai yayi a k’asan tare da zira wa ceiling ido. Can wayar tasan ta soma ringing again nanma yanaji be d’aga ba se a karo na uku yayi rarrafe ya d’aga idanunsa wani dushe dushe suke gani mai yama kasa gane wake kira kawai picking up yayi ba tare da yace komi ba.

      “Hello Anas?” Cewar Abuu shirun dayaji yasa yasake fad’in “hello? Anas baka ji ne? Hello?”
      Ai kawai Anas ya fashe da kuka cin wayar kamar d’an yaro. Hankalin Abuu in yayi dubu be tashi ba gashi basu san wani hotel Anas ya kama ma. “Anas! Anas until when zaka koyi rungumar k’addara ne wai? Kasani Babanka ya riga y rasu duk wannan abinda kakeyi ba dawo dashi zeyi ba. Haba! Mana Anas sekace bana miji ba, man up please. Kap kowa jira yake ka bud’e company’nka amman kak’i se yaushe wai? Iyye?”  Shiru kukeji ba response ko kukan ma yadena ji. “Hello? Anas!” Aikam tuni Anas yayi hanging up call d’in se kuka yake ba makawa. Shi har yanzu be yarda cewa Baba ya tafi ya barsa ba, Baba yatafi yabar masa company’nsa daya kula dashi. Yana cikin kukan Shettima ya kira yanaji yak’i d’agawa kusan missed calls biyar sannan ya d’aga nanma shiru yayi bece komi ba.

      “Hello Ya Anas” muryan Shettima ya jiyo. “Ya Anas kana ina?” Shiru yayi be amsa saba. “Ya Anas dan Allah kana ina? Wallahi duk mun damu ka fad’amin inda kake.” Amsar wayar Amal dake kuka tayi “Ya Anas yanzu seka tafi kabarmu dan Allah ka dawo gida” ta kuma fashewa da kuka. Jin kukan Amal yasa sa magana bayan ya daidaita muryarsa dan kar tagane a bige yake. “Shhh! Kinji Angel bar kuka, zan dawo amman ba yau ba.”
“Toh kana ina?” Ta tambaya.
      “Ina nan cikin Maiduguri.” Amsar wayar Shettima yayi “Ya Anas tell me ina kake inzo in sameka.”
     “Nooo bareyi kazo ba right now am drunk banasan su Abuu da Ummie suzo...” Aiko ya fara magana kamar zararre “kar su zo sugan ni ahaka sukamu da cancer” bama ciwon zuciya ba. Yad’anyi dariya “wayasani ko suma su mutu.”

         “Ya Salam!!!” Shettima ya fad’i. “Me ya same sa Ya Shettima?” Amal ta tambaya tana  kuka. “Ba komai” Shettima ya mata k’arya “jeki ina zuwa.” A sanyaye ta tashi ta fice. Tana fita Shettima ya dawo kan wayar.
        “Ya Anas what are you saying? Yanzu fisabilillahi tun tafiyar ka can kata shaye shaye? Ina kake yanzu.”
     “Chill little bro! Karka damu am somewhere safe.”
       “Ya Anas ka fad’amin inda kake inzo in duba ka please kaji?”
      “Saboda kazo dasu Ummie da Abuu sugane ina shaye shaye?” Anas yafad’i idanunsa suna kakkafewa besan sanda yabada address d’inbama kawai ya zarce bacci. A gurguje Shettima ya fito ya samu su Abuu a parlour duk hankalinsu ya tashi. “Ya haka? Ina zuwa?” Abuu ya tambayi Shettima. “Wajen Ya Anas zani Abuu.” yabasa amsa.

       “Tsaya muje tare toh mana.”
       “A’a Abuu please kayi hak’uri yace inje ni kad’ai bareji dad’i ba in ya ganmu duka kubar damuwa Ya Anas is somehwere safe.”
        “Anya kuwa Shettima?” Cewar Ummie cike da damuwa. “Kabari muje duka mu gansa dan Allah.”
      “Ummie please kar mu fara ce in ce, Ya Anas made it clear to me ni kad’ai yakeson in je kuyi hak’uri.”
    “Bakomai Shettima Allah kare kakuma isar masa d sak’on.” Abuu ya fad’i.
       “Toh Abuu” nan ya ja mota ya fice. Daidai ya isa harabar hotel d’in yafito bema san room number’n da Anas ke ciki ba, ko daya tambayi Anas d’in kuwa shima ce masa yayi besani ba tsantsan yadda ya bugu kawai.

     Reception ya wuce yayi tambaya k’in fad’i masa tayi acewarta ko yazo cutar dashi ne. “‘kaninsa ne ni can’t you tell? Bakiga muna kama bane?” ya daka mata tsawa. “Now tell me his room number.” Kallon fuskarsa tayi a tsorace sannan taga eh fa suna kama “I'm sorry sir room 21 CEO’n Flames Enterprises yake.” Da gudu ya haura sama zuwa room 21. A bud’e ma ya tarar da k’ofar yana sa kai warin giya ya masa sallama. Salati kawai yake yana bin d’akin da kallo kwalb’an giya sekace na siyarwa. Toshe hancinsa yayi tare da rufo k’ofar akan gado ya tsinci Anas yayi ruf da ciki se bacci yake. Kwata kwata singlet ne a jikinsa seda short nicker. Gashin kansa daya tarwatse ya rufe kad’an daga cikin fuskarsa. Juyar dashi Shettima yayi tare da kiran sunan sa. Shiru kukeji ba amsa. “Ya Anas! Kana jina?”
     “Uhmmmm” ya fad’i idansa rufe yana bacci. Giara masa kwanciya Shettima yayi tare da rufe sa da bargo sannan yakoma k’asa yakira masu aiki suka kimtsa d’akin tsaf aka sa room freshner me uban k’arfi da dad’i dan kora warin giyan.

    Baccin awa uku Anas yayi sannan ya farka a hankali ya soma bud’e ido ya saukesu kan Shettima. K’ok’arin zama yake Shettima ya taimaka masa.
      “Ya Anas how are you feeling?”
    “Yaushe ka shigo nan? Ya kasan ina nan?” Tambayar da ya masa kenan.
       “Kai kafad’a min, but it doesn’t matter. Ya Anas this has to stop. Ya isa fisabilillahi me damuwarka ne? kai bakasan meh k’addara bane a rayuwa? Kashe kanka kakeson yi kwalaban giya kusan 30 a d’akinka hauka ne kuma abin?”
      Ba tare da ya amsa saba yace, “inasu Abuu kataho dasu ne?”
       “Ban taho dasu ba amman believe me ina komawa gida zan sanar dashi da Ummie wannan halin naka na shaye shaye tunda you are not ready to change. Ina ka tab’a jin dan an ma mutum rasuwa seya soma shaye shaye haka? Haba mana Ya Anas.”

         “I’m sorry” ya fad’a a hankali cike da jin haushin abinda yayi. “Shettima I’m sorry, giyan ne kawai in nasha nakejin problems d’ina sun tafi. Shettima kubar ganin laifi na please abubuwa ne sun min yawa I'm just 24 baran iya managing babban Enterprise kamar na Baba ba. Baran iya ba, it is beyond my will.” Sekuma ya fashe da kuka. Da had’in Allah da Annabi da kuka sannan Shettima yasamu yayi convincimg Anas kan bud’e company’n.

       Wanka yasa sa yayi yana fitowa ya masa ordering abinci sosai Anas yasamu yaci. “Thank you Shettima, bansan ya zanyi ba without you.” Hugging nasa Shettima yayi “me too brother dan Allah ka rage shaye shayen nan kar alcoholic level naka ya haura yazama toxic, dan Allah.” Hugging nasa back Anas yayi “in shaa Allah zan rage.” Bayan sun sako juna Shettima yace, “lets go ga kayakin ka nan duk na shirya maka.”

     Tare suka sauk’o bayan Anas ya biya bills nasa suka dawo gida cikin motocin su. Amal na zaune bakin k’ofa tun d’azu tana jiran dawowarsu gate taji an bud’e da sauri takai dubanta ganin motan Ya Shettima k’aramar benz C230 yasa ta koma baya ta zauna tana sake juyawa kawai taga motar Ya Anas tsalle ta daka tayi wajen parking da gudu yana fitowa sukayi huggibg junansu sosai. “I miss you Ya Anas” tace tana hawaye.

*© miemiebee*

No comments: