Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 15
BY MIEMIEBEE



★★★★★
    _5 months later..._

               Shak’uwa ne me k’arfin gaske ya shiga tsakanin Anas da Mr. Muh’d, ladabi da biyayya kam Anas ya iya duk wanda yaji ana cewa Anas na shaye-shaye ze k’aryata zancen. Basu tab’a samin matsala da Mr. Muh’d ba aikinsa duk yanayi me kyau tun da yayi joining enterprise d’in abubuwa suka sake improving fiye da da. Family’n Anas a yanzu haka sun dawo Maiduguri da zama a unguwar New GRA. katafaran gida Abuu ya sai masu da taimakon Anas. Gida ne mansion d’aki kota ina. Rayuwa alhamdulillah yanzu, ansa Amal a Ruby Springfield College. Shettima kuwa ya soma attending UNIMAID a inda yake karanta accounting.

     Anas yayi introducing family’nsa wa Mr. Muh’d sosai suka shak’u da juna. Sanin yadda Anas keson Amal yasa shima Mr. Muh’d yakeson Amal sosai, musamman yadda take sasa dariya duk sanda suke tare in su Anal sunyi hutu kullum tana office wajen Mr. Muh’d datake kira da grampa, wane family haka suka zama. A birthday’n Anas Mr. Muh’d ya basa sabuwar mota pil cikin leather k’irar mercedes-benz SLK. Tunda Anas yayi mota walak’anci ya k’aru ahaka yanzu a list nasa yanada mata 33 da yayi breaking hearts nasu. Leaving life nasa yake to the fullest duk sanda su Baana suka shigo Maiduguri kuwa shan giyan ranan na daban ne. Suna waya sosai da friends nasa Abdoul da Musty.

     Yau ranar ta kasance Monday as usual ya soma shirin office, Shettima da ba lectures se da rana se bacci ake sha. Amal da ba office zata ba amman ta riga Anas tashi tare suka had’a breakfast su biyunsu sukaci bayan sun gama ta rakasa har parking lot yashiga cikin sabuwar motarsa sukayi ba-bye da juna sannan ya fice. As usual yashirya wa Mr. Muh’d schedule nasa na ranan yakai masa. “Welldone Anas, kana k’ok’ari sosai nace zanen project d’incan kasamu kayi kuwa? Kasan mutanen daga Ghana zasu zo yau akoi board meeting da za’ayi by 4:00PM zamu masu presenting.”

      “Eh Baba nayi yana nan ajiye cikin shelf a store room floor 2.”

      “Good, se meeting d’in zanbar care d’in a hannunka. Akoi inda ake samun professional waiters a Fahmaz coffee shop (inda Fannah ke aiki) kayi waya da masu wajen kamana booking.
   
    “Okay Baba, I’ll be going” nan ya zarce office nasa inda ya kira number’n me Fahmaz coffee shop d’in.

    *****
     “Ya Suleiman ga call from Flames Enterprises.” Fannah ta danna kira wa Ya Suleiman dake waje. “Ki d’aga kiji meneh, I'm busy here.” Hannu tasa ta d’aga tare da yin shiru bata ce komai ba. “Hello?” Anas ya fad'i cikin muryarsa me tafiya wa kowace mace da imani. “Hello” Fannah ta fad’i in return. This is Fahmaz Coffee shop, how can I assist you?”

      Jin muryar mace ne yasa ransa ya b’aci take. A fusace yace, “ai nasan Fahmaz Coffee shop d’inne saisa na kira so just shut up plus haka aka koya miki wajen aikin naku in kun d’au waya kuyi shiru?”

         “Lalle ma wannan mutum anyi d’an iska” cewar Fannah a zuci “shi ya kira kuma yana jiran nice in soma yin magana?” Dukda bame san magana bace amman taji barata iya hak’ura ba so take ta sa koma waye ne shi in his rightful position sekuma ta tuna wannan business related matter ne she shouldn’t take it personal.

       “I'm sorry. How can I assist you?”
    “Mstchww” yaja tsuka sannan ya cigaba “we need 5 waitresses and 5 waiters from your coffee shop here at Flames Enterprises by 4:00PM.”

     “Okay copied” tace.
        “Bama tolerating late coming you guys should make sure 4 d’in ya muku anan.”
       “Lalle ma wannan mutumin” cewar Fannah a zuci.

        “Ko baki ji bane?” Zatayi magana ya katse dagangan.  Ciro telephone d’in tayi daga kunnenta tana kallon wayar cike da namaki wannan wani irin bawan Allah ne me uban jijji dakai haka? Mstcw taja tsaki daidai lokacin Asma’u ta shigo “yau Fannah ke tsaki? Keda waye ne haka?” Ta bud’e baki zatayi magana Flames Enterprises d’in yasake kira sanda ya kusan tsinkewa sannan ta d’aga “yes.”

       “Don’t use that tongue with me young lady” cewar Anas in a serious tone daya tsorata Fannah kum tayi shiru. “Incase clueless mind naki be baki idea ba, you have to be here now saboda coffee zakuyi serving ba drinks ba. So zakizo in baki details d’in plus don’t be late bana jiran mutum sede a jirani.” Shiru tayi tana mamakin wannan bawan Allah. “Are you there? Cause bana repaeating kaina twice”

        “Yes I’ll be on my way.” Nan ya katse wayar. Tsuka takuma ja “lallai akoi arrogant people dayawa a duniya what is he feeling like? D’an Adam de ba wanda yafi wani we are all equal.” Asma’u dake kallonta tace, “ji yadda kike magana sekace bakisan Anas ba.”

     Fannah tace, “Anas? Waye shi?”
     Asma’u tace, “no wonder sesa kike tada jijiyoyin wuyanki haka, ni rananda ya kira na d’aga bakiga zagin duniyan daya min ba aike yamiki mutunci ma.”
     “Toh waye shi? Whats he feeling like?”
      “Shine PA’n Mr. Muh’d na Flames Enterprises kuma ance Mr. Muh’d nasan sa tamkar d’an cikin daya haifa, cewa ma yake Anas d’in d’ansa ne.”
     “Ikon Allah! Lallai kam.” cewar Fannah cike da mamaki.
     “You better go kafin yasake kira ya balbale ki.” A sanyaye Fannah ta fice bata tsaya ko inaba se Flames Enterprises can akayi directing nata zuwa office na Anas tsaye take a bakin k’ofar office nasan takasa shiga zuciyarta se bugawa take musamman ma data d’aga kai taga ansa *Mr. Fauzy* asaman. Tafi minti biyu tsaye a wajen sannan jiki na k’yarma hannu na b’ari tayi knocking k’walli d’aya tal jin ba’a amsa ba yasa ta k’ara d’aya “come in” taji muryan na miji ya fad’i authoritatively. Tabbas tasan wannan murya shine wanda yace mata thank you rananda Mr. Muh’d ya bata bandir na N500 kawai haka taji zuciyarta na bugawa tarasa dalili.

     Numafashi taja sosai sannan ta bud’e tashiga. Wannan office shi ake kira da Aljannan duniya tana shiga k’amshin turare ya buga mata hanci ga wani uban sanyin da office d’in ya d’auka ko ina tsatsaf yake files, papers da books duk anyi arranging nasu. Hijabinta iya guiwa takuma daidaita sa sannan tayi sallama.

     “Salamu alaikum” mutum ta hango kan kujera da P cap (facing cap) akansa wanda ya b’oye kamanninsa. Sanye yake da black long sleeve shirt wanda ya mugun amshe farar fatarsa me kyawun gaske. Yanada fad’i dadai, na matashi ne me jini a jik’a. Laptop ne a gabansa se faman danne danne yake akai he is si focused akai, can yad’an tsaya ya sha wani abu cikin cup wanda Fannah batasan ko ruwa ne ko juice ba can ne tagane ashe soda ne.

           “Zaki iya dena kallo na haka dan ba TV bane ni, and you don’t knock and say Salamu alaikum all at thesame time you choose either one.” Ya fad’i batare da ya d’aga ido yaga kowaye bane. Kunya taji kamar ta nitse k’asa dan kunya “taya yasan ina kallonsa toh?” Ta tanbayi kanta a zuci. “I'm sorry” ta fad’i cikin muryar ta dake b’ari.

     *I'm sorry nasan chapter’n nan yayi gajere sosai compared to other chapters d’in bayan nawa ne har yanzu na ciwo. In shaa Allah zan yi k’ok’ari inyi dayawa gobe. Thank you for the lovely prayers and warm concern. I love you all*

No comments: