BY MIEMIEBEE
“Malam baran iya shiga ganin Fannah ba, if only zan iya bata raina wallahi zanyi.”
“Addu’a zamu mata Maman Aiman kinsan dole ke zaki kwana da ita.”
“Yanzu Malam kud’in asibitin fa? Taya zamu biya? Wallahi duk d’an iskan da yama Fannah wannan abu be kyauta ba.” Ta kuma fashewa da kuka hak’uri Baba ke ta bata. “Karki damu da wannan, zan sayar da shanu na in shaa Allah zamu biya bills nata dashi, fatan mu Allah bata lafiya”
“Shikenan yanzu dama shanun nan kad’ai muka mallaka, Allah ya isa wallahi.” A sanyaye suka mik’e zuwa d’akin Fannah, Baba na bud’e k’ofa suka hango Fannah kwance kan gado ba alaman nishi a tattare da ita.
Da gudu Mami tayi kanta ta tsuguna tare da rik’o hannunta se kuka take zubawa. “Maman Aiman addu’a zamu mata kuka baida amfani barin koma gida in d’ibo muku abubuwan da zaku buk’ata, kiyi hak’uri” ahaka ya fice isarsa keda wuya ya tarar da Afrah se safa da marwah take a parlour tana ganinsa tayo kansa. “Baba ya kun sami Ya Fannah?” Kallon daya mata yasa jikinta yayi sanyi take idanunta suka cike da hawaye “Baba dan Allah meya sami Ya Fannah?” ta tambaya tana kuka.
“Afrah da rungumar k’addara aka san musulmi, mun samu Fannah amman yanzu haka tana asibiti.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Baba me kake nufi? Meya samu Ya Fannah?”
“Bata da lafiya Afrah, mun... Mun...” Sekuma yayi shiru hawaye na cika a idanunsa sakamakon hakan ya sake tada ma Afrah hankali. Tana kuka tace, “Baba dan Allah ka fad’a min meya samu Ya Afrah.” Zaunar da ita yayi ya bata labarin komai kuka Afrah keyi sosai kamar zata cire ranta sam tace seta bisa asibitin taga yarta.
Ba yadda Baba beyi ba dan hanata amman ta dage setaje. Aiman kuwa ta jima da bacci, bayan sun gama had’a abubuwan da zasu buk’ata Baba ya rakata ya tsara mata abin hawa sanda suka b’ace ya dawo ciki. Tafiyar minti 15 ya isar da Afrah asibitin, bayan ta biya sa kud’insa tashigo ciki direct d’akin Fannah ta wuce.
Tana bud’o k’ofar taga Mami tsugune gefen Fannah se kuka takeyi take itama wani kukan ya faso mata da gudu taje ta rungumi Mamninsu suna kuka sosai. Sunjima suna abu d’aya sannan Mami ta tambayeta “Afrah me kkeyi anan ina Babanku?”
“Mami yana gida na zo ne in tayaki kwana.”
“Afrah bekamata kiga yarki a wannan yanayi ba da kin koma gida.”
“Haba Mami! Ya Fannah fa yayata ce taya zakice haka?” Nan ta jiyo tana kallon Fannah wacce take kamar gawa. Wani sabon kukan tasoma ta rungumeta, tana kuka “Ya Fannah dan Allah karki mutu ki barmu, Allah ze sak’a miki in shaa Allah.” Da kyar Mami ta lalasheta tayi shiru.
Mami ko kayan tean da Afrah ta had’o musu susha tea ma takasa sha hankalinta duk yabi ya tashi. Afrah bata tab’a ganin Maminsu cikin tashin hankali irin wannan ba.
Kwana Mami tayi tana nafilfilu tana rok’an Allah haka itama Afrah bawanda yayi bacci cikinsu.
****
Washegary da safe misalin k’arfe 8:00AM babban likita daga TH na Maiduguri ya iso. Aikin kusan awa uku akayi kan Fannah sannan likitan yafito. Baba, Mami, Afrah da Aiman dake rik’e a hannun Afrah duk sukayi kansa “likita ya jikin ‘yar tawa?” Cewar Mami jikinta se b’ari yake.
“Ku kwantar da hankalinku in shaa Allah ‘yarku zata samu sauk’i tana cikin state of coma ne yanzu within 5-7 days in shaa Allah zata farfad’o.”
“Alhamdulillah!” kukeji a wajen. “Likita amman har kwana biyar? Kana nufin barata san inda take ba har nan da tsawon kwana biyar ko bakwai?”
“Eh Hajiya, she've been through alot, raping at this tender age ba k’aramin abu bane, tamugun jin jiki, gakuma ruwan daya mata duka again yasa ta kamu da pneaumonia but in shaa Allah inta farfad’o everything will be alright za’a bata magani karku damu.”
“Toh likita mungode sosai Allah biya.”
“Ba komai” ya fad’i sannan ya fice.
A hankali Umma ta soma kuka “Malam yanzu har kwana biyar ko sati ‘yata zatayi batasan inda take ba? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
“Maman Aiman godiya yakamata muyi tunda Allah yabar mana ita be karb’i abinsa ba, mu cigaba da addu’a in shaa Allah zata samu sauk’i.”
*ANAS*
_Bawan Allah dan Allah kayi hak’uri kar ka lalata min future, wallahi baran iya baka abinda kake nema ba I'm just 15 dan Allah karka lalata ni kayi hak’uri ka rufa min asiri_
Firgit Anas ya farka daga bacci yana numfashi da k’arfi sosai wanda hakan yasa Shettima tashi shima daga bacci tun jiya yaga yanayin wansa ya canza koda ya tambayesa meh kuwa ce masa yake ba komai, wannan karan ne na farko da Anas ya soma b’oye masa abu. Gadonsa ya bari yaje yasamu Anas tare da dafe kafad’arsa. “Anas lafiya? Ka jima fa bakai mafarkin Ummimi ba, meya faru kuma yau?”
“Ba mafarkin Ummimi nayi ba.” cewar Anas yana raba ido.
“Mafarkin me kayi toh?”
“I don't want to talk about it karka damu its okay.” Anas yayi k’ok’arin calming kansa.
“Its not okay Anas, tun jiya nake lura da kai, something is bothering you and you’re keeping it to yourself. Tell me.”
“Nace maka ba komai” Anas yayi insisting. A hankali ya mik’e ya wuce bayi. Tun shigarsa bayin ba abinda yakeyi se tunanin mafarkin dayayi akan yarinyar jiya, ko kad’an besamu yaga fuskarta ba a mafarkin. Ruwa ya riga watsa wa a kansa sannan yayi wanka yafito ya shirya kayakinsa da komai dake yau ze tafi Maiduguri, gobe ya wuce Abuja daga can kuma se London.
Yana fitowa daga d’akin nasu ya rufo k’ofar yana juyawa sega Amal idanunta sunyi ja “my Angel waya tab’aki?”
“Ya Anas wai yau zaka tafi baraka sake dawowa ba se nan da 5 years?”
“Waya fad’a miki haka?” Ya fad’a yana wasa da gashin kanta.
“Ya Shettima ne kuma wai kana barin gidan nan ze dakeni wai dama tarani yake, Ya Anas dan Allah kar ka tafi” ta rungumesa da tsayinta daidai kunkuminsa. Sama ya d'agata “stop crying kinji Angel? very soon zan dawo kuma duk sanda Shettima ya tab’aki ki d’au wayan Ummie ki kirani I promise in na dawo zamu rufesa a d’aki mumasa dukan tsiya.”
“Dagaske Ya Anas? Zamu masa duka?”
“Sosai ma bulala zan baki ki zanesa se yayi kuka.”
“Yeyyy!” Hugging nasa tayi “I love you Ya Anas.” “I love you too Angel. Sauk’o to muje wajen Abuu.”
“O’o ni muje a haka ka d’aukeni for the last time.” “Okay Angel” ya manna mata kiss a goshi sannan yaja akwatinsa suka fice. Suna isa parlour ya sauk’eta tare da gaishe da Abuu sannan Ummie.
Breakfast suka ci bayan sungama Abuu ya zaunar da Anas.
“Anas kaga karatu zakajeyi ba hutu ba kuma kafi kowa sanin wahalar da mukayi kafin muka samo maka wannan scholarship I'll be very angry inhar baka je kacika mana burinka na zama architecture ba.”
“In shaa Allah Abuu” cewar Anas dake kallon kan carpet.
“Kasani kuma duk abinda kakeyi Allah na kallonka, kowa yasan ya rayuwar London yake, inbanda iskanci ba abinda sukeyi, ba ruwanka da zuwa beach bale kaje kaga abinda ze hana ka d’aukan karatu. Qur’ani shine guidance naka, karka kuskura kabari rana ya wuce ka baka d’au Qur’ani ka karanta ba. Ba ruwanka da ‘yan mata ko friends na banza. Ba ruwanka da shaye-shaye Anas. Kajini ko bakaji ba?” ya gargad’i Anas tare da rik’e kunnensa.
“Naji Abuu na gode in shaa Allah zan kiyaye duk wannan abubuwan daka lisafo, nagode.”
“Toh Baba na nikam nasan ko ban ja maka kunne ba kasan what is right and wrong, ban tab’a doubting tarbiyarka ba. Allah baka sa’a ya kareka daga kowani irin sharri Baba na.” Cewar Ummie.
“Ameen Ummie nagode.”
****
“Amal kukan me ne kuma haka sekace mutuwa yayan naki zeyi? Makaranta fa zasa in shaa Allah ze dawo.” Cewar Ummie tana lalashin Amal dake ta kuka.
“Bar shakwab’a de Ummie ke kike biye mata ma ai, tayi kukan jini tagadama ta mutu.” Shettima ya fad’i yana ma Amal dariyan mugunta. Harara ta watsa masa me rai da lafiya “toh nak’i kukan” tasa hannu ta share hawayerta “kaine zaka mutu mugu kawai.”
“Ke! Rashin kunya kike min?” Ya mik’a hannu ze finciko ta daga jikin Ummie, hannu Ummie tasa ta make hannun nasa da k’arfi “okay dan Amas yatafi zaka soma cin zalin Amal ko? Toh kasani Anas yace duk sanda ka tab’a ta in kira sa a waya in fad’a masa dan haka ka mayar da hankalinka. Kai kullum kata biye wa ‘yar yarinya duk kabi kasa ta raina ka.”
Gwalo Amal tamasa harda sa hannu kan kunnenta. “Ni shikenan Ummie kullum ma wannan maras kunyan zaku na ba wa gaskiya wallahi kicigaba Allah kawo rananda za’a barni dake gidan nan.” ya cize yatsa.
“Karki kula sa Amal taho muje mu siya miki sweet ga kud’i nan dayawa Anas ya ajiye miki.” Juyawa tayi tasake ma Shettima gwalo sannan suka fice da Ummie.
*****
Da misalin k’arfe 1:00pm Ummie ta kira wayar Anas ringing kad’an yayi ya d’aga “hello Ummie” yafad’a cikin muryarsa me dad’in gaske.
“Baba na ya gajiyan hanya?”
“Alhamdulillah Ummie tun d’azu muka iso ai, ina gidan chairman ahaka.”
“Toh yayi kyau, Babana kaji abinda Abuu ya fad’a maka ai? Nasan kanada hankali kuma kasan abinda ya kamata kar kayi abinda ze haddisa mana matsala kaji ko Babana?”
“In shaa Allah Ummie karki damu, ina Angel d’ina?” “Tana parlour tana kallo barin kai mata.” Nan ta mik’e takai wa Amal “ga Ya Anas nasan yanason ku gaisa.”
“Ya Anas ina wuni?”
“My angel ya kike?”
“Lafiya, har kun isa London d’inne?”
Murmushi kad’an yayi wanda hakan yasake bayyano da kyansa. “A’a Angel da saura sosai ina Maiduguri ne yanzu se gobe zamu wuce London.”
“Okay! Nagane. Ya Anas kaga d’azu Ya Shettima ya nank’washeni akai dan yaga baka nan.”
“Shettiman? Bari ki riga irgamin duk mugunta daya miki ina dawowa zamu masa duka.”
“Yeyy! Ya Anas I love you ina kallon frozen se anjima.”
“Yawwa Angel d’ina bo-bye.”
*FANNAH*
_6 days later..._
“Mami kukan ya isa mana dan Allah, ki dubi yadda kika rame dan Allah.” Cewar Afrah dake rik’e da Mami itama tana hawaye.
“Afrah kiyi hak’uri ba san ra’ayi na bane nima, yau kwanan ‘yar uwarki shida bata san inda take ba taya baranyi kuka ba. Gani nake kamar zata tafi tabarmu. Allah ya isa, haka kawai Fannah bata masa komai ba ya zab’i ya wulak’an ta ta. Allah ze sak’a mata.”
“Shhh Mami dan Allah karkiyi magana haka, in shaa Allah Ya Fannah zata farfad’o lets not lose hope Mami.”
***
Da azahar misalin k’arfe 1:30PM wani dattijo yashigo cikin asibitin, kallo d’aya za’a masa asan wan Baban su Fannah ne. Zekai shekaru irin 50 a duniya. Baba dake zaune a bakin k’ofar d’akin Fannah ne ya hango wan nasa nan ya mik’e “sannu da zuwa Ya Khaleel.”
“Sannu dazuwa fa kace? Ashe iskancin da ‘yarkan tayi kenan shine ka b’oye min kak’i gaya mun, toh Allah ya sanar dani gaskia.”
“Haba ya Khaleel ya kake magana haka? Kafi kowa fa sanin halin Fannah ba halinta bane tarayya da d’a na miji.”
“Mstww seka gayawa iska ai. Baga erinta ba kullum in na maka magana kan ka hana yarinyan nan ganin samari me kake fad’i? Cemin kake aure zaka mata ba ga erinshi ba, d’aya daga cikin samarukan nata ya mata fyad’e.” Daidai lokacin Ahmad saurayin Fannah da mahaifinsa suka shigowa.
“Alhj khaleel me kake cewa?” Cewar mahaifin Ahmad a rud’e.
“Ai kajini Alhj Suleiman. ‘yar k’anina Fannah ce, saurayi ya mata fyad’e gata can kwance a gadon asibiti yau kwana shida bata san inda take ba.”
“What!?” Alhj Suleiman ya daka tsawa. “Malam Aliyu shin abinda wan ka ke fad’i gaskiya ne? Abinda ya faru kena! kace mana wani ne ya mata fiad’e?”
Kwata kwata Baba ya kasa magana ya rasa me yayi ma wan sa Ya Khaleel a duniya ya tsanesa da family’nsa haka. Abin nasa tun daga hassada ya soma tun sanda Fannah ta sauk’e Qur’ani bayan ga d’ansa Farouq dakeda shekaru 22 ko izu biyu be haddace ba. Tun daga lokacin ya d’au tsanan duniya ya d’aura wa Fannah.
“Aww bakaji me nace ba kenan?” cewar Ya Khaleel. “Da zaka sake tambayarsa kome yasamu ‘yar iskar ‘yar nasa.”
“Abba wallahi nasan komin yaya Fannah bara tayi abinda Alhj Khaleel ke fad’a ba.”
“Rufa min baki! Yaro dakai me kasani? Ai gashi baban nata ya kasa k’aryata zancen. Gaskia I'm very disappointed in you Malam Aliyu, na yarda da kai da ‘yarka taya zaku min haka nida d’a na?”
“Abba dan Allah kyi hak’uri mujira Baba yayi explaining. Wallahi nasan Fannah yarinya ce me tarbiyya barata aikata abinda ake accusing nata kai ba.”
“Amman fa yaron nan baka da hankali.” Cewar Ya khaleel. “Kana nufin kafini san ‘yar tawa ne? In gaskiya tazo dole a fad’e ta.”
“A’a barsa Alhj Khaleel I've heard enough. Ahmad taho mu wuce I can’t take this anymore. Gara da Alah ya bayyana mana halinta tun kafin ka aureta.”
“Abba dan All-”
“Rufa min baki! me zakayi da yarinya me bin maza? Ina kanajin abinda baban nata yace? Saurayi ne ya mata fiad’e ko har yanzu so kake kacemin kanasan auranta?”
“Ya isa!” Baba ya daka tsawa. “Kafad’i duk abinda zaka fad’a amman kar ka kuskura kasake kirar ‘yata da sunan me bin maza saboda ko kad’an ba halinta bane. In banda d’anka Ahmad, Fannah bata san wani d’a na miji ba.” Ze k’ara magana Ya Khaleel ya katse sa.
“Awww! yanzu kuma so kake kace Ahmad ne ya mata fiad’en kenan?”
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment