TANA TARE DA NI... PAGE 04
BY MIEMIEBEE
Cikin kuka tace, “dan girman Allah bawan Allah kayi hak’uri I beg of you please.” Jikinta se rawa yake tana hawaye. “Bawan Allah dan Allah kayi hak’uri I'm just 15 ba abinda zan iya baka have mercy on me please dan Allah.” Ko k’adan be saurareta ba hijabin jikinta yasoma k’ok’arin cirewa. “Wayyo Allah Mami na! Baba! dan Allah kuzo ku taimakeni! ihu take sosai.”
Hannu yasa ya rufe bakinta. “Duk mata haka kuke, mesa zanji tausayinki? Data gudu tabarmu ta tausaya mana neh? Why will I have mercy on you? I hope you tell her abinda zan miki yanzu saboda itama ta d’and’ana little daga cikin bak’in cikin data sanyamu time da ta tafi ta barmu” Yana d’aga hannu daga bakin nata ya yaga hijabin nata into two. Ihu ta sake sakarwa “bawan Allah dan Allah kayi hak’uri karka lalatani dan girman Allah, kaji tausayi na I'm just 15 years dan Allah ka rufa min asiri karka b’ata min future”
“Data tafi ita taji tausayin mu ne?”
A rikice bakin ta na rawa tace, “ww..wa ce? Ni bansan wacce kake fad’a ba bawan Allah ban tab’a ganinka ba seyau kayi hak’uri dan Allah, karka lalata ni.” Be saurareta ba ya yaga kayanta. Nan ta shiga tare k’irjinta kuka sosai Fannah takeyi tana rok’an wannan bawan Allah'n haka ba tausayi ba inani yayi raping (fyad’e) nata.
Tun tana iya jure zafin har ta sume wajen, kaca-kaca yayi da ita sannan ya fice yabarta ruwan sama ma dukan sumemmiyar jikinta. Shi kansa besan ya akayi ya isa gida ba a daren, kawai ganin kansa yayi bisa kan gado.
A hankali ya bud’e blue eyes nasa wansa Shettima yagani a kansa. Tunanin meya faru yakuma yake nan ya soma lokacin da aka soma ruwa yace dasu Baana ze tafi sukayi k’ok’arin hanasa amman ya k’i jinsu ya hau tafiya can cikin wata lungu.. Wata lungu... Daga.. Can kwata kwata seya kasa tuna meya sake faruwa.
“Anas how are you feeling? Sanda na fad’a maka karka bi su Baana kak’i kasan yadda ruwan saman nan yamaka duka kuwa? In akayi wasa seka kamu da mura.” cewar Shettima fuskarsa a d’aure
“Ina Abuu?” Anas ya tambaya. “Ka gode wa Allah be ganka ba sanda nashigo dakai nan. Anas fisabilillahi mesa baraka rungumi k’addara ka manta da zancen Ummimi (mahaifiyarsu) a rayauwarka ka yafe mata ba? You're blaming yourself for her mistakes, misleading your life in the process. Haba mana Anas. Saboda Ummimi kasoma shaye shaye me haka please? Yanzu saboda ita ka kusan kashe kanka, abinda tayi ya riga ya wuce se mu rungumi k’addara mu barta da halin ta.”
“No Shettima I can never do that, tariga ta juya min rayuwa, my life can never be normal kamar yadda kakeso, I can never move on barni haka kawai inta misleading rayuwar nawa har zuwa sanda zan mutu. Images of yadda ta tafi ta barmu will never leave my head, they are stuck in it forver”
“Anas wai kai mesa bakajin magana ne ko dan ni k’aninka ne kafisan babba ya maka magana? Bari Abuu ya dawo I think is about time yasan gaskia shima, I've been keeping your secret for how many years now? A ganina with time zaka mance komai amman tunda you are not ready to change, tunda baka iya rungumar k’addara ba zan fad’a wa Abuu komi idan ya dawo.”
Sede daya juyo ya kalli Anas yaga ko k’adan ma hankalin sa ba a gunsa yake ba, yayi nisa cikin duniyar tunani.
“Anas?” Ya kira sunansa. Shiru Anas yayi be amsa ba dan haka ya d’an jijjik’a sa. “Yarinyar...” Anas yace fuskarsa cike da damuwa. Se yanzu ya tuna yaga wata yarinya acikin lungun. Amma sam ya kasa tuna ya fuskarta take ko fara ce ko bak’a ko kyakkyawa ko munana, ko doguwa ko gajeriya shide yasan yaga yarinya cikin lungun.
“Wata yarinya kuma Anas? Yau kai ke kirar mace cikin gidan nan?”
“Yarinyar Shettima ina take?”
“Wai wace yarinya Anas, me kake fad’i?” Shettima ya fad’i fuskarsa cike da mamaki
“Yarinyar Shettima, ina take? Ina ka tsince ni?” Cewar Anas.
“Can gaba da gidan gona and also meya sami kayanka duk jini na duba ka banga ciwo ba.”
“Jini fa kace? Ina kayan nawa?” Anas ya fad’a a rikice.
“Na wanke already.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Abinda Anas keta nanatawa kenan duk yasa Shettima kid’imewa.
“Wai meke faruwa ne Anas? Wani abu ne?” “A’a nothing thanks please in baraka damu ba I want to be alone in d’an huta thanks.” Shettima na fita Anas ya rufe ido so yake ya tuna fuskar wannan yarinya amman ya kasa, “ina take? Mena mata? Mesa Shettima yace yaga jini ajikin kayana. Oh no! Nayi blaming yarinyar da batasan komi ba akan laifin da Ummimi tayi. Oh no! Nayi raping d’inta subhanallah shikenan nazama mazinaci, Ummimi baran tab’a yafe miki ba abinda kika min, kin cuceni” Dakyar bacci yayi gaba dashi...
****
FANNAH
“Malam wallahi aiken maggi nan shagon bakin titi nace taje mun kuma har yanzu bata dawo ba, wayyo Allah inaji a jikina abu yasamu Fannah tah.”
“Maman Aiman ki kwantar da hankalinki Fanmah yarinya ce me hankali tasan abinda takeyi barata tab’ayin abinda zesa mu cikin damuwa ba.”
“Abin da nake nufi kenan Malam” Mami ta fad’a cike da tashin hankali.
“Fannah bara ta tab’a yin abinda ze samu cikin damuwa ba saidai in za’a tilasta mata.”
“Me kike nufi kenan Maman Aiman?”
“Malam wallahi ji nake a jikina Fannah ba lafiya ba wayyo Allah tun kafin Maghrib fa na aiketa yanzu har Isha bata dawo ba, Allah ba lafiya ba nashiga uku!”
“Maman Aiman ki kwantar da hankalinki yanzu d’auko hijabinki ga lema anan muje mu duba nan mak’ota ko halan tashiga tana jiran ruwan saman ya d’an saurara.” Nan ta d’auko hijabi sunzo fita kenan Aiman ta fito daga d’aki “Mami ina zakuje?”
Idan Mami cike da hawaye tace, “nemo Ya Fannah zamuyi Aiman, bata dawo gida ba tun d’azu” daidai lokacin Afrah ma tafito “zan biku Mami.” tace idanta cike da hawaye tunda take bata tab’a shiga tashin hankali kamar na yau. Fannah ba mutumiyar yawo bace, ba inda take zuwa banda boko tunda ta kammala haddan Al~Qur’aninta. Dole ne wani abu yasameta a hanya, fatansu Allah sa ba sharri bane.
“A’a Afrah ki zauna da Aiman a gida in shaa Allah yanzu zamu dawo.”
“Mami what if something bad ya samu Ya Fannah fa? Please kibarni inje” tafad’a hawaye na tsiyaya a idanunta cike da tausayi da tsoro.
“In shaa Allah ba abinda ze sameta” cewar Baba “ku zauna yanzu zamu dawo.” “Toh Allah kare” Afrah tace. “Ameen” Mami da Baba suka amsa a tare sannan suka fice cikin ruwan sama. Aiman ce ta rik’o hannun Afrah, “Ya Afrah me ze samu Ya Fannah?”
Murmushin dole ta k’irk’iro “in shaa Allah ba komai karki damu kinji? Ya Fannah will be alright.”
***
“Malam suka ce Fannah bata shigo nan ba innalillahi malam dan Allah ina zataje? Ina aka kaimin ‘yata?!”
“Maman Aiman panicking is never a solution kizo mu dudduba kusa ko zamu ganta cikin shagu nan bakin titi” Haka fa iyayen Fannah suka ta duba sak’o sak’on unguwar tasu ba Fannah ba alamarta har sun fidda rai se Mami ta tuna shagon dake gaba da wata lungu a sabuwar unguwa tace suje su duba, sunayin wajen kuwa sega Fannah kwance a k’asa half naked ruwan sama yamata tsinannen duka ko numfashi battayi.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!” kawai ke tashi gun both Baba da Mami were shocked hawaye gangara suke daga kumatunsu suna kallon yadda aka walak’antar masu ‘yarsu. Mutuwan tsaye Mami tayi Baba ne yayi k’arfin hali yaja zanin ta dake gefenta ya rufe mata jikinta dashi tare da rungumota yana kiran sunanta sam bata amsa ba dake ko numfashi battayi. Alokacin Mami ta sakar dawata erin k’ara
“FANNAAAHHHHH!!! WAYYO ALLAH!” Da gudu tayo kansu tare da jefar da leman ta karb’e Fannah tareda rungumota tana kiran sunanta “FANNAH! FANNAH! Dan Allah karki tafi kibarmu dan Allah kitashi wayyo Allah!” Kuka kenan!
Mota Baba yasamu da k’yar aka sa Fannah ciki suka wuce babban asibitin dake hukumar Bama. Nan take akayi emergency da ita sam Mami ta kasa daina kuka shikansa Abba kuka yakeyi duk yadda yayi ya hana kan sa kuka ya kasa. Hannun Mami ya rik’e yana bata hak’uri tana kuka tace, “mesa Malam? Mesa se Fannah ta za'ai wa haka? Hankalinta yayi yawa ace an mata wannan tsiya. Malam shikenan an rusa wa ‘yata future Allah ya isa ma duk wanda ya mata wannan d’anyen aiki barin tab’a yafe wa ba...” ta fashe cikin wata erin matsanancin kuka.
Rungumota Baba yayi yana bata hak’uri shima yana kukan. “Nima kaina abinda ke d’aure min kai kenan, wani azzalimi ne kawai yayi taking advantage na innocence nata saboda Fannah bawai tana mu’amala bane da maza bale ace saurayi ne yamata wannan abu, Ahmad ne kawai ke zuwa wajenta kuma nasan Ahmad bare tab’a aikata mumunar abu kamar haka ba.”
****
_3 hours later_
K’ofar d’akin da Fannah ke ciki ya bud’u likita ya bayyana daga bayansa. Da sauri su Mami suka taresa. “Ya ‘yar tamu likita ya jikin nata?” cewar Mami da Baba a tare. Kai ya k’ada a hankali fuskarsa cike da tausayi. “Likita dan Allah karka fad’a min ta rasu, dan girman Allah” Mami ta fashe da kuka Baba yana bata hak’uri.
“Iyayen Fannah kuyi hak’uri amman munyi duk iya abinda zamu iya dan ceto ran ‘yarku, mun kasa, ya gagare mu, mun kasa at all ruwan saman ya mata duka sosai har na fitan hankali, yabi ta kunnenta da hanci har baki, bayan haka kuma ga raping nata da akayi wanda aka mugun ji mata ciwo. Zafin datayi witnessing yafi k’arfin jikinta yafi k’arfin shekarunta. Yarinya ce sosai. Kuyi hak’uri dan Allah amman kar kuyi losing hope anyi waya dawani likita daga Maiduguri Teaching Hospital gobe da sassafe ze iso ya dubata inhar da abinda ze iya toh se mu godewa Allah.”
Mami dake kuka kamar zata cire ranta tayi k’arfin halin fad’in “likita me kake nufi kenan? har yanzu ban fahimce ka ba ‘yar tawan tana raye ne kokuwa ta mutu?”
“Maman Fannah ni kaina banda amsar wannan tambaya zuciyarta na bugawa yana aiki amman kuma bata numfashi, mun samata oxygen munyi komi still ba progress, kwata kwata bata responding to stimuli.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Malam sun kashe min ‘ya shikenan Fannah ta tafi ta barni, ta barmu Malam” takuma fashewa da wata masifaffiyar kuka Baba na bata hak’uri, shikansa hawaye yake zubdawa shar shar.
“Baban Fannah ‘yarku bata gama mutuwa ba tunda tana numfashi, duk me numfashi aikuwa nada rai kenan. Addu’a kawai zaku sata ciki sosai, Allah sa tayi making it through the night in shaa Allah in gobe likitan yazo seya duba ta. Allah bata lafiya ya k’ara maku hak’uri. Excuse me please.” Nan ya fice. Har k’asa Mami ta sauk’a tana kuka.
In ta rasa Fannah ta rasa komai a duniya cikin yaranta uku ba wacce takai Fannah hankali, ‘yar da zaka aiketa sau d’ari a rana barata b’ata rai ba bara kuma tayi fushi ba. ‘yar da kana ce mata bari ta bari kace yi kuma tayi. ‘yar da is ready to sacrfice the last kobo she have just to make her parents happy. Barata iya rayuwa ba Fannah ba. If only zata iya bada ranta asawa Fannah da tayi.
Kuka take sosai, abin tausayi, tanayi Baba nayi tabbas shima kap cikin ‘ya‘yan sa babu kamar Fannah. Kalmar son kai ko k’adan Fannah bata sani ba, she can give up her own happiness for others...
*©miemiebee*
No comments:
Post a Comment