Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 13
BY MIEMIEBEE

_washegari..._
      Kasancewar yau Asabar bayan Anas yayi wanka yayi breakfast yayi shirinsa na kullum T shirt da pencil trousers ya feffeshe da turare tare da taje gashin kansa yayi styling nasa me kyau sannan ya rataya jakar laptop nasa da credentials nasa ke ciki. D’an fita ganin gari zeyi tunda Monday ze koma Bama.

      Tafiya yake cikin unguwar Old GRA yana d’an kalle-kalle yadda kowa yake aikin gabansa can yaga mutane sun taru gu d’aya se hayaniya ke tashi wajen, a hankali ya taka izuwa wajen shima dan ganin meke faruwa. Yawancin architects ne awajen seda masu construction kuma zane ne babba a gabansu se musu suke sun rasa gane ya zasu gudanar da aikin. Daga wata gefe kuwa wani dattijo ne zeyi erin shekaru 65 d’innan yayi tagumi ya zuba musu ido sunata shirmeh. Kallo d’aya Anas yayi wa zanen wajen ya gano zanen babban gini ne ko erin company ko industry haka. Daya sake kallo kuwa seya gano matsalar da suka samu wajen zanen murmushi yayi sannan yayi giaran murya “may I interrupt?” yace dasu.

     Tas kowa wajen ya juya yana kallonsa, wasu suna admiring kyansa wasu kuma mamakin blue eyes nasa suke kode bature ne? Amman kuma farin sa bekai na turawa ba toh fah. Na zaunen ne yace “sure please” tare da mik’a ma Anas paper’n. Dattijon kuwa har yanzu na zaune yana kallonsu. Amsar pencil da cleaner Anas yayi yad’an goge wani waje a zanen ya giara daga k’asa sannan yayi haka ma daga sama. Yana gamawa ya juya paper’n yana kallon babban nasu na zaunen bayan ya d’an kalla aikuwa sega abinda suke san sucire d’in yafito, building d’in is in perfect position. “Wow!” Yayi exclaiming “saurayi you are incredible! ku tafawa wa wannan saurayi please.”Nan take duk mutanen wajen suka d’iba da tafi suna hailing Anas.

     Dattijon dake zaunen ne ya taso da karar tafiyarsa irin na gayu me kan gwal d’innan ya iso wajen a hankali. Cikin muryar manyanta yace, “meke faruwa anan?” Babba na zaunen ne ya juya da paper’n yana nuna masa “gashi Mr Muh’d toilet da ake buk’ata a last floor d’in yafita building d’in is in perfect position yanzu.” Kai Mr Muh’d ya giad’a a hankali “good.” yace. Babba na zaunen ya cigaba da cewa “wani saurayi ne anan yanzu ya giara yana zuwa kawai ya amshi papern ya d’anyi goge goge kawai ya fitar he must be a genius. Ina kake ne?” Yana dubawa kuwa se ba Anas har ya juya ya cigaba da tafiyarsa.

         “You two” Mr Muh’d ya nuna yaran aikinsa guda biyu “ku bisa ku kira min shi.” A papare suka yi inda Anas yabi suna gudu suna binsa can suka gansa ya tsaida taxi ze shiga “hey! Hey! Bawan Allah ka tsaya” sam be jisu ba gashi basu san sunan saba. Can d’ayan yace, “me blue eyes!!!” da k’arfi cak Anas ya tsaya ya juya yana kallon inda yajiyo kiran. Bada jimawa ba suka iske sa. Hannu d’ayan ya mik’a masa suka gaisa. “Uhm I'm Kacallah wannan co-worker nane Yunus mune wanda kayi saving building drawing namu yanzu. Thank you”

         “Oh!” Anas yad’anyi murmushi, “that was nothing kar ku damu” ya juya ze shiga taxin. Yunus ya tsaida shi “erm dan Allah d’anyi hak’uri ka tsaya Boss na wajen aikin mu neh CEO’n Flames Enterprises babban company’n dake Maiduguri keson maka magana.”
       Zaro blue eyes nasa yayi “me?” Ya nuna kansa cike da mamaki.
      “Eh” Kacallah yace “you! You did what muka kasayi duka for that yanason ya maka godiya and am very sure zeyi honouring naka saboda Mr Muh’d mutum ne me kirki.”
     “Okay” Anas yace... Har yanzu ji yake kamar a mafarki wai CEO’n Flames Enteeprises keson masa godiya, sosai yasan Enterprise d’in kullum cikin NEWS se anyi maganan enterprise d’in yadda suke successful. Shi koda yake neman aiki ma be lek’a can ba a tunaninsa ma barasu kallesa ba bale su d’auke sa.

     Kacallah ne ya katse masa tunani, “blue eyes baka ce komai ba.”
     D’an murmushi Anas yayi “you can call me Anas, suna na Anas.” Kacallah yace, “wow suna me dad’i but still I prefer blue eyes sorry to ask muslimi ne kai?”
       Kallonsa Anas ya tsaya yi _daman ina kama da christians ne?_ Ya tambayi kansa.
      Ganin Anas be amsa saba yasa ya giara zancen nasa “uhm don’t feel offended please bawai kamin kalan arne bane kawai your eyes...” ya nuna idanun Anas da yatsa “nad’au bature ne kai.”
      Sosai Anas yayi mrmushi, “toh ai ban kaisu fari ba” yace.
          “Eh nasani ko irin black Americans d’innan ne kai.”
         “To ka kwantar da hankalinka ni nan da kake gani na kanuri ne daga Bama dangi na kap ba christian.”
       “Ohhhh!” Kacallah da Yunus suka fad’i a tare suna giad’a kai. “Ikon Allah!” cewar Yunus. “Kanuri amman zallah? Baka had’a dawani yare ba?”
      Toh fa an tab’o gogan namu, ya washi yakira yaren Ummimi amman ya ya iya dasu? dole ya fad’a musu ko zasu bar kallon da suke masa.

          “Mahaif-” se zece mahaifiya ta seya gagara dan koda wasa baisan kiran Ummimi dasunan mahaifiyarsa shi Ummie yasani mamansa ba Ummimi ba. Ganin sun zura masa ido yasa kawai yace, “mahaifiyata shuwa arab ce, mahiafina ne kanurin.”
 
      “Aihoooo aiko da alama” cewar Kacallah “sesa kake da kyau haka, masha Allah. Toh blue eyes muje Boss namu nasan ganinka.” Sallamar me taxi d’in yayi sannan ya bisu har gaban Mr Muh’d suka kaisa. “Mr Muh’d gashi nan” suna fad’in haka suka ja da baya duk suka bar wajen ya rage daga Anas se Mr Muh’d.
      “morning sir?” Anas ya gaishesa tare da durk’ushewa har k’asa mutumin be amsa ba illa kallon Anas dayake har Anas ya shiga tsoro daga bisani Mr Muh’d yace, “morning boy, get up please.” Nan Anas ya mik’e yana kallon k’asa. “I will first of all like to thank you for saving my men and company in all.”

      Anas na murmushin dole yace, “ba komai Sir, don’t make an issue out of it.” Cike da mamaki Mr. Muh’d ke kallon Anas jin yayi hausa. “Kanajin hausa kenan?” ya tambayesa.
     Mamakin erin tambayan Anas ke wai dagaske aka gansa bara’a d’au yana jin hausa bane? Dole ya sai black lens (k’wayan ido) a kasuwa ya soma sawa.
      “Sosai inaji Sir d’an nan ne ni ai, kanuri nake daga Bama.”
     Sanda idan d’an dattijon ya warwaru. “Kaid’in?” Ya tambaya in disbelief.
      “Eh sir” kafin Mr Muh’d yasake wata maganar Anas yace, “nasan you must be wondering ya nake da blue eyes haka aka haifeni amman d’an nan ne ni kuma muslimi ne ni my name is ANAS IBRAHIM FAUZY.”

     Kai Mr. Muh’d ya giad’a alamam ya yarda. “Toh masha Allah Mr. Fauzy kanada kyau tubarkallah.” Murmushi Anas ya masa “na gode Sir.”
      “Kana kirana da Baba, I once had a son as you.” Sekuma mood nasa ya canza.
      Nan Anas ya gano rasuwa d’an nasa yayi kenan. “I'm sorry Sir.. I mean Baba.”
     “Bakomai Mr. Fauzy. Aeroplane crash ne ya samemu time da zamuje hutu Paris nida d’ana Sultan da matata sekuma da iyayena, bayan jirgin yayi crashing atake duk suka rasu ni kad’ai nayi surviving a family na dukda nima naji ciwo sosai a sanadin haka na rasa k’afata na hagu anyi aiki sosai amman ina yak’i gyaruwa sesa kaga ina tafiya da stick (sanda).”

     Tausayin bawan Allah’n nan Anas yaji ya kamasa, sarai yasan how it feels to be alone, not to have a family shi Ummimi kawai suka rasa amman rayuwarsu ta tab’arb’are bale shi nasa da ya rasa komai. “I’m so sorry Baba Allah ya jik’ansu da rahmah.” “Ameen Mr Fauzy sede ana nema na awani meeting yau gashi har...” Ya d’aga hannunsa ya kalli agogon hannunsa “8:30 yayi.”

        “Ba komai Baba I’ll sit here in jiraka its my honour meeting with you, nasha ganinka a NEWS you’re such a successful man.” Murmushi kad’an Mr. Muh’d yayi “lets go” cike da rashin fahinta Anas yace, “excuse me?”
     “Lets go to the meeting together.”
     Blue eyes nasa ya zaro “Baba thank you for the offer but I’m not invited kar inje a koreni.”
    “Hahaha!” Mr. Muh’d yayi dariyan manya. “Not in kana side d’ina so lets go?”
      Kai Anas ya giad’a masa. Waya Mr. Muh’d yayi bada jimawa ba wata prado 2016 bak’a tasha wanki har kamar mirror jikinta yake ya zo yayi parking a gabansu. Fitowa wani yayi daga gaba ya bud’e k’ofar baya, hannu Mr Muh’d ya nuna wa Anas da nufin ya shiga a sanyaye ya shiga tare da rik’e jakar laptop nasa daya rataya a kafad’arsa kan cinyarsa, bayan shigansa Mr. Muh’d ma yashiga a hankali driver’n yasoma tuk’i.

     Basu tsaya ko inaba se wata babban conference hall tun fitowarsu daga motar mutane suka soma layi jiran su gaisa da Mr. Muh’d. Mamaki ne yacika Anas mutane kamar su cinye Mr. Muh’d wasu kuwa tambaya suke kowaye Anas amsar dayake basu ne yasa Anas shocking wai “he is my son.”

       Wajen VIP aka zaunar da Mr. Muh’d shima Anas yasamu kujera a gefen sabon Babansa (lol). Tambayoyi sosai Mr. Muh’d ya riga yi ma Anas kan ina yayi karatu? Sheraunsa nawa? Tambayoyi de turum. Daga k’arshe ya buk’aci Anas da ya nuna masa CV’nsa dan yagani Allah yaso Anas kullum yana yawo dashi nan ya ciro yamasa presenting.

      ****
      “Fannah! Fannah” kirar Boss na wajen aikinsu. “Yes Boss” ta fad’i bayan da ta iso. “Ga can table na VIP Mr Muh’d ne CEO’n Flames Enterprises.” Ido Fannah ta zaro tare da kewayo wa tana kallonsa ba shakka tana ganinsa a NEWS kap Maiduguri ba wanda yakaisa kud’i.    
       “Kinga saboda kinfi sauran ‘yan uwanki fasali yasa ke zanbawa chance d’innan kije kiyi serving nasa drinks dashi da saurayin gefensa dukda cewar yau na soma ganinsa naji ance wai Mr. Muh’d da bakinsa yace d’ansa ne kinga ko sekije kid’an tatso mana su. Kiyi amfani da kyanki ki ja attention na d’an nasan.”

     Fuska Fannah ta d’aure ko juyawa ma takalli saurayin da akace d’an Mr Muh’d d’in batai ba. “Ya Suleiman wai mesa kake magana haka ne? Nikama b’ata min rai nafasa kai musun gasu Asma’u ka kira sukai masu.”
           “Haba Fannah ke bakisan wasa bane? Ai wasa nake miki. Ungo ga plate nasu na shirya yi hak’uri ki kai musu.” Kallo ta watsa masa sannan ta d’aga ta fice. Murmushi yayi haka suke cikin fad’a kullum shida Fannah sarai yasan batada interest cikin samari shikuwa yata neman taokanarta, in aka ajiye wannan agefe kuwa shida Fannah suna shiri sosai tamakar sister’nsa ya d’auketa. Shine d’an me coffee shop na wajen aikin su Fannah’n. Saboda haka duk wani aikin da akeyi shike bada orders.

     Tunda Fannah ta soma tafiya zuwa table na Mr. Muh’d dan kai masu drinks da d’ansa bata d’aga kai ba. Kanta a k’asa tana isa table d’in ta gaishe da Mr. Muh’d da fara’arsa ya amsa sannan ta ajiye mishi cup nasa, ta mik’a hannu ta ajiye wa Anas nasa shima. A yayinda yake answering call ko d’aga ido ya kalli wacece ma beyi ba kawai “thanks” yace. Fannah itama da kanta ke k’asa bata d’aga kai ta kalle sa ba kawai de tasan waya yake. Ta juya zata tafi kenan Mr. Muh’d ya kira ta da “waitress” cak ta juyo “yes sir.”  “Take this away” ya nuna cup na gaban Anas dake kan waya har yanzu ko kallon direction nasu baiyi “ki kawo masa irin nawa”  “okay” tace sannan ta d’aga tana juyawa taga Asma’u sekuwa gashi kan plate nata akoi erin na Mr. Muh’d nan ta d’aga ta aza kan table d’in. “Here you go Sir” tace sannan ta juya zata tafi dakatar da ita yayi sannan ya zira hannu a aljihu ya ciro bundle na d’ari biyar ya mik’a mata. “Gashi ko mungode.”

     Fannah tasha jin ana cewa Mr. Muh’d nada kyauta bata tab’a tabbatar da hakan ba se yau. Amsa tayi hannu bibbiyu ta masa godiya. “Ba komai wannan nakine bawai na baki bane kije ki kai wa boss naki, wancan na zuwa daban. Keep this”
         Murmushi take sosai “Thank you sir! Thank you” nan ta fice daidai lokacin Anas ya katse wayar dayake yi tare da kewayo wa. “Kai da waye ne?”
         “Nida Abuu ne mahaifina.” Ya amsa a takaice.

          “Okay gashi an canzo maka tunda you are allergic to wancan flavour’n.”   “Thank you” yace “gashi ban samu na bata hak’uri ba nasa ta tayi sahu biyu.”
       “Bakomai don’t worry.” Atare suka sa cup nasu a baki suka d’anyi sipping sannan suka mayar suka ajiye. “So Mr Fauzy naga credentials naka you have such an excellent result, I'm ready to offer you a job a Flames Enterprises as my Personal Assistance (PA) akan albashi N500,000 (dubu d’ari biyar) dakuma weekly allowances N5000 (dubu biyar) kowani sati for a start kenan inhar naga ka iya aiki kana kiyayye komai kuma naji dad’in aiki dakai there will be additional salary for you. So? Will you accept my offer?”

     Anas ji yake kamar a mafarki albashi dubu d’ari biyar? “Yes! Yes Baba nagode sosai, in shaa Allah zaka sameni me kiyaye duk wani dokokin da ka kafa min. This is amazing nagode sosai yau sati na a nan Maiduguri ina neman aiki ban samu ba segashi ka bani wanda ban tab’a zaton zan samu irinsa ba I can’t wait in kira Abuu in sanar daahi. Nagode sosai Baba Allah saka da alkhairi.”
 
     Kallonsa Mr. Muh’d yake yana murmushi he made Anas happy, kawai tunawa yake da d’ansa.

   
     *© miemiebee*
NAGODE LOADS FOR THE WARM CONCERN YOU GUYS HAVE SHOWN ME, I LOVE YOU ALL!
     b

No comments: