Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 07
BY MIEMIEBEE


        *FANNAH*

      _3 days later..._
   
     Kwanan Fannah uku a asibiti tasamu k’arfin jiki aka sallamesu, ayau suke shirin dawowa gida, Alhamdulillah jikin nata da sauk’i sosai saboda anti-biotics datake sha masu k’arfi ne sosai. Baba ya sayarda shanunsa da shi ya samu ya biya kud’in asibitin ta da kuma na magunanta.

     Daidai sun sauk’o daga keke na pep kenan se ga irin almajiran unguwan nan sunzo sun tsaya gabansu.

         “Fannah! Dama ashe ke d’in kariya ce me bin maza, sekitayin abu kamar ‘yar malam saliha to Allah ya tona miki asiri tunda saurayi yayi miki ciki.” Hannu Mami ta d’aga ta wanke sa da mari. “In na sake jin wannan munanan kalamu daga bakinka kaji na rantse seka kwana a asibiti, bakai kad’ai ba dukanku nan. Fannah ba kariya bace abinda ya sametan nan k’addara ce. Maza ku fice min daga kallo.”

    Baya sukayi kad’an sannan suka soma wak’a “kariya! Kariya! Fannah kariya Fannah kariya!” Hannun Fannah kawai Mami taja suka shiga ciki a yayinda Baba ya koresu.
    Kuka Fannah keyi sosai. “Yanzu shikenan Mami kallon kariya za’a na mun? Shikenan rayuwata ta lalace Mami.”
        “Shhh karkiyi magana haka, karki saurare wad’ancan almajiran basu masan me suke fad’i ba.” Hugging nata tayi har sanda Fannah tayi shiru.

      Da yammacin ranar around k’arfe 4:45PM Ya Khaleel da d’ansa Farouq suka shigo gidansu Fannah. Mami da Afrah suna had’a girkin dare suka masu sannu da zuwa, ba abinda Afrah ke masu se harara. “Ke Afrah jeki kira min mahaifinku dakuma ‘yar ku kariyan can.” cewar Ya Khaleel.

           “Kawu Khaleel bamuda kariya a gidan nan.” Ta fad’a stubbornly.
          “Ke ni keke gaya wa magana? Iyye?”
     “Kawu kayi hak’uri Afrah kibasa hak’uri kije ki ma Babanku da Fannah magana.” A sanyaye ta mik’e taje ta kira Baba sannan takira Fannah a tare suka fito. Fuskar Baba a tamk’e ya zauna kan tabarman da Ya Khaleel da d’ansa ke kai ba tare da ya musu magana ba.

       “Ina wuni kawu?” Gaisuwar Fannah.
        “Yawwa sannu an sallamoki kenan. Se a kiyaye aukuwan na gaba kafin wani saurayin yasake fiad’e ki.”

     Har tsakiyan kanta tajiyo wannan kalamai ba ita kad’ai harsu Baba da Mami da Afrah. “Ya Khaleel in kasan batun daya kawo ka gidana dan kaci zarafin ‘yata ne dan Allah kayi hak’uri na had’aka da Allah ku tashi ku tafi.”

       “Ba seka koremu ba yanzu zamu tafi. Magana d’aya biyu na zoyi nan saboda haka nakeson ku bud’e kunnuwanku ku saurareni. Kunfi kowa sanin yadda ake k’yamatan kariya a gari, ba uban da ze so d’ansa ya auri macen da batada budurci. Fannah kuwa ‘yata ce dukda abin kunyan da ta mana ina san ta saboda haka zan bata wa d’a na Farouq.”

     “What!?” Baba yayi exclaiming.

     “Bari na gama mana k’ani na. Na riga nayi wa Baba magana kuma ya goyi bayan zancen d’ari bisa d’ari bawai nazo nan bane in baku choices saboda bakuda choice inbanda ku yarda mu rufa wa kariyarku asiri dan na tabbata kap garin nan bame san aurenta. Kinji ai Fannah? Ga Farouq nan mijinki, kina k’are secondary ze rufa miki asiri ya aureki zaki iya gode masa saboda wannan jahadi yayi. Auren kariya ba wasa bane.”

     D’ago jajyen idanunta tayi ta azasu kan Farouq dake ta mata murmushi. Hawaye se gangara suke kan kumatunta, kuke take sosai. Tasani a yanzu kam kamar yadda Kawu ya fad’i ba na mijin da zeso aurenta saboda ta rasa budurcinta martabatar ta, amman duk da haka gomma ta mutu batai aure ba data auri Farouq. Farouq baida tarbiyya ko kad’an d’an iska ne ba aikinsa se bin mata Allah kad’ai yasani ko baida cutar k’anjamau ma. Ba yadda za’ayi ta auresa.

       “Kawu dan Allah kayi hak’uri ni baran auri Ya Farouq ba, dan Allah ka rufa min asiri.”

        “Ji shashasha dabadan Farouq nada imani bama jinki ze yarda ya aureki ne? Ajinki a kariyan da kike yanzu zaki samu na miji kamar Farouq yace ze aureki ne? Inba mahaukaci ba wallahi ba na mijin de so ya aureki gara ma tun wuri kinsan ina ke miki ciwo”

      “Enough Ya Khaleel!” Cewar Baba a fusace. “ ‘yata barata auri wannan d’an iskan ba. Mungode da alfarman da kuka bamu amman bamuso da in aura wa ‘yata d’an iska kaman Farouq na gommaci kartayi aure a duniya. Yaro ko gaishe dana gaba dashi be iya ba. Ku tashi kubarmin gida zanje in samu Baba in masa magana yaja da baya da wannan zance. Fannah bata san Farouq saboda haka barin tilasta mata ba.”

      “Aww haka kace kenan? Yanzu har zaka bud’e baki ka kira d’a na Farouq d’an iska? Kariyarka kuma fa? ai nakega sede ace mata ‘yar guguwa, aure tsakanin Fannah da Farouq kuma consider it done bari ta k’are shirmen secondaryn nan kuga ikon Allah. Wawiya ana taimaka miki kina wawanci mschww Farouq tashi mu tafi da Allah.” Suna ficewa Fannah ta ruga d’aki da gudu ta baje kan katifar ta tana kukan cire rai. Afrah ce tabiyo bayanta itama kukan take tabbas Fannah tana cikin tsaka me wuya duk wanda ya aikata mata ta’addancin can ya cuce rayuwarta har a bada.

       Tun ba yau ba Fannah ta tsani Farouq taya za’ace shi zata aura? Kasheta akeson yayi?

     “Yi hak’uri Ya Fannah dan Allah kibar kukan nan in shaa Allah baraki auri Ya Farouq ba.” D’ago jajayen idanunta tayi “Afrah shikenan ni haka rayuwata zata k’are cikin k’unci da bak’in ciki? Mesa se ni Afrah? Mena tab’ayi da ba kyau to deserve all this? Duk abinda addini na yace inyi inayi wanda kuwa ya haramta ina k’ok’arin nisantar kaina daga aikatasu. Mesa seni wancan saurayin zeyi raping? Mena masa Afrah? Mesa seni za’a ce zan auri Ya Farouq kinfi kowa sanin halinsa. Kullum yana nan a bayan gari yana kwanciya da mata, Afrah dan Allah ki taimaka min.” Ta kuma fashewa cikin matsanancin kuka.

     Itama Afrar kuka take ta rungumi yarta tana bata hak’uri.

     ****

        “Malam dan Allah kayi wani abu karka bari Kawu ya cimma burinsa na aura wa Fannah aure da Farouq kafi kowa sanin halin Farouq so nawa ake kamasa a bayan gari? Dan Allah kaji k’an ‘yarmu Fannah. Ko kad’an she’s not to blame for what happened to her fiad’e aka mata munyi iya binciken da zamu iya mun kasa samun waye ya mata wannan d’anyen aikin.” Ta fashe da kuka.

      “Maman Aiman in shaa Allah barin bar Fannah ta auri Farouq ba. Yanzun nan zanje in samu Baba in masa magana kishiga ciki kibata hak’uri ki kwantar mata da hankali dan Allah. Ni na wuce...”

****

     “Ina wuni Baba?” Gaisuwar Malam Aliyu Babansu Fannah ga mahaifinsa da Ya Khaleel.
       “Lafya Aliyu, ya jikin Fannan?”
      “Da sauk’i Baba.” Ya amsa yana kallon wansa Khaleel da d’ansa dasuke zaune a gefen mahaifin nasu.
       “Nasan maganan daya kawo ka Aliyu saboda wan ka Khaleel yamin bayanin komi yanzu. Kasani wan ka bare tab’a maka abinda ze cutar dakai ko iyalinka ba. Kafi kowa sanin halin da ‘yarka tashiga kallon kariya ake mata agari me bin maza-”

      Malam Aliyu katse mahaifin nasu “amman Baba ai duk munsan ba haka asalin abar take ba, fiad’e aka mata.”

      “It still will not change anything Aliyu, in mu mun yarda da hakan mutane fa? Baramu iya fahimtar dasu ba. Kap garin nan ba mahaifin da ze b’ar d’ansa ya auri wacce batada budurcinta tattare da ita kasani Aliyu. Allah ya kawo mana sauk’i gida ga wan ka nan Khaleel he is ready ya rufa wa ‘yarka asiri ya d’au d’ansa ya aura ma ‘yarka dukda ba cikakkiyar mace take ba yanzu amman har ka bud’a baki kace bakaso? Ina zaka zo ka kai ‘yar taka?”

    “Baba in shaa Allah, Allah ze kawo mata miji wanda ze sota a yadda take.”

     “Har tsawon yaushe kuma zaka tsaya kana jiran wannan rana da bakasan ranan zuwanta ba? Iyye Aliyu? Bana sake jin wani zance, Fannah zata auri Farouq wannan shine san da muke mata bamusan tak’are rayuwarta batayi aure ba.”

      “Baba dan Allah kayi hak-”

   Baba ya katse sa. “Aliyu wannan shine karo na farko da kake k’ok’arin bijire min, kar muyi haka da kai. Farouq.” ya waiwayo da kallonsa kan Farouq

    “Na’am Baba.” cewar  farouq.

    “Kanason Fannah zaka aureta koda bata da budurcinta a tattare da ita?”

        “Eh Baba ina santa k’anwa tace koda duniya sun k’ita ni baran k’ita ba.”

    “Masha Allah” Baba yace. “Kaikuma fa Khaleel ka yarda d’anka ya auri macen da tarasa budurcinta?”
   
      “Na yarda Baba” cewar ya Khaleel. “Fannah ‘yata ce matuk’an ina raye zanyi duk iya abinda zan iya dan in kula da ita in rufa mata asiri.”

   “Toh masha Allah kadeji Aliyu. In nine kai godiya zanyi wa Khaleel da Farouq.”

    “Baba amman Fannah batasan Farouq, bata tab’a sansa ba, taya zamu tilasta mata auren wanda bata so.” Cewar Malam Aliyu.

      “Wannan kuma ba me wuya bane, in suka soma ganin junansu a hankali zasu shak’u. Allah dad’a had’a kawukan ku.”
    “Ameen” Ya Khaleel ya amsa banda Malam Aliyu dake ji kamar yayi kuka.

****

     “Sannu da dawowa Malam” cewar Mami tana k’ok’arin shimfid’a masu tabarma. Bayan sun zauna take tambayarsa ya had’uwan nasu ya gudana. Kai ya kad’a a hankali take jikinta yayi sanyi.

      “Maman Aiman Ya Khaleel ya riga ya saye Baba nuna masa yayi intensions nasa are clean tsakani da Allah yakeson ya aura wa Fannah Farouq saboda tsantsan tausayi.”

    “Malam amman ai duk munsan badan haka bane.” Mami ta katse Baba. “Tun ba yau ba idanun Kawu suke kan Fannah shikansa yasan tana da tarbiyya mekyau da hankali so yake ya aura wa Farouq Fannah saboda ta giara masa d’a ita kuma tasha wahala in the process.”

        “Ba k’arya cikin magananki Maman Aiman ni kaina abin nan ya dameni bansan ya zanyi ba, tausayi Fannah take ban matuk’a yarinya me hankali ace arasa ma wa za’a d’aura wa k’addara erin wannan se Fannah.” yaja numfashi.

   “Uhn uhn Malam kayi istigifaar kar kayi sab’o. Wannan Allah kad’ai yasan mesa ya d’aura wannan mumunar k’addara kan Fannah bekamata muyi ma Allah shisshigi ba.”

     “Hakane Maman Aiman Astaghfurullah.”

     “Yanzu Malam shikenan sede mu zuba ido muna ganin ‘yarmu zata auri wannan d’an iska? Ba abinda zamu iya mata? Innalillahi!”

     “Da akoi abinda zan iya da nayi Maman Aiman banasan Fannah ta auri Farouq ko kad’an. Ran Baba ya b’aci ya dage se Fannah ta auri Farouq inhar na hana aikuwan wannan aure, zamu iya samun sab’ani da mahaifina.”

       Fannah dake lab’e ajikin bango tana sauraronsu ba abinda takeyi se hawaye. Daidai lokacin wani yaro yashigo gidan bayan ya gaisheda Mami da Baba yace “wai Fannah tafito inji Farouq.”  “Barata fito ba” cewar Baba a fusace. “Kace masa barata fito ba inji mahaifinta.” Nan Fannah dake lab’e tafito “kace masa ina zuwa.”  “Fannah!” Mami da Baba suka kira a lokaci d’aya.

         Tana kuka tana maganar, “Baba naji duk abinda kuka fad’a barinso saboda ni kasamu matsala da Baba ba. Muyi hak’uri mu rungumi k’addara fatarmu Allah sa hakan shi yafi alkheri, Allah sa auren Farouq ba sharri bane a gareni, addu’an da nake so kumin kenan. Barinje kirarsa kar yaje yasamu Baba ya fad’a masa wani abu daban yajawo maka matsala.” Tana kaiwa nan ta fice.

     Kuka me k’arfi Mami ta fashe da shikansa Baba sanda ya zubda hawaye, babu kamar Fannah, yarinya me hak’uri da hankali dole yasan abinda zeyi ya hana aukuwan wannan aure.

     Tana fitowa taga Farouq zaune kan benchin da take zama kullum da Ahmad nata take hawaye ya ciko mata a ido. “To ke kuwa Fannah haka ake hira? Haka kika sabayi ne in samarukan ki sunzo wajen ki? Taho nan mu zauna mana.”
       Kafin tace meh Farouq ya taso ya cafke hannunta da sauri ta waske hannun nata daga rik’onsa. Tana kallonsa da jajayen idanunta.

    “Meh haka kuma? Yau na miji ya soma rik’e hannunki ne? Kinga nifa ki sake jikinki dani tunda nasan ciki nasan waje ba sekin tsaya kina proving min innocence ba.” Hannun nata yasake rikowa da k’arfi sannan ya aza d’ayan hannun sa kan fuskarta yana shafawa. “Ji laushin jiki wai a haka ma kinbar samaruka suna tab’awa kenan.”

       K’ok’arin k’watan kanta take amman ta kasa se hawaye take yi “Farouq kasake ni bana so, kadena tab’ani.” K’in saketa yayi “meh aciki dan na tab’a mata ta ko kin manta a matsayin mijinki nake yanzu.” Matso da fuskarsa yayi sosai kusa da nata. Numfashinsu yana had’uwa. Kafin ya hankara Fannah ta tsinke sa da mari wanda besan sanda ya saketa ba.
 
     Hawaye take sosai “karka kuskura ka sake tab’ani in kai d’an iska ne toh ni ba ‘yar iska bace, in ka saba tab’a mata anyhow ni ba d’aya daga cikin ‘yan matan da kasaba tab’awa bane.”

   “Dallah can kariya kawai, keda kike bin maza kowa ya sani, zaki wani zo kina min zak’in baki. Kuma barikiji in fad’a miki duk sanda kika kuskura kika sake marina wallahi kinji na rantse sekin sake kwana a asibiti. Humm!” ya sakar da wata shu’umar murmushi “bari a aura min ke zaki yaba wa aya zak’inta. Se gobe ko baby, ki kula min da kanki please karki sake bin wani har abu yakuma shiga tsakaninku nasan you are itching to be with a guy.”

*© miemiebee*

No comments: