Tuesday, 27 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 89
BY MIEMIEBEE







      Daidai tashiwan Anas daga bacci kenan, da k’yar ya iya ya raba jikin Fannah da nasa dan wani sabon salon baccin da ta koya bata bacci se in akansa. Bayan ya tura ta gefe yasake lullub’eta da bargo sannan yayi pecking nata a goshi. Bayi ya nufa yayi wanka agurguje yasa mint blue shirt da farin ¾ wando. Kitchen ya nufa yasoma had’a musu Chocolate-chip cookies for breakfast, in less than an hour yagama komai se coffee daya had’a musu, dining table ya shirya tsab sannan ya koma d’aki dan tayar da ita, zaune ya tarar da ita se murza idanunta take. “Good morning Flower har kin tash-” besamu daman k’arisa maganan ba dan yanayin daya tsince ta ciki kamar kuka take, daya gama k’arisowa kusa da ita kuwa seya tabbatar da hakan zama yayi a gefenta.
   Cike da tashin hankali yake maganar. “Omg! Flower why are you crying?” Kasa amsa shi tayi kawai tayi hugging nasa a yayinda kukanta ya tsananta. Bayanta yake bubbugawa a hankali, “shhh! Kibar kuka kinji I’m here stop crying Flower” seda ya tabbata tayi shiru ya d’agota. “Meya faru?”
    “Habeebi promise me baraka tab’a barina ba, promise me please.” Ta sake matsesa ajikinta tana meh cigaba da kuka.
    “Shhh! I will never leave you Fannah, never ki kwantar da hankalinki *_INA TARE DA KE_* forever.” Hannu yasa ya share mata hawayen ”meya kawo wannan zance? Kinyi mafarki ne?” Kai ta gyad’a masa. “You want to talk about it?” Nan kuma ta kad’a mai kai “I’m afraid Habeebi.”
    “Toh shikenan is okay, tashi kiyi wanka yanzu.” Ba musu ta miqe ta amshi towel dayake miqa mata bayan ta cire kayan jikinta ta d’aura towel d’in “Habeebi ka rakani bathroom d’in wallahi tsoro nake wai Ya Farouq na ciki.”
     “Mafarkin Farouq kikayi dama?” Cike da tsoro ta gyad’a kai. “Karki damu Farouq is gone foever.”
   “Nasani Habeebi still ina tsoro ka rakani please” hannunta ya riqe yakaita har bathroom d’in tabarsa yafito tak’i labule taja ta tare kanta shiko yana zaune akan hand basin bayan data gama suka fito tare man shafawanta ta nema kap kan mirron babu. “Habeebi kaga lotion d’ina?” Se ayanzu ya tuna ya had’a cikin akwati d’azu. “Bangani ba Flower, babu akan mirron?” yayi qarya.
   “Babu” tayi maganar tana nufan wardrobe dan ciro sabo.
   “Wait wait!” yayi sauri ya dakatar da ita, “babu achan ga vaseline chan ki shafa.”
  “Habeebi wai me kake b’oyewa cikin wardrobe d’innan ne?”
   “Kan Farouq ne aciki kika kuskura kik-” be samu daman k’arisa maganan ba sanadiyar tsallen da Fannah ta daka se a jikinsa ta tsaya chak! hannu yasa ya tare ta kafin ta fad’i. “Na tuba wallahi barin bud’e ba, dan Allah kabari ina vaseline d’in zan shafa.” Dariya sosai ya tsaya yi “toh muje mu shafa miki amman sauk’a tukuna.” ya gwada cire hannyenta dake rataye a wuyansa, kafad’a ta buga nufin barata sauk’a ba tare da sake kankamesa, haka tana zaune kan cinyarsa ta shafa manta. Kayan ta daya cire mata wani baqin abaya ya miqa mata, “gashi sa.”

     “Habeebi abaya nefah.”
   “Ina sane ai” ya gyad’a mata kai.
   “Toh ina zamuje da zan sa abaya?”
  “Ikon Allah! Mom Hanan ko d’an bincike seya baki hanya wani irin bincike ne haka?! Allah kika sake questioning d’ina zan bud’e wardrobe d’in Farouq yafito.”
   “Nabari nabari please kabar fad’in sunansa Hanan zatayi kuka.”
   “Toh Mom Hanan na dena” yayi managar hannunsa na akan cikinta. “Flower yaushe Hanan zata soma motsi I want to feel her.”
    “Dr tace se pregnancy’n yakai zuwa 16 weeks and Hanan is just 8 weeks yanzu kaga da saura.”
    “Ohh kice min se cikin ki yayi k’aaaatoo Hanan zata fara motsi.” Hannunsa ta d’aga daga kan cikin nata “nifa na fad’a maka bawai wasan nan na sani dariya bane banaso.”
    “Toh I’m sorry yi sauri kisa kayanki.”
  “In nasa ina zam-” bata k’arisa maganan ba tayi tsit dan ta tuna da abinda Anas yace mata akan ta sake masa tambaya ze ciro kan Ya Farouq cikin wardrobe. Kamar baby ya riqota a hannu zuwa dining table yasan ta da kewaye kewaye kar idanunta sukai kan akwatinan nasu.

    “Habeebi harda breakfast kamana yau wow!” Yana bud’e flask d’in k’amshin abincin ya mamaye wajen gabad’aya se shaqa Fannah ke tana d’igan miyau. “Baby hurry up and serve me yunwa nakeji.”
   “Kwad’ayi kike ji de.” K’aramar tsuka taja ta bugesa gefe ta amshi flask d’in taja gabanta ta soma chi. Tsayuwa yayi yana kallon ta cike da mamaki ganin takusa cinyewa ba shi yayi magana “Flower nifa ban chiba karki cinye duka.”
    “Ayyah Habeebi, Hanan kuma fah? Kayi hak’uri kabarmu mu cinye mana.”
    “Bawani Hanan d’innan glutton (meh shegen cin abinci) kawai.”
   “Kafad’i koma meh mu cinye?” Kai ya gyad’a mata yana murmushi yadda takecin abinci na bala’in kashesa. Bayan da ta gama yaje yayi frying sausages ya karya dashi shima. Bayan da suka gama ya tattara dining table d’in “Flower jekisa mayafin abayan naki we are going somewhere.”
   
     “Ina kenan Habeebi?”
   “Aww! inje inciro kan Farouq ko?”
   “A’a please nayi shiru.”
  “Better jeki shirya ina jiranki and karki bud’e wardrobe d’in ni na fad’a miki.”
   “Toh Habeebi kazo muje tare wallahi tsoro nakeji” seda yayi ta mata tsiya sannan ya rakata yana ganinta tana shiryawa har tagama tayi arabian rolling mekyau me amsarta sannan ta feffesehe da turare d’ayan da kad’ai tagani kan mirron ta tambayi Anas ina sauran turarukanta kuma tana tsoron kar yaciro kan Farouq daga cikin wardrobe. “Kingama?” Ya k’are maganar hannunsa k’ark’ashin hab’anta yana kallon fuskarta datasha light makeup.
    “Eh nagama semeh kuma yanzu?”
  “Se...” Yakai bakinsa kan nata “Habeeb-” be sake mata baki ba seda ya tand’e maroon strawberry flavor jan bakin data shafa tas.
    “Haba! Habeebi” tayi maganar lokacin da ta juyo tana kallon bakin nata a mirror. “Mena sharemin jan bakin yanzu?” Tayi pouting lips nata.
   “Saboda yamiki kyau sosai and banason in mun fita mutane suna kalla min ke, because you are mine Flower, as from today banason ki sake yin makeup in zamu fita okay?”
   “Nikam wannan Habeebin” tayi maganar chan k’asa k’asa tana zumbure zumbure.
   “Yes Flower kajol da nude lipstick kawai na yarda kina sawa kinji?” Shiruu “nace kinji?”
   “Naji-” katsesa yayi “good, agida kawai na yarda kina kwalya.”
   “Habeebi gaskia akwai ka da son kai amma kaika iya d’aukan wanka kamar me zuwa gidan biki idan zaka fita.”
    “Toh mijinki neni ai” be jira ta sake magana ba yajata waje zuwa mota sannan ya dawo ya kai boxes nasu mota dake se game nata take ta  bugawa ko kad’an bata ga me yake ba seda ya shigo mota ya tambayeta “Mom Hanan are you ready?”
   “Do I have a choice bayan baka sanar dani ina zaka kaini ba.”
   “Karki damu you’ll find out soon.” Seda ta bari sukayi nisa da tafiya ta yadda barasu iya komawa gida ba, balle yace ze ciro kan Farouq tasoma jero masa tambayoyi wanda duk ciki ba wanda ya bata straight answer.

     Wani tambayan ma seda ta ga sun dosa hanyan airport “Habeebi wai me zamuyi anan?†
    “Flower inda zaki d’an k’ara hak’uri everything will turn out cool.” Badan tanaso ba tayi shiru waje yanema yayi parking sannan ya fito da ita a yayinda wani security ya cicciro musu luggages nasu “Habeebi wannan fa akwatina ne a hannun mutumin nan” tayi maganar tana bin mutimin da kallo.
  “Yes ina sane Flower” ya jawota jikinsa.
   “Toh a ina ya samu?”
   “Acikin booth kayakin mune aciki.” Cike da mamaki da rashin yarda tsantsan mamaki ta d’ago kai tana kallonsa. “Kayan mu aciki? Kana nufin tafiya zamuyi?” Gira ya d’aga mata.
    “What?! Habeebi-” yatsansa ya aza a lips nata “shhhh! Nasan me zakice ban fad’a miki ba you are not ready barakije ba but please don’t say so kinji? Don’t ruin this I’ve worked hard for it.”

    Hugging nashi tayi abinda beyi tsammani ba a tunaninsa she will freak out tace masa barata jeba. Cikin sauti cike da jin dad’i tayi maganar, “Taya zance barinje ba Habeebi bayan nasan you worked hard for it I just hope we will enjoy inda zaka kaimu. Me, you and our Hanan Habeebi.” Dad’in kalamunta yaji sosai yayi hugging nata back “we will in shaa Allah Flower, I love you dearly.” Bayan tayi breaking hug d’in ta ciro wayarta daga jakarta “me zakiyi Mom Hanan?”
   “Zan kira Mami in sanar da ita.” Wayar ya amsa “don’t worry na riga na sanar da ita lets just go, hope you are ready to go fly to Abuja?”
   “Abuja? Okay I am ready.” Wajen private jet nasa wanda be tab’a tafiya dashi ba yau ne karo na farko suka nufa se admiring jirgin Fannah ke bata tab’a ganin kalan jirgin ba se a TV.
    “Habeebi mu kad’ai zamuyi tafiyan ne?”
    “Yes Flower this is my private jet ba public jirgi bane.”
   “Ohhh wow! Its amazing baka tab’a fad’a min ba.”
   “Sorry nima ban tab’a using nashi ba seyau tun kafin muyi aure na saya I mean tun lokacin dana fara sonki Flower I was hoping Allah ze kawo min ranan da zan shiga ciki dake that is when we’ve accept each others love just as we did a very long time ago now, I love you Flower” Kyakkyawar fuskarsa ta shafa “I love you too Abu Hanan.” Hannunta ya riqe suka shiga ciki bayan angama komai da komai sauran tashiwar jirgi Fannah tasa suka karanto add’o’in kariya. Tun anan Anas yagano ta soma jin tsoro dan kuwa this is her first time shiga jirgi.

    Seatbelts Anas yamusu tighting aiko ta riqo hannunsa gagam “Habeebi na fasa tafiyan ina jin tsoro please su tsaya.” Dariya yakeson yi amman ya b’ata rai. “Flower just keep calm muna tashi everything will be normal.”
    “No Habeebi ni kawai kace musu su tsaya” a hankali jirgin ya fara tafiya bata wani ji tsoro ba seda jirgin ya fara tashi anan ta fara kuka harda hawaye hannunta Anas ya matse cikin nasa yana fad’a mata dad’ad’d’un kalamu ahaka har suka tashi da suka fara flying kuwa seta bar jin tsoron. A hankali ta bud’e idonta d’aya sannan d’ayan. “Kin dena jin tsoron?” Kai ta gyad’a a hankali “are we flying already?”
   “Yes Flower we are kiduba window kiga.”
   “A’a tsoro nakeji.”
   “Ki leqa ba abinda ze sameki am here.” Cike da tsoro ta leqa kad’an da wuri ta dawo da kanta ciki “calm down Mom Hanan ki kwanatar da hanakalinki ko kinason Hanan ma taji tsoro ne?” Kai ta kad’a masa “good” yace tare da pecking nata, headphone ya ciro yasamata akai tare da kunna mata qira’a. Cikin ‘yan mintuna suka iso Abuja nan ma da suka zo landing kad’an ya rage Fannah batayi kuka ba.

   Transcorp Hilton Hotel Abuja suka sauk’a zuwa Azahar bayan sunchi abinci sun sake wanka suka wuce embassy’n USA  kasancewar a New York Anas yakeson suyi rainon Baby Hanan. Dad’i sosai Fannah taji daya sanar da ita plans nasa, sun gaji iya gajiya wai haka ma dan da sanin ido kenan aka samu aka gama musu abubuwan on time zuwa jibi everything will be ready seya rage sauran tafiya. Koda suka dawo gida Fannah takasa fitowa daga mota dan gajiya Anas ne ya cirota da kansa yakaita har zuwa d’akinsu. Akan gado ya direta kafin ya juya ta riqo kolan rigarsa tajasa jikinta kafin yayi wani k’wararren motsi ta kifa bayansa da gadon ita kuma ta haye kansa. “Habeebi bacci nakeji.”
    “Flower bamuyi Sallan isha bafa.”
   “I know Habeebi mubari zuwa 10-11 haka se muyi please.” Shiru yayi tare da aza hannunsa kan bayanta yana shafawa a hankali. In the next 5 minites Fannah tayi bacci. “Flower!” ya kira ta shiru ba amsa.
    “Flower har kinyi bacci?”
   “Uhmm” tayi groaning cikin baccin. D’an murmushi ya saki tare da pecking kanta. A haka shima ya samu yayi bacci se 11:27PM Anas ya tashi anan sukayi Sallah suka chi abinci sannan suka watsa ruwa suka sake komawa bacci.

     Kwanan su biyu a Abuja Anas ya sama masu visa. Washegari around 8:00AM suka d’au flight zuwa New York kamar sabon shiga haka tata jin tsoro ma yau.

     _10 hours later... Exactly 6:00PM a Nigeria 1:00PM a kuma New York_
 
     Su Anas suka shigo NY gajiya kam ansha sosai, musamman Fannah kusan duk a kwance kan gadon dake jet d’in ta yini amman hakan be hana k’afafunta kumbura dam ba.
    A MANDERIAN ORIENTAL HOTEL NY suka sauk’a. Fannah de takasa b’oye k’auyancinta inwhich Anas found so adorable and cute komai tagani seta tambaya. Warming jikinsu sukayi cikin had’ad’d’en jacuzzin dake bathroom d’in sannan suka yi ordering abinci sukaci.

     Baccin sauk’e gajiya suka yini sunayi ranan da daddare bayan sun idar da Sallan isha sunci dinner Anas yahau massaging wa Fannah k’afafunta da suka kumbura bayan daya gama mata kuma suka kwanta.
     Washegari basu fita ko inaba a d’akinsu suka wuni ba abinda suka tsinana wa kansu banda romancing juna da suka yini sunayi se the next day suka fita ganin gari leisure points da dama erinsu 911 Memorial Guided Tour with Museum, Disney on Broadway Exclusive, Magic Walking Tour, NBC studio, central park, Brooklyn bridge, 9/11 Memorial and Museum, da sauran su suka jejje se killing selfies suke Fannah nawa Afrah da kishi kamar ya kasheta sending. They had alot of fun se Maghrib suka dawo masauk’insu all tired. Sallah kawai sukayi suka miqe kan gado se bacci.

      Haka fa rayuwa ta cigaba da kasancewa Mr. And Mrs. Fauzi cikin so da k’aunan juna, zamansu a New York ba shiyasa Anas hana Fannah sa hijabi ba dukda kuwa in aka gansu se an tsaya ana kallonta amman kamar yaddda bata damu ba haka shima Anas d’in, sosai yake kishin Flowersa. Baby Hanan nasu kuwa se girma take a yanzu haka cikin Fannah nada 5 months da anganta anga me ciki dan ko har ya b’ullo kai tun anan Anas ya fara neman tsokananta dan haka tama bar zama da vest inya nan se baggi kayakin da zasu b’oye mata‘yar cikin nata, ga yadda taciko dam iya cikowa Anas baya iya hak’ura da ita yanzu aduk lokacin da ya kalleta se sha’awan ta ya taso masa kullum suna cikin yin abu d’aya.

   ****
      Yau ranar ta kasance Tuesday ayau ne Mr. and Mrs Fauzi zasuje duban gender’n Baby’nsu tunda cikin yayi k’wari, dukansu bugawa zuqatansu ke barin ma Anas dakeson ‘ya mace kamar hauka.

****
     Murna gun Anas da Fannah baya misantuwa da aka tabbatar musu mace ce baby’nsu. Sabon siyayya Anas yace zasu soma yiwa Baby Hanan yanzu da aka tabbata Hanan d’ince a hanya, inbawani ikon Allah ba.
     Ta ward d’in karb’an haihuwa suka fito aiko Fannah na ganin yadda mata masu ciki ke nak’uda yadda suke shan azaba ta rushe wa Anas da kuka. Kuka na sosai seda suka nemi waje suka zauna hankalinsa duk yabi ya tashi ya rasa meya sata kuka haka, just a while ago she was happy jin sex na baby’nta yanzu kuma tana kuka to meh dalili? Ko ta dena san ‘ya mace sena miji ne?

    “Flower is okay kinji stop crying please ya isa” ya cusa ta ajikinsa yana bubbuga bayanta har izuwa lokacin da tayi shiru.

*© MIEMIEBEE*

  beeenovels.blogspot.co.ke