Wednesday, 28 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 90
BY MIEMIEBEE








 
     
       “Flower mesa kike kuka? Do you want to talk about it?” A nitse ta d’ago kanta daga k’irjinsa ta share hawayenta sannan ta masa nuni da ward d’in. Cike da rashin fahimta yace, “what about it Flower?”
    “Habeebi baka ga yadda matan suke kuka bane? Yadda haihuwan ke basu wahala Habeebi I’m afraid” tasake rushewa da kuka. Kallonta ya tsaya yi Fannah barata ishesa da kallo ba. Sake kwanto da ita yayi a jikinsa yana bubbuga bayanta “is okay kinji bar kukan ya isa, you will have a safe and easy delivery in shaa Allah zamu cigaba da miki addu’a bar kukan haka ya isa.”
    “Habeebi ina tsoro kasan wasu matan daga labour room se lahira suke wucewa Habeebi banason in mutu ban rik’e Hanan ba.”
    “Flower kibar magana haka wayace zaki mutu baraki riqe Hanan ba? In shaa Allah zaki shiga labour room kuma kifito fine and good banason irin maganan nan kinji? Stop crying ya isa.” D’agota yayi sannan ya share mata hawaye “lets go and eat.”

    Ba musu ta miqe tana manne a jikinsa har suka isa gun motansu. Yana cikin driving ya juyo ya kalleta tayi lamo jikin kujeran tana kallon window.
    “Flower kinsan you are funny koh.” Ba tare da ra juyo ba ta amsa shi, “menayi kuma yanzu?”
   “Kukan da kikayi mana, gaskiya banason Hanan ta d’auko kukanki abu kad’an kuka.”
    “Sekayi ai kai dama in baka nemi tsokana naba bakajin dad’i.”
   “Oh common Mom Hanan chill please wasa nake miki.” daga nan bata sake che masa k’ala ba.
    A Restaurant Manhattan Anas yayi parking bayan ya fito da ita daga motan sukayi ciki, table dake kusa da bakin k’ofar ya zaunar da ita a yayinda ya yi ciki dan yimusu order kasancewar traditional restaurant ne. Fannah na zaune ita kad’ai kan kujerar tayi jugum har a yanzu hankalinta be kwanta ba regarding mata masu nak’uda data gani d’azu daga bisani ta d’ago kai tana kallon k’ofar seji take kamar ana binta da kallo data dudduba kuwa se bataga kowa ba.

     Kamar daga sama taji hannu dafe kan kafad’ar ta a razane ta d’ago kai acewarta ma kidnapping nata za’ayi harta bud’e baki zata sa ihu setaga mace ce ‘yar uwarta anan ne hankalinta yad’an kwanta. Bata tab’a sa matan a ido ba amman kuma she is sure ba a yau ta fara ganinta ba zuciyarta se rad’a mata take she’ve met this woman before amman ta rasa a ina.
    “Sannu Sister yi hak’uri in na razanar dake please.” matar tayi magana cikin muryarta wanda sosai yayi kama da wata wanda Fannah tasani amman ta rasa gane a ina, no matter how tayi ta tuna a’ina tasan muryar ta kasa.
   “A’ah ba komai Aunty” cewar Fannah har a yanzu se kallon wannan babbar mace me k’imanin shekaru 45 take tana me tunanin a’ina ta tab’a ganinta.
    “Toh nagode nace dan Allah wancan da kuka shigo dashi just a while ago mijnki ne?” Shiru Fannah tayi tana  nazarin ko ta bata amsa kokuwa kar ta bata saboda question d’in is too private. Shirunta ya sake bawa matar damar magana. “I’m sorry please karkiji tsoro ba abinda zan miki suna na AYSHA kuma ‘yar Nigeria ce nima kamar ku kawai I want to know ne please ki fad’amin.”
    “Eh mijina ne.” tayi maganan idanunta cikin na Aysha, hawaye ne suka soma gangarowa kan kumatun Aysha wanda yamugun bawa Fannah mamaki toh kode son Anas nata wannan Aysha ke da har zatayi kuka da ga jin ance yanada aure.

    “Aunty Aysha mesa kike kuka?”
  “Babu, babu ba komai sunan mijin naki A... A... Anas koh?” cike da mamaki Fannah ke kallonta har taya tasan sunan Anas? Ta bud’e baki zatayi magana kenan Anas yakira ta from far behind.
   “Flower!” Da sauri ta juya izuwa direction nasa, drinks biyu ne riqe a hannunsa “wannan ko wannan kikeso.” Murmushi ta saki sannan tayi nuni dana hannun daman nasa, ido ya kashe mata sannan ya koma anan ta juyo dan cigaba da magana da Aysha sede ta duba gabas da yamma kudu da arewa bataga Aysha ba. A nitse ta miqe ta fito waje tana kewaye kewaye ko zata ganta amman ko alamarta babu, badan tanaso ba ta dawo ciki ta zauna shima Anas bada dad’ewa ba yadawo da plates nasu a hannunsa nata ya ajiye mata a gabanta. “Thank you Habeebi amman basu da waiters ne sekai zaka kawo mana da kanka?”
    “Ninaso Flower, kinsan white people d’innan da shegen son mata banason su kalla min ke.” Dariya sosai take “over possessive ba” tace cikin dariya.
    “Na yarda whatever lets eat.” Cike da jin dad’i suka soma chin abincin daga bisani Fannah tace, “yauwa Habeebi bakasan meba.”
  “Meneh?” Ya tambayeta tare da kai spoon baki yanacin abincin.
   “Shiganka ciki wata mata ‘yar babba haka tazo ta sameni take tambayana wai ko kai miji na ne dana tabbatar mata mijina ne kai sekuma tasoma min kuka wai sunan ta Aysha kuma abinda yafi ban mamaki ma yadda tasan sunanka, nayi nayi intuna a ina na tab’a ganin ta amman na kasa ‘cause her face seems familiar.”

    Spoon daya kai bakinsa ya maido shi plate d’in tare da d’ago blue eyes nasa yana kallon Fannah. Anan data kuma k’are masa kallo itama se ta tuna a ina tasan kamannin fuskan Aysha, anan tagane a’ina ta tab’a ganin fuskar Aysha ashe cikin family photon su Anas ne wanda ya goge fuskarta, anan ta gane Anas nata ke kama da Aysha, muryar Amal kuwa sak na Aysha ce. Aysha itace Ummimin su Anas. Ummimi na raye bata mutu ba.

    “Kikace meh?” Cewar Anas alokaci d’aya yaji lisafin k’wak’walwarsa na gushewa jin an ambaci Aysha sunan mahaifiyarsa da ya tsaneta fiye da komai a duniya.
    “Habeebi Ummimi nagani, wallahi ita nagani just a while ago.”
    “Whaattt?!” Ya tambayeta cike da k’in yarda.
   “Habeebi itace wallahi itace, Ummimi ce tana raye tashi mu neme ta I know she is somewhere close to us” kafin ta miqe Anas ya zaunar da ita har a yanzu besan meyake ciki ba tunaninsa duk ya jagule kayinsa na juyawa. K’arfin hali yayi yace, “ba ita bace Flower, Ummimi ta mutu inma bata mutu ba tana chan bangon duniya da mijinta da yaranta saboda haka ba ita kika gani ba lets eat and leave this place.”
   “Hab-” katse ta yayi a tsawace “I said enough ba ita bace!” Ta mugun firgita barata iya tuna when last Anas ya mata tsawa haka ba ‘yar k’ollan dake ciko mata a ido tayi sauri ta shanyesu bata sake ce masa komai ba.
    Sunfi minti biyu zaune ahaka ba tare da sunce da juna ko uffan ba, abincin gabansu ma duk sun kasa chi as Fannah ta zura wa Anas daya zurfafa cikin tunani ido.

      _What if abinda Fannah ke fad’i gaskia ne dan kuwa be tab’a fad’a mata asalin sunan Ummimi ba how comes zata sani inhar bawai taga Ummimin bane dagaske. Amman kuma is it possible? Meze kawo Ummimi New York? Dakansa ya amsa wannan tambaya._
     _Ai koda tazo tafiya ce mana tayi wanda ze aureta yace ze kaita k’asar waje meaning k’asar waje nan New York ya kawota kenan?_

    Kai ya girgiza a sauri “No it can’t be!” yayi maganar a fili. Hankalin Fannah yayi matuqar tashi ganin hankalin Habeebinta ba’a kwance ba.
     “Habeebi is okay kaji? Ya isa haka Abu Hanan.” tasa hanky ta share masa zafaffun gumin dake k’eto masa. “Lets go” yace da ita tare da miqewa ya riqo hannunta suka fito suka kama hanyan lot kamar ance Fannah juya ta juya idanunta basu sauk’a ako ina ba sekan Ummimi dake tsaye daga bakin k’ofan Restor d’in, sanye take da hijabi bak’i iyaka guiwa fuskarta duk alamun hawaye, kallo d’aya za’a mata agano tsantsan rashin kwanciyan hankali da wahala tattare da ita amman duk da hakan kyawun halittan fuskarta wanda su Anas suka d’auko be gushe ba.

     “Habeebi” Fannah takira sunansa tare da dakatar da tafiyarta badan yanaso ba yatsaya shima batare da ya raba hannayensu ba. “What is it Flower? Lets go!” Yayi maganar cikin wani erin murya. “Habeebi ka juya ka ganta gata chan” a hankali yake karkato da kansa har ya juya gabad’aya sannan ya d’ogo blue eyes nasa ya miqar basu sauqa ko ina ba se akan Ummimi. Kallonta yake cike da rashin yarda, sam yakasa yarda Ummimi ce yau a gabansa shekaru nawa rabuwansa da yasata a ido? 15 good years, memories na incident daya faru lokacin tafiyar Ummimi ne suka soma masa yawo a k’wak’walwa.

      “Anas” yaji muryar Ummimi dake nan kamar na Amal na tsamo sa daga duniyar tunanin daya wula, a gabanshi yaga Ummimi tsaye idanunta cike dam da hawaye tana kallon cikin idanunsa. “Anas... My.. My... My son... Anas my son” tasa hannu akan kumatunsa tana shafawa a hankali ayayinda k’arfin kukanta ya dad’u, shi kansa Anas idanuwansa sun kad’a sunyi jazir, he don’t even know what he is feeling fatansa kad’ai Allah sa dukkannin wannan mafarki ne.
     “Anas my son kamin magana dan Allah.” Hannunta ya sauk’e daga fuskarsa cike da k’in yardan itance a gabansa. “Ummimi?” Ya kira sunanta. “Kece?”
    “Nice Anas, Ummimi ce mahaifiyarka, Ummimi ce your own very real mother, Anas nice.” Duk yadda yayi dan shanye kukan yakasa besan a lokacinda yasoma zubar da hawaye ba, Fannah dake tsaye a gefensu tayi shiru ta k’ure musu ido tana kallon yadda suke zubar da hawaye.
     “Anas kayi min magana please” yunk’urin hugging nasa tayi wanda sakamakon haka yaja baya da wuri. Hannun Fannah ya rik’o “lets go Flower” nan ya juya.
   
    “Anas!... Anas! dan Allah ka tsaya.” Cewar Ummimi cikin sautin kuka. “Habeebi please ka tsaya ka saurareta kaji please” Fannah tayi maganar tana k’ok’arin tsayar dashi amman sam yak’i saurarenta. Murfin motan ya bud’e mata “get in!”
   “No Habeebi I’m not getting in, taya zaka bar mahaifiyarka haka?”
    “Fannah kinga banason abinda ze had’ani dake just get in” zata sake magana ya daka mata tsawa “I said get in!” Shi da kansa yasata cikin motar sannan ya zagaya ya shiga shima ya kunna motar. Ta window Fannah ke kallon Ummimi dake kuka sosai tana bin motar nasu da kallo amman Anas kota kanta beyi ba.

  **** _Some hours later..._
     Zaune Anas ke akan wresting chair yayi shiru, tun dawowansu bema Fannah magana ba itama haka bata huce da masifan daya mata ba d’azu ba, zaune take kan gado tana kallon sa a nitse ta miqe taje ta samesa tana tsaye akansa amman ko kewayowa ya kalleta beyi ba. “Habeebi” ta kira sunansa tare da zama kan cinyansa.
    “Yes Flower” yayi maganar not paying attention to her, hannunsa ta d’aga ta had’a da nata. “Habeebi I’m sorry for crossing you earlier.”
   “Is okay Flower ni yakamata in baki hak’uri for shouting at you I’m sorry kinji?”
    “Ba komai ya wuce muje mu huta.” Kai ya kad’a mata “banajin bacci just go, nap well Baby Hanan” yayi maganar hannunsa kan cikin Fannah.
   “Mesa baraka kwanta ba Habeebi ba haka na sanka ba tunanin Ummimi kake?”
    “I don’t want to talk about her Flower jeki huta.”
   “Habeebi yakamata ka cire son zuciya kayi facing reality, duk abinda Ummimi ta maka kamata yayi kayi hak’uri ka yafe mata, uwa uwa ce yanzu zakaso ace Hanan ta min kalan abinda ka ma Ummimi?”
    “For God’s sake Flower kidena kwatanta Hanan da Ummimi, Allah raba Hanan da halin Ummimi banason maganan ta karki sake d’auko min maganar ta.” Zata sake magana ya katse ta “am I clear?” Badan tanaso ba ta gyad’a masa kai ta sauk’a kan cinyansa ta koma gado ta miqe. Batasan a lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba.

     A hankali ya miqe ya nufa wardrobe tare da ciro wallet nasa family picture’nsu ya bud’e yana kallon fuskar Ummimi. “Why do you have to show up Ummimi? Why? Bayan duk mun mance dake munyi moving on mesa zaki dawo ki sake hargitsa mana rayuwa as you did before, why? Mesa bakida tausayi ne?” Ganin bayida amsoshi ga wannan tambayoyi ya haye gadon ya kwanta a gefen Fannah tare da kwantar da ita jikinsa hannunsa na akan cikinta.

   “Hanan in shaa Allah baraki d’au halin Ummimi ba, baraki ma yaranki abinda Ummimi tama Daddy’nki ba.” Daidai nan Hanan dake ciki tayi kicking take Fannah ta tashi “Habeebi Hanan ta motsa yanzu” murmushi ya k’irk’iro mata “yes Flower nima naji” hannunsu duka suka kai kan cikin nan Hanan tasake motsawa. Dad’i kamar ya cinyesu both suna feeling baby Hanan insu.

    ****
     _Washegari 1:30PM_
   Anas na tsaye a gaban mirror a bathroom fuskansa shaving cream ne da alama shaving zeyi danko riqe yake da shaving stick a hannu amman sam ya kasa yi, gabad’aya hankalinsa bayya a jikinsa ko bacci yakasa jiya se tunanin Ummimi yake, duk yadda yasan ze iyabi dan hana tunaninta yayi amman ya kasa the more yana hana kansa the more yake tunanin nata, Fannah ma takasa bacci ta zauna awake with him ko kad’an bayason maganan Ummimi koda Fannah ta taso da maganar masifa yake mata sosai wanda shima ba a son ransa yakeyi ba, he just can’t take it.

    Ya zurfafa cikin tunaninsa next abinda yaji shine hannun Fannah akan nasa tana amsar shaving stick d’in kwata kwata besan lokacin da ta shigo ba. Sanye take dawani silky dogon riga me spaghetti hands. “Habeebi take it easy please banason ina ganinka cikin damuwa.” Juyo da fuskarsa tayi ta soma yimasa shaving d’in lightly kamar yadda take ganin yanayi. Bece mata komai ba har seda ta gama masa ta wanke mai fuskar tare da share ruwan da towel. Kallon kansa yayi a mirron, sosai shaving d’in yamasa kyau saboda bata kwashe gashin duka ba, tabar sajen da kuma beard nasa wanda suka had’e kad’an very light irin na larabawan nan sosai yayi kyau.
   “Flower kin ma fini iya shaving d’in ban tab’a leveling haka ba” yayi maganar yana shafa kan gashin fuskar nasan. “Thank you sweetheart.”
   “No big deal Habeebi” Hannayenta ya had’a gu d’aya tare da pecking nasu, “Flower ko baki fad’a ba nasani you are mad at me saboda abubuwan dana riga miki jiya, I’m sorry kinji? I’m sorry for shouting at you and Hanan”
     “Na sani Abu Hanan you don’t have to be sorry komi ya wuce muje muci abinci amman yau ba anan nakeson chin abinci ba.”

    “Fad’i duk inda ke da Hanan kukeso muje muchi.”
  “A Restaurant Manhattan mukeso” (inda sukaga Ummimi jiya) kai ya girgiza mata “no Flower baramu je chan ba choose any other place amman banda chan.”
    “Ayya Habeebi chan nakeso.”
   “Flower NO! And that stays that bara muje chan ba.” Ba tare da tace komai ba ta k’wace hannayenta daga nasa ta fice zuwa d’akinsu tare da kwanciya kan gado tana jin footsteps nasa ta soma rera kukan qarya.
    “Flower yanzu kuka kike saboda nace bara muje chan ba?” Yayi maganar yana k’ok’arin d’agota. Shuresa ta shiga yi “ka sakeni nikam bana so stop touching me.”
    “Haba Mom Hanan I’m sorry kinji?”
  “Banji ba ni ka sakeni.” Kunnuwansa ya riqe both “Flower I’m sorry kiyi hak’uri.” Da hanzari ta suk’e hannayen nasa “ni bance kabani hak’uri ka ka kaini Restaurant Manhattan kokuma karka sake min ko Hanan magana.”

   “Flower kiyi hak’uri mana ki zab’i wani restor daban.” Banza dashi tayi tare da juya masa baya. “Mom Hanan magana fa nake miki...” Nanma shiru “Mom Hanan” still shiru “toh naji tashi muje Restaurant Manhattan d’in” a ransa yana me addu’an Allah yasa kada su had’u da Ummimi. Cike da ji dad’i ta miqe tare da brushing masa ligjt kiss a lips “thats my Abu Hanan! Lets go” kallonta kawai yake cike da adoration.


*© MIEMIEBEE*

 beeenovels.blogspot.co.ke

12 comments:

Abusuhaylarh said...

tnjk you a lot dear mrs. miemie

Unknown said...

Sabon babi kenan yayi Allah yaqara basira

Unknown said...

Wannan book is killing me every single day😂😂thnka dear

Unknown said...

Wannan book is killing me every single day😂😂thnka dear

Unknown said...

😂 Allah ya kara miki basira and thumb up👍

Unknown said...

Weldondear

Unknown said...

Weldon dear

Unknown said...

Tanks sis

Unknown said...

One trouble has gone nd another is back again

Unknown said...

Pls sis ki kara mana

Unknown said...

Sis we re Waiting oooo

Unknown said...

Sis