BY MIEMIEBEE
Kallonta yake kamar TV a yayinda take sauri sauri tayi tagama dan zuwa samin Yusuf. Guda 4 tayi cikin goma amman wani zogi hannunta ke mata saboda tsawon mails d’in, idanunta ta d’ago tareda maraice fuska koze d’an ji k’anta. Sosai shima yaji ta basa tausayi amman kuma ya ya iya? In yace tabari definately zata je ta samu Yusuf abinda baiso kenan, shikuma bayasan raini bayasan tasan kishinta yake ta d’au ko sonta yake (ni Miemie nace toh da ba sontan kake ba?) Yanason ce mata barata fita da Yusuf ba amman bayasan ta d’auka da wani manufa ta d’au ko santa yake kanta ya soma girma. Kansa ya kawar daga gareta kawai dan kar tausayinta ya kama sa tare da concerntrating akan laptop nasa.
Bayan tasamu tayi guda takwas ta d’ago kai “Mr. Fauzi please kayi hak’uri nagaji.” Banza da ita yayi. “Mr. Fauzi please” nanma bece da ita komi ba dan yasan muddin bakinsa ya bud’u zece ta ajiye shikenan, abinda baiya so kenan. Wayarta ne ya soma ringing tana kai dubanta taga Yusuf ke kira bayan ta d’aga tace, “Yusuf I’m sorry wallahi aiki ne yad’an rik’eni amman I’m almost done yanzu zan sauk’o.” Nan ta katse.
Anas dake sauraronta yace a ransa yanzu zaki sauk’o ba? We shall see. Bayan 10 minutes tagama, wani hamdala ta saki se murza yatsunta take dan azaba. “Sir gashi na gama” ta sanardashi alokacin da take tsaye gaban table nasa. Amsa yayi yana dubawa one-by-one komai yayi sede bayasan ya barta ta tafi, taya zataje tayi having lunch da Yusuf bayan gashinan, bayan tasan tare suke ci always, Isn’t he her boyfriend? Ai koda relationship nasun na k’arya ne still be kamata ba. Besan meh ba amman yanzu bayasan ganin Fannah da wani d’a na miji in ba shiba.
“Sir can I go now?”
“Wait” yace, tare da zaro d’aya daga cikin papers d’in “seda nace miki be careful banason cancelation kalli nan. D’au new plane sheet ki sake copying.” Kamar wacce zatayi kuka tace, “ayyaahh manaaaa Sir mana, letter ‘f’ nefa kawai nayi canceling its not looking rough ai.”
“Ma ke kenan, to me it is morethan rough...” Yacigaba da duban sauran nan ya tsakula wasu guda ukun da tad’anyi light mistakes, in aka had’a dana farkon hud’u kenan. “Recopy them all duk kinyi omiting mistakes”
Baki ta sake, “Mr. Fauzi wallahi barin iya ba dan Allah karka min haka.”
“Miss Aleeyu what is wrong with you? I am paying you bawai aiki kike min kyauta ba d’auka kije ki zauna ki gama yanzu.” Ya fad’i authoritatively tare da kawar da kallonsa daga gareta. Harara mai rai da lafiya ta watsa masa ganin bai ganinta sannan ta tattara ta koma ta zauna. Yusuf takira ta basa hak’uri kan fitarsu bareyi ba seko next week saboda tasan ba yanzu zata gama ba, hannunta yayi tsami layi d’aya ta rubuta seta tsaya taja yatsunta.
“Ba komai” yace “Allah kaimu” tare da katsewa.
Dad’i sosai Anas yaji dayaji tace ta hak’ura. Kallonta yake tayi ta tsaya tayi ta tsaya tana gama guda d’aya tausayinta ya kama sa, tasowa yayi daga kujeran sa ya nufo gabanta, ita a zatonta ko yaga mistake na ‘a’ da ‘e’ da tayi ne yazo mata masifa. A maraice tace, “Sir dan Allah kayi hak’uri don’t make me recopy it please, wallahi guda d’aya ne kuma bara’a gane ba” ta k’are maganar kamar wacce zatayi kuka. Tsugunawa yayi a gabanta, ido wuru-wuru ta zaro meyake shirin yi? Kafin ta kawo wani abu a ranta ya ja hannunta a hankali, bugun zuciyarta taji ya k’aru, a hankali take k’ok’arin k’watan hannun nata gudun karya k’ara mata wasu papers d’in. Biron ya amsa ya ajiye tare da bud’o tafin hannunta me uban laushi yana mata tausa a hankali daga kan yatsunta har zuwa wrist nata.
Har wani sanyi sanyi takeji saboda yadda hannun yayi tsami yana mata ciwo amman kuma be kamata tabar masa hannunta yana tab’awa harda mata tausa ba. “Ermmm Mr. Fauzi” ta fad’i tana k’ok’arin karb’e hannun nata, sarai yagane tanason k’watan hannunta ne amman be kula ta ba, hasali yi ma yayi kamar be san tanayi ba, sanda ya tabbata ya mata tausan da yaci ace hannun ya bar zafi ya bari. Mik’ewa yayi ya koma ya zauna ba tare da yace da ita komi ba, dukda kuwa so yake ya bata hak’uri amman inaaa girman kai!
Bayan ya zauna ta d’aga biron daga inda ya ajiye da nufin cigaba da rubutun tunda ba cewa yayi ta bari ba. Bece komi ba har yanzu se da yaga zata fara rubutun. “Keep the pen, stop it, don’t write.” Ya bata wannan commands. Kallonsa take fuskarta d’auke da kan mamaki. “Sir bangama bafa-”
“I know” ya katse ta, “just kibari don’t write again.” Dad’i sosai taji yanzu seta samu tafita da Yusuf ma tunda Boss yace tabari. Arranging papers d’in tayi ta kai ta ajiye masa kan table sannan ta koma ta d’au jakarta ta saqala, duk kallonta yake bece komai ba seda ta kai bakin k’ofa ya daka mata kira “Miss Aleeyu!” Har tsakiyar kanta tajiwo muryarsa. Juyowa tayi tana b’ari dan firgitan da tayi. Toh me tayi kuma yanzu? Da hannu yayi gesturing nata kan tazo. Taku take k’afa na rawa har takai gaban table nasa.
“Who asked you to leave?” Ya tambayeta yana kallon cikin idanunta. Da sauri ta kawar da kallonta elsewhere ba tare da tace komai ba. “Am talking to you!” ya fad’a ad’an tsawace duk ransa yabi ya b’aci har yanzu be yarda Yusuf nada gut daze ce zekai Fannah cin abinci ba, yaushe ma yagama ciyar da kansa kuma awani local restaurant zekaita ko hotel ma bare iya kama musu ba to talk more of ya musu reserving.
I’ina tasoma “ermm.. Si.. Sis.. Sir naji kace in ajiye in bari kuma aikin daka sani kenan.”
“Amman nace ki tafi?” Kai ta girgiza a hankali. “Good kinga book shelve d’in can?” Kai ta giad’a tana kallon shelve d’in. “Jeki min arranging nasu.”
Kallon shelve d’in ta tsaya yi nakusan ‘yan mintuna sannan back to Mr. Fauzi. Itade bata ga abin gyara cikin shelve d’in ba ga books nan duk anyi arranging nasu tsatsaf. “Bakiji me nace bane?” Ya tambayeta.
“Naji Sir amman kuma naga ba abin gyara ciki, shelve d’in is well arranged.”
“Toh ni banasan arrangement d’in na hannun dama a k’asa nakeson su koma hannun hagu a sama. Na tsakiya ki dawo dasu second to the last row, second row ki raba into two a 4th raw...” Haka ya ringa juye-juye. Kallonsa take kamar tayi kuka, ita ba abinda taji ma inbanda na hanun dama a k’asa su koma hannun hagu a sama.
“Well baraki fara bane?”
“Zan fara” ta amsa sa a takaice murya k’asa k’asa. Jakarta ta ajiye ta nufa wajen book shelve d’in. A hankali ta fiddo da na saman tayi replacing nasu dana k’asan kamar yadda ya buk’ata, a yayinda shikuma ya katse duk wani abinda yakeyi yana kallonta ko kyafta ido baiyi.
Itade Fannah arranging take yadda taga dama, chan ta tsaya admiring wani latest english novel data jima tana nema bata samu ba. «Half Bad by Sally Green» kusan na minti biyu tana kallon littafin sannan ta had’a da sauran ta cigaba. A takaice de seda ta kusan awa tagama had’a uban book shelve na Anas dake nan kamar library. Daidai lokacin k’arfe 11:30AM kenan. Tagaji iya gajiya.
“Sir na gama” tace all exhausted, ga wani uban yunwan daya keto mata lokaci guda. Bece da ita komai ba illa d’akinsa da ya nufa bayan like 5 minutes ya fito se k’amshin turare yake, gashin kansa ma ya sake gyarawa, kallonsa Fannah ta tsaya yi. “My girlfriend” yace da ita yana kallonta dawani killer smile tattare da fuskarsa shikansa yasan yayi kyau yau. Zuciyarta taji ya tsallaka bugu uku lokaci guda, kai ta d’ago a rikice tana kallonsa da ita yake koko a’a. “Me?” Ta tambayesa tana nuna kanta.
“Yes you, you are my girlfriend ko kin manta ne?” Lallai ma! Kallansa take cike da mamaki yanzu yagama azabar tar da ita yawani zo yana shegen murmushinsa yana kiranta girlfriend nasa. “I’m hungry muje muci abinci nasan kema you must be hungry.” Yunwan takeji amman ta dake “no I’m not ni barinje ba kawai ka sallameni in koma gida.”
“No ba gidan da zakije, we are going to eat, oya stand up na baki 5 minutes kije ki kimtsa a office naki.” Yi tayi kamar bata ji saba.
“Miss Aleeyu! Don’t try my patience.” Ganin bai kallonta ta galla masa harara kan zata cire idanta sannan ta mik’e tare da jan jakarta ta fice zuwa office nata wajen book shelve d’in ya nufa yad’anyi dube-dubensa. Exactly after 5 minutes d’in yafito daga office nasan itama a daidai lokacin ta fito.
Light makeup nata ta gyara ta hanyan k’ara powder da zalla datayi sekuma d’aurinta data sake gyarashi. Gyalen nanan yadda yake d’azu ta yafasa kamar yadda Afrah tamata d’azu. Kallonta yake wane ze had’iyeta. A hankali cikin k’asaita ya tako gabanta gam ta rufe idanta tana jiran ya fara suburbud’a mata surutu setaji ya kama hannunta take ta bud’e idan so take tace masa ya sake mata hannu sekuma ta tuna there will be no point doing so dan ba jin maganarta zeyi ba. Wajen elevator’nsa suka nufa bayan daya bud’u tace, “Sir semun nunawa duka ‘yan office naka muna dating ne? Kabari in mun fita anan amnan yanzu ka sakemin hannu please.” Ko tanka ta beyi ba illa janta waje da yayi suka soma tafiya.
Take floor d’in yakama da surutu da gulma kowa se tofa albarkacin bakinsa yake k’us-k’us dan sun san halin Boss yanzu seya buga fire! Kunya ne ya rufe Fannah kamar ta nitse k’asa yanzu shikenan zasuce daman abinda ita da Mr. Fauzi keyi kenan kullum a office nasa, soyayya. Da idansu ya had’u da receptionist kuwa harara ta watsa mata dan ta jima da fad’awa tarkon san Mr. Fauzi koda ta fad’a masa kuwa tatas ya mata ya k’yamace ta. Ignoring nata kawai Fannah tayi, Yusuf dake shigowa yanzu ne yagansu tare da Mr. Fauzi amman ko kad’an idanunsa be kai kan hannun su ba.
“Fannah!” Ya danna mata kira a yayinda ya gama k’arisowa kusa dasu. “About the lunch I think zamu-” be k’are maganar ba idansa ya sauk’a kan hannun ta dana Boss. Ido wuru-wuru ya zaro sekace a mafarki! Me had’in Fannah da Boss to kodai soyayya sukeyi? Fannah da hanaklinta zatayi soayayya da me shaye shaye?
“Oh I’m sorry bansani bane daban gayyaceki lunch d’inba” ya fad’a tare da juyawa. Fannah ji take kamar ta nitse k’asa. “Yusuf” Mr. Fauzi ya kira sunan sa chak ya tsaya tare da kewayo wa. “ *SWEETHEART* baki sanar dashi bane dama? Why?” Shiru tayi bata amsa saba. “Tell him now to clear all doubts.” Nan ma bata tanka saba.
Hannunta dake cikin nasa ya matse yadda ze d’an mata zafi.
“Na zata na fad’a masa, Yusuf I’m sorry.”
“Sorry for what? Don’t apologise *HONEY* fad’a mashi yanzu.” Shiru tayi duk takaici yabi ya cikata.
“ *QUEEN*,ko yunwan ne bakiya son magana? I’m sorry yanzu zamuje muci abincin just tell him kinji *HONEY BOO?* ” Wai meke damun Mr. Fauzi ne ta tambayi kanta so yake yayi ruining friendship nata da Yusuf ne ko me? In yacigaba da abinda yakeyi ai se Yusuf ya d’au k’arya ta masa d’azu batun aikin dayace ya mata yawa, se yace ko k’arya ta masa daman fita zatayi da Mr. Fauzi take b’oye masa.
Ido kawai ta rufe tace, “Yusuf I’m sorry ban fad’a maka ba, Anas is now my boyfriend excuse us please zamuje muchi abinci.” Mamaki ne sosai ya ratsa Yusuf lallai ma Fannah tacika ‘yar halak.
“I’m sorry for delaying you, by the way congratulations” a sanyaye ya juya yayi tafiyarsa, binsa da kallo Fannah tayi, ji take kamar tayi kuka, mesa Mr. Fauzi ze mata haka? Bata sake ce masa komai ba har suka isa hotel d’in shi da kansa ya bud’e mata k’ofa se dad’i yakeji saboda yasan definately yanzu Yusuf da yake zaton saurayinta ne ze rabu da ita tunda ya gansu tare.
Abinci kala d’aya ya musu ordering kafin abicin ya iso ba abinda Anas yake inbanda kallon Fannah shi inama haka zata namasa shiri kullum. Duk lokacin data d’aga kai setaga ita yake kallo. Da k’yar kalamun dayakeson kiranta dasu tun d’azu da safe suka fito yanzu, “you are looking beautiful today.” Kai ta d’ago tana kallonsa da mamaki karara a fuskarta. Wayace mata tayi kyau? Mr. Fauzi? Kode k’arya kunnuwanta suke mata. “Eh sir?” Ta tambayesa.
“Not Sir, Anas” yayi warning nata.
“Anas me kace?”
“Nace kinyi kyau yau.” Ido wuru-wuru ta zaro yau wata rana Mr. Fauzi ya yabata, sede bata san meh ba seta tsinci kanta cikin jin dad’i, toh se meh dan yace tayi kyau? Se komai ya faru k’wak’walwarta ta bata amsa. Murmushin jin dad’in datayi k’ok’arin kawar dashi ne ya kub’uta mata, kallon ta Anas yake dad’i yaji yasata murmushi. “Thank you” tace a hankali cikin jin dad’i, take ta nemi bak’in cikin daya tusa mata ta rasa. “You too kayi kyau.”
“I know already ba sekin fad’a min ba, I always look good.”
Toohhhh! Ta d’ago kai tana kallonsa yaga shima ita yake kallo, shegen girman kai tace a zuciyarta wai I always look good irin yasan shi kyakkyawan nan ne, Allah raba mutum da erin wanga hali.
“My girlfriend nasan ban isa in hanaki kallo na ba amman kallon yayi yawa unless you wanna eat me up.”
Wai lallai ma tace a ranta wato shi ya zage yana kallona in ni nad’an kallesa yace wani na cika kallo.
“But Sir naga nima ai kallo na kake, kuma tun d’azu tunda nashigo office naka yau.”
“Toh ai dan na kalleki doesn’t mean anything, ni kawai kallon ki nake saboda kin d’an yi kyau yau kuma ni bada wata manufa nake kallonki ba amman kinga ke kullum cikin kallona kike, day and night kuma da wata manufa kike kallo na. I can see it in your eyes, kallon soyayya kike min nikuma nayi warning naki don’t fall for me.”
Bakin Fannah seda ya kusa fad’i a k’asa dan yadda ta sakosa. “Nide ba kallon soyayya nake maka ba.” Ta fad’a tare da kare kanta.
“Ohonki nide na fad’a miki *SWEETHEART* don’t fall for me.” Dadai lokacin abincinsu ya iso. Waiter’n ranan ne ya kawo musu wanda ta tambayesa nawa ne kud’in plate. “Wow Miss Aleeyu you are looking amazing.”,Murmushin daya k’ayata ta tasaki “thank you.” Wani kallo Anas ya watsa wa waiter’n take yaji wani bak’in kishi ya tokaresa ji yake kamar ya tashi ya shaqure sa ai shi yakamata ya yaba kyan da tayi ba wani daban ba, kuma yayi.
“Can I have your number?” ya tambayeta, “zanso zama abokin ki.”
“K’ato dakai?” Anas ya tambaya a fusace, “toh barata bayar ba. Ko kunya ma bakaji ma mschww! Boss naka zan kira yayi firing naka next time baraka sake cewa kanasan wata da abokanta ba, stupid kawai.”
“Mr. Fauzi I’m so sorry dan Allah naga PA’rka ce am sorry please.”
“She is not my PA she is my girlfriend.”
“Omg! Mr. Fauzi please forgive me wallahi bansani ba.”
“Damuwanka, Boss naka zan kira abincin ma mun fasa ci.” Wallet nasa yaciro ya irga kud’in ya wurga masa.
“Fannah lets go” ya fad’i a fusace. Dakewa tayi, “Anas” ta kira sunansa cikin wani irin salon muryan da bata tab’a amfani dashi ba. “Calm down kaji? Calm down please.”
A hankali yaji hankalinsa na kwantawa. “Calm down please” ta sake fad’i. Idanunsa da suka kad’a taga sun soma dawowa asalin farin kalansu.
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment