BY MIEMIEBEE
Kamar wanda bareyi magana ba yace, “naji tashi mu tafi.”
“Promise me baraka kira boss nasa ayi firing nashi ba.”
“Thats none of your business, he deserves to be fired.”
“Please Anas for me, please karka kira Boss nasa kaji Anas? Please.”
“Fannah no!” Ya fad’a ad’an tsawace.
Fuska ta maraice, “Shikenan tunda d’an wannan ma baraka iya min ba” jakarta ta tattara ta mik’e da niyyan tafiya gyalenta ya rik’o. Da k’yar bakinsa ya iya furta “no don’t go, barin kira Boss nasan ba, just don’t go.” Dad’i taji sosai da murmushi ta juyo tana kallonsa “thank you, so ka hak’ura muci abincin anan?”
“No not here, lets go somwhere” be jira tace wani abu ba yakama hannunta suka fice, gidan baya suka shiga dukansu a yayinda driver ya kunna mota. Ita yanzu Fannah damuwarta d’aya ne yadda zata masa wa’azi yadena rik’e mata hannu, tana son tabisa a hankali ne kar ta had’a masa komai lokaci d’aya shiryuwan ma yace yafasa akoma gidan jiya. Gaban wani makeken hotel driver’n ya tsaya bayan ya bud’e musu k’ofa Anas yafito sannan ita, ciki suka shiga hannunta rik’e cikin nasa sede yau da mutane cikin hotel d’in zaune suna cin abinci ana ganinsu aka soma gulma k’us-k’us. Magana take iya yadda Anas ne ze jiyota.
“Anas kad’an sake min hannu kaga duk maganan mu suke kaji please.” Banza yayi da ita ya nufa wajen receptionist. “I want to reserve this place now.”
“Okay sir bara a sake karb’an customer ba, but bari na cikin su gama please.”
“Kasan ko waye ni? I said reserve it now ka koresu duka I will pay you double of the money.”
Ido ya zaro sosai jin double, “okay sir, bari amusu magana.” Haka mutanen suna ji suna gani aka kaisu wani d’an waje suka k’are cin abincin chan, aka barwa Fannah da Anas kad’ai makeken wajen. Kujeran tsakiya suka zauna ya musu ordering abincin, bayan minti uku abincin nasu ya iso spoon nasa ya d’aga ya soma ci, yayi spoons biyar yaga ko tab’a nata batayi ba.
“Fannah why are you not eating? Acanzo miki ne?” Kai ta girgiza “Anas dole in zakaci abinci sekayi reserving ne?”
“Yes wani abu ne?” ya tambayeta yana cin abincin sa.
“No-” kafin ta k’ara fad’in wani abu yace, “banasan surutu while eating just keep quiet and eat okay?” Kai ta giad’a masa ta soma ci a hankali, kamar kullum yagama yayi zaman jirarta, wayarsa dake ringing ya d’aga “okay then” yace tare da katsewa. Bayan tagama ci ya biya suka fice gidan gaba ya bud’e mata cike da mamaki tace, “Anas ina driver’n yaje?”
“He went somewhere, I’ll be the one to drive, enter.”
“Sir zan tafi da kaina” haka kawai taji batason tana shiga mota dashi kad’ai.
“Miss Aleeyu kina b’ata min lokaci zanje masjid get in.” Zata sake magana yace, “now” a tsawace.
Ta tsorata amman ta dake “sir ni zan tafi da kaina.”
“I’m your boyfriend ko kin manta? Kishiga ko in d’aga ki in saki ciki da kaina.” Miyau ta had’iye tashiga a hankali danko tasan Anas baida kunya tsab ze d’agata. Nan ya rufo k’ofar, not long enough yatada motar, agogon hannunsa ya duba yaga 15 mins to 12:55PM lokacin sallan juma’ah. “Fannah” ya kira sunanta, nan tabar kallon windown da takeyi ta juyo dad’i sosai yake mata yadda Anas ke kiran sunanta ‘Fannah’ cikin daddad’an muryarsa, har setaji ta sake k’aunar sunan nata inama dashi yake kirarta kullum. “Yes” ta amsa sa.
“Can you wait in idar da sallan juma’ah se in kaiki gidah?” Kai ta giad’a masa daga nan be sake cewa komai ba a inda manyan mutane suke parking motocinsu yayi parking nasa a space da aka tanada masa, a kunne yabar motar dan AC’n daya kunna mata. “I’ll be right back.”
“Okay” tace masa tana kallonsa har ya b’ace cikin mutane, shiru ta zauna tana d’an kalle kallenta chan bacci ya d’auketa wanda batasan yaushe ba. Bayan 25 ninutes Anas ya dawo yana bud’e motar yaga Fannah na bacci da wuyanta karkace gefe d’aya, gyalenta kuwa rabinsa ba’a jikinta yake ba hakan yabawa Anas daman k’are wa k’irjinta kallo, yayi kusan minti d’aya yana kallonta sannan take ya kawar da kansa yana girgizawa “no this is not approppriate.” Zagayowa yayi ta side nata ya kwantar mata da kujeran yadda zatafi jin dad’i tare da gyara mata kanta agarin haka d’ankwalinta ya kunce. “Oh no!” Anas ya fad’i k’asa k’asa. Allah yaso ribbon natan be kunce ba, yanayin gashin dake kwance kan goshinta da sajenta ya tsaya yana kallo, besan sanda ya d’aga hannunsa ya shafa kan sajen fuskartan ba, ganin ta d’an motsa yaja hannun nasa baya da sauri gudun kar ya farkar da ita. Mayafinta yaja a hankali ya rufe mata k’irjinta dashi, kanta kuwa d’ankwalin ta ya bud’a ya d’an rufe mata gashinta sama-sama sannan ya rufo k’ofar yadda bareyi k’ara ba.
Side nasa ya nufa ya shiga ya zauna sede sam ya kasa kunna motan a gudunsa kar ya fara driving kuma ta tashi in suka d’an hau kan bomb. Zama yayi tare da ciro wayarsa yana chatting yana zaman jiran tashin Fannah. Bacci sosai takeyi chan ya juyo yana kallonta, kallo na sosai, cameran wayarsa yashiga yayi positioning sannan ya d’auketa picture d’aya, ganin tayi kyau ya k’ara mata d’aya kasa hak’ura yayi seda ya mata pictures kusan hamsin har anan bata tashi ba. Gallery ya shiga yana ganinsu one by one ko d’aya ya kasa deleting cikin hamsin da biyun duk ba wanda be masa ba. Awa biyu Fannah ta d’au tana bacci se 3:00PM ta tashi sam Anas yak’i tada ita meetings guda biyu dayake dashi, Kacallah yakira dan tunasar dashi amman haka ya fasa zuwa dan yadda bayasan ya tada Fannah yace ayi rescheduling kawai.
A hankali ta soma bud’e idanunta har tagama bud’e su fuskar Anas ta soma cin karo dashi sede ba ita yake kallo ba hankalinsa na kan wayarsa. Kanta ta tab’a taji d’ankwalin ya since, data kai dubanta kan jikinta kuwa taga an rufeta da mayafin ta wanda she is sure ba ita tayi ba, toh waya mata? Mr. Fauzi? Omg! Yanzu yaga k’irjina ta fad’a a azuci. Gyaran murya tayi wanda yadawo da attention nasa kanta.
“Se yanzu kika ga daman tashi? You’ve been sleeping for about 3 hours.”
“What?!” Tayi exclaiming tana kai dubanta wajen agogon motan taga 3:03PM “Ya Salam!! Banyi Sallah ba.”
“Toh laifin waye? Shikenan mutum ba’a iya bar masa AC kunne seyayi bacci?”
Kunya taji sosai ita kanta batasan sanda tayi bacci ba. “Kinsan meetings nawa nayi canceling saboda ke?”
Kanta a sunkuye tace, “I’m sorry ai da ka ta dani.”
“Ni ban iya ta da mutum in yana bacci ba, a banza kin samin ciwon kunne.”
“Ciwon kunne kuma?” Ta tambayesa ba tare da ta kallesa ba.
“Yes, da wannan minsharin da kika tayi.”
Minsharin kuma? Ta nanata a ranta. Tunda take ba’a tab’a ce mata tana minshari ba se yau. “Sir but bana minshari ni fah.”
“Awww maqaryaci kikeson kirana kenan?” Ya tambayeta tare da d’age gira.
“A’a ni ba abinda nake nufi ba kenan.”
“So bayan kin gama b’ata min precious time kin sa min ciwon kunne da maqaryaci zaki sak’a min?”
“I’m sorry” tace ba tare da ta kallesa ba. Motar ya kunna suka soma tafiya har bakin k’ofar gidansu ya kaita, bayan ya sauk’e ta tamasa godiya “wait” yace mata. Gefen k’ofar sa yasa hannu yaciro littafin d’azu na «HALF BAD» data jima tana nema ya mik’a mata, kallonsa ta tsaya yi cike da mamaki. “Ungo amshi.” Bata san sanda ta soma murmushi ba “but sir-” katseta yayi “jeki karanta.” dad’i sosai taji wanda ta kasa b’oyewa “Thank you so much” tamasa godiya tare da ficewa, seda ya tabbata ta shiga gida ya juya shima yatafi.
*****
_Washegari..._
K’arfe 8:00AM na safe Anas ya tashi da hoton Fannah yayi sallama danko yana tashi ya d’au wayarsa yakai kan pictures nata daya d’auka jiya. Yafi minti uku yana kallon pictures d’in sannan ya tashi ya nufa toilet bayan ‘yan mintuna ya fito shirin sa na kullum da safe yayi ¾ da vest all in black sannan yafita. Already yasamu kowa kan dining table bayan ya k’arasa ya zauna suka gaggaisa. Amal dake gefensa tace, “Ya Anas ni rabuwa da inyi game a wayarka harna mance.”
“Angel duk game da nake dashi fa kema na miki installing.”
“Ya Anas ni nafison yi anaka.”
“Naji gashi” nan ya mik’a mata wayar.
“Yeyy! Thank you.”
“Wai Amal ke ana breakfast baraki ajiye wayan ba?” Cewar Ummie.
“Ayyi mana Ummie.”
“Ajiye wayan” Abuu ya fad’a ba wasa. “Se in kin gama breakfast naki kiyi.”
Kamar wacce zatayi kuka tace, “Ya Anas kace musu su barni inyi.”
“Toh da Ya Anas da Abuun waye babba?” Cewar Shettima
“Abuu fad’uwa d’aya kawai zatayi seta karya ko Angel?”
“Eh Ya Anas.” Nan ta buga d’ayan tana fad’i tace, “Ya Anas mu d’au selfie tunda duka munsa black clothes.” Ba musu yace, “okay” nan ta shiga snapchat ta d’aukesu, sosai sukayi kyau. Gallery ta koma tana zooming faces nasu mistakenly hannunta yayi gefe aiko hoton Fannah ya bayyana. “Ya Anas wannan ba hoton Fan-” bata k’are maganar ba yasa hannunsa ya rufe bakinta da sauri.
“Shut up kinji?” Sanda ta gyad’a kai ya sake mata bakin. “Don’t tell anyone kinji Angel zan kaiki shopping anjima.”
“Shopping kad’ai Ya Anas?”
“Toh meh kikeso?” Duk wannan magana da suke su Abuu sun zura musu ido suna kallonsu.
“Acanza min waya.”
“Angel kap ajikinku masu iphone 6 nawa ne? Ai naki ne babba.”
“Ni 6+ (plus) nakeso.”
“Toh naji zan saya miki karki fad’awa kowa kinji.” Kai ta gyad’a masa.
“Meh wannan abun da ba’aso a sanar damu”Abuu ya tambaya.
“Babu” Anas ya basa takaicaccen amsa. “Ni zan fice se anjima” ya fad’i tare da d’aukan wayarsa. “Baba na ka fasa karyawan kenan?” Ummie ta tambaya. “Eh Ummie zanje inchi a waje.”
Allah Allah Shettima yake su k’are breakfast yaje yabuga cikin Amal har seta fad’a masa abun. Bayan sun k’are yaje ya sameta kwance kan gado a d’akinta da ipad nata se temple run take bugawa. “Amal” ya kira sunanta alokacin daya zauna kan gadon nata ko noticing nasa batai ba dan yadda hankalinta yabi game d’in.
“Ke Amal!” ya sake kiranta.
“Meh?” ta fad’i tana cigaba da buga game nata. Ganin inba wai amsar ipad d’in yayi ba barata basa hankalinta ba yasa hannu ya k’wace. Kuka ta fashe masa da “wallahi Ya Shettima Allah ya isa nayi nisa fa ka kama ka k’wace kuma sena fad’awa Ya Anas. Kabani ipad d’ina.”
“Da Allah mumu kawai kika san dawata magana nazo miki da?”
“Banasan ji ni tunda garin Allah ya waye ban kula kaba, kabani Ipad d’ina ko in fad’awa Abuu.”
“Haba Angel d’in Ya Anas ‘yar gaban goshi yi hka’uri kiji?”
“Meh?” ta tambaya tana zumburo d’an bakinta.
“Batun hoton da kika gani wayan Ya Anas ne d’azu nakeson ki d’an fad’amin kinji Amluuluu na, ‘yar autar mu guda.”
“O’o ni barin fad’a ba, bani Ipad d’ina.”
Hannunta yaja ta fad’a jikinsa take ta tashi tana mayar da gashinta baya. “My Amaluuluu tell me mana zan kai ki shopping.” Dariya ta b’arke da, “kaida ko ka kai mutum shopping befi ka siya masa chocolates guda biyar ba kace ya isa, banaso. Ya Anas yace ze siya min 6+.”
“Ke dad’i na dake bakida wayo, yaushe Ya Anas ze siya miki 6+ wallahi k’arya yake miki, trust me.” Kafad’a ta buga da nufin o’o.
“Fad’amin mana hoton waye ne?”
“O’o barin fad’a ba, ai dama na fad’a maka wataran zakazo neman abu wajena. Barin fad’a ba ni kabani ipad d’ina.”
“Mumu kawai karki fad’an, tayi tsami maji.” Nan yamata wulli da ipad d’in. “Ke dama ba’a harka dake mschww.”
“Eh d’in mutum ace se gulma.”
****
Anas ne zaune a paint house nasa har yanzu be karya ba pictures na Fannah kawai yake ta kallo, ganin ba mahalicci se Allah kawai ya danna mata kira, ringing d’aya biyu ta d’aga “hello Mr. Fauzi” kasancewar Afrah batta d’akin.
“Fannah” yakira sunanta.
“Na’am” ta amsa.
“I’m hungry.” Toh nikuma nice me baka abinci tace a ranta. “Toh Mr. Fauzi me zan maka? Kaje kaci abinci mana.”
“Not until nasha coffeen ki.” K’arya ta masa, “banida lafiya bareyi infito ba yau Mr. Fauzi.”
Yanaji yagano k’arya take. “Toh shikenan, I’ll look for my beer insha kawai.”
“A’a please karka sha.”
“Then come.”
Nisanta tayi chan tace, “okay, naji zanzo karka sha please kaji?”
“Then kizo da wuri in bahaka ba zan sha.”
“Mr. Fauzi promise me baraka sha ba please.” Shiru yayi bece komai ba “please...”
“Okay.” Nan ya katse. Daman tayi wankanta, d’aya daga cikin had’ad’d’un abayoyin da Anas ya siya mata irin na ‘yan Sudan d’innan tasa. Rolling tayi had’ad’d’e me kyau gashin ta yamata acuci me kyau. Tana fitowa suka had’u dasu Mami tsakar gida suna aikin breakfast da Afrah bayan gaisuwa Mami ta tambayeta “ina zakije haka Fannah da wannan uban kwalya?”
“Kai Mami jan baki fa kawai nasa ko in goge?”
“A’a barsa ina zakije?”
”Mr- I mean Anas ne yake nema na zeyi introducing d’ina ma wasu business colleagues nasa.”
“Aww hakane? Toh Allah kiyaye, Fannah banda yawon banza kinji? Ni na yaba tarbiyyan Anas ba irin ‘yan iskan mazan nan bane amman still ki kiyaye kinsan shi D’A NA MIJI DA SABON SALO yake, a kullum” (book na Lubiee finest!)
“In shaa Allah Mami na tafi.”
“Asha love lafiya, in an sai ice cream kuma a tuna damu” cewar Afrah. Banza da ita Fannah tayi tana fitowa ta tsari napep. In 25 minutes time ta iso paint house na Anas. Golden side bag nata ta daidaita sannan ta k’arisa, bell ta danna yana zaune a parlour ya taso ya bud’e mata. Kallonta yatsaya yi kamar ze cinye ta, sosai abayan ya karb’eta. “Kinyi kyau” yace da ita. Batasan lokacin da ta soma murmushi tana blushing ba. “Thank you” tace tana k’ok’arin kare fuskarta. Gefe ya matsa mata ta shiga, direct kitchen ta nufa ta had’a masa cikin flask biyu harda na gobe sannan ta juye saura cikin cup ta kai masa. “Sir zan koma.”
“No girlfriend wait for me in gama se in kaiki.”
“Karka damu I can manage.”
“No girlfriend your boyfriend insists, kidena so kina kaiwa kasuwa kinji girlfriend?”
“Ni kadena cemin girlfriend please, ai ba cikin mutane muke ba.” Killer smile nasa ya sakar mata sannan ya cigaba da shan coffeen sa yana gamawa ya d’au key’n sa “lets go ko girlfriend?” Ba gardama ta mik’e suka fita shi da kansa ya bud’e mata motar nan suka fice.
Cool music ya kunna a motar. Fannah kuwa in akoi abinda ta tsana befi wak’a ba. “Anas” ta kira sunansa cikin siririyar muryarta.
“Yes Fannah” ya dawo da kallansa a gareta yana tuk’i.
“Nace will you mind turning off the music, please?”
“Why?” Ya tambayeta.
“Anas ba kyau.”
“Mene ba kyau d’in?”
“Jin wak’an.” Ta amsa sa.
“Ke shikenan komai ba kyau, shaye shaye ba kyau, rik’e hannu ba kyau yanzu kuma jin wak’a ba kyau?”
“Mr. Fauzi narkekken dalma ake sama duk me sauraren wak’a a kunne, is better ka kunna karatun Al~Qur’ani kana sauraro mala’ikun rahma suna sauk’a.” Shiru yayi bece komai ba. “Kaji Mr. Fauzi my boyfriend.”
Kallonta ya juya yayi this is the first time take kiransa her boyfriend seyaji kawai yanasan ya fasa jin wak’a ma gabad’aya. “Zaka dena?” Ta sake tambayar sa nanma bece komai ba. “Please Anas, for me, please kaji?”
Kai ya gyad’a mata. “Sir say yes please.” Nisanta yayi “yes zan dena.”
“Yeyy! Mr. Fauzi thank you, now promise me daga yau baraka sake jin wak’a ba.”
“I promise”. Ya amsa ta a takaice nan ya ciro CD d’in yayi wulli dashi waje. “Zan siyo qira’a gobe ko anjima.”
“Yawwa Mr. Fauzi, thank you so much.” Daidai lokacin Kacallah ya soma kiransa bayan ya d’aga Kacallah ya masa wasu bayanau. “Okay bari zanje gida yanzu in duba I think yana d’akina okay. Will call you back.”
“Fannah” ya kira sunanta yadda takeso. “Na’am” ta amsa tare da juyawa. “I suppose to take you home amman I need to get something daga gida it won’t take long kin yarda?”
“Yes ba komai” ta amsa sa. Gaba da gidansu kad’an yayi parking. “I’ll be right back, don’t leave this car kinji ba? Karki shiga cikin gidanmu, am I clear?” Kallonsa take cike da mamaki shikuma rowan gidansu yake? mschww, thank god ba ita tace ya kawo ta ba. K’in amsa sa tayi.
“Fannah Aleeyu am serious karki shigo ni na fad’a miki” yana kaiwa nan ya fice sekuma ya sake dawowa ya kashe AC’n “kafin ki sake min bacci a mota.” Harara ta watsa masa ganin bai kallonta had’ad’d’en gidan dake layin taga ya shiga. “Mschwww sekayi ai.”,Wayarta ta ciro ta cigaba da buga candy crush nata. Bayan minti biyar shiru Mr. Fauzi befito ba har yanzu kaman ance ta d’aga kai ta hango dawakai guda biyu sun fafaro da gudu mutanen kansun ma sun kasa controlling, “wayyo Allah doki! Nashiga uku!” Fannah uwar tsoro ai bata san lokacin da ta fita daga motar ba a 360 bata fad’a ko ina ba se gidansu Anas.
*© miemiebee*
No comments:
Post a Comment