Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 48
BY MIEMIEBEE


     _5:00AM_
  Shettima ne ke knocking bakin k’ofan d’akin Anas, bacci Anas yake sosai wanda ya jima beyi erinsa ba ko jin knocking d’in baiyi. “Bam bam bam! Ya Anas katashi Asubah yayi.”
   Cikin gigin bacci yace, “naji seka b’alla k’ofan neh?”
    “Ya Anas bazaka masallaci bane?” Shi se yanzu ma ya tuna ana zuwa masallaci bayan na juma’ah.
   “Barinje ba zanyi a gida.” Dama amsan da Shettima ke jira kenan, Ya Anas baisan zuwa masjid inbanda na juma’ah daya zamo masa dole sekuma in Abuu ya tilasta masa. A sanyaye ya juya Abuu dake tsaye a parlour yana jiransu ya tambaya, “ya ina wan naka?”
    Qarya Shettima ya masa, “wai kansa ke ciwo zeyi a gidah.”
   “Toh Allah sawaqa.” Da “Ameen” da Shettima ya amsa sa suka fice. Se 5:15AM Anas ya tashi yayi sallah bacci ya koma se 7:00AM ya tashi ya soma shirin office yau kawai yaji yanasan sa jampah kasancewar yau Juma’ah. B’angaren da yake adana jampopin nasa ya bud’o suna nan turum ba adadi, dubawa yake chan yaciro wani sky blue half jampa yasa, se inche tunda nasan Mr. Fauzi be tab’a yin kyau kamar na yau ba, ba k’aramin amsar kayan yayi ba, cufflinks nasa masu tsada yasa. Fefes yafita bayan yagama feshe kusan rabin designer turarukan sa, jakar laptop nasa ya saqalo daidai yafito yaga Abuu zaune kan dining yana shan coffee. Cike da girmamawa yagaishe da Abuu tare da nufan dining space d’in shima dan had’a tea.

     “Ya jikin naka?” Ya tambayesa.
  Jiki kuma? ya tambayi kansa kode qaryan da Shetitima yayi dan rufa masa airi batun zuwa masjid d’azu kenan? “Da sauk’i.” ya amsa.
       Good, Anas I hope kana tsokaci da lokacinka, yau sati d’aya ya tafi cikin 6 months dana baka, kasani ko minti d’aya barin k’ara maka akai ba.” Ko uffan Anas bece masa ba, amman take blue eyes nasa suka k’ada ransa ya b’aci, se faman had’a tea’n sa yake.
   “Anas dakai nake magana.”
   “Naji” yace tare da ajiye flask d’in, tean ma ya fasa had’awa ya gommaci ya tafi da yunwa. Ficewa kawai yayi ransa na tafasa. Yawonsa ya fice se to 8 ya isa office ko amsa gaisuwan da ake masan ma beyi. Ganinsa cikin jamfa duk ya basu mamaki se kallon sa suke.
     “Sir you are looking awesome” cewar Mubarak. Wani kallo Anas ya watsa masa. “You are fired!” Ya daka masa tsawa. “Sir I’m sorry dan Allah kar kayi firing d’ina.” Bello dake gefensa ya basa tausayi. “Sir he is sorry please, consider this.”
    “Kaima kanada bakin magana kenan? Follow him you both are fired kuje ku samu Adam.” Nan ya nufa wajen elevator’n sa ko ya akayi yaga d’an wani stain kan floor d’in oho. “Wa yayi mopping floor d’innan yau?” Baki na b’ari Abdul Hamid dake gefensa yace, “Boss Yakurah ce.”
    “Jeka sameta and tell her she is fired inform Adam yayi replacing nata now, am I clear?”
   Baki na b’ari yace, “yy..yyes sir” nan Anas ya haura zuwa office nasa se huci yake shikad’ansa gawani uban yunwan dayakeji dan rabuwansa da abinci tun jiya da rana.



     *****

      “Ya Fannah kisa wannan d’in mana wallahi yayi kyau kuma ai Ya Anas zeji dad’i idan ya ganki dashi tunda shi ya siya miki.” Cewar Afrah tana mik’a mata wata electric blue gyale.
    “Banaso! Ha’an! Barin sa,ba kema kinsan ba burgeni gyalen nan yake ba, hijabi na mutunci na.”
     “Haba mana Ya Fannah ace saurayinki ya siya miki abu kik’i sawa? Gaskia ba haka ake soyayya ba.”
    Kuma fa haka ne, Fannah ta fad’i a ranta, inhar ta cigaba da behaving bata damu da Mr. Fauzi ba definately Afrah da gane ganenta zata gano bakin zaren wataran. Kai amman kuma bata so, bata son sa gyalen.

      “Barin sa ba ki miyar” ta bata amsa tana k’ok’arin ciro hijabinta daga cikin drawernsu, daidai lokacin Mami tashigo. “Ya Fannah amshi kisa mana.” Cewar Afrah.
   “Meke faruwa ne?” Mami ta tambaya tana k’arisowa cikin d’akin.
  Kafin Afrah tayi magana Fannah ta tareta “ermm babu komai Mami dama Afrah na tambaya ko gyalen hannuntan ya tafi da kaya na.”
   “Eh sosai ma ya tafi, yau kuma gyale za’a sa neh?”
    A kunyace tace, “eh mana Mami ko kin manta Anas ne ya kawo min.”
    “Toh yayi kyau Allah kiyaye hanya.”
   “Ameen Mami.” Gyalen ta amsa gun Afrah dake mata murmushin tsiya yafawa tayi harda rufe kai dashi. “Haba Baaba, meh haka sekace goggo? Ai tsofi aka sani da yafa gyale haka kawo kiga.” Nan Afrah ta tsara mata gyalen sosai tayi kyau.

    “Meh haka?” cewar Fannah tana kallon kanta jikin madubi. “Sekace neman miji zani? Batsan yayi yawa mana Afrah.”
  “Wallahi beyi ba Ya Fannah, dan Allah karki b’ata kibari a hakan.” Da k’yar Fannah ta yarda ta fice, tafi minti biyu tsaye bakin k’ofar Enterprise d’in amman takasa shiga se kunya takeji. Da k’yar ta iya ta shiga Yusuf ta soma tararwa da sauri ya nufi kanta “Fannah barka da kika zo! Dan Allah kije ki ba Boss hak’uri wallahi da safen nan yayi firing mutane uku.”
   
    “Mutane uku?” Fannah ta zaro ido. “Dalili?”
    Nan ya labarta mata komai... “kinsan haka yake in ransa a b’ace, please talk to him.”
   “Karka damu I’ll try.” Nan ta haura sama, jan bakin da Afrah tasa ta sawan dolen ta sa hannu tana gogewa sede koda ta ciro madubi ta duba taga yana nan kan yanzu ta shafa saboda 24hours ne. Tsuka taja, a hankali tayi knocking bakin k’ofar san. “Enter” yace. A hankali ta waina k’ofar ta shiga alokacin ko juyawa yaga waye ne beyi ba as ya zage se masifa yake kan wayan da yakeyi. Kallonsa Fannah ta tsaya yi dan yadda jampan jikinsan ya mugun amsar sa bata tab’a ganinsa da jamfa ba kuma setaga kamar jampan ma yafi amsar body figure’nsa. A’a to kodan bata tab’a ganinsa dashi bane? Wow! amman gaskia yayi kyau kasa kallonsa tayi musamman yadda gashin kansa ke sheqi.

       “Fire them dukansu ukun, fire them and replace them with better ones, am I clear?” Ding! Ya katse wayar. Nan ne ya juyo dan ganin ko waya shigo. A hankali blue eyes nasa suka sauk’a kan Fannah kallonta ya tsaya yi dan wani kyan da tayi, daga kan d’aurinta, yadda ta yafa gyalen, lace d’in jikintan, d’inkin da komai ya masa kyau. Fuskarta kuwa ba inda yakaisa yin kyau, dark red jambakin da tasa ba k’aramin haska skin nata yayi ba. Kallonta yake itama tana kallonsa duk suna admiring kyan junansu sekuma gashi kamar sun had’a baki duk suka sa blue kaya sede nashi light nata dark.

      Haushin da Abuu ya tusa masa ya nema ya rasa daga ganin Fannah. Ita ta fara kau da kai sannan shima ya kawar. A hakali ta tako izuwa gaban table nasa “good morning Mr. Fauzi.” Ta gaishesa beko amsa ba, kallonta kawai yake kai ta d’ago a hankali tana kallonsa taga shima ita yake kallo kuma koda suka had’a ido beji kunya ya kawar da idanunsa daga gareta ba. Ganin kallon bana k’arewa bane tace, “ermmm let me make you coffee sir./ Be ce mata komai ba ta juya.

    2 minutes later ta gama had’awa ta kawo masa tare da ajiye wa agabansa. Ganin baida niyan sha tace, “please take it sir” magana take masa a hankali dan abinda Yusuf yace mata kan ran Boss a b’ace yake yau. Sip d’aya ya kai baki tana tsaye a kansa. “Sir” takira sunansa cikin siririyar muryarta. Be amsa ba illa dawo da kallonsa dayayi a gareta.

   “Ermmm nace can you do me a favour?” Shiru yayi chan yace, “what is it?”
    “Sir please kadawo da wad’anda kayi firing... Please.”
    “No barin dawo dasu ba, bana son shisshigi, just make me coffee and leave ga chan flask d’in achan” ya nuna mata da yatsa.
   “Please fa nace, do this for me please, will you?”
   “No Miss Aleeyu, they are useless workers sesa nayi firing nasu.”
  “Sir saboda ance maka kayi kyau? Is it a crime? Yanzu nima in nace maka kayi kyau sekayi firing d’ina?” Ta tambayesa, shiru yayi bece komai ba.
  “Toh Mr. Fauzi kayi kyau yau, kayi kyau sosai. Is that it? Fire me toh.”

    “No Miss Aleeyu stop it! I can’t fire you, I just can’t.”
   “Why Mr. Fauzi? kamar yadda suke mutane nima haka nake, abinda zaka musu shi zaka min, be fair please.”
   “No Miss Aleeyu, you are diffrerent, kidena had’a kanki dasu. Kina min abubuwa da dama dayaci ache nayi firing naki amman I can’t.”

     “Toh kayi hak’uri ka dawo dasu please kaji Mr. Fauzi? Yi hak’uri this job is their only source of income yi hak’uri zasu kiyaye nan gaba.” Shiru yayi bece komai ba kuma bayida niyyan magana.
   “Mr. Fauzi must I beg on my knees zaka dawo musu da aikinsu? I’ll do it.”

    “No don’t! Zan dawo musu da aikinsu, don’t kneel.” Yayi warning nata dad’i taji sosai. “Sir are you serious?”
    “Yes kije kice Adam ya dawo dasu.”
   Cike da jin dad’i tace, “thank you sir, thank you” nan ta fice taje ta sanar da Adam godiya duka suka riga mata kamar su cinye ta. Bada jimawa ba ta dawo office na Anas. Coffee ta had’a masa cikin flask sede duk sanda ta d’aga kai ta kallesa shima ita yake kallo, har ya soma sata feeling uncomfortable. Gyalen nata tayi yunk’urun d’agawa zuwa kanta.

     “Stop, kibarshi haka” yace da ita. Yi tayi kamar bata jisa ba, se k’ok’arin d’agawa take. “Miss Aleeyu as your Boss and boyfriend I said stop it, okay?” Ya fad’a a tsawace nan ta bari wayarta dake side bag nata ne ya soma ringing nan ta ciro ganin Yusuf ke kira ta d’aga a takaice. “Hello?” On the other side yace;
  “Our life saviour!”
Murmushi ta saki wanda yasake fidda kyanta. “Kai dan Allah, ba komai don’t worry.”
    “Dama kira nayi  dan na sake miki godiya and to offer you a lunch saboda in sake nuna miki godiyata.”
    “Haba Yusuf is it necessary?” Duk wannan waya da takeyi Mr. Fauzi na zaune yana kallonta wani kishi yaji wanda be tab’a feeling ba ya tokaresa jin ta ambato sunan Yusuf wato dashi ma take wannan murmushi sekace an mata albishir d’in shiga aljannah, lallai Yusuf you wanna die ya fad’i a ransa.

     “Awwn! Lunch zaka siya min?... Aww tare zamuje muci?... Are you sure?... Toh nagode zan sauk’o yanzu... Thank you.” Nan ta katse wayar. “Mr. Fauzi zan tafi dama had’a maka coffee kace inzo yi nayi zan tafi, se anjima.”

   Bece mata komai ba as tunanin wani aiki ze bata tayi dan hanata fita da yake. Chan ya duba gaban table nasa yaga wasu mails da Kacallah ya kawo masa jiya wanda za’ayi reprinting nasu. Har takai bakin k’ofa ya kira sunanta “Miss Aleeyu!” Chak ta tsaya tare da juyowa. “Yes Sir?”
   “Come” yace da ita ba musu ta k’ariso. Pen da plane sheets guda goma ya irga ya mik’a mata tare da had’a mata da mails guda goman. “Gashi min copying wad’annan da neat handwriting don’t make any mistakes.” Kallon papers d’in ta tsaya yi sannan takoma kan Anas. “Mr. Fauzi kai kace fa am nomore your PA kuma yanzu kana bani aiki?”
 
   “Yes Miss Aleeyu, na canza mind d’ina ne yanzu in aiki ya taso zan iya saki tunda mu bibbiyu ne kawai, kiyi sauri I need them ASAP.”
    “Ayyah Mr. Fauzi kaifa kace ba aiki yanzu kuma...” Katse ta yayi “hurry Miss Aleeyu yau Juma’ah ne zanje masjid.”
   “Toh Mr. Fauzi ayi printing nasu mana ba sena rubuce su ba.”
   “Yes Miss Aleeyu rubuce su nakeson kiyi hurry up go and sit acan.” Zata sake magana yace, “now!” A d’an tsawace. Batada wani option haka taje ta zauna tafara copying tana rubutawa. Kallonta yake. Daidan ki kenan se muga ya ke da Yusuf d’in zaku fita lunch. Yace a zuci. Huh! Nima yunwa nakeji bari ta gama muje muci breakfast/lunch tare daga chan sena wuce masjid.


*kuyi hak’uri abinda yasamu kenan yau*
*© miemiebee*

No comments: