Saturday, 28 July 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 26



    Asuban fari alarm na Afzal yayi ringing, bayan ya kashe ya kunna bedside lamp ya kewayo yana kallon Nazeefah dake ta bacci a hannunsa cikin kwanciyan hankali. Peck yayi placing mata a goshi had'e da furta "Allah sassauta miki wannan kishi Rabba'atul Bait, I love you" cike da dabara ya rabata daga jikinsa ya sauk'a daga kan gadon ya nufi bayi. Bayan ya fito yayi shirin zuwa masallaci sannan ya shiga tayar da ita.

  "Ta shi kiyi sallah zan wuce masallaci" yana tabbatar da ta tashi ya fice.
  Dawowansa ya tarar Nazeefah bata d'akin dama yasan za ayi hakan. Kwanciya yayi kan gadon ya koma bacci kasancewar yau Asabar ne ba aiki. Se wajajen goma sha d'aya ya tashi bayan yayi wanka ya d'au wayansa ya fice parlour inda ya tarar da Nazeefah zaune kan kujera tana faman latsa wayanta. K'amshin turarensa ne ya buga mata hanci, ba shiri ta d'ago kai tana kallonsa ba k'arya yayi kyau ina irin morning shower glow d'innan? Se wani k'yalli fatan jikinsa yake k'ark'ashin ranan dake haskowa ta window. Daga bisani ta kawar da kanta badan wai kallon sa ya isheta ba se don haushinsa da take ji.

  "Rabba'atul bait yau ba gaisuwa?" Ya tambayeta yayin da yake takowa zuwa inda take. Shiru ta mai ko kallonsa bata sake d'aga kai tayi ba. "Good morning Babe" ya gaisheta had'e da sauk'e mata light kiss a gefen baki. Hannu tasa ta dirje cike da takaici wanda ya mugun basa dariya amma ya dake tare da yin tari dan korar da dariyan.
  "Islamiyya fa yau bazaki je ba?" Shide a dole seya sata magana.

  "Mallam kana damuna da surutu please."

  "Rabba'atul Bait please kiyi hak'uri haka nan" ya fad'a had'e da zama a gefenta "Nasan nayi miki ba dai-dai ba and I'm sorry bazan gaji da baki hak'uri ba but please kar ki 6ata tsakanin mu saboda Amal."

  "Seka fasa aurenta tunda baka son tsakanin mu ya 6aci as simple as that."

  "Tayaya kike tsammanin zan iya fasa aurenta bayan an riga an gama komai, mey kikeson incewa iyayenta bayan nan duk hidiman da Abba da Ummi suka yimin ya tafi a iska kenan?"

  "I don't care, kade sani zaman lafiyanka da na ita karuwar taka yayi depending akan hakan."

  "Subhanallahi! ki daina kwatanta Amal da karuwa Nazeefah tunda bata yi miki komai ba kuma baki ta6a ganinta tana wani alfashan ba."

  "Bata yi mun komai ba?" Ta tambayesa yayinda take k'yalk'yalewa da dariya. "Bata yi mun komai ba fa kace? Tana shirin k'wace mun miji ka ce bata mun komai ba?"

  "Amal bata da shirin yin hakan Nazeefah, wannan abu da kikeyi shi ze sa in nisantar da kaina daga gareki please cut it out."

  "Oh really? So what do you expect me to do then? To fold my arms? K'ara aure fa kake shirin yi, kuma se three weeks to auren kake sanar dani how do you expect me to act? Ince Allah sanya alkhairi?"

  "Hak'urin nan dey shi zan cigaba da baki I know am at fault but abinda kike yin nan kuma ba shi ze hanani fasa auren nan ba kisani fa kaman yadda nake son kasancewa dake haka nakeson kasancewa da Amal, nasan da zafi amma idan kika hak'ura komi mey wucewa ne Nazeefah, I'm never leaving your side and as far as am concerned kece Rabba'atul Bait d'ina not Amal."

  "K'aryar banza kawai" tayi maganan had'e da mik'ewa "Ni zan fita ina iya kai yamma kumma kafin in dawo kuma."

  "Breakfast d'ina fa?"

  "Ban girka ba kana iya samun karuwar taka aww sorry amaryar taka ta girka maka" bata kai da jin abinda zece ba ta wuce d'akinta. Nan da nan ta fito sanye da hijabi shide Afzal bece mata komai ba banda binta da ido da yayi. Gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i Nazeefah isn't at all ready to understand him, anya kuwa ze iya da wannan bala'in da yake neman afka masa?

   Gidansu aminiyarta Rumaysa ta taje inda take bata labarin abinda ya faru.

  "Kar ki gaya mun Babe!" Tayi exclaiming.

  "Wallahil azeem aure Ya Afzal ze sake yi, ga chan akwatunan fad'an kishiyansa ko kallonsu ma banyi ba."

  "Chab! Amma shiko meyayi zafi da ze k'ara aure? Kode kun samu matsala ne?"

  "Wallahi lafiya k'alau Babe ni daya sanar dani ma na kasa yarda I can't believe for all these while he's been deceiving me."

  "Ai na miji bashida guarantee komin dad'in ki dashi idan be ci miki amana ba baya jin dad'i yanzu ya zakiyi?"

  "Wallahi ban sani ba jiya ina gidan Suwy nake tambayarta mafita tace wai mafitar d'ayace."

  "Wai meh?"

  "Malaman tsubu."

  "Boka de!" Rumaysa tayi exclaiming.

  "Hmm ai nima nace ba dani ba a iya fahimtan addinin da nayi Allah na yafe ko wani irin zunubi amma banda shirka har mey yayi zafi akan wata shegiya in jefa kaina ga halaka."

  "Gaskiya kam wannan shawara batayi ba amma shin wacece yarinyar wai?"

  "Ina ko zan sani yanzu haka wata banza ce."

  "Kode ze iya yuwawa yarinyan nan da muka gansu tare ranan a Unimaid garden ne?"

  "Waya san masa ne da uban kwashe-kwashen nan nasa."

  "Tsaya ya yarinyar take? Kin ta6a ganinta ko a hoto?"

  "Eh kuma kinsan mey? Allah ba jiya na fara sata a ido ba tabbas nasan na wayi fuskan nata a wani wajen amma na kasa tunawa."

  "Ke ze iya yuwuwa a school ne tunda chan take itama."

  "I doubt a school ne, a de wani wajen muka had'u da ita omg! Wallahi na tuna tabbas itace wacce mukayi clashing da ita a asibiti lokacin da Ya Afzal ba shi da lafiya, Wallahi itace. Itace wacce Sultan yake tambaya ta ko naga ficewarta kutuma amma an jima ana raina mun wayo!" Tayi exclaiming.

   "Lalle kam ashe har zuwa dubansa tana yi a asibiti."

  "Gashi kuwa am very sure flasks d'incan ma da Ya Afzal yace wai na Umman Sultan ne na yarinyar nan ne wallahi Ya Afzal babban mak'aryaci ne."

  "Ke ba Afzal naki kad'ai ba fa duk maza mak'aryatan kansu ne wallahi sede kawai k'aryan wani yafi na wani, mutanen nan basuda amana ko kad'an imagine yana gadon asibiti rai a hannun Allah amma still yana cin amanarki, tirrr wallahi."

  "Ai shiyasa bazan bari auren nan ya yuwu ba, dole ne in hana aukuwan auren nan."

  "Aikam kada ki yarda wallahi ba da keba kishi da 'yar shuwa."

  "Aww shuwa ce?"

  "Sosai ma bakiga kalan halittarta bane? Shuwa ce kawai ba tayi hasken su sosai bane."

  "Shegiya sena tabbata na lahira ya fita jin dad'i ai."

  "Yanzu ya zakiyi? Lokaci ya riga ya k'ure miki."

  "A'a kam wallahi da saura."

  "Kefa kikace sati uku ya rage, how??"

  "Wallahi ban sani ba one thing am sure of is aure de komin yaya ne baza a d'aura ba."

  "Tsaya tukuna ki kwantar da hankalinki ai ba haka akeyi ba, an dena tada hankali yanzu idan miji ze k'ara aure."

  "Ban fahince kiba so kike kice in nad'e hannu kaman sokuwa in zuba masa ido ya k'aro auren nan?"

  "Nahhh ba haka nake nufi ba yanzu ya tsakaninki da Afzal d'in?"

  "Oho mishi ni tun jiya ban sake yi ta kansa ba, yana ta lalashina yana bani hak'uri amma nak'i hakan. Yanzu haka sau biyu nake girki amma banyi da shi kwanciya ma ba a d'akinsa na kwana ba seda nayi bacci ya cicci6eni ya kaini d'akin nasa muka kwanta, da asuba da na tashi na sake komawa d'akina ba wai shi mata biyu yake so ba ze gani sena d'aga masa hankali ya rasa meke masa dad'i."

  "Lmao kai amma Nazeefah bakida dama" ta fad'a tana dariya. "Wanga gashi haka? Karfa ya k'one."

  "Ki barshi mana, a jiyan ma ai ya neme ni na hana sa kaina na fake da cewa ina haila."

  "Innalillahi! Wallah baki da dama" ta fad'a tana ta faman dariya.

  "Allah bakisan yadda zuciyata ke tafasa bane Rumy, da Ya Afzal ya k'ara aure Allah gara na rasa kwalin degree d'ina."

  "Kai de don Allah!"

  "Wallahi am damn serious, ke bazaki gane irin son da nake yi mishi bane, akanshi fa ina iya yin komi shirka da kisa ne kawai bazan yi ba wallahi."

   "Calm down calm down duk beyi zafi haka ba kinsan mey nakeso da kene?"

 "Sekin fad'a."

  "Pretend like everything is cool kar ki nuna masa auran nan ya dameki in fact ina son idan kin koma gida yanzu kije ki basa hak'uri kiyi tuban muzuru kice kin amince ya k'ara auren."

   "A dalilin mey?!" Nazeefah ta katse ta cike da rashin hak'uri.

 "Ke matsalata dake gajan hak'uri ki tsaya mana ki saurareni."

  "Ina jinki."

  "Yauwa kinga by doing so zey amince dake kuma ze yarda dake."

  "Kaman ya kenan?"

  "Ina nufin zakiyi earning trust nasa ko wani irin 6atancin aka zo aka fad'a akanki da wuya ya yarda koda kuwa maganan daga bakin mahaifiyarsa ce saboda ke kin riga kin nuna masa kin rungumi k'addarar ki a shirye kike da kuyi zaman lafiya da 'yar uwarki. Da fari yanzu zamu bayyana kan mu a dinan auran nasu ne kice masa zaki je don ki tayasu murna, kinga kowa ya ganki seya jinjina miki harta iyayen nata anan kuma se mu samu mu rugurguza musu komai. Babban aikin namu kuma seta shigo gidan, aya zamu gasa mata a hannu, mun ringa had'a kanta dana Afzal d'in kenan ta yadda koda ta fara kai k'aranki gunsa baze saurareta ba sabida ya riga ya amince dake, ya yarda dake, a hankali har k'orafin da take yi masa a kanki ze soma ishansa tunda de ke gashi baki ta6a furta kalman 6atanci akanta ba hasali ma idan kuka zauna da shi yabata kike kinga anan ze fara ganin kaman ita Amal d'in munafika ce tana son ta shiga tsakaninku ne ta fiddaki daga gidan ki. Toh fa anan hankalinsa ze soma karkatowa kanki ita ko idan tayi sake mutuwan auran nata kenan."

  "Wow wannan shawara tayi, amma ai ni auren ne gabad'aya bana son a d'aura Rumy, bani ma son ta shigo gidan bale ta samu d'uwawun zama."

  "Kema kinsan hakan ba me yuwu bane se de idan zaki d'au shawaran Suwy wanda bazan barki ki d'auka ba."

  "Yanzu haka ina ji ina gani kenan zan fara sharing Ya Afzal da wata shegiya ina raba kwanciya da ita?"

  "Karki damu zamu ci mata uwa idan ta shigo gidan, da k'afan da ta shigo dasu zata fita trust me."

  "Promise you'll not fail me babe."

  "Haba har yaushe na ta6a baki kunya I've got you."

  "I know I will always count on you thank you so much."

  "Karki damu kede kawai ki kwantar da hankalinki wallahi kishiya tayi kad'an ta d'agawa mutum hankali. Kuma kinga ke Allah ma ya taimakeki Afzal nada kirki wallahi wasu mazajen idan suka kusa yin aure wulak'anta uwar gidansu suke amma kiga ke fa har wani tattalinki yake kina mai iskaro."

  "Ai yasan abinda yayi be dace bane shiyasa."

  "Even still Babe ajinki maza suna da kunya ne? Wallahi dan wata shegiya achan karki 6ata tsakaninki da mijinki nifa idan nine ke wani irin mahaukacin soyayya ma zan fara nuna wa Afzal d'in yanzu, kin gane ai ki haukatar da shi da soyayyarki yadda ko 'yar shuwan chan bata isa ta d'auke mishi hankali ba."

  "Kai da wuya fah, kinsan shuwan nan da concussion nasu da iya asirce miji."

  "Yafi kayan mata ne, ai da kayan mata suka dogara su ma, dan haka kema zamu nemo miki akwai wata k'awar Mummy tana had'a kayan matan nan kuma bakiga yadda ake saya ba."

  "Kai Babe!"

  "Ina gaya miki, relax kar ki wani tada hankalinki mugun trap zamu shirya wa 'yar shuwan chan seta gwammace kid'a da karatu."

  "Shiyasa nake yinki sosai wallahi har naji hankalina ya d'an kwanta."

  "Ai ya kwanta ma gabad'aya, keda Afzal mutu ka raba wallahi takalmin kaza."

  ****
 Bayan sun idar da sallan Azahar Nazeefah ta d'au Rumaisa a mota sukayi gidan k'awar Mummy suka sai mata masu tsadan cikin kayakin, bayan matar tayi mata bayanin yadda za'ayi amfani da su suka sake komowa gidansu Rumaysan ba ita ta koma gidanta ba se wajajen biyar da rabi. Shiganta parlour taci karo da Afzal zaune kan kujera yana aiki akan laptop nasa. Jakan nata ta rik'e da kyau gudun kar ya zame asirinta ya tonu. Gyaran murya tayi had'e da yin sallama. A hankali ya d'ago kansa tare da amsawa sannan yayi mata sannu da zuwa.

  A ranta sam bata da niyyar amsawa amma dan dole tayi in order to keep up with the act.

  "Kin dawo?" Ya tambayeta yana neman ajiye laptop nasan.

 "Eh" ta amsa.

  "Your food is ready then" da mamaki ta tsaya kallonsa "Girki kayi?" Ta tambaya.

  "Yes spaghetti."

 "Wow!" ta numfasa ai ita ta d'au idan ta dawo gida wani fad'an zasu 6arke da ita. Shin wai shi Afzal d'innan wani irin mutum ne? Ko yayi fushi ma ta fita tun safe amma se yanzu take dawowa? Fa duk yadda takeson ta tsanesa hakan ya gagara sema reasons da zesa ta k'ara sonsa yake bata. "Taho muje in had'a miki ruwa ki watsa se muci abinci ko?" Yayi maganan yana k'arisowa inda take.

  "Ni a k'oshe nake."

  "Ba za kici girkin Ya Rouhin ki ba? Kar kiyi mun haka please" yayi maganan had'e rik'o hannunta cikin nasa. "Let's eat kinji?" Kai ta gyad'a a hankali sannan suka k'arisa d'akin. Bayan ya sirka mata ruwan ya d'auko mata towel ya barta ta cire kayan nata ma yak'i wai sam shi ze cire mata. Haka har bayin ya kaita sannan ya fito bayan ta watsa ruwa ta yi alwala ta fito, wani dogon rigan daya ware mata a gefe ta sanya ta feffeshe jikinta da turare sannan suka fito dining inda yayi serving nasu abincin sukaci. She can say he's very good at cooking saboda ba k'arya abincin yayi dad'i. Sosai take son ce masa girkin yayi dad'i amma tuna yana da niyyan kawo mata kishiya seta fasa. Shi da kansa ya tattare plates d'in bayan sun gama sannan ya ja kujera ya zauna agefenta tare da had'a hannunsu gu d'aya yana shafawa a hankali.

  "Nazeefah I'm sorry kinji? Nasan na miki ba dai-dai ba kamata yayi tun kafin asa rana in sanar dake batun Amal amma son zuciya ya hanani I just want you to know that bawai nayi hakan dan inyi hurting naki bane I just couldn't muster the courage to tell you, I respect you alot Nazeefah gani nake idan na sanar dake ranki ze 6aci ni kuma gudun hakan nake, bana son abinda ze 6ata min ke but I'm sorry if my actions ended up hurting you, I'm so sorry kinji?"

  "It's okay Ya Rouhi ka dena bani hak'uri haka."

  "Eh??" Ya tambayeta cike da k'in gaskata abinda kunnensa suka jiye masa.

  "I should be the one who's sorry, forgive me kaji?"

  "You have nothing to be sorry for Rabba'atul Bait, na fahimci halin da kike ciki and na sani kishi dole ne hak'uri kawai nake son ki k'ara akan wanda kikeyi."

  "Ba komai ya wuce."

  "Kin amince in k'ara auren?" Kai ta gyad'a masa a hankali, janyota yayi ya azata kan cinyarsa ba. "Like forreal? Kin amince?" Nan ma kan ta kuma gyad'awa. Besan lokacinda ya had'e lips nasu gu d'aya ya shiga kissing nata ba, bata 6ata lokaci ba ta shiga mayar masa da martani sun d'au lokaci suna abu d'aya sannan a hankali yayi breaking kiss d'in had'e da rik'o fuskanta "I love you Babe, Allah miki albarka."

  "Ameen Ya Rouhi I love you too." Wani kiss d'in ya sake sauk'e mata a goshi "Thank you so much da wannan had'in kan da kika bani, bazan ta6a mancewa da hakan ba Nazeefah and I want you to put you trust in me kisani zanyi iya k'ok'arina don ganin nayi adalci tsakaninki da Amal you have my words." Hannunta ta d'aga ta zagayesu a wuyansa had'e da sauk'e masa kiss a gefen lips nasa "I trust you Ya Rouhi, I believe in you ka dena damuwa kaji?" A hankali ya zagey nasa hannun a kunkuminta yana me sake matso da ita kusa da shi.

  "Thanks Babe."

  "So tell me a ina kuka had'u da Amal d'in?"

  "Tun kafin muyi aure muke tare da ita."

 "So she was your first love."

  "I'm sorry but yes she is."

 "Wow toh meyasa baka aureta ba tun farkon?"

  "Relationship namu wasn't a love at first sight thing, daga baya ne nayi developing feelings mata and I had to marry you saboda inyi biyayya wa Abba kaman yadda kema kika aureni don yin biyayya wa Daddy ko ba haka ba?"

  "Hakane kam so tell me about her, inda hali inason jin komi akanta."

  "Ask me anything."

 "Like her age, school, family'nsu da komai."

  "Itama yarinya ce kaman ki sai dai zata girme ki da shekara d'aya zuwa biyu haka, sannan tana attending unimaid itama."

  "Haba wani department?"

  "Nursing tana part three."

 "Wow kace mun samu likita a gida kenan so waye mahaifinta?"

    "Ba wata 'yar babban gida bace, mahaifinta ma ya rasu agun kakanta take."

  "Allah sarki wace yare ce toh?"

  "Shuwa ce."

  "Shuwa?" Ta nanata sekace bata sani ba "Ya Rouhi yanzu da shuwa kakeson ka had'ani kishi? Ni na ma yi surrender, ai kaima kasan ban isa inyi kishi da 'yar shuwa ba."

  "Inji waye? Da mey ta fiki ai yadda kike da kyau itama hakan ne."

  "Ba wani ta fini kyau."

  "Amma ai kin fita hasken fata."

  "Bawani ai naga hotonta a wayan ka itama fara ce."

  "Even still kin fita, kyau kuma dukan ku kyawawa ne."

  "Hmm Allah de baka ikon yin adalci a tsakaninmu Ya Rouhi."

   "Se inda k'arfi na ya k'are in shaa Allah Nazeefah shiyasa nake son ki kwantar da hankalinki kisani kece babba a gidan nan, it doesn't matter Amal ta girmeki as far as we all are concerned kece Rabba'atul Bait ba kuma wanda ya isa ya k'wace martaban hakan daga gareki ba."

  "Bawani nasan tana shigowa ka d'anata zaka mance dani tunda gashi Allah yayi sabuwa dal take a leda."

  "Ai kema a sabuwanki na sameki Nazeefah I'll do my best to love you both equally."

  "Toh Allah ya baka iko."

 "Ameen abinda nake son ji kenan taho muje ki duba kayakin naki."

  "Ni bana so."

  "Why? Kayan basu miki ba a dad'o wasu?"

  "Sekuma in kaisu ina? Ai ahakan ma sunyi yawa kaya sekace nice amaryar."

 "Just to tell you how much I love you."

  "Thank you Ya Rouhi."

 "Always babe, taho muje ki duba toh kin ko san zannuwa iri d'aya Ummi ta sai miki keda 'yar uwarki?"

  "Allah sarki Ummi, Allah kad'ai ze iya biyanta." Da haka suka nufi d'akin nata inda ya jera mata akwatunan. Sosai tasha mamakin adadin kayakin da suke ciki tamkar itace amaryar. Bayan sun gama dubawa suka shiga shirin sallan maghrib. Haka nan tun daga ranan ba a sake jin kan Nazeefah da Afzal ba, shawarar k'awarta ta d'auka. Wani irin soyayya da kulawa na musamman ta fara nuna wa Afzal fiye da na da. Afzal couldn't ask for more rannan har buk'atansa tayi da ya had'ata waya da Amal su gaisa, ba Afzal kad'ai ba ita kanta Amal taji dad'in sauk'in kai irin na Nazeefah. Lafiya k'alau suka gaisa har ita Nazeefahn takeyi wa Amal fatan alkhairi.
 
  Tsaf Afzal da Nazeefah suka shirya abinsu yau sukaje duban gidan Amal inda Nazeefah ke ta yabawa kayakin d'akin Amal akan sunyi kyau, hakan ba k'aramin burge Afzal yayi ba, yadda Nazeefah ke k'ok'arin 6oye kishinta don ta farinta masa. Be sanar da ita komai ba bayan kwana uku ta dawo daga unguwa kawai ta tarar an sake furnishing mata parlour da exact kalan kujeru da rug na Amal banbancin kawai color ne. Godiya tayita yi masa, ita kam dad'in har yayi mata yawa, tunda ta nunawa Afzal ta amince da auren nan tasamu wani girmamawa na daban daga garesa, kud'i yake bata anyhow ko bata tambaya ba, ga wani tarerayarta da yake yi.

  A haka ne har Allah ya kawo satin bikin Afzal da Amal wanda aka fara da walima wanda aka had'a da na sauk'an Al~Qur'anin da tayi, ita tazo na biyu a gwajin da akayi musu. Sosai ta samu kyautuka da dama ciki harda kujeran hajji wanda ta bawa Papi, kaman yadda Abba yayi alk'awari shiko kyautan mota ya bata k'irar Matrix. Bayan walima akayi Kamu washegari wanda Amal ta bala'in yin kyau acikin pitch asoebin ta, ga lallen nan da makeup nata komi ya zauna. Afzal kansa ya kasa daina kallonta through out the event sece mata yake tayi kyau. Washegarin kamu akayi wushe-wushe wanda ta sanya laffayan da Afzal ya sai mata. Ranar Asabar aka d'aura aure akan sadaki dubu d'ari da sisin gold arba'in. Da yammacin ranan dangin ango sukazo suka d'aukan amaryarsu, kukan da Amal taci kam ba a cewa komai da k'yar aka samu aka fiddota daga gidan nasu aka kaita family house nasu Afzal inda aka shiga shiryata for dinner. Achan Nazeefah da k'awarta suka saci idan mutane suka d'auke head na Amal. Bayan an gama kwalliya za a shiga d'aurin kai, d'ankwali yace ku neme ni. Ba duban duniyan da ba'ayi ba amma babu hankalin kowa ya tashi gashi lokaci se k'urewa yake. Cikin masu neman head ana jan Allah ya isa aharda Nazeefah da k'awarta.

   Da shirun yayi yawa ne Afzal ya kira Amal don jin ko lafiya.

  "Yaya an d'auke mun head d'ina" ta sanar dashi tana kuka.

  "Kaman ya an d'auke? Tayaya?"

  "I don't know" tana fad'in haka ta katse wayar don yadda kukan yaci k'arfinta. Hawayenta Maamah ta shiga share mata tana bata hak'uri akan in shaa Allah za'a samu. Ummi ya kira next ya tambayeta meke faruwa.

  "Wallahi head na Amal aka d'auke."

  "Tayaya Ummi? Shin baku ajiye mutum ya kula da kayakin nata bane?"

  "An sa wallahi har mata biyu ni kaina ban san yadda hakan ya faru ba."

  "Toh yanzu ya za'ayi?"

  "Akwai wani bridal head wrap na 'yar k'awata Umaima yanzu haka ta fice taje d'auko mata nata da ta sa a bikinta tace color d'in exactly iri d'aya da na Amal ne."

  "Please make sure she looks perfect Ummi and ki bata hak'uri ta daina kukan I love her."

  "Karka damu ka kwantar da hankalinka zan kula da komai" da haka sukayi sallama. Bayan 20 minutes Umaima ta iso da bridal head wrap nata sosai kuma ya shiga da kalan kayan Amal kaman yadda ta fad'a. Nan da nan makeup artist ta d'aura mata da ikon Allah kuma d'aurin ya mugun amsan Amal har ma fiye da yadda asalin head natan ze kar6eta, Nazeefah da Rumaysa haushi kaman ya kashesu. Sosai maroon color d'in ya kar6i skin na Amal se hoto ake tayi mata ta ko ina. Nan da nan aka shiga tafiya, motan ango na isowa su Maamah suka k'arisa da Amal ciki. Afzal na iya rantsewa be ta6a ganin kyakkyawan halitta kaman ta ba.

  "My bride you look so beautiful" ya sanar da ita.

  "Thank you Yaya, you're not looking bad yourself."

  "Is everything okay?" Kai ta gyad'a a hankali "I'm just nervous."

  "I've got you okay?" Yayi maganan had'e da sauk'e mata light kiss akan hannunta. K'aramar murmushi ta sakar masa ahaka har suka k'arasa wajen da za'ayi event d'in. Nazeefah sarai tasan an hana zuwa da yara ta kikki6i wata cousin nata mey shekara shida taje da ita. Ana cikin presentations progammes of event kafin a k'ariso na cutting cake Nazeefah ta tura cousin natan da taje ta ture table na cake d'in. Ana shagali kawai aka ji k'aran rushewan abu a k'asa, da table da cake d'in duk sun tarwatse. Hankalin kowa ya tashi a wajen barin ma na Amal da Afzal wannan wani irin musiba ce? Nan aka shiga tambayan kowa yashigo da yaro sede ba wanda keda masaniya game da hakan, yarinyar ma k'aramar munafuka ana tambayanta wa ya shigo da ita ta bushe ido wai babu mota kawai ta gani ta shigo. Securities kuwa koda aka tambayesu dalilin da yasa suka bari ta shigo se sukace su basu ga shigewarta ba k'ila tabi cikin manya ta 6ace acikin su kasancewar Nazeefah ta biya su kud'i ta rufe masu baki.

   Kuka kawai Amal ta farayi wajen farko head nata aka d'auke yanzu kuma aka tarwatsar mata da wedding cake. Haka aka lalla6a aka kammala event d'in ba walwala tattare da kowa barin ma Ummi data sha aiki don tabbatar da cewa komi ya tafi dai-dai. Se hak'uri Afzal keta bawa Amal cikin motan amma ina ta gagara yin shiru. Ajikinsa  ya kwantar da ita har suka isa gidan nasu wanda se wajajen sha d'aya da rabi k'awayen Amal suka watse ya rage Afzal kad'ai da amaryarsa.

  Kazan amarcinsu ya shigo dashi d'akin inda take zaune a tsakar gadon kanta a sunkuye se kuka take tayi ta ciki-ciki. Ledan ya bud'e yayi serving nata se anan ya tuna be ibo cups ba, dawowan da zeyi kawai ya tarar da Amal tana kuka shark'af-shark'af. Da hanzari ya nufi kanta yana tambayarta ko lafiya amma ina ko amsasa ta kasa banda kukan nata ma daya tsananta.

  "Lily what's wrong? Wani abu ne?" Kansa ne ya mugun d'aurewa kode missing k'awayenta take ya tambayi kansa "Lily please stop crying" hak'uri ya shiga bata saidai ta gagara yin shirun. Daga bisani kawai ta fad'a jikinsa yayin da kukan nata ya tsananta, rungumeta yayi gam a jikinsa yana shafa bayanta yana mey fad'a mata kalamai masu kwantar da hankali. Sun kai tsawon minti talatin a haka, "Lily?" Ya kira sunanta lokacinda yaji tayi lamo a jikinsa. "Lily?" Duba fuskan ta da zeyi ya tarar har bacci ya d'auketa.

  A hankali ya d'agata daga jikinsa had'e da mik'ar da ita akan gadon. Wayanta da ya kusan fad'i a k'asa ne yayi sauri ya tare kafin yace ze ajiye idonsa yaci karo da sak'on da ya nuna last Amal ta karanta wanda ya kasance daga unknown number. Har ya ajiye wayan watak ra'ayin tace masa ya karanta, kasancewar wayan nata ba password haka ya basa daman bud'ewa ya shiga karantawa kaman haka

  _My dearest Princess, today two souls of yours have turned into one, I want you to know that you two are the most beautiful couple I’ve ever seen. May your love grow stronger and stronger during your married life. May you always be together as one and never split apart no matter the difficulties you may face in your future life._

  _Yours Abdul, Xx_ 😘

  Har cikin ransa shima yaji ba dad'i tabbas ya shiga tsakanin wannan masoya guda biyu, Allah sarki ashe akan Abdul take wannan kuka. Mayar da wayan yayi ya ajiye sannan ya rage kayan jikinsa ya fad'a bayi ya watsa ruwa. Da towel d'aure a kunkuminsa ya shiga wardrobe na Amal inda ya ciro mata d'aya daga cikin sabin kayakin baccinta. K'arisawa kan gadon yayi ya shiga tada ita sede ina baccin nata yayi nauyi daga k'arshe ya yanke shawaran barinta ta kwana da kayan kawai sede kuma yayi tunanin kayan zeyi nauyi da wuya idan zata ji dad'in bacci aciki. Outerwear d'in ya cire a hankali ya rage fitted gown na cikin, a hankali ya zuge zip d'in har k'asa har anan bata tashi ba cewa da yayi bari ya ja kayan k'asa mutumiyar ku ta tashi a firgice had'e da k'urma wani d'ankaren ihun daya kusa tunzurar da Afzal daga kan gadon.

  "Shh! It's me Afzal calm down calm down" ya shiga ce mata a hankali yayinda take ta hak'i tana ja da baya.

  "Ba wani abun zan miki ba kayanki nakeson in canza miki gani nayi kaman ya miki nauyi bazaki iya kwanciya da shi ba." Kanta tayi saurin kawarwa ganinsa da tayi ba kaya ajikinsa banda towel dake d'aure a kunkuminsa.

  "Lily?" Ya kirata amma shiru tayi gun se neman kare jikinta take tana tattara wuyan rigar nata sama kasancewar ya zuge zip d'in k'asa se k'ok'arin zamewa yake. "Lily?" ya sake kiranta sede tak'i juyowa ta kallesa murmushi ya sakar gano wai kunyan ganin sa ba kaya take mik'ewa yayi ya nufi side nasa acikin wardrobe d'in ya zaro jallabiya d'aya ya sanya "Juyo to nasa kaya" ya sanar da ita bayan ya dawo ya zauna. A hankali ta kewayo da kallonta a garesa "Taho in tayaki cire kayan kisa wannan ko zaki watsa ruwa tukuna?"

  Kai ta kad'a a hankali.

  "Toh ai ya kamata ki watsa ruwa tunda kin tashi Lily kiyi refreshing kanki you'll feel much better." Nan ma kan ta sake kad'awa "Okay na gane kunya na kikeji ko? Zan fita in baki waje ki shiga kiyi wankan idan kin shirya sekiyi mun magana okay?" Ganin bata da niyyan amsa sa ya mik'e ya fice. A hankali ta janyo wayanta ta shiga sak'on da Abdul ya tura mata had'e da sake karantawa yayinda wani kukan ke neman kauce mata. Typing reply tayi as;

   _Thank you so much Ya Abdul, Allah yabar zumunci._ sannan ta ajiye wayan ta mik'e da shakka-shakka ta shiga rage kayan jikinta gudun kar Afzal ya bankad'e k'ofar ya tarar da ita ba riga.
 
    Acikin minti ashirin ta gama duk wani shafe-shafen da zatayi, kayan da Afzal ya d'auko matan ta d'aga tana duba. Yanzu wannan d'an iskan kayan yake tsammanin zata sa? Ai ba maraban wannan da babu komi na jikin mutum gani za ayi. Wardrobe natan ta nufa ta shiga neman wani na daban sede inaa duk kayakin bana kamala a ciki. Yau akeyinta meyasa Ummi za tayi mata hakane? Ko d'an me riga da wando babu se masu net guntaye iya cinya ai kuwa bacci da towel ya kamata. Hijabi ta sanya akan towel d'in ta koma kan gadon ta zauna. Wani d'an banzan yunwa ne ya soma damunta bata san lokacinda ta hau kan kazar data gani k'ulle cikin ledan ba ta shiga ci ana cikin haka Afzal daya ji shiru yace bari ya lek'o, bud'e k'ofan da zeyi suka had'a ido hud'u da Amal. Kunya ta jiyo tamkar ta nitse k'asa, da sauri ta kawar da kanta ta shiga ture ledan gefe. Murmusawa yayi ya k'araso ya zauna kusa da ita. "Ci abinki kinji? Dama naki ne" Juice d'in yaja ya tsiyaye mata a cup tare da tura mata gabanta. A hankali ta shiga ci bayan dan ta gama ta kwankwad'e juice d'in akai.

  "Kin k'oshi bazaki k'ara ba?" A hankali ta gyad'a kanta "Thank you" ta furta.

  "Don't mention kina buk'atan wani abu?" Yadda kuka san kurma haka ta cigaba da amsa tambayoyinsa da jiki.

  "Lets sleep then ko baki fad'a ba nasan a gaje kike." Yana tu6e jallayabiyan nasa Amal ta shiga kare fuskanta oh! Shi kam ya had'u da aiki. Daga chan k'arshen gadon ta ja pillonta ta kwanta, had'e da juya masa baya. Da mamaki ya tsaya kallonta bade da hijabin take shirin kwanciya ba? "Lily?"

  "Uhmm?" Ta amsa ba tare da ta juya ta kallesa ba, shi kam wai baya jin kunya ne yake tsayuwa akan gajeren wando zalla a gabanta? Ta tambayi kanta, ita kam kunya ma baze barta ta kallesa ba.

  "Da hijabin zaki kwanta?"

  "Uhmm" ta amsa. Takowa yayi izuwa gabanta ya zauna nan ta kulle idanta gam. Hannu yasa ya gwada d'aga hijabin nata da mamaki ya tarar da towel k'ark'ashi. Tirk'ashi!

  "Lily!" Yayi exclaiming, bud'e idon da zatayi taga yana rik'e da k'asan hijabinta nata da hanzari ta k'wace ta shiga rufe jikinta.

  "Wai mey haka? Da towel d'in zaki kwanta?"

  "Uhmm" ta amsa.

  "Dalili?" Wai har ma dalili yake tambayarta? Shin bega kalan kayan bane ko a haka yake tsammanin zata sa? "Kefa Lily!"

  "Yaya baka ga kayan bane" se anan ta bud'e baki ta amsa idanta a rufe har yanzu.

  "Meya samesa?" Ya buk'ata.

  "Bazan iya sawa ba" ta amsa a takaice. Kayan ya d'ago daga kan side drawer yana kalla, besan lokacin da dariya ya kauce masa ba. "God help me" ya furta a hankali. Anya kuwa ze iya da kunyan nan nata? Yaga irin kayan da Nazeefah ke kwanciya da su kenan wasun ma wannan yafi su kamala.
  Ido d'aya ta bud'e tana kallonsa.

  "Mey anan d'in da bazaki iya sawa ba Lily? Hungo tashi kisa."

  "Ni gaskiya bazan saba kabarni haka kawai I'm good seda safe."

  "A ina aka ta6a kwanciya da towel ki tashi kisa mu kwanta bacci nakeji."

  "Toh Yaya na hanaka kwanciya ne?"
 
  "So kike muyi fad'a ko?" Yayi maganan had'e da komawa gefenta ya zauna "Ko kisa kokuma in sa miki na k'arfi kinsan ba Mami bale kice zakiyi ihu ta taimakeki."

  "A'a Yaya dan Allah kayi hak'uri karka mun haka."

  "Toh amsa kisa."

  "Yaya bazan iya sawa ba dan Allah kayi hak'uri."

  "Fa bazan barki ki kwanta da towel ba."

  "Kayi hak'uri zuwa gobe zanje kasuwa in sai kayan baccin masu riga da wando se in fara sawa I promise bazan sake kwanciya da towel ba amma ka barni na yau d'in." Dariya sosai ta basa wai kam da abinda takeyi d'innan idan da kuma cewa yayi su raya first night kaman yadda kowasu ma'auratan keyi fa? Ashe seta tara masa jama'a. Ganin fa bata da shirin sanya kayan kawai ya damk'o hannunta. Wai d'an karen ihu tasa seda ya tsaya toshe kunnensa. Shin wani irin laushi hannun nata keda sekace auduga.

  Kuka ta shiga yi yayinda yake k'ok'arin raba ta da hijabin nata.

   "Zan sa wallahi zan sa da kaina dan Allah karka cire min hijabin Wallahi towel d'in ya warware kayi hak'uri" nan ma dariya ta basa sosai amma ya bone se kokowan cire hijabin yake. Kuka Amal ke tsakaninta da Allah tana rantsuwa akan ya saketa zata sa da kanta. Seda ya bata wuya sannan ya saketa "That's my Lily sanya toh da hannunki ina kallonki ko zaki shiga bathroom?"

  Kai ta gyad'a a kid'me.

  "Je ki sanya toh ina jiranki." Batayi musu ba ta mik'e har tana neman cin tuntu6e ta nufi bayin. Hijabin nata ta kwaye ta ajiye a gefe sannan ta d'ago kayan ta shiga neman ta inda zata sa. Chan ta samo wuyar rigar ta sanya, gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta surrata kap ba abinda be nuna ba, amma ko se Allah ya d'ibe ma baturen daya d'inka wannan kaya albarka. Yanzu a haka ne Afzal yake son taje ta samesa su kwanta sekace wata sabuwar karuwa? Uhn uhn kam gaskiya baza ayi haka da ita ba.  Ina ma ace da brazier a ciki da d'an sauk'i amma haka ba komai gaskiya da sake. Tunanin ya zata fita ta d'auko bra ta sanya ta soma ana cikin haka kawai taji Afzal ya wangale mata k'ofar ba notice. Ashe bata sa key ba, wani irin d'ankaran ihu ta k'urma had'e da juya mai bayanta yayinda ta shiga kare k'irjinta tana kakkarwa.





RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨

4 comments:

Unknown said...

Thanks dear

fatima said...

Thanks dear.. Allah ya Kara basira.. Sorry nazeefa Allah ya sa miki hakuri

Unknown said...

Hahha I can't stop laughing. Lily wannan wauta haka?
Nazeefah Allah ya ganar dake
Miemie godia babu adadi Allah ya kara basira.

Unknown said...

Am new in this page. We all enjoy this novel lov you dear