Friday, 27 July 2018

RANA D'AYA!

BY MIEMIEBEE
PAGE 25



    Shirye-shiryen biki kuma aka shiga yi na sosai, kaman yadda akayi bad'ad'in bad'a haka aka kuma. Kyautan gida Abba ya sake yiwa Afzal a matsayin gudumawan da ya bayar. Sosai Ummi take taimaka wa Afzal, kusan komi ita takeyi, duk wani abinda yake buk'ata fa toh tun kafin ya furta zata tambaya masa gun Abba. Akwatuna har guda ashirin da d'aya aka had'a wa Amal sannan na Nazeefah kuma set mey k'waya shida na fad'an kishiya. Kusan duk zannuwan da suke cikin na Amal akwai su a na Nazeefah babancin kawai na Amal sunfi yawa ne. Abinda ya kama daga kan kayan kitchen, gadaje, kujeru, show glasses, rugs, da komai Ummi ne suka siya, ba yadda Mami batayi da ita ba akan ta bari ko wani abu k'adan ne su kawo yaso se a had'a kud'in ayi siyayyan amman Ummi tak'i kasancewar Afzal ya rok'eta da komin yaya karta yadda ta amsa koda kobo ne daga gun su. Sude kawai suyi focusing akan abincin da za'a dafa.

     Mutum na iya rantsewa 'yar Ummi ce zatayi aure don kalan kayakin d'aki masu tsada da alfarman da ta sai wa Amal. Gida yayi kyau sosai se wanda ya gani. Yau ana saura sati uku d'aurin aure kenan.

***
   "Halo Yaya?" Tace bayan ta d'aga wayan.

  "Na'am Baby" ya amsa.

   "Yaya wai yaushe ka fara kirana da Baby?" Yau kam ta kasa hak'ura seda ta tambayesa. Kusan sati kenan yana kiranta da hakan, kuma da gan-gan yake gano bata so.

  "Jimin 'ya da ba sunanki bane?"

  "Ni Amal ne suna na."

  "Baby'n fah?"

  "Sunan gida ne."

  "Ni d'in ba d'an gida bane?"

  "Ni ba haka nake nufi ba kawai na gwammaci kana kira na da Amal ne."

  "Toh nak'i ni Baby nafi so."

  "Toh Allah taimake ka, ina yini?" ta gaishesa.

  "Lafiya d'an fito waje kinji?"

  "Yaya ka fa san an fara yimun gyaran jikin."

  "Se akace baki sake tako waje?"

  "Toh ai Yaya idan na rink'a fita muna had'uwa bazaka ga effect na gyaran jikin ba."

  "Nide fito ina jiranki." Nan da nan ta janyo hijabinta tasa ta fita taje ta samesa.

  "Tabarakallah gaskiya Allah yayi halitta anan" ya ce da ita lokacinda ta shiga motan "Masha Allah, Abba yayi gaskiya da yace na iya za6i kin ganki kuwa?"

  "Kai Yaya kadena zolayata mana."

 "I'm damn serious wai ma yaushe ne auren? I can't wait any longer."

   Wani irin ruwa cikinta ya d'auka, ba shiri ta had'iye miyau had'e da tambayansa,
  "Uhm so what brought you here?" Don canza topic d'in.

  "Is it a crime idan ango ya zo ganin amaryarsa sati uku kafin aurensu?"

  "Ba wai haka nake nufi ba I mean akwai matsala ne?"

  "Ohh wato ma haka kika miyar dani se idan akwai matsala nake tahowa ko?"

  "Goodness! Nifa ba haka nake nufi ba."

  "Toh yaya ne?"

  "Babu nayi shiru."

 "Yauwa da yafi kam so jiya kika gama bada haddanki duka wai ko?"

  "Eh."

  "Congratulations then, Allah sanya albarka aciki yasa idan kika tashi haifo mun yara ki haifa mun hafizai kaman ki Lily I'm so proud of you."

  "Ameen Yaya thank you" ta amsa tana mey jin kunyansa.

   "Yauwa wai inji Ummi tunda aka shiga yi maki jere baki je kinga gidan naki ba?"

  "Gida na kuma? Gidan mu de." Ba k'aramin dad'i lafazin nata yayi masa ba.

 "Toh gidanmu" ya gyara kaman yadda ta buk'ata.

 "Eh amma Mami tace cikin satin nan zamuje."

  "Toh ni nazo in kaiki ne yanzun."

  "Toh ai ya kamata in sanar da ita kafin nan."

  "I've already done that so don't worry."

 "Toh shikenan."

  "Kafin nan ina fatan kuna waya da tailor'n naki? Idan fa baki tak'ura mata da kira kad'an ne daga cikin aikinta tayi disappointing naki se ranar dinner'n yazo ki rasa kayan sawa."

  "Yaya ni dole ne se anyi wannan dinner?"

  "Wannan kuma seki tambayi Ummi tunda ita tace zatayi, da kud'in d'inkin ki dana komai ita tace zatayi handling ni karki sani cikin shirgin ku."

  "Toh ai laifinka ne da kace mata baka buk'ata tunda de Allah yayi wannan ba shine auren ka na farko ba ai zata ji."

 "Kefa kike gani kaman ba wannan ne aurena na farko ba tamkar sabon saurayin da ze angwance nake jin kaina so be calling the tailor on frequent basis kina mey tuna mata kayan naki, okay?"

  "Toh shikenan."

  "Sekuma batun wushe-wushe da kamu ko? Lokacin aurenmu da Nazeefah naga su Mummy sunyi mata and I can say I absolutely loved everything about the event inason a naki ma ayi."

  "Yaya dan Allah kayi hak'uri nifa ban ga amfanin tarukucen nan ba wallahi hanyan kashe kud'i ne kawai, kayan dinner kad'ai kusan dubu d'ari biyu wannan kuma nawa zasu ce? Ni gaskiya banason kashe kashen kud'in haka ya isa."

  "Toh banda ke da abunki wushe-wushe kam ba al'adanku bane ku shuwa? Ai ya zamo dole kiyi."

  "Bawani dole d'innan ni kashe kud'i ne bana so."

  "Laffaya nefa kawai zakisa."

  "Shi d'in bada kud'i za a siya bane?"

  "Lily wai ni ke miki magana kina jayayya dani?"

  "Ni ba jayayya da kai nake ba Yaya, a matsayina na wacce zaka aura ne nake yi maka gyara."

  "Toh banaso se anyi wushe-wushen da kamun ga wannan" yayi maganan yana d'auko wata bak'ar leda daga backseat. "Gashi" ya mik'a mata. Amsa tayi ba musu ta bud'e sabon laffaya ta gani me uban kyan k'arshe irin na 'yan Sudan masu d'ankaren tsadan nan. Yaya!" Tayi exclaiming.

   "Yayi miki?"

  "Fisabillahi nawa ka kashe a nan?"

  "So kike in fad'a miki kud'in saboda kice baza ki sa ba? Ki kwantar da hankalinki ba tsada."

  "Mey k'arya..." se tayi shiru

  "Naji mey k'arya d'an wuta bade hakan ze sa in fad'a miki kud'in ba, so yanzu an gama da maganan wushe-wushe se kuma na Kamu."

  "Ni wallahi 6arna da kud'i ne banaso ga walima ga wushe-wushe ga dinner mey na wani kamu kuma? Kai baka tausaya wa kanka dasu Abba ne kam Yaya? Ni gaskiya ba wani kamun da za'ayi."

 "Allah baki isa ba."

  "Har Allah fa kace Yaya?"

  "Eh baza kiyi auren nan dry ba mey sekace auren dole za ayi miki? Ai ko na Nazeefah da na dolen ne ma anyi celebrating se naki ne zaki wani ce a'a? Ko so kike ki nuna mun auren dole ake shirin miki Lily?"

  "Yaya ba haka bane kashe kud'in ne ya isheni dubi ko tsinke fa ka hana su Papi siya."

  "Ai ni na d'auke muku ba ku kukace nayi hakan ba kuma ko a addinance ma ya halatta idan miji nada k'arfi ya d'auke wa matar da ze aura da iyayenta nauyin komai so ki daina bothering kanki kinji? Ni naso in d'auke muku kuma ko a ina ma yin hakan ba laifi bane."

  "Thank you so much Yaya Allah k'ara bud'i, I really like this laffaya, wallahi yayi kyau sosai."

  "Ameen glad you like it, so kin amince ayi kamun? I'll just talk to our wedding planner."

  "Nikam a'a wushe-wushen ya wadatar."

  "Mey laifin in anyi duka toh Lily?"

  "A'a gaskiya nikam guda d'aya za'ayi."

  "Toh wa ze hak'ura cikin mu?"

  "Yaya kai babba bazaka hak'ura ba?"

  "Nak'i hak'uran."

  "Toh shikenan ni k'arama zanci girma."

  "Nak'i yarda da hakan."

   "Toh kuma?"

  "Duka biyu za'ayi."

  "Wai kam cire kud'i ba amfanin nan baya damunka ne? Wallahi haramun ne ko sena ja maka aya tukun?"

  "Ko ki yarda ko in samu Papi ince mishi gashi tun kafin ayi aurem kina mun rashin kunya ina miki magana sam bakiya ji."

  "Ni yaushe na yi maka rashin kunya? Sharri zaka soma min tun kafin in shiga gidan naka?"

 "Toh ki amince kai karma ki amincen da kin k'i da kinso se anyi duka hungo wannan" yayi maganan yana d'auko wata bak'ar leda dake ajiye gun k'afansa. "Mey wannan d'in?" Ta tambaya tana warware ledar. Invitation card na programme of events na auren nasu ta tarar aciki, ashe duk surutun nan da yakeyi har ya riga ya sa an buga komai ciki harda kamu da wushe-wushen kawai neman sata surutu yake.

  "Ashe har ka sa an buga."

  "Dama in fad'a miki ne kayan da zakisa a kamun already na gun tailorna bada measurement naki."

  "Ni wallahi har kunyarka nakeji Yaya komai kai kakeyi."

 "Ba wani abin kunya dama al'adan yarabawa ango shi keyin komai ko cokali mace bata kaiwa gidanta so stop bothering yourself."

   "I know thank you won't compensate but thank you so much Allah k'ara bud'i."

  "Ameen don't mention so mu tafi?"

  "Eh muje ba kace ka riga ka sanar da Mami ba?" Da haka ya jasu suka wuce gidan nasu wanda yake unguwan Old GRA. Amal seji take kaman komi a mafarki yake faruwa, koda wasa bata ta6awa kawowa a ranta cewan wataran zatayi aure acikin fankacecen gida irin wannan ba, itama 4 bedroom flat ne da parlour biyu se kitchen da store d'aya da kuma guest toilet d'aya. Ita ba abinda yafi burgeta ma kaman yadda aka k'aya kitchen natan, yadda komi yake in purple and white gaskiya ba k'aramin kud'i su Ummi suka kashe ba. Addu'a tayita yiwa Afzal da Ummi dan idan ba addu'ar ba bata tsammanin akwai abinda zata iya yi da ze iya biyansu kalan d'imbum alkhairin da sukayi mata. Gida sekace mutum na aljannar duniya. Bayan ya sauk'eta a gida sukayi sallama sannan ya biya gida gun Ummi.

   "Kayakin Nazeefan kazo d'auka ko?"

  "Eh Ummi are they ready?"

  "In a moment, amma Prince kace akwati shida be isheta ba se har an yi mata goma? Sekace itace amaryar?"

  "Ummi kinsan halin Nazeefah yanzu haka idan taji na Amal 21 nata shida wallahi ba k'aramin tada mun hankali zata yi ba."

 "Lallai kam kai kaso amma ban ta6a jin inda akayi kayan fad'an kishiya set goma ba shidan nan da muka had'a mata a farko yayi."

  "Ayi mata goman kawai kowa ya huta."

  "Toh shikenan kayaki suna hanya sun kusa isowa."

  "Alright toh thank you so much Ummi Jazakillahu khair."

  "Ameen wa iyyaka, ya amaryar tamu? Munyi waya da Mami d'azu tace wai ka d'auki Amal ka kaita duban gidan nata."

  "Eh wallahi lafiyarta k'alau tana gashe  ki ma."

  "Ayya ina amsawa, yaya gidan tace wai? Komi yayi mata ko?"

  "Sosai ma, bakiga kalan godiya da addu'an da tayita yi maki ba wallahi."

  "Allah sarki 'yar albarka kace mata kar ta damu."

 "Ai ko na fad'a mata, wai ayi kamu da wushe-wushen da yake kaman al'adansu wai sam baza ayi ba walima ya wadatar ita bata son kashe kud'i dinner'n ma ta amince ne saboda tana jin kunyarki" ya sanar da ita. Dariya sosai Ummi tasa. "Ai ustazancin Amal takan nan kam se a hankali, kuma fa ba komai yake hanata amincewan ba tuna yadda zata fita ba mayafin kirki a idon jama'a ne yake damunta."

  "Ai kaman kin sani da fari ma cemun tayi wai abaya zata sa zuwa gun dinner'n" Nan ma wani dariyan Ummi ta kuma sawa "Kai!! Amal takan nan drama queen ce, ai nace da tailor'n nata tayi mata decent d'inki, kayan da baze bayyana jikinta ba."

  "Hakan yayi sosai."

 "Toh Allah bada zaman lafiya ya nuna mana ranar auren nan."

  "Ameen Ummi thank you for all that you've been through for me wallahi bansan ta ina zan fara biyanki ba."

  "Ba komai Prince karka damu bayan kai fa ba kowa idan ban yi maka abinda kakeso na lalata ka ba wa zan lalata toh?"

  "Your boy loves you so much."
 
  "I love him even more."

  "So mey Daddy'n Nazeefah yace bayan da Abba ya sanar dashi zan k'ara aure?"

  "Me kuwa zece? Ya taya ka murna mana ai har ya sanar da mahifiyar nata ma don jiya ta kirani take cewa in tayaka murna."

  "Ayyah Alhamdulillah toh."

  "Yanzu dey matsalar d'aya ce Nazeefah Allah sa tayi maka kyakkyawan fahimta duk da cewan ka makara, yaci ace ka sanar da ita da jimawa."

  "Ameen fah wallahi ni har tsoro ma nakeji kinsan kalan zafin kishinta kuwa? Akwai lokacin da Amal ta ta6a kawo mun aldeb sena zuba flasks d'in acikin fridge bakiga yadda hankalin yarinyan nan ya tashi ba da ta ci karo da flasks d'in."

  "Aikam daga yadda take magana ma mutum ze san tana da zazzafar kishi Allah de sa ta yayyafawa zuciyar tata ruwan sanyi tayi maka kyakkyawar fahimta."

 "Ameen Ummi" bada dad'ewa ba akwatunan da yasa a k'ara d'in suka iso nan ya had'a dana farkon ya cika goma cus aka sanya masa a booth. Sallama sukayi da Ummi sannan ya fice, se hasbunallai wa ni'imal wakeel yake ta nanata cikin motan yau yasan se gobara ya kusa tashi masa a gida.

   A cikin motan ya baro kayakin ya k'arisa ciki. Mik'ewa tayi tamai sannu da zuwa had'e ba sa light kiss on the lips.
  "Ya Rouhi ina kaje haka tun d'azu ina jiranka?"

  "Akwai wasu ababen da na kula dasu ne I'm sorry for keeping you waiting."

  "Ayyah ba komai muje in had'a maka ruwa kayi wanka food is ready." D'akin nasa suka k'arisa nan da nan ta had'a masa warm water sannan ya shiga. Tana cikin ninke kayakin sa da ya cire dan kaisu laundry room wayan sa dake kan gado ya shiga ruri bata damu ta duba wa ke kira ba ta cigaba da harkar gabanta. Call d'in na tsinkewa meshi ya sake kira se anan ne tayi tunanin bari ta lek'a taga ko waye ne, idan Ummi ce tace mata yana wanka.

  'Lily❤️💕' taga yana flashing akan screen d'in bayan nan ga picture'n Amal da yayi saving contact d'in dashi. Wani irin mumunan fad'i gabanta yayi bata san lokacinda ta shiga yin kakkarwa ba. Tabbas ta wayi fuskan nan amma ta rasa a ina, kode a makaranta ne? Kai da wuya toh a ina ta waye ta? Da hanzari tayi picking kafin call d'in ya tsinke had'e da yin shiru.

  "Halo Yaya?" Amal ta soma da cewa.

   "Kina neman waye?" Nazeefah ta tambayeta, Amal na jin muryan tasan na Nazeefah ne bata sake cewa komai ba kawai ta katse wayar. Nazeefah bata kai ga ajiye wayan ba Afzal ya fito daga bayin d'aure da towel a iya kunkuminsa. Kallo d'aya yayi mata yasan ba lafiya ba, idanunsa na sauk'a akan hannunta da ke rik'e da wayan nasa kuwa ya gama tabbatar da abinda ke faruwa. Tabbas Amal ce ta kira Nazeefah kuma ta d'auka. Innalillahi! Meya hanasa shiga da wayan nasa bayi kaman yadda ya saba? Sam ba haka yaso ba, yafi son ya sanar da ita komai da bakinsa ba wai ta gano hakan da kanta ba. Nauyayyan numfashi ya sauk'e sannan ya k'arisa inda take tsayen har yanzu.

   "Nazeefah-"
 
   "Da abinda zaka sak'a mun kenan Ya Rouhi?" Ta katse sa.

  "Meya faru? Mey wayana keyi a hannunki kuma if I may ask?"

  "Kiranka akayi na d'aga" ta amsa.

  "Kawo muga" ba gardama ta mik'a masa kaman yadda ya k'udura a ransa kuwa Amal d'in ce ta kira.

  "Wacece ita? Meyasa take ce maka Yaya? Mey ma'anan wannan hearts da suke gaban sunanta?" Ta jero mai tambayiyo a lokaci guda.

  "Nazeefah calm down."

  "I can't calm down Ya Rouhi I can't! You mean to tell me for all this while dama kana da wata a waje? Wow!" Ta numfasa cike da d'umbun mamaki se ganin al'amarin take kaman raha.

   "Nazeefah I'm sorry but wallahi inada niyyan sanar dake komai."

  "Sanar dani mey? Akan kana da budurwa? Seriously Ya Rouhi? Meney bana yi maka a gidan nan da zaka za6i ka k'untata mun haka? Why do you have to flirt behind my back?" By now har idanunta sun soma cikowa da hawaye.

  "Nazeefah please don't cry" ya fad'a a kid'ime. Hannun sa tayi saurin cirewa kafin ya samu ya rik'e ta. "I'm not flirting behind your back kema kinsan ba hali na bane hakan, I respect you a lot to hurt you like this."

  "Then explain mey contact na yarinyan nan keyi a cikin wayanka da kuma dalilin da zaisa tana kiranka Yayanta."

   "Sunanta Amal and am willing to marry her." Wani irin mumunan fad'i gabanta yayi aure de?
  "Aure?" Ta nanata cike da k'in yarda. "Aure Ya Rouhi? Aure kake shirin yi?"

  "Yes Nazeefah ina son in k'ara aure kuma Amal nike son in aura, kiyi hak'uri na rashin sanar dake da wuri da banyi ba but kar kiyi tunanin nayi hakan ne don inci zarafin ki. Not at all, I do have a reason for not informing you, nafi son se na gama had'a miki kayan fad'an kishiyanki ne, auran namu is in three weeks time in Allah ya yarda."

  "No!" kai ta shiga kad'awa yayinda take k'aryata duk wani abinda ya fad'a, take wan irin sharp headache ya kamata. "This can't be possible" ta shiga cewa "It can never be possible dan Allah kace wasa kake mun Ya Rouhi" ta rok'esa yayinda take hawaye sosai.

   "Dan Allah kibar kukan haka Nazeefah."

  "Aure fa kace Ya Rouhi? Mey nayi maka da zaka auro mun kishiya? Idan wani laifin na maka wanda ban sani ba dan Allah ka sanar dani a shirye nake da in baka hak'uri amma please let this be a joke."

  "It is no joke Rabba'atul Bait and ni baki yi mun laifin komai ba, I love you, you know that right?"

  "No" ta katsesa "You don't love me Ya Rouhi, you've never loved me, inda kana so na da baza ka ta6a tunanin yi mun kishiya ba, why? Why?" Tuni ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Rungumota yayi niyyan yi amman sam ta hanasa da k'yar ya samu ya rufe ta gam ajikinsa yayinda kukan nata ya tsananta. Sun dad'e a hakan yana ta bata hak'uri amma ina ta kasa hak'uran se kuka take. Chan ya d'agota daga jikinsa ya shiga share mata hawayen nata "Come with me" ya buk'aceta. Batayi gardama ba ta bisa a baya yayinda ya rik'e hannunta cikin nasa ya jata izuwa parlour inda D'anladi ya jera akwatunan nata.

   "Do you believe it's not a joke now?" Ya tambayeta a nitse.

  "Mey wannan d'in?" Ta tambayesa a hankali.

  "Kayan fad'an kishiyanki Nazeefah." Bata iya k'ara yin magana ba yayinda ta rushewa da wani fitinannen kuka mey tsuma zuciya. Shikenan ya tabbata aure Afzal zeyi amma ko be kyauta mata ba, na mey zeyi mata kishiya bayan duk wani abinda yake so tana mishi, bayan nan ace seda aure ya rage sati uku ze sanar da ita? Me tayi da za ta fuskanci hukunci me tsauri haka daga garesa? Bazata iya zama da kishiya ba, da ta zauna da kishiya gomma ta rasa ranta.

  "Ya Afzal you're such deceit, ka cuceni kaci amanata kuma ka sani I'll never forgive you, I'll never forgive you for tricking me that you did. For all these while you made me believed you loved me ashe ba haka bane wasa da hankalina kawai kake chan a waje kana da wacce kakeso kake kuma son ka aura ka kasance da ita, me na ta6a yi maka da zaka mun wasa da hankali haka? Ashe k'arya kake mun duk sanda ka ce ka yafemun."

   "Ko da wasa Nazeefah, ki yarda da ni idan nace miki na yafe miki na kuma mance da duk wani abinda kikayi mun da a baya, I'm terribly sorry Nazeefah bazan gaji da baki hak'uri ba ki sani ina sonki, I really do love you."

  "No you don't love stop lying to me" Hannayenta biyu ya had'a acikin nasa  "I'm not lying to you Nazeefah, I really do love you wallahi I do."

   "Wallahi k'arya kake you don't love me you've never once loved me" ta k'aryatasa cikin tsananin kuka. Tausayi sosai ta basa barin ma ganin yadda hawayen ke tsiyaya daga idanunta, na matuk'a ta basa tausayi.

  "Nazeefah please stop crying" yayi maganan yana k'ok'arin rungumarta sede tak'i barinsa. "Don't you dare touch me!" Be saurareta ba haka na k'arfi yayi hugging nata ya shiga shafa bayanta a hankali yayinda yake showering kisses akanta. "Shhh! I've got you, I love you so much."

  "Idan da har kana so na da baza ka fara tunanin k'aro aure ba" tayi maganan had'e da raba jikinta da nasa tana share hawayenta "Mey yayi zafi da zaka yi mun kishiya Ya Rouhi? Mey ka ta6a nema a gidan nan ka rasa, girki ne inayi maka, ina respecting naka ina tsaftace maka muhalli baka ta6a neman hak'k'inka a guna ka rasa ba, duk abinda kace kana so shi nakeyi wanda baka so kuwa koda hobby na ne ina k'ok'arin dainawa, mey yayi zafi da har seka k'ara aure?"

  "Nazeefah kin manta ni miji ga mata hud'u ne? Bayan nan bakisan mata sun fi maza yawa a al'umma ba yanzun? Idan kowani na miji yace mace d'aya kacal ze aura sauran kuma waze auresu? Bakiya son 'yar uwarki ta raya sunna itama ta cika umarnin anmabin mu SAW?" Nasiha ya shiga yi mata sosai saidai ina kishi ya riga ya rufe mata ido bata jin kira.

  "No Ya Afzal! Bazan bari ka auro wata muddin ina raye, bazan zauna da kishiya ba."

  "Wayace kishiya zan auro miki Nazeefah? Abokiyar zama zan kawo miki."

 "Bana sonta bana so."

  "Nazeefah please calm down kiga baki ma santa ba fa amma kike cewan baki sonta, Amal is a very nice girl ina da tabbacin you two will get along."

  "Bana son sanin ko ita wacece ina ji ina gani bazan bari wata ta sace mun kai ba Ya Afzal, I'll do whatever it takes in tabbata wannan aure be auku ba you'll see."

   "Nazeefah-"

  "Kuma ka tattara kayakin fad'an kishiyanka or whatever you call it bana buk'ata" tana kaiwa nan ta nufi d'akinta ko amsa kiran da yakeyi mata batayi ba. Hijabinta ta sanya ta d'au makullin motarta yana ganinta yasan fita zatayi be hanata ba saboda yasan ba amfani ko da yayi maganan ma ba sauraronsa zatayi ba. Kad'an ya rage bata take k'afan D'anladi ba da ta zo fita daga gate d'in, gida ta wuce direct se d'akin Mummy.

  Khalifah ta tarar mik'e kan gado se faman latsa wayansa yake.

  "Ya Nazeefah" ya kirata had'e da mik'ewa zaune.

  "Ina Mummy?"

  "Tana wanka" ya amsa take.

  "Jeka d'auko mun ruwa" tayi maganan tana cire hijabinta.

  "Ni shikenan kinzo ki fara aikan mutum ba" ya watsa mata harara.

  "Nace kaje ka d'auko mun ruwa wallahi kar ka bari in sauk'e haushin da nakeji akanka."

  "Ki sauk'en mana a jinki zaki iya duka na ne?" yayi maganan had'e da mik'ewa, daga bakin k'ofa ya wulla mata gorar ruwan da ya d'auko matan sannan ya haura sama d'akinsa. Kad'an tasha ta rufe ta ajiye, bada dad'ewa ba sega Mummy ta fito.

  "Ha'ah Nazeefah ce a gidan namu yau."

  "Mummy" ta kirata tana turo baki tamkar wacce zatayi kuka.

  "Meya faru?"

  "Mummy kina jin Ya Afzal wai aure ze k'ara."

  "Dama bakida labari ne?" Mummy ta tambaya tana mey zama a gefenta.

  "Aww kina sane dama?"

  "Eh though nima ban dad'e da sani ba be sanar dake bane ke?"

  "Wallahi se yau yake fad'amun."

  "Ai na d'au kina da labari auran sauran sati biyu ne ko uku nema."

  "Wallahi Mummy bazan yarda ba adalilin mey ze auro mun wata? Wai harda akwatin fad'an kishiyansa."

  "Guda nawa?"

  "Ni nama irga ne amma yafi shida de naga kaman."

  "Toh ai ki godewa Allah."

  "In godewa Allah fa kika ce Mummy? Uwar mey zanyi da kayan fad'an kishiyan nasa? Tsirara nake yawo ne?"

  "Kiga Nazeefah kowa yasan kishiya da zafi amma idan Allah ya k'addaro maka toh fa dole ne ka hak'ura banda ke da abin ki an riga an sa rana, rana ya gabato ajinki akwai borin da zakiyi ne da ze hanasa yin auren?"

  "Wallahi auren nan bazata saku ba komin yaya ne se nasan yadda zanyi in hana aukuwan hakan."

  "Uhn uhn fa Nazeefah kar ki bari kishi ya kaiki ga halaka ki kwantar da hankalinki don za ayi maka kishiya bawai hakan na nufin mijinka baya sonka bane, kefa da bakinki kikace yayi miki kayan fad'an kishiya ai yaci ace kin hak'ura Afzal na sonki ke kanki kin sani, a zamanin nan ba kowani na miji bane ze yiwa uwar gidansa akwati dan wai ze k'ara aure. Ga akwati ba d'ayaba ba biyu ba keda kanki kikace zasu fi shida."
 
   "Son banza so a baki, wallahi baya sona da yana sona da baze ma fara tunanin yin wani auren ba mene bani yi masa da zece seya sake aure. Ke yau shekara nawa kuke tare da Daddy meyasa bece ze sake yin wani auren ba? Idan ba fitina ba mata nawa yaga Abbansa ke da daze kama yace shi se yayi mata biyu."

  "Kowa da ra'ayinsa Nazeefah. Kisani Afzal daban yake da Abbansa ko ni dake nan ba d'aya muke dake ba. Shi kishiya kuma tana kan kowa wallahi ko ni nan ban isa in bugi k'irji ince Daddy'nku baze k'ara aure ba, a yau d'innan yaga dama ze k'ara auransa, hak'uri ya zama dole."

  "Ni wallahi bazan yarda ba auren namu dududu shekara nawa ne befa kai uku ba, ya bari ma idan na gama haihuwa na mana amma ko k'wark'wata ban ajiye ba har ya fara tunanin yin wani auren, Allah bazata saku ba."

   "Ta ma riga ta saku ne fah Nazeefah don banga abinda ze hana aukuwan auran nan ba idan ba mutuwa ba. Dan Allah ki rufa min da Daddy'inku asiri ki d'au hakan a matsayin k'addarar ki, ni kaina zan saki a addu'a Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi."

  "Amma Mummy kin ban dariya har akwai alkhairi ne acikin kishiya?"

  "Toh kije Nazeefah kiyi duk abinda kika ga ya dace amma idan kika zo kika rasa auren naki daga k'arshe kar kiyi blaming d'ina nide na fad'a miki" bata sake cewa komai ba ta ja hijabinta ta fice. Gidan k'awarta Suwaiba ta nufa da ikon Allah kuma mijinta baya gida. Zama tayi ta irga mata halin da ake ciki, sosai Suwaiba ta ji mata takaici amma ta nuna mata lokaci ya riga ya k'ure ba yadda za'ayi a hana aukuwan auren.

  "Taya zakice haka Suwy? Nida nake cewa zaki share mun hawaye idan nazo."

  "Wallahi ba yadda za'ayi saidai idan malamai zaki fara bi."

   "Malamai? Wasu irin malamai kenan?"

  "Malaman tsibu nake nufi."

  "Subhanallahi Suwy! Kin san ko yin hakan shirka ne?"

  "Tabbas na sani amma kuma idan bada su ba mutum baze ta6a iya mallake mijinsa ba kinga Ibrahim (mijinta) idan nace masa zauna ya zauna se abinda nakeso yakeyi I can't bear the risk of sharing my husband da kowata shegiya idan a shirye kike gobe goben nan ina iya kaiki gidan malami na ya share miki hawaye."

  "A'a kam gaskiya zan zauna inyi tunani am sure akwai wata hanyan da zanbi in hana aukuwan auren nan ba tare da na fita daga musulinci ba."

  "Toh sani de ya rage wa me shiga rijiya kije kiyi shawaran anytime your mind is made up, gidan malam kullum a bud'e yake yana maraba wa bak'i."

  "Toh ni zan wuce."

  "Bari in raka ki."

  "A'a yi zamanki keda kikayi nauyi, Allah de raba lafiya."

  "Ameen toh se anjima." Maimakon ta zarce gida ta wuce gidan wata k'awarta Maimuna har bayan maghrib tak'i dawowa gida. Tun Afzal na trying numbanta har ya gaji ya dena don kashe wayan tayi gabad'aya don kar ya tak'ura mata. Se wajajen k'arfe tara ta dawo gida. Tana shiga sega Afzal zaune kan kujera kallonsa tayi sannan ta kawar da kai ji take kaman ta nad'a masa duka don takaici. Daga bisani ta shiga takawa bata kai ga shiga corridorn da ze kaita d'akinta ba ya kira sunanta. Banza da shi tayi se akaro na biyu sannan ta tsaya had'e da kewayowa.

  "Ina kikaje?" Ya tambayeta. Shiru tamai ko ta kallesa ma bale wai tasan yanayi.

  "Magana nake miki Nazeefah ina kikaje? I've been trying to reach you but am sure da gan-gan kika kashe wayan naki don kar in sameki, yeah?"

  "Gida naje, wayana kuma ya mutu ne ba charji" ta amsa sama-sama.

  "Don't think of lying to me, na kira Mummy tace tun La'asr kika bar gida so where did you go?"

  "Gidan k'awata excuse me" bata kai ga juyawa ba ya dakatar da ita mik'ewa yayi ya tako zuwa inda take tsaye. "Da izinin wa kika fita sannan ya dace a matsayin ki na matar aure ki fita se cikin daren nan ki dawo?"

  "Kayi wa kanka fad'a kafin kayi mun Malam, ya dace a matsayin ka na magidanci amma kana neme neman mata? Bayan nan se three weeks to d'aurin aurenka zaka sanar da ni a matsayina na matarka?" Sosai ransa ke 6aci duk lokacinda ta kwatantasa da mey neme nemen mata sanin ba halinsa bane amma ya ya iya? Dan dole ya danne zuciyansa, yasani duk acikin zafin kishin ne don haka yayi mata uzuri.

  "Look Nazeefah" yayi maganan had'e da aza hannunsa a kafad'unta "I know this's not going to be easy on you, I know how it must hurt, ina sane da komai shiyasa nake rok'anki da kiyi hak'uri dan zan k'ara aure bawai hakan na nufin mabud'in wahala maki bane kokuwa wai zan mance dake ko in walak'anta ki. Nazeefah I love you, I'm proud to have as my Rabba'atul bait, Amal might be my bride but kece uwar gida na, which applies being my soul. Please karki bari kishi ya rufe miki ido yayi destroying relationship namu, I love you Nazeefah and I don't wanna lose you."

   "Duk k'arya ne" ta fad'a had'e da sauk'e hannayensa daga jikinta "wallahi duk k'aryar banza ce inda kana so na da bazaka ta6a tunanin k'ara aure ba."

  "Nazeefah dan zan k'ara aure ba wai hakan na nufin na daina sonki bane, zan k'ara aure saboda sunna ne, ki d'au Amal a matsayin 'yar uwarki ba kishiya ba."

  "'Yar uwa fa kace? Kar ka sake kwatantata da 'yar uwata dan duk mutumin dake shirin sace maka miji ba d'an uwanka bane, Amal mak'iyata ce bana k'aunarta, bazan ta6a sonta ba kuma muddin ka auro ta a gidan nan toh wallahi kaida kwanciyan hankali kunyi sallama sena tabbata na tada maka hankali fiye da yadda ka tadamun nawa yanzu mu zuba da kai a gidan nan muga" tana kaiwa nan ta wucesa ta shige d'akinta had'e da sa key. Ruwa ta watsa ta sauk'e sallan Isha sannan ta fito in search of what to eat. Afzal ta tarar zaune kan dining yana shan corn flakes ko ta kansa batayi ba ta zarce kitchen ta shiga dafa indomie. Bayan da ya gama sha ya shiga yayi joining nata a kitchen d'in.

  "Ni baza a dafa dani ba?" Ko juyawa ta kallesa batayi ba wai gani yake kaman wasa take ko? Ze gani.

  "But I'm hungry."

  "Kula da yunwan ka ya tashi daga kaina ya koma kan na amaryar ka. Idan har bazaka iya jure yunwan ba your bride is just a call away kana iya fita kaje ka sameta daman ka saba" ta basa amsa ba tare da ta koda juya ta kallesa ba. Be sake cewa komai ba ya jira ta, bayan data gama girkin yabita har cikin d'akinta. Duk yadda takeson ce masa ya fita haka ta hak'ura, tasan da gan-gan yake hakan don ya sata yin surutu. Bayan da ta gama ci ta sinche bathrobe dake jikintan ta sanya kayan baccinta ta feffeshe jikinta da turare sannan ta kewayo garesa "Malam kana iya bar min d'akin zan kwanta."

  "Yau kuma nine Malam? Ba Ya Rouhi?" Shin wai ya d'au wasa take? Ze sha mamaki na lahira seya fisa jin dad'i.

  "Ka de jini ka fice mun a d'aki."

  "Naji anan zamu kwana yau?"

  "Malam am damn serious ka fice mun daga d'aki zan kwanta."

  "In kinga nabar d'akin nan to dake ne in fact hak'k'i na ma nakeso, I need my wife."

  "Idan a garinku ana kusantar matar da take haila toh bismillah" ta sanar dashi cike da rashin kunya. Duk yadda yaso 6oye dariyansa ya kasa "Baby kin manta yanzu kika idar da sallah ne?" Yayi maganan yana nuni da sallayar da tayi sallan akai. K'aramar tsuka taja "seka cinye d'akin idan ya zama abinci" sannan ta janye pillonta ta fice. Bayanta yabi izuwa d'ayan d'akin data shiga, haka suka tayi k'arshe tazo ta kwanta a parlour akan d'aya daga cikin couches d'in. Sarai yasan kujeran ba iya d'aukansu zeyi duka ba amman ya bita har kai dan neman magana, kusan rabin jikinsa akan nata yake.

  "Wai don Allah meye haka?" Bata kaiga mik'ewa ba ya jata nan ya samu ya baje akan kujerar had'e da aza ta akan k'irjinsa. Gagam ya matseta yadda ko k'wak'k'war motsi bazata iya ba.

  "Malam ka sakeni!"

  "Shhh let's sleep baby."

  "Ka sakeni ko sena shak'e tukun?" Adjusting nata yayi yadda zata na iya nishi da kyau amman bawai ya saketa ba. Duk kalan suratan da tayi-tayi hakan besa ya saketa ba, dan kanta ta daina surutun sabida yadda ta galabaita. Acikin awa d'aya bacci mey nauyi yayi awon gaba da ita, seda Afzal ya tabbata baccin nata yayi nauyi sannan a hankali ya sauk'eta daga jikinsa. D'agata yayi cike da dabara ya kaita d'akinsa ya shinfid'a ta akan gadon had'e da gyara mata kwanciya. Bayi ya fad'a ya watsa ruwa sharp-sharp sannan ya fito ya kwanta a gefenta had'e da kashe musu wuta. Pillonsa ya kawo kusa da nata sannan ya zagaye hannunsa a jikinta wane wanda wani ke shirin k'wace masa ita, a hankali bacci ya d'aukesa.




RANA D'AYA!
#RD

Love... King Miemiebee👄✨

1 comment:

Unknown said...

Osheey Miemie, more ink to ur pen
Nazeefah wannan kishi haka saikace WERE kardai kisa kanki a wahala wurin bin malamai gwara ki yayyafama zuciyanki ruwan sanyi.