(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
8⃣9⃣
Kwana uku Saalihah tayi a asibiti sannan aka sallameta. Gdy tayi sosai wa dr Hassana, sede koda ta tambayeta yatayi tasamu ta fito da gaskian al'amarin murmushi tamata tace, "thats my littel secret." A ranan abba ya samu Saalihah yace "Saalihah ummanki ta gaya min duk wani abinda kkayi da, da gdan da muke ciki da komai, ta gya min komai inason sanar dake na yafe miki komai ne ni, Allah cigaba da shirya min ke Saalihah." "Nagode abba, ngd sosai." Kayakinta dana Habeeba kap daddy yasa aka tattaro masu aka kaimasu gdansu.
Saalihah is missing her Fudail already sede ba kamar yadda yake missing nata ba. Fudail ji yake kamar ya kashe kansa kawai ya huta. Kullum cikin waya sukeyi da Fudail nata a koda yaushe tana mak'ale da wayarta a kunne suna hira. Morning, afternoon, evening and good night mssgs kullum seya mata sendn nayau daban na gobe daban yana gaya mata yadda yake missing nata. Ranan kam har flowers red roses ya kaimata, duk sanda yazo kuma se sunsha kisses nasu sannan yake tafiya, Wani san dayake mata yanzu kam koda ance ga paper da biro ya rubta bare iya ba, is just like a copied assigbmnt (lol). 'yan biyun Saaly kuwa suna nan cikin k'oshin lfya.
A yau daddy yasa sa gaba seyaje sun daidaita da Asma'u haka ba yadda ya iya. Da yammacin ranan yajesa gdansu Asma'u. Bada jimawa ba tafito ta samesa ko fitowa daga motar beyi ba, har ciki tzo ta samesa, tare da gaishesa. Ko amsawa beyi ba illa wani deadly look daya bata wanda sanda ta d'iga fitsari a wandonta.
A hnkl cikin nitsattsen murya yace, "Asma'u nasan barakiso ki auri wanda baya sanki bako?" Kai ta giad'a masa. "Toh ynzu kina komawa ciki kisamu mummy ki gaya mata bakia sona, sbd bana sanki Asma'u baran b'oye miki ba Saalihah nakeso nd inhar kinaso na abinda nakeso zakimin go nd tell mummy you don't love me kinga se mu rabu in peace." "Chabdi!" Abinda tafad'a knan "ai wlh kayi k'arya wata mace ce zata bar na miji kaman ka yayi slipping of her fingers, ban tsammanin akoi wannan mace, ai aurena dakai consider it done. Tunba yau ba nakesonka, gashi Allah ya amsa min addu'ata na cika min burin aurenka...
...Am sorry baran iya maka abinda kakeso ba Fudail." Sterring motar ya buga "you're asking for it Asma'u bcuz kinga am being nice yanzu kka d'au banda tough side ko? Toh wlh in kkayi pushing thru da maganan auren nan bliv me sekinyi regretting sanin Fudail a rayuwarki. Now get out of my car." Ba gardama ta fita tace masa ta window "I love you and so I must marry you, nxt zuwanka ka kawo min gashi me dad'i." Tana kaiwa nan ta shige gda. Fudail ji yake kamar yasa hannu aka yayi ihu. Wai wannan ballagazan ne Ikleema ke fad'in tayi masters? Aiko a k'auyen garinsu tayi masters baratana k'auyencin nan ba, da ita da gashin sunci k'anyansu.
Yana isa gda yaga daddy na zaune a gefen parking lot. Nan yayi parking yafito ya gaishe sa sannan ya mik'e da nufin shiga site nasa. Kiransa daddy yayi dan dolensa yadawo. Daddy ya tambayesa "ya kunsamu kun daidaita kuwa?" A ransa yace, "koda bamu daidaita ba zakayi backing out ne?" A fili yace, "eh munyi." Daddy yace, "masha Allah." Fudail besan sanda yafara kuka ba "daddy dan Allah kayi hkr ka janye wannan mganan wlh banasan Asma'u daidai da rana d'aya ban tab'a santa ba daddy dan Allah kayi hkr wlh nayi nadaman abinda nayi ma Saalihah kuma I've asked for her forgiveness and tayafemun." D'an murmushi daddy yasaki sannan ya ninke newspaper'n dake hannunsa. "Yayi kyau kafin na manta daga yau bansan ka sake kiran Saalihah ko ka tura mata mssg in har kayi to Allah ya isa na ze bika."
Salati Fudail kawai yake ta nanatawa "daddy, kasheni kakeso kayi? Ka tausaya min daddy dan Allah kayi hkr wlh nayi nadaman abinda nama saalihah, d'an adam ajizi ne na tuba daddy..." "Baka tuba ba Fudail kuma bakayi nadama ba dole ka auri Asma'u ko kanaso ko bakaso." Besake fad'in komi ba ya ruga site nasa da gudu ya baje kan gado se kuka yakeyi me tsuma zuciya pictures na Saalihah yashiga yana viewing yana kuka. He cant actually believe what is going on.
Habeeba ya kira bayan ta gaishesa ya gaya mata sak'on daya keson tagayawa Saalihah batun aurensa takuma bata hkr. Dan koda wasa be tab'a gayawa Saalihah daddy nasan aura masa Asma'u ba dan bayya san hnklinta yatashi, seyau yace Habeeba tagya mata. Koda time da baaba ta gayamata a asibiti kuma bata sa hnklin ta ta ji ba. Bayan sun gama wayar Habeeba taje tasamu Saalihah a d'akinta jiki a sanyaye ta zauna kan gado dake Saalihah ta hanata zama a k'asa.
"Anty." Take Saalihah ta jiyo "na'am Habeeba ta ya akayi?" "Lfya anty uncle ne ya turoni" Cike da zumud'i Saalihah tace, "bade yazo ba? Kice masa ina zuwa" "a'a anty ta waya ya kirani."
Take mood na Saalihah ya canza, mene ze gayawa Habeeba da bare gaya mata ba. "Toh inajinki" ta fad'a. "Anty cemin yayi in baki hkr wai he's so sorry bare sake contacting naki ba sbd daddy ya hanasa yakuma ja masa Allah ya isa inhar ya kuskura ya sake kiran ki, yanzu haka mgnan auren sa da Asma'u ake bayadda beyi da daddy ya hkr ba amman yak'i, wai sam seya aura masa Asma'u."
"Habeeba tell me you're joking. No dan Allah daddy ya rufa mana asiri inhar yanaganin sbd abnda Fudail yamin ne ze masa auren dole wlh ni na yafe masa dan Allah yayi hkr. Wayyo Allah na" kuka tasoma yi tana ihu. Duk su umma suka shigo suka soma bata hkr zobenta wanda yabata tun a NY take ta kallo tana kuka haka tatayi har sanda bacci b'arawo ya saceta.
Koda ta kira number'n Fudail kuwa switched off ne baishiga. Ba yadda su umma basui da ita ba amman takasa barin kukan. Itacewa ma tayi zata kira daddy in person tabatasa hkr amman umma ta hanata aganinta yin hakan yazama rashin kunya
Saalihah tayi hkr kawai ta rungumi k'addara. Haka fa tun da ga ranan rayuwan wad'annan masoya yafara crashing. Kullum cikin tunanin juna suke suna kuka. Fudail kuwa sekace d'an da ake kora islamiya kullum daddy ke koransa zuwa zance gun Asma'u koda yafitan kuwa yawonsa yake zuwa ba wajen Asma'u dayake zuwa.
A yau sauran wata biyu bikin Fudail da Asma'u. Fudail ya koma tamkar sabon mahaukaci har gomma Saalihah ma. Cikin sati ukun da suka gudana kuwa Saaly tafara bin duk wad'anda taci amanarsu dan neman gafararsu. Gashi tana kud'i cikin acct nata takuma sayar da sauran golds nata da brazillian hairs nata duk ta had'a. Daga gdansu Ibrahim d'an chairman tafara zuwa a bakin gate kuwa ta had'u dashi ta k'arisa tamasa sallama da far'ara ya amsa sannan yace, "ummi ko umma?" Murnmushi tayi tace, "ko d'aya wannan Saalihah ce." Kansa ne ya rud'e haka de tamasa bayanin komai takuma nuna masa ta tuba tazo ya yafe mata ne tsakaninta da Allah.
Ta irga masa 45k data tab'a sace masa ta mik'a masa saidai sam yak'i karb'a yaji dad'in tuban da tayi dama haka akeso gashi kuwa yanzu ai ta shiryu tunda har tayi aure. "Na yafe miki Saalihah, Allah yafe mana gabad'aya." Gdy sosai ta masa nan ne tad'an ji relief ta sauk'e nauyi d'aya kanta.
Daga nan ta wuce gdan bawan Allahn data tab'a masa sharrin zina. Yana zaune a tsakar gdansa tashiga tayi sallama ta durkushe har k'asa ta gaishesa at first ma beyi recognising face nata ba se daga baya ya ganeta, tambayan da Ibarajim yamata shima ya mata yace, "Umma ko Ummi?" nan ta bayyana masa komai takuma nuna masa tayi tuban gaske ta irga masa dubu hamsin nasa ta ajiye masa. At first cewa yayi bare yafe mata ba dan ganin ko tuban gaske tayi sede yaga hkr ta cigaba da bashi can tace zata tafi ta gde da lokacinsa daya bata, Allah yafe musu gabd'aya. Kiranta yayi ya mik'a mata kud'in tare da cewa ya yafe mata Allah yafe musu gabad'aya. Yakuma nuna mata dad'in shiryuwan datayi haka de Saalihah ta riga bin wanda tasan gdajensu tana neman gafarasu.
Saidai ta nemi Yunusa da Suleiman sama da k'asa ta rasasu.
Sauran kuwa awajen da karuwai suke layi ta samesu, in sunzo d'iban 'yan mata seta duba faces nasu intayi recognising nasu seta masu bayanin komai takuma tambayesu kud'in su saura suna amsa saura kuma suna yafe mata saura kuma cewa suke su barasu ma iya tuna ta ba amman ko ma meh sun yafe mata. Harta alhj na mata sanda Saaly taje ta nemi gafarsa kuma ya yafe mata. Phaary da Bint kuwa duk sun musulinta ynxu sbd lesson da suka koya daga raywuwar wata k'awarsu da samari suka mata fiad'e suka kuma kasheta suka yanke sauran shashin jikinta. Tun daga lokacin suka ahiryu suka soma facing studies nasu, khadeeja kuwa tazama babbar k'awarsu.
Koda Saalihah takaimusu visit makaranta tagansu kansu a had'e ba k'aramin dadi taji ba ganin frnds nata sun shiryu se maganan aure ma sukeyi. Se tsiya suke mata wai maman unborn.
Tana kallon pictures cikin wayar Khadeeja suna hira kawai setaga hoton Yunusa. Cike da mamaki ta tambayeta ko waye shi and waye d'inta ne. Murmushi tayi sannan tace, "wannan ai d'an uwa na ne kuma aynxu haka mun kusa aure." Cike da mamaki Saalihah tace, "aure?" Khadeeja tace, "eh wani abu ne ko kinsan sa ne?"
No comments:
Post a Comment