Tuesday, 30 January 2018

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...
(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
      written by miemie👄
                  9⃣1⃣


 
          Da yammacin ranar asabar su Saalihah suka fita outting da Fudail nata bayan sun gama yawonsu suka zarce hysaan meat and beverages. Nanma ji take kamar ta bisa ciki su siya tare amman dan yadda tagaji tabarsa ya shiga shi kad'ai. D'an kalle kalle takeyi can taga alhj me range rover land rover data tab'a sace mai mota. Ba k'aramin dad'i taji ba da sauri tafita taje ta masa sallama shimade daya ganta be ganeta ba sanda tata masa bayani can yagane ta tambayi forgiveness nasa sam yace shifa bare yafe mata ba se in ta biyasa motarsa kokuma ya tara mata mutane. Daidai nan Fudail yafito ya nufo gabansu tare da tambayan Saaly meke faruwa. "Honey ka tuna wanda na gaya maka akan I once sold his range rover land rover? Ans ina namansa? To Gashi nan shine guy d'in. Nan suka gaisa da Fudail, Fudail yayi dashi ya hakura amman yak'i daga k'arshe da ran Fudail ya b'aci ya mik'a masa card nasa kan yakira sa gbe su hadu a gu kaza.

      Alhj me mota kam yak'i yarda sanda ya kira numbern yaga ya shiga sannan ya barsu suka tafi. Koda suka shiga mota kuka Saaly tafara masa tana tunanin ina zata samu mota ko kud'in da zata biya wannan bawan Allah Fudail kuwa hkr kawai yake bata yana assuring nata everythng is gonna be alright amman sam tak'iyin shiru. Haka ranan suka kwana hnklinsu duk a tashe se kuka take masa.

       Washegary tun around six na safe Fudail ya fita da kyar ya iya ya raba jikinsa daga rik'on data masa ba tare da ya tada ita ba. Gda yaje yasamu daddy ya masa bayanin komai sekuwa cikin motocin daddy akoi range rover land rover'n alhj me motan can. Ba gardama daddy ya mik'a masa key'n gdy yamasa sosai daddy ya nuna masa ba komai. Gda ya koma around 8 ya tada Saaly sukayi wanka dukda cewar yanzu batasan suna wanka a cewarta wai ze mata dariya tunda tayi nauyi yanzu amman ina shi ko kad'an hasali ma da cikin tafi masa kyau. Se shiri sukeyi shide be gaya mata ina zasu jeba dan haka tazama so curious in knowing ina zasu jen. 9:00AM on the dot suka gama shiri a daidai gaban office nasu Fudail suka tsaya can sega alhj me mota shima ya paso. Yana isowa suka gaisa da da Fudail. Hannu Fudail yasa a pocket ya ciro key'n mota ya mik'a masa, cike da mamaki alhj me mota yace, "wannan fa key'n me?" Fudail yace, "press d security" tare da matso da Saalinsa kusa dashi nan mutumin ya danna kawai seyaji wani mota yayi k'ara a bayansa yana juyawa yaga exactly motarsa harda colour'n ba abinda ya raba. Juyowa yayi da bakinsa a bud'e yana kallon Fudail cike da mamaki haka Saaly ma takasa rufe bakinta. Toh ina Fudail ya sami motar? Koda shike ba abin mamaki bane yanada kud'i daddy nada kud'i. Tayi assuring kanta.

       Alhj me mota yace, "dnt tell me wancan mota tace?" Fudail yace, "koba erinshi bane motar taka?"  "Sosai erin nawa ne har paint d'in. Kai amman nagde.x Fudail yace ur wlcm yanzu de ko kaga matata akan hanya u wont accuse her of anything tubda darling husband nata y biya ka motarka ko?" Tare da manna wa Saaly data manne a jikinsa not letting him go kiss a goshi.

          Alhj me mota yace, "sosai ngd once again. Amman dama kanada motar ne kokuma ajiyan kaje kasiya dan gaskia kaban mamaki." Fudail yace, "kana mamaki ne well u don't have to cuz my dad is a minister and koda badan wannan bama am rich enough to pay u ur car. We are going  a tsufar da mota lfya."

     Nan yaja hannun Saalinsa suna swinging arm har suka shiga mota. Shide alhj me mota mamaki ya cikasa dan wannan motar har kamar tafi sabuwr motarsa sabo ma. Dad'i kashe sa. Acikin motan Saaly tace, "honey" har yasaki key seya tsaya. Matsowa kusa dashi tayi tayi kissing nasa passionately, a hnkl tayi pulling out tare da rik'o kyakkyawar fuskarsa "thank you so much Fudail, you mean the world to me. I can't ver forgive myself in nayi maka wani abu someday..."  "Shhhh u dont have to thank me inkinga na miki abu is becuz you deserve it." Nan yasa key ya kunna motar "ready?"  "Ready baby" tace masa tana murmushi. Nan suka soma tafya Fudail yama alhj me mota honk sannan suka fice.

      Haka rayuwa take ma Fudail da Saaly dad'i nothing is going in their way. Umma kuwa tana k'ok'arin zuwa ganin lfyr 'yarta da jikokinta. A watan da cikin Saaly ya cika 7 months ne aka ma Fudail transer from Bauchi to Abuja, yakuma k'ara samun matsayi a office. Murna gunsu baya misantuwa. Sede Saaly zatayi missing frnds nata da family sosai. Masu aiki musamman Fudail yayi hiring, su suka masu packing duka kayakinsu. Ko tsinke Saaly bata d'aga ba. Habeeba se murna take zata Abuja birnin tarayya cikin jirgi! Dududu kwana uku ya daukesu aka gama masu parking aka sa kayansu cikin wasu manya manyan motoci guda biyu suka kama hanyan Abuja. Su Saaly kuwa se gbe zasu tafi a jirgi kominsu is ready sauran tafya. A ranan mutane dayawa suka zo suka riga musu sallama yawancin collegues na Fudail na office ne. Su ameenatu, ruky, phaary, bint  khadeeja duk sunzo suka sha shagalinsu sukayi pictures.

      Se can da yamma kowa ya watse ansha kuka kam. Saaly ta mugun gaji ga cikin nan yayi k'ato da kyar take zama take tashi akoda yaushe Fudail ke assiting nata yin komi. Cikin 'yan biyu se a slow. Tausa yata mata a daren ranan har tasamu tayi bacci shima ya kwanta...

No comments: