Wednesday, 17 May 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  5⃣3⃣



           Bata san sanda hawayen suka soma d'igowa a k'asa ba dagudu ta fad'a toilet tayi locking, Fudail yabi bayanta yana bubbuga k'ofar sweetheart lfy? Open the door kinji? Yi hkr let me in. Yacigaba da bubbugawa Saaly na zaune akan WC se kuka take yi kamar zata cire ranta tace a ranta am so sorry Fudail I can't let you in banasan in tayar maka da hnkl. Shiko jin k'aran kukan ta ba k'aramin tayar masa da hnkl yake ba se bubbuga k'ofar yake yana jijjik'awa Saalihah sweery yi hkr ki bud'e kinji? Se k'ara volume na kukan nata take sam takasa bud'e masa. Daman shi ko d'azu data gaya masa missinh umma take yasan k'arya kawai take masa dan kukan datayi d'azu yafi k'arfin ace missing umma take.

         Haka har ya gaji da bubbuga k'ofan ya sulale k'asa ya zauna a bakin toilet d'in yace Saalihah I love you, nasan kina jina and am very sure kinada babban reason daya sa kka zab'i rufe kanki a toilet to cry all by yourself. Knkw that, I'll always be by urside, ur problem is also mine, we are in this together sweery. Remember the first time muka fara had'uwa kika kusa fad'i? Na taro ki dukda bansan wace ke ba but tun alokacin nasan we will become something special in future.

         Tana zaune kan toilet sit d'in ta d'an rage sautin kukanta jin wannan sweet words da Fudail nata ke gaya mata. Kwata kwata seya kashe mata jiki kukan ma taji ya tsaya. A sanyaye ta mik'e tana tafiya kakar wacce k'wai ya fashe ma a ciki ta je ta bud'e k'ofar take Fudail ya juyo tare da mik'ewa jikinsa ta fad'a yasa hannunsa ya zagayeta a yayinda ta sake tusa kanta cikin jikinsa.

          Bayanta yake shafawa a hankl hab'ansa kan gashin kanta. Tace am sorry Fudail, dan Allah kar kayi fushi dani. Fudail yace shhhh don't think like that banga reason da zesa inyi fushi dake ba am very sure kinada reason dayasa kke acting strangely lately, I just hope I can be of helo to you sweetheart, bana son ganinki kina kuka. Nan ya d'agota daga jikinsa tare da rik'o 'yar fuskarta da hannayensa bibbiyu kan kumatunta tell me sweetheart nasan ba missing umma kawai kke ba, mene?

            Murmushin dole ta k'irk'iro idanun nan sunyi ja zir kamar cala ta d'ago both hands nata tana murzasubsoftly akan hannunsa dake fuskarta Fudail I have a bad feeling ina ganin kamar am about losing you, gani nake kamar za'a rabani dakai and that is my biggeat fear bana san rabuwa dakai Fudail baran iya rayuwa ba kai ba. Hawayen dake k'ok'arin gangarowa daga idanunta yasa hannunsa ya share.. Never sweetheart in shaa Allah nothing will ever come btw us, I'll always stand by your side. Yayi assuring nata tare da bata peck a goshi. D'an sanyi taji a ranta duk da tasan the moment Fudail yasan gaskia akanta duk wannan kalamun dayaje fad'i zasu koma history. Ita har ga Allah ynxu da zata iya gathering courage data gaya masa amman barata iya ba. Dole ne tajira rananda asirinta ze tonu tayi facing k'addara dan daba dan halin umma ta gada ba da haka duk be faru da ita ba.

         Hannunta ya ja ya kwantar da ita kan gado tare da rufeta da bargo ya manna mata kiss a kumatu sannan ya je ya kashe laptop nasa ya hauro gado tare da kashe bedside lamp d'in. Rungumota yayi yana gaya mata dad'add'un kalamu har tasamu tayi bacci ahaka shima bacci ya d'aukesa.


beeenovels.mywapblog.com

No comments: