Wednesday, 17 May 2017

KAMAR KUMBO KAMAR KORENSA...


      written by miemiebee👄
                  5⃣1⃣



        Ajiyar zuciya tayi sannan ta sauk'o daga kan gadon ta wuce toilet tayi wanka tafito ta cancare kwalya tasa wata lace nata purple fitted riga da skirt daya mugun karb'anta, ta d'aura kanta erin d'aurin ntwrk innan. Jakarta ta d'au ta ciro d'ayar wayarta k'irar samsung galaxy s7 edge tasa new line nata na New York aciki sannan ta kunna dan iphone  nata yayi running out of charge ita kuma ta manta bata had'a ba se ynxu. Message frm T boi ta fara coming across with, zuciyar ta ta hau bugun d'ari d'ari. Takai da bud'ewa kawai taga T boi na kiranta sekace daman jiranta yake ta kunna wayar. Toh ina ma yasamu new line nata? Bayan su Phaary ne kawai suka santa da layin. B'ari jikin Saaly yake sam takasa picking call d'in ta kuma kasa katsewa haka har ta tsinke.

        Nan ya sake bugawa a hnkl ta d'aga ta kai kan kunnenta ba tare da tace komi ba T boi yace, "hello Saaly?"  "Na'am" tace bakinta na b'ari yace, "kin kyauta knan?" Tace, "kamar ya na kyauta?" Tana mgnan tana kallon bakin k'ofa cuz at any moment Fudail yana iya shigowa dan bata san inda yaje ba. T boi yace, "aww tambayata ma kke? Dama kina da wanda kkeso bayan ni?" Saaly tace, "calm down T boi lemmi explain..." T boi ya katse ta "explain what Saaly? Kinci amanata sanin kanki ne ina sanki kuma inada burin san auranki kema kin sani amman tunda kkayi watsi da soyayyar danake miki ki bud'e kunnuwanki kiji da kyau wlh wlh tunda baran sameki as mata ta ba no one will have u either zanyi duk abinda nasan zan iya inga na cimma burin rabaki da Fudail, enjoy yourself while ur wedding last!" Yana kaiwa nan yayi hanging.

         Tuni idan Saaly ya cike da hawaye da muryarta me rawa tace, "hello...? Hello?" Jin ba amsa ta sauk'e wayar ta ajiye kan gado. Hawaye se ambaliya suke a fuskarta dan ta san halin T boi sarai ze iya aiwatar da abinda ya fad'a mata ynxu. "Innalillahi! Nashiga uku taya T boi ya samu number na? Cikin bint ko phaary wace tabasa? Taya yasan Fudail na aura? Innalillahi dan Allah T boi ka rufa min asiri karka min haka". Nan ta sa hannu ta share hawayen nata ta d'au wayarta ta kira number'n T boi har ta tsinke be d'aga ba se akaro na biyu, nan ma bece komi ba dan haka tace cikin kuka;

       "T boi dan Allah kayi hkr wlh ba amanar ka naci ba, ban aureka bane sbd ni ba matar ka bace, Allah be rubuta kaine zaka kasance mijina ba sesa na auri Fudail. Dan Allah ka janye maganar da kayi ka rungumi k'addara..." Katseta yayi "in rungumi k'addara? Ai wannan ba k'addara ba sunansa Saaly, inhar bakison nayi somethng nasty is simple ki bar Fudail ki dawo gareni shknan and no one will get involved nor harmed".  "Ta yaya Tasleem? (Asalin sunan T boi) ta yaya zan rabu da mijin da aka d'aura mana aure just some days ago?..." Yace, "ta yaya nima kkeson I should just sit back inganki kina more rayuwarki dawani d'a na miji ba niba? Kiyi adalci mana Saaly."

        Saaly da kuka yafi k'arfinta tayi k'arfin hali tace, "Tasleem dan Allah in kanayi wa Allah kuma in kana so na do this for me. Kafita daga harkana assume baka tab'a sanin wata Saalihah a rayuwarka ba wlh kamin haka kagama min komai a rayuwa nikuma na maka alk'awarin sa ka cikin kowace addu'ata kan Allah had'a ka da rabonka kaima." Dariya sosai Saalihah tabawa T boi, yace, "ai wannan ba so bane Saaly, kisan dan san da nake miki ne yasa baran iya barin wani na miji ya zauna dake ba, baran iya yarda wani d'a na miji ya faranta miki ba, kigane mana! Saaly"  tace, "wannan ba so bane Tasleem inhar kana so na wlh zaka hak'ura da san da kakemin ka rungumi k'addara, love isn't about being selfish".  "Gafara can har ke kin isa kice min am selfish? Ai inhar someone is being selfish anan to kece, kece Saalihah tunda kinsan sarai tun kafin a miki aure kinada wanda kkeso but kka k'i gayamun har ana sauran sati bikinki muna waya dake kuma kina karb'an kud'i a guna kinga ko kece selfish ba niba."

          "Tasleem dan Allah kayi hakuri ka mance da komai in kan kud'inka ne wlh kafad'i ko nawa kakeso zan mayar maka dashi." T boi ya qyal qyale da dariya "Saaly masoyiyata knan! aikinsan ina sonki ko nawa ne zan iya kashewa akanki, this is how much I love you!" Saalihah bata iya fad'in komi ba takashe wayar. Ta fashe cikin wata irin matsanancin kukan da ta jima batayi ba, kuka take sosai just about komai nata ya fara tafiya mata perfectly and smoothly d way takeso T boi ze zo yamata ruining rayuwarta by threatning her kan ze raba ta da Fudail nata ko taya.

        "I can't loose you Fudail, I really can't. Nayi nadamar saninka Tasleem bantab'a zatan zaka iya min haka ba. Wayyo Allah!" Daidai nan Fudail ya shigo d'akin da broad smile akan fuskarsa. Ganin haka yasa Saaly tasa hannu ta goge hawayenta dan kar Fudail yayi suspecting wani abu. Gabanta ya nufo ya tsuguna; "sweery na dawo". Juyowa tayi ta kallesa sannan ta k'irk'iro murmushin dole "sannu da zuwa honey" tabasa hug "me aka siyo min?" Tayi k'ok'arin b'oye mood nata saidai kallo d'aya Fudail ya mata yasan ba lafya ba, ba haka yabar Saalinsa ba dole   something must be bothering her.

     
   beeenovels.mywapblog.com

1 comment:

Blogger said...

There's a chance you are qualified to get a Samsung Galaxy S8.