BY MIEMIEBEE
PAGE 69
March, 2017
Kai zallah ta iya ta gyad'a mar saboda yadda takeji ajikinta. Sake rungumeta yayi gagam dukda yadda baya jin dad'in hot temperature'n tan amman don da tace he should hold her. A hankali bacci yayi gaba da Zeezee, Al'ameen kuwa har yanzu hankalinsa ya kasa kwanciya. Tun aurensu da yayi shekara biyu yanzu be ta6a Ganin Zeezee a irin wannan situation ba, duk rashin lafiyanta baifin ciwon kai kona ciki wato menstral cramp, he is so worried ganinta a irin wannan condition. A hankali da k'yar wahalallen bacci ya d'aukesa shima se Maghrib ya tashi ya kwantar da Zeezee a gefe sannan ya fice bayi yayi alwala ya fito. A hankali ya sake gwada temperature'nta inda yaji ya sauk'a sosai, dad'i sosai hakan ya sanya sa. A hankali ya shiga tada ita har seda ta bud'e idanunta tayi setting nasu akan handsome face nasa.
"Princess how are you feeling?" Kai ta gyad'a mishi as an answer.
"Kin d'an ji sauk'i ko muje asibiti?"
"I am feeling normal Sweetheart kawai wanka zanyi in warware."
"Are you sure?"
"Yes ai na gaya maka, fever'n come and go ne."
"Alhamdulillah toh tashi na had'a miki ruwan wanka kiyi se muyi sallah."
"Zamuyi a gida?" Ta tambaya murmushin face nata na dad'a bunk'asa a rayuwa tanason Al'ameen yana janta sallah.
"Yes Princess."
"Yeyy! Thank you." Da kansa ya d'agata chak a sama har bayin ya direta, da wankan ma cewa yayi ze mata amman tak'i don haka ya bata privacy. Tana fitowa tasa kayan daya cire mata suka idar da Sallan.
Wajajen 8:30pm Al'ameen ya fito daga d'aki ya samu Zeezee dake kwance a parlour bisa kan kujera. "Princess bazaki ci komi ba ke zaki kwanta?"
"Bana sha'awan cin komai Sweetheart don't worry, come over." Ba gardama yaje ya zauna gefenta inda ta kwanta a jikinsa before 9pm har bacci ya saceta. Yana gama kallon sports nasa ya d'auketa ya kaita d'aki sede mamakin lamarin Zeezee yake. Bata ta6a kwanciya bata ci abinci ba se yau, bayan nan kuma a kullum duk rananda ya dawo daga tafiya Zeezee bata barinsa as suna satisfying needs na junansu amman yau ko ta kansa bata yi ba. Da wannan tunani a ransa ya kwanta gefenta tare da janta jikinsa yayi bacci.
Washegari ma haka suka sake tashi Zeezee ba lafiya ta yarda suje asibiti kuma tak'i ganin ya dage se sunje tashiga yi mai kuka dan dolensa ya yarda sukayi zaman gidan kamar yadda takeso. Breakfast ma shi ya musu yau, taci ma ta kasa da k'yar ya samu tad'an ta6a ta sake komawa bacci. Ciwo kaman me aljanu, sha biyu na wucewa kuma ta dawo old self nata ta girka musu lunch se anan take neman hak'k'inta gun Al'ameen, yamma na sakeyi kuwa ta sake falling sick. Har tsoro rashin lafiyan nata ya soma bawa Al'ameen sekace me jinnu. Sunyi hakan na kusan kwana hud'u ana biyar suna zaune akan dining suna having lunch bayan Zeezee tayi biting kaza tana ci kawai taji yana tada mata zuciya, se kawai tajiyo amai a guje ta ruga bayi ta shiga kwararo amai shima Al'ameen da sauri ya bi bayanta.
"Ya Al'ameen please karka k'ariso it's disgusting." Tace dashi a wahalince. Be saurareta ba ya k'ariso cikin bayin tare da aza hannunsa akan bayanta yana shafawa back and forth a hankali yana me mata sannu. Aman ta cigaba dayi wane zata harar da kayan cikinta. Tana gamawa ya tayata wanke bakinta sede ko tsayuwan arziki Zeezee bata iyawa don jiri, daman ba wani abincin arziki take ci ba kwana biyu ta kuma sake yin amai. "Princess zaki iya tsayuwa?"
"Zan iya Sweetheart don't worry." Tana gwada mik'ewa daga tsugunen da taken kawai ta fad'a jikinsa ba control don jiri, da sauri ya taro ta. "Zainab you are terribly sick we need to see a Dr." Daga nan ya d'agata ya kaita d'aki tare da kwantar da ita akan gado. Hannunsa ta rik'e kafin ya juya, "Ya Al'ameen stay with me please."
"Zainab zan kira Dr ne from all seeing bazaki iya zuwa asibiti ba, ina zuwa."
"You can call her later yanzu please stay with me." Be sake mata musu ba ya kwanta a gefen nata, a nitse ta aza kanta bisa k'irjinsa. "Zainab?"
"Na'am" ta amsa sanyi-sanyi.
"How are you feeling?"
"Sick Ya Al'ameen" ta ansa sincerely. "Ji nake kaman zan mutu."
"Shhh! Bazaki mutu ba in shaa Allah zaki samu sauk'i I'll call a Dr."
"Thank you."
"But Zainab what do you think is wrong with you?"
"Ya Al'ameen I don't know am not a Dr."
"Symptoms shows that you are pregnant" ya fad'a shi kansa besan how and when ba kawai abinda zuciyarsa ke raya masa kenan.
Bata san a lokacin da ta miqe zaune ba duk da rashin lafiyan da takeji "pregnant?" Ta nanata cike da mamaki. Sekuma ta shiga kad'a kai, "no it can't be possible Ya Al'ameen, I can't ever get pregnant please karka sa ranka I don't want you disappointed."
"Zainab listen to me, when last kika ga period naki?"
"Ya Al'ameen please..."
"Just answer me Zainab when?"
"Ya kamata shekaran jiya yazo bai zoba but nasan zezo soon enough."
"Zainab you are actually pregnant shi yake jawo miki wannan morning and evening sicknesses d'in."
"Sweetheart ba pregnancy bane kad'ai ke jawo hakan, it might be a malaria fever ni nasan I can't ever be pregnant shiyasa nakeson kaima ka cire a ranka tun wuri please."
"And ni na fad'a miki juna biyu ne dake, here look at the mirror bakiga kin k'ara haske da k'iba ba?" Kallon kan nata tayi sannan back to him "well it might be ko dan ina jin dad'i ne."
"Dad'in exams ko kuma na rashi na? You have no reason to add weight like this Zainab except for you are pregnant."
"Am not Ya Al'ameen."
"We'll see about that nide nasan akwai little soldier na ko Princess anan, zan kira Dr Sammy" Yayi maganan hannunsa aze akan flat cikinta. Hannunsa tabi ta d'aura nata akai "Ya Al'ameen are you sure about this? Do you really think that am pregnant?"
"Yes Princess evidences sun nuna, two days ko nema na bakiya yi unlike before this is another strong symptom."
"Ya Al'ameen bana son in yarda da hakan, banason se Dr ta iso tace mana am not pregnant I don't want to disappoint you, please kabar fad'an ina da ciki."
"You are pregnant Princess I won't ever stop saying so."
"I really do pray so, ba wanda ze kaini murna da farin ciki idan har Dr ta tabbatar mana da eh cikin ne dani, banida burin daya fiye min inga na azurtaka da zuri'ah Ya Al'ameen, ina son inga kids namu sun saka a tsakiya kuna wasa, inason inga na cika maka gidan nan da cute kids just as you are, imagine just how cute it'll look."
"And in shaa Allah that time has come Princess, nasan akwai little sodlier na ko Princess anan soon enough zasu fito, I love you Princess I love you so much."
"I love you more" ta amsa alokacin da yake neman kissing nata, da gan-gan yayi hakan. Shutting kiss nasan tayi tana turasa da wayo "Princess I need you, I need My woman."
"Ya Al'ameen please kayi hak'uri ko zuwa gobe am feeling weak yanzu."
"See!" Yayi exclaiming "I told you ciki ne dake kink'i yarda gashi you are loosing interest in this which is another sign ai da gan-gan na tambayeki."
"My Soldier do you really think so?" Tayi maganan itama tana soma yarda da batun eh cikin ne da ita. "Yes Princess bari in kira Dr" anan ya mik'e ya kira Dr Sammy inda ta sanar dashi tana zuwa. Hannu Zeezee ta aza akan flat cikinta tana shafawa a hankali what if am really pregnant? Ma'ana mahaifata bata 6aci ba kenan? Oh Ya Allah! Ka tabbatar min da hakan, ba abinda Mijina yake so kaman yaga jininsa ya Allah ka tabbatarmin cikin ne dani tayi add'uar cikin ranta. Komawa kan gadon Al'ameen yayi yajata jikinsa ta kwanta. "Princess yaushe little Princess d'ina zata shigo duniya ne? I want to meet her."
"Sweetheart nothing is certain yet, bari Dr tayi mana confirming tukuna."
"Ai ni na riga nayi confirming, Dr kawai zata duba min how old My Little Princess or Soldier is, amman ciki kam akwai. Akwai a jiya na anan" yayi maganan tare da aza hannunsa kan cikinta yana shafawa a hankali. Kai ta d'ago tana kallon cikin idanunsa a hankali tace, "I love you My Soldier."
"I love you more" ya fad'a tare da pecking forehead nata. Bada dad'ewa ba Dr Sammy ta iso inda har d'aki Al'ameen ya shiga da ita. Dr'n so cute tana setting eyes nata akan Zeezee dake kwance amman tana neman zama ganin shigowar Dr'n, tun anan ta gano juna biyu ne da Zeezee."Congratulations Brother."
"What for Dr?" Al'ameen Ya tambayeta a cikin duhu.
"Your wife is pregnant!" Farin cikin da Al'ameen da Zeezee suka tsinci kansu ciki is indescribable.
"I told you Princess, you are carrying my baby." Yayi maganan sounding delighted. "Dr are you sure?" Zeezee tayi tambayar hannunta dafe kan cikinta still not believing, a yayinda Al'ameen ya k'ariso gefenta ya zauna.
"Yes Dear, ba semun miki wani gwaji bama, yanayin ki kad'ai ma shedan kina d'auke da juna biyu ne."
"Alhamdulillah" cewar Al'ameen totally out of words bema san na cewa ba tsan-tsan farin ciki. Hugging Zeezee yayi "we've finally made it Princess, thank you." Ya sanar da ita a kunnenta tare da pecking forehead nata. Murmushi ta mar tare da d'ago kanta daga jikinsa ta tambaya;
"Dr but how is that even possible? Nayi kusan shekara uku ban ta6a yin koda 6ari ba saboda wani maganin hana d'aukan ciki da akata d'ura min for good 6 months, yanzu kuma kice am pregnant? Side effects d'infa? You mean to say Mahaifata bata lalace ba kenan?"
"Wow! Thank God Mrs Al'ameen, shi dama magani da aikinsa a jiki da kuma side effects nasa Yana determining environment na mutum ne, genes structure and also kalan abin da mutum ke ci matters. Wani zakiga yayi ta shan magani amman bayi mai aiki wani kuma da zaran ya sha yake samun waraka. Same goes to the side effects of drugs, ke daman tun chan Allah be k'addara miki haihuwa bane se yanzu, if not mahaifarki is good tunda har kika iya kika d'au ciki but if you still don't believe me, muna iya k'arisawa asibiti na mu duba miki mahaifar muga if maybe abu kad'an ya sameshi kinga se ayi treating da wuri sannan kuma mu duba cikin naki how many weeks or months ne." Kwantar da Zeezee dake zubda hawayen jin dad'i da farin ciki Al'ameen ya kuma yi a jikinsa "cry no more Princess, kinji bayanun Dr Sammy ni dama I told you nothing is wrong with your womb, still kina son a duba mikin?"
"Kai kanaso a dubamin ne Sweetheart?"
"Nifa na gaya miki ba abinda ya samu womb naki Zainab, haihuwa ne Allah be kawo ba se yanzu."
"Toh shikenan zamu bita kawai ayi scanning mana baby'nmu ko?"
"Yes Princess." Ya fad'a tare da pecking forehead nata. Excusing nasu Dr Sammy tayi sannan Al'ameen ya shirya Zeezee da kansa duk suka fice asibitin.
Achan aka yo scanning cikin Zeezee inda aka gano tana d'auke da cikin d'an d'aya which is a month old! Printing photos d'in Zeezee tasa akayi mata, har yanzu ta kasa believing komi gani take tamkar mafarki take wai ita ke d'auke da cikin Al'ameen nata yau? Wow! Yau kamata yayi ta kwana tana godewa Allah wai bama na bata daman d'aukan cikin Al'ameen ba, a'a na hanata d'aukan cikin Adeel saboda ayau tasan da ace Allah ya sanya rabo tsakaninta da Adeel da har yanzu mak'ale mata ze nayi yana using d'ansu ko 'yarsu as a reason.
Maguna kad'an aka rubuta musu na hana zazza6i da kuma amai suka dawo gida. Wani irin tattalinta Al'ameen ya shiga yi sekace gold ko zama da tashi shike tayata yi. "My Soldier Baka san too much of GATA ba kyau ba?" Tayi maganan kanta na aze akan cinyansa suna zaune a kan kujera a parlour.
"Meya faru kuma?" Tasowa tayi ta zauna, "tunda muka dawo daga asibiti mana, ko zama zanyi kace kai zaka zaunar dani."
"It's because I love you Princess, kuma fa yanzu ba ke kad'ai bace, akwai little Princess d'ina anan." Murmushin jin dad'i ta sakar mishi. "Toh idan ka saba min da gata haka kuma ranan da baka nan fah? Gashi dama ba zama kake ba nasan zuwa next week zaka ce zaka koma" ta k'are maganan with a sad face.
"Oh come on Princess, taya zan tafi in barki a wannan condition d'in, I'm staying here with you."
"Dagaske My Soldier?"
"Yes Princess zan rok'esu sumin extending stay d'ina."
"Oh! I love you so much" ta fad'a tare da hugging nasa sosai, hugging nata back shima yayi suna masu feeling love na juna. A hankali ta raba hug d'in tace, "Sweetheart I can't believe that I am actually pregnant with your baby I love you beyond expectations." Hugging nata yayi a hankali yana shafa bayanta "I love you more Princess, you are my happiness." Zatayi magana kenan wayan Al'ameen yashiga ringing a tare suka kai duban su suka ga Mama Babba ke kira, without hesitation Al'ameen ya d'aga bayan sun gaisa ta tambayi ya Zeezee ya amsa da lafiya sannan yace, "Mama I have a huge suprise for you" maganan yayi yana kallon Zeezee yana mata murmushi, itama murmushin take mai.
"Toh Only Son wani suprise kuma yau Mama ta samu?"
"Are you ready?"
"Al'ameen wai kakar ka ka miyar dani ne zaka gayan abu ma seka yita jamin rai?"
"Uhm-uhm its about Zainab."
"Meya sameta? Kace min fa k'alau take."
"Your grandchild is on board Mama, Zainab is one month pregnant." Abinda Mama ta dad'e tana jiran ji kenan rananda zataga jikanta daga only son nata, gaskiya ne mahak'urci mawadaci, ada har shaytaan raya mata yake tayi ma Al'ameen magana game da rashin haihuwar nasu jin shiru, su Aysha ma gabad'aya sun k'osa kullum cikin tambayarta suke yaushe matar Ya Al'ameen zata haihu, se gashi Allah ya kawo ranan. Tsan-tsan murna Mama tama rasa na cewa. "Al'ameen dagaske kake?" Abinda kad'ai bakinta ya iya furtawa kenan. "Dan wallahi idan na gano wasa kakemin zaka gamu dani."
"Mama zan miki k'arya ne? Zainab is preganant."
"Oh! Allah! Alhamdulillah! dan dad'i banma san ina zan sa kaina ba Al'ameen, ashe lokaci ne kawai beyi ba? Toh Allah ya bata lafiya ya inganta yakuma sauk'e ta lafiya. Kai! Naji dad'in wannan labari, finally jika na zai iso daga gun Only Son d'ina kace in soma had'a akwati na kawai."
"Aifa ki fara in 8months time jikanki ze iso." Se dariya k'asa k'asa Zeezee dake gefensa take bond na Al'ameen da mamanshi ba k'aramin burgeta yake ba itama wataran tanason taganta haka da d'anta.
"Ina Zeezeen bata please" Kallon Zeezee yayi wanda da sauri tayi mai ido nufin yace bata kusa don kunya ma takeji.
"Ermm tana bacci."
"Ayyah toh dama kana barinta tana hutawa kaji ko?"
"Mama kuma wani irin magana kike?"
"A'a gaya ma nake ai nasan ku yaran zamanin nan, idan kaga kuma bazaka iya hak'ura ba seka tattara kayakin ka kadawo Abuja don yanzu hutu Zeezee ke nema."
"Oh Allah! Help me." Kad'ai ya furta.
"Help Zeezee de, nide na gaya maka Al'ameen kana barinta tana hutawa, kuma duk abinda takeso kana yi mata kaji ko?"
"Naji Mama" ya amsa don a rabu lafiya kawai.
"Yauwa d'an albarka, bari su Salmah su dawo in sanar dasu wannan great news, ka gaishemin da Zeezee please nima zuwa anjima zan kirata."
"Toh."
"Yauwa ka kula da ita fa sosai aikin k'arfi du ba nata bane yanzu, kar a tak'ura wa jika na."
"Toh Mama am hanging up."
"Uhum sannu Al'ameen d'ina." Tana fad'in haka ta katse wayan. Nan Zeezee ta 6arke da wani mahaukacin dariya har rik'e cikinta take, wani kallo Al'ameen ya bita dashi "kuma dariyan me kike haka?"
"Babu" ta fad'a in between laughter.
"Aww don Mama tace min ina barinki kina hutawa kike min wannan dariyan?"
"No I'm sorry Sweetheart ba dariyan ka nake ba" tayi saurin fad'a sede ta kasa tsagaita dariyan har yanzu.
"Wai ni Mama me ta d'auke ni ne? Bunsuru kome da zata wani cemin in barki ki huta, ai Allah ma sheda na ne." Ya k'are maganan tamkar zeyi kuka. "Haba My Soldier" tayi maganan tare da matsowa kusa dashi tayi cupping face nasa "kai ma kasan thats not true, kai da sena neme kama kake bani hak'k'i na tukuna, kasan waye asalin bunsuru?" Kai ya kad'a yana bin bakinta da kallo.
"Adeel, Adeel is the true defination of bunsuru, Mama kawai ta fad'a maka ne incase in ba haka ba nima shedar kace you are not a sex addict Sweetheart." Ta k'are maganan tana yimai murmushi. Dad'i sosai kalamunta suka sanya sa. "Thank you Princess."
"Most welcome Sweetheart, can I kiss those sugar lips?" Tayi maganan tana bin kan lips nasa da yatsarta. Da wuri ya kad'a kai tare da sauk'e hannunta daga fuskansa, "meh kikeson Mama tace? Ina kina jin warning data kashe min anan? Ni zan koma Abj ma gobe."
"Ai wallahi k'arya ne" tayi maganan tare da had'e gira tana tura mai bakinta.
"LOL Princess wake k'aryan? Ni?"
"Ni bance kaiba amman de k'arya kace zaka koma Abj gobe."
"Zaki hanani ne?"
"Sosai wallahi, I need you to stay" tayi maganan tare da zagaye hannayenta akan wuyansa, kafin yayi wani k'wak'k'waran motsi tayi owning lips nasa suka fad'a kan gadon da baya.****
*****
Allah da iko yake, abinda ya kama daga kan Mama har izuwa kan Yasmeen all couldn't believe that Zeezee is pregnant, seda kowa ya cire rai sannan Allah yayi making wonders nasa, murna da farin ciki kam yakasa gushewa a zuk'atansu. Duk se fatan Allah ya sauk'e ta lafiya suke. Zeezee fa batada sana'ar data fi tayita aza hannunta kan flat tommy'n ta tana shafawa a kullum har yanzu gani take wane a mafarki ne wai tanada ciki, cikin ma na Ya Al'ameen nata. Even though tana shan maguna hakan besa zazza6in safe da yamman dake daminta ya dena ba sede kam ya ragu ba laifi. Tayi kusan sati uku ana abu d'aya kullum sannan a hankali ya d'auke.
****
Zeezee na zaune bisa sallaya bayan ta idda sallan isha Al'ameen kuwa ya fita masallaci ta jiyo ringing d'in wayarta. A nitse ta miqe ta d'aga cike da jin dad'i ganin Ya Ibraheem ke kira.
"Halo My Ya Ibraheem."
"Na'am Autan mu tawa ta kaina."
"Na'am, Ina yini?"
"Lafiya ya kike ya Maj-Gen?"
"Lafiya qalau ya takwarana da Aunty Fatee dakuma Maamah?"
"Kowa lafiya ashe wata taci wake ban sani ba." Shima wai ze rama abinda tayiwa Fateensa lokacinda ta keda cikin Maamah.
"Wake kuma Ya Ibraheem aina?" Tayi maganan cike da rashin fahimta.
"Eh wani yaba wata wake itako ta kar6a ba."
"Laaaaa! Ya Ibraheem!" ta fad'a cike da kunya alokacin data gano inda ya dosa. Kare fuskarta ta shiga yi as if yana gabanta.
"Eh ko ba haka bane?"
"A'a nikan bansan me kake fad'a bama."
"LOL toh Allah sauk'e ki lafiya we are all here for you okay?"
"Thank you Ya Ibraheem I love you all so much."
"Allah sa wake biyu de kikace ki sambad'o mana twins."
"Kai Ya Ibraheem wato kaima ka rama wa Aunty Fatee ko?"
"Wata taci wake de."
"Wani kuma ya bawa wata wake ba."
"Ai Fatee na is not pregnant kede kikaci wake." Mocking nata yata yi yana neman tsokanarta har seda Al'ameen ya dawo sannan sukayi sallama.
"Toh wa kuma Princess ta samu take ta wannan dariya haka?" Alameen yayi maganan yana k'arisowa kan gadon bayan ya rage kayan dake jikinsa. Itama hijabin nata ta cire sannan ta matso ta kwanta gefenshi tace, "sannu dazuwa Sweetheart."
"Thank you Princess" janta yayi ya kwantar da ita a jikinsa.
"Waya saki dariya haka?"
"LOL nida Ya Ibraheem ne fa yake neman tsokana na."
"Ayyah how is he and his family?"
"Duk suna lafiya."
"Masha Allah yau ma bazaki ci abinci ba zaki kwanta?"
"Nasha corn flakes d'azu am full just hold me inyi bacci." Hannunsa d'aya tana kwance akai d'aya kuma yana k'ark'ashin rigarta yana feeling baby'nsu. "As you wish Baby machine, sleep like a baby, I love you okay."
"I love you more My Soldier Daddy'n unborn d'ina.." Da haka sukayi falling into a beautiful sleep.
*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
3 comments:
Tanx MIEMIEBEE , Allah ya kara basira.
Thank you sis, Allah ya karo basira.
plsss sis we ar waiting
Post a Comment