Thursday, 9 February 2017

‘YAR GATA CE!

*BY MIEMIEBEE*
Page 46
 Febuary, 2017

   _I solemnly dedicate this page in honour of my sweetheart in disguise *MAMAN FADEEL* Thank you for everything Big Sis your Lilly loves you so much, Allah yabar zumunci❤❤❤❤_


     



   Tana hawaye sosai tace, "Adeel mena ta6a yimaka a rayuwa? Mesa ka tsaneni haka ka lalata min rayuwa? Don kai na rasa komi nawa har iyaye na na yafe saboda na kasance tare da kai amman kake wulak'antani haka? Wallahi a da ko had'e sama da k'asa za'ayi acemin ga abinda zakazo kamin bazan yarda ba." Sosai ta qare maganan tana kuka. Bayan ya samu yayi stopping fire'n da estinguisher yace, "toohhh!" cike da mamaki "yanzu kuma what lead to all these nonsense talks? Saboda zan miki kishiya? Wai tsaya tukun mata nawa Allah ya halitta min? One, two, three upto 4 dan nace zan k'aro d'aya bama biyu ko uku ba kike neman gayamin magana? Kuma fa auren nan da zan qara inada dalili na-"
  "Meye dalilin naka Adeel?" Ta katse sa "Mene bana maka as a wife? Ina maka girki ina k'ok'arin baka farin cikin daya kamata a kullum, baka ta6a neman had'a kwanciya dani na hanaka ba koda kuwa am not in the mood me kakeso nayi maka again? Na lasa tafin k'afanka ko me kakeso?"
   "Naji kinayin all the above stated activities amman zaki iya bani family ne? Nagaji yanzu haihuwa nakeso, kekuma bazaki iya ba your womb is damaged shikenan so kike dukan mu biyu muyi asaran auren da mukayi?"
  Hannu tasa ta share rolling tears nata, "Adeel ji yadda kake magana as if daga halitta nane mahaifata batada kyau tun farko, kaine nan fa ka lalatamin mahaifa amman ji yadda kake magana kayi adalci mana."
   "Kifa dena kawo min zancen adalci dan kema bakisan ma'anarsa ba, inhar da kinsani da bazakiyi wa Al'ameen abubuwan da kika mai ba."
  "Hakane Adeel thank you so much for teaching me such a valuable lesson in life I shall never forget it. Tabbas na tafka babban kuskure rabuwa da Ya Al'ameen masoyi na na haqiqa na aureka."
   "Sede nadaman kam dan se in a lahira keda ki sake rayuwa dashi zaman ki a gidan nan dindindin! Kafin na dawo kuma ki tattara nan ki dafa min lunch ni na gaya miki." Anan ya fice ita kuwa ta sauqa har qasa tana kuka na haqiqa bazata iya kwatanta kalan nadaman da tayi ba ashe Al'ameen shine masoyinta bata ta6a sani ba? Seda tayi ta godewa Allah sannan ta shiga had'a mai lunch.

    Tsabagen tashin hankali ko yunwan ma bataji, tana baje a kan tiles a d'akinta wayarta ya shiga ruri tana dubawa taga Mama bazata iya tuna when last Mama ta kira taba don haka ta d'aga without wasting time.
   "Assalamu Alaikum ina ini Mama?"
  "Wa'alaikis salam ya kike Zainab?"
  "Laf-" sekuma ta rushe da kuka.
  "Helo Zeezee?" Cikin sautin kuka ta amsa da "na'am."
  "Kukan me kuma?"
  "Mama fa har ansa date na bikin nasu bakiga abinda ya kawo min as kayan fad'an kishiya ba. Mama ban gaya miki bane amman yanzu bazan iya concieving ba."
  "Subhanallah! Aina aka tabbatar miki da hakan?"
  "Asibiti Mama."
  "Subhanallah! Are you sure matsalar daga kece kuwa?"
   "Daga nine Mama for six months Adeel yata d'uaramin wasu capsules ban ta6a sanin na hana d'aukan ciki bane seda ya gama rusa min mahaifa."
   "Ya Salam!! Wannan abu dame yayi kama? Amman Zeezee bakida wayo ne da zaki tashan magani har na tsawon watanni shida without asking him name ne?"
  "Mama I trusted Adeel with all that I got ban ta6a tsammanin ze cutar dani haka ba gashi yanzu har gori yakemin yana kira na da 'yar sadaqa kokuwa wacce bazata iya haihuwa ba Mama inda nasan da haka da ko Ya Wakeel kukace in aura zan aura saboda za6in iyaye is always the best kuyi haquri ku gafirceni wallahi naga gwagwarmaya a rayuwa kuma bayan family mutum baida kowa again, nayi nadaman dikkannin abubuwan dana aikata muku tun ina k'arama."
  "Ya isa Zeezee ki k'ara haquri wataran se labari no situation is permanent kinji?"
  "Naji Mama nagode ya Baba?"
  "Yana nan k'alau."
  "Toh ki gaida min shi harda Ya Omar ma, Ya Ibraheem ma don Allah kibasa haquri, kona kirasa bai d'agawa he is still mad at me."
  "Zan masa Allah rufa mana asiri ya kawo sauqi cikin lamarinki."
  "Ameen Mama nagode sosai."
  "Yauwa se anjima" anan ta katse wayar. Tunanin ya zatayi ta jawo hankalin Baba kan Zeezee take amman takasa saboda anytime ta taso mai da maganan Zeezee ko sauraronta baiyi.

   *^*^*
   Haka fa preparation na biki ya cigaba da gudana, Zeezee de aikin kullum itace ta kuka gashi sede zance be had'ata da Adeel ba seya zageta koya gaya mata baqar magana had'e da goranta mata ba. In banda dad'a rama ba abinda take yi. Ahaka har watan bikin Adeel da Ruky Mama ya iso, cikin ikon Allah aka soma biki aka gama lafiya wanda cikin duk events d'in ba wanda Zeezee taje kullum tana maqale a d'aki tana kuka.
   A daren randa aka d'aura musu aure aka kawo amarya gidanta. Convoy ne sosai motoci se shiga ciki suke har ya zammana saura ba inda zasu samu shiga seda suka faka a waje. Zeezee na leqe ta window tana kuka se tuna time na bikinta da Al'ameen take itama yadda convoy ya had'u mata amman nata da Adeel wane akuya aka d'auko daga ita se shi aiko anan ma ya isa ya mata gori "why didn't I  thought of this before?" Ta tambayi kanta. Daren ranan gabad'aya ta kasa samun sukuni ita rabonta datasa Adeel a ido ma tun kamin a soma wedding events nasun, any time tunanin yanzu haka Adeel na tare da wata suna shan soyayyansu yayi hitting nata se ta rushe da kuka haka seda garin Allah ya soma wayewa ta samu tayi bacci.

    Some hours afterwards... Site na Ruky Mama @ 11:46am.
   Kwance take bisa jikin Adeel hannunta d'aya akan chest nasa tana wasa da d'ad'd'aikun gashin k'irjinsa "Baby am hungry" ta fad'a a shagwabance. Ruky Mama ta kasance 'yar duma-duma za a iya cewa tana da k'iba dake a k'oshe take b'ul-b'ul tana da kyau dai-dai gwargwado uma tsayayyiyar mace ce.
   "Toh ki tashi kiyi warming kanki kink'i." Yace da ita yana shafa fuskarta.
  "Bazan iya ba the pain is too much."
  "Yi haqur kinji? Nasanki fa da juriya."
  "Toh Baby breakfast fah? Will I be the one to cook?"
  "Haba! Meye amfanin Zeezee a gidan nan da har zakiyi girki?"
  "Are you sure Baby? Zata fyarda ta girka mana?"
 
"Yes Sweetheart karki damu." Kissing nasa tayi passionately "I love you."
   "I love you more."
  "Nifa ban yarda da wannan I love you d'in ba nasan kaje ka sameta abinda zakana gaya mata kenan itama."
  "Inji wa? Rabona dana sata a ido I can't even remember seriously wancan batada wani amfani I use her for sex and cooking kuma kinga gaki yanzu kin fita zuma da dad'i ba abinda ze sake shiga tsakani na da ita."
  "Are you sure Baby?"
  "Dont you trust me?"
  "I do Love."
  "Good tashi toh muje kiyi warming kanki." A hankali cike da so da k'auna ya samu tayi warming kanta sannan sukayi wankan sunnah suka fito. Nan ma da kansa ya shafa mata mai se wani binta yake sekace 'yar gwal sun gama shiri fes suka koma suka kwanta tana manne a jikinsa. Hannu ya miqa ya d'au Wayansa tare da kiran Zeezee sede har 2 missed calls bata d'aga ba se ana uku.
   "Yauwa Ke Arrange breakfast for us ki kawo immediately kinji?" Lallai ma ta furta a ranta sannan ta kashe wayan. "Hello? Hello? This rascal wants to die" ya furta angrily.
   "Babe ka barta kawai ka siyo mana."
  "No way meye amfaninta? Excuse me kinji I'll be right back."
  "Don't take long okay?"
  "Okay Sweetie" nan yayi pecking lips nata sannan ya fice. Chan a d'akinta yaje ya tarar da ita tana aikin kuka bubbuga k'ofan yayi seda ta juyo tana kallonsa da swollen eyes nata. "Hanging call zakiyi a kaina?" kaman a kyaftawan ido ya nufi gadon tare da fincikota daga kai cike da mugunta. "Magana nake miki!" Ya fad'a a tsawace "ko sekinji sauqan mari zaki ansani?" Kai ta kad'a abin tausayi tana me cigaba da kukan.
  "Zaki had'a breakfast d'in kokuwa sekinji na jaki?"
   "Zan had'a muku" ta furta tana kuka sosai.
  "Maza wuce ina kallonki" anan ya saketa and ba gardama ta nufi kitchen ta fere doyan ta tafasa sannan ta musu doya me k'wai a jiki sannan fried egg separate a gefe. Cikin food warmers  nata tasa takai dining table ta ajiye duk anan Adeel na zaune a parlour yana jiranta.
   "Ke anan kuma zaki barsu? Cemiki akayi Ruky zatazo nan?"
  "Aina kakeson na ajiye?" ta tambaya a hankali abin tausayi.
  "Site nata zaki kai mata."
  "Adeel nida ita waye babba? Waye uwar gida?"
  "Wannan kuma keya dama inma kece kakar gidan can ta matse miki nide ki kai wa matata breakfast natan."
   "Wallahi Allah bazan kai ba kai bakada imani ne? In zakayi adalci nida ita waya kamata ya kawo ma wani abinci?-"
  "Ke ya kamata ki kai mata" ya katseta "and sai kin kai d'in, ce miki akayi Ruky sa'ar kice?"
   "Bazan kai ba abun kuma ai ya koma iskanci." Belt nasa taga ya zare yana nannad'awa a hannu "zaki d'auka kikai kokuwa?" Kallonsa ta tsaya yi totally short of words dagaske yanzu dukanta yakeson yi? "Kina kallo na ajinki bazan iya baki kashi bane anan in kuma saki ki kai matan?"
   "Zaka iya tunda kai mahaukaci ne zan kai mata amman kasani wallahi kaima Allah baze barka ba Adeel idan baka gani akanka ba toh kajira akan 'ya'yanka."
   "Aikin banza d'aga ki kai mata" one more look tamasa sannan ta kad'a kai ta jera flasks d'in kan tray ta shiga tafiya inda yake binta a baya. Zaune kan kujera a parlour suka tarar da Ruky Mama dagangan bayan fitan Adeel ta canza outfit nata tasa bomb short da vest da rabin nononta a waje suke. Koda taga Zeezee batai niyan karb'anta ba illama miqewa datayi tana twisting ass nata gasu sunyi ukun na Zeezee ta nufi inda Adeel ke tsaye tare da pecking nasa a lips "Babe it took you so long."
   "Am sorry kinji? Lets eat nasan you are starving." Anan ne Zeezee ke ajiye musu abincin kan dining seda Ruky ta bari Zeezee ta juyo sannan ta sake kaiwa Adeel wani hot kiss d'in me tsayi fiye dana d'azu. Kawar da kai Zeezee tayi sannan tahau tafiya dan basu space takai da fita Adeel ya rik'o hannunta.
   "Baki iya gaisuwa bane?" Kallonsa ta tsaya yi full of suprise, murd'a mata hannu cike da mugunta yayi ganin she's not ready to talk, hawayen datake ta neman had'iyewa taji sun soma tsiyaya daga kumburarrun idanunta  "ina kwana?" Ta gaishe da Ruky Mama tare da miyar da kallonta kan hannun nata da Adeel yak'i sakewa har yanzu. Seda Ruky ta gama k'are mata kallo sannan tana sake lumewa jikin Adeel ta amsa da "lafiya sannu da aiki mungode sauran kuma lunch ko Babe?"
  "Yyess" ya amsa jiki na rawa "me kikeso for lunch?"
  "Fried rice and with chicken of course."
  "So kinji ko?" Ya maido da kallonsa kan Zeezee ganin batada niyyan amsawa ya sake murd'a hannun nata. Tana hawaye sosai tace "naji" se anan ya sakota wajen ta riqe da other hand nata tana kare mai kallo yadda yayi pink shar sannan ta fice tana kuka me tsuma zuciya.

   Ruky kam a cinyan Adeel ta zauna gabad'aya ta dak'ula mai lisafi da wannan annen shirin dake jikinta, yaci ya bata ahaka har suka samu suka gama karyawan a yayinda Zeezee ke chan a kitchen nata tana gyaran kaji tana duban sauce na fried rice, tana aikin tana kuka har ta samu ta gama ta kai musu. Batayi sallama ba ta fad'a cikin parlourn nasu ko d'aga kai ta kallesu batayi ba se k'aran kisses da suke exchanging kawai takeji, da wuri-wuri ta ajiye musu ta fito ta nufi site nata inda ta cigaba da kukan daga inda ta tsaya.

   Da irin wannan rayuwa da take leaving tasan na lahira ma yafita jin dad'i. If only she can talk back to Adeel tace mai bazata sake yimai girki ba da tayi amman sanin mahaukaci ne shi yana iya mata duka ya illatar da ita ya cuceta na har abada yasa kawai bata biye masa takeyi mai abinda yakeso tunda no situation is permanent she believe one day she'll be free from misfortunes na Adeel.

   Haka Adeel ya cigaba da wulak'anta Zeezee a gidan. Har Ruky ta samu sati bata ta6a hura wuta ba a gidan as girkin safe, rana da dare duk Zeezee keyi tana kai musu nan ma duk shiganta seta tarar da baqin ciki don daga ta kamasu suna kissing juna se Ruky na zaune a cinyansa suna romancing juna. Cikin satin nan Adeel be ta6a ya kwana a site na Zeezee ba in short bayida ma niyyan dawo mata kullum yana maqale da Ruky suna baza love.
    Yau Lahadi exactly one week one day da bikinsu Adeel kenan, kaman kullum da safe bayan shida Ruky'nsa sun yi wanka sun shirya tsaf ya tambayeta me takeson karyawa dashi bayan ta fad'i mai ya d'au waya ya kira Zeezee seda ya kusa tsinkewa ta d'aga tare da yin shiru.
   "Kin d'auka kinyi shiru k'ona min airtime kikesonyi kome? Mschww! Ni tashi ki had'a mana breakfast indomie Ruky ta keso ni kuma chips."
   "Haba Adeel in anyi na marmari da amarci kuma ai yanzu is high time Ruky'n ta soma girki itama kayi adalci mana."
  "Bazan yiba ko kin manta matsayinki ne a gidan nan? Cooku kin gane? Zaki girkan ne ko bazaki girka ba?"
   "Gaskiya bazan girka ba ai ba baiwar kuce niba" tana kaiwa nan ta katse wayar. "Babe ya kukayi da ita?" Ruky dake kwance jikin Adeel tayi maganan.
    "Excuse me Bebe yarinyan nan wants to die ina zuwa."
   "Wai bazata girka ba?"
  "Barta" ya fad'a fusace.
  "Calm down kaji? Ka barta d'in kawai zan girka mana."
   "No way ita zata girka ina zuwa" yana kaiwa nan ya fice wani maqirin murmushi ta saki "a sannu a sannu zan kashe auren naku" tace a ranta tana murmusawa.

   Site na Zeezee ya nufa direct izuwa d'akinta. Banging k'ofar yayi wane ze 6alla seda ta firgita "kikace meh?" Yayi maganan yana nannad'e belt dake hannunsa.
   "Bazan girka ba na muku na sati na gaji." Dosan gabanta yayi "repeat it again! Har in saki aiki kice bazakiyi ba?" Anan ya d'aga belt d'in sama ready to beat her up, "repeat yourself."
   "Zane ni zakayi yanzu Adeel?"
  "Ba zana kad'ai ba Zeezee faffasa miki wannan fitsararren bakin naki zanyi zaki girka kokuwa a'a?"
   "Bazan girka ba-" kafin ta hankara tajiyo sauqan belt zuwaat! A bayanta nishi taja dan zafin da taji, tare da matse idanunta take hawaye suka soma tsiyaya "zaki tashi ne ko sena k'ara miki?" Tana kuka na haqiqa tace;
   "Adeel ni ka d'aga belt ka zana yau akan wata?"
   "An zane kin, kuma inhar baki miqe ba zan qara miki d'aya."
   "Adeel bana blaming naka akan kalan abubuwan da kake min saboda nasan gir6e abinda na shuqa nake, alhaqin iyaye na dakuma na masoyina Ya Al'ameen ne ke bina amman kasani muddin nagama gir6ewa zaka nemen kamin wannan wulaqancin ka rasani kasani no situation is permanent. Kana ganin kayi sabuwar mata kake neman maida ni kashi a bola wallahi Allah yafika kuma shi ba azzalimin bawansa bane, girki kakeso zanyi muku tunda nida kaina na jefa kaina cikin wannan situation amman inhar ka sake d'aga abu ka ta6a min lafiyan jiki kasani bazan ta6a yafe maka ba wannan ma  ban yafe ba."
   "Ki fad'i koma me girki ne in bakiyi ba jikinki ze gaya miki Ruky indomie nikuwa chips." Hawayenta ta share sannan ta miqe a nitse tabar mai d'akin tana yi musu girkin tana kuka ahaka har ta samu ta gama ta kai musu.
  Bayan sun gama ci Ruky ta langwab'e fuska "Baby" ta kirasa wane zatayi kuka.
   "Na'am Babe."
   "Baby wanke-wanken nan yau nakega sede su kwana na samu cut a hannu na d'azu" ta nuna mai inda ta manna bandage dagangan.
   "Awch! Sorry Babe."
   "Its okay ko Zeezee zata iya wanke min na yau?"
  "Why not barin kirata tazo ta tattara." Nan ya d'au waya ya kira Zeezee alokacin tana miqe kan gado tana kuka tajiyo ringing na wayarta tana dubawa taga shine, bata 6ata lokaci ba ta d'aga  "kizo da wuri" yace da ita tare da katsewa. Without wasting too much time ta wanke face nata sannan taje ta ga kiran nasa. Daga bakin k'ofa ta tsaya "ki k'araso ki tattara plates d'in ki wanke Ruky ta yanke a hannu."
   "Aunty Zeezee se hak'uri wallahi yankewa nayi jiya garin yankan albasa."
  "Ma hak'urin me kike bata?" cewan Adeel "ba aikinta bane zo ki tattara." Kallonsu both tayi sannan ta kad'a kai ta qarasa ta tattara plates d'in ta fita dasu, nan da nan ta wanke ta shanya su. Chan da La'asr Adeel da Ruky suka shirya tsaf zasu unguwa har sun fito se Ruky cike da qissa da dabara kamar yadda ta saba tace, "Baby bazamu sanar da Zeezee zamu fita ba? Karta leqa mu taji shiru hakan ba dad'i."
   "Mesa kike damuwa da ita ne wai? Lets go da Allah."
  "Please for me lets tell her where we are going."
  "For you only muje" dad'i sosai taji nan suka nufi site na Zeezee alokacin tana zaune kan dining ga abinci a gabanta amman takasa ci gabad'aya ta fad'a kogin tunani har suka shigo bata sani ba "uhm-uhm" Adeel yayi clearing throat nasa se anan ta maido da kallonta garesu. Ganin haka Ruky tayi saurin kama hannun Adeel ta had'a danata "sannu Zeezee dama zamu fita ne Baby ze kaini shopping nan Jifatu nace bari mu sanar dake karki jimu shiru." Data gama sauraronta kawai seta kad'a kai ta d'au plate nata ta miqe "Allah kare" tace dasu ba tare data kallesu ba ta fice zuwa d'akinta. Achan ta bud'e sabon dandalin kukan, bazata iya tuna when last Adeel ya kaita shopping ba Allah shi kyauta. Ruky kuwa shopping sosai Adeel yayi mata kaman ba gobe bayan sun dawo gida ta babbaje kayakin kan gado turare d'aya ta d'ago ta miqa mai  "gashi wannan ka kai wa Zeezee kaji Baby."
   "Naki ne ina ko bakiya so ne?"
  "Inaso ai biyu na siya ka kai mata wannan kaji?"
   "Mesa? Ki manta da ita mana."
   "Please Babe matarka cefa itama yakamata yau kaje ka kwana mata ma ai."
   "Kin gaji dani ne haka?"
  "Haba wane ni nagaji da kai ai abin marmari ne kai kawai inason wa 'yar uwata abinda nakeso wa kaina ne kaje kaima ka bata haqqinta I know she must be missing a lion as you!" Dad'i sosai yaji yadda takirasa da lion "are you sure Babe? Nifa nace bazan sake kwana mata ba bana buk'atar ta again."
   "Yi haquri de Baby na ita tanayi nasani."
  "Naji amman se later during the night toh."
  "Yauwa kaga kafin nan nima seka bani abinda ze d'ibe min kewanka."
   "Come here" ya buk'aceta jikinsa taje ta fad'a nan suka fad'a wani duniyan na daban***

   9pm Ruky tasa Adeel gaba sam seya kwana da Zeezee yau, har doorstep na Zeezee tayi mai rakiya sannan takoma site nata, seda yaga tayi shutting door nata yashiga ciki direct d'akinsa ya nufa ya watsa ruwa sannan ya fito ya nufi nata d'akin. Miqe kan gado ya tarar da ita amman ba bacci take ba.
   "Ke tashi ki dafa min indomie" shiru tayi kaman bata jisa ba "ko bakiji ba?" ya tambaya a fusace.
  "Naji" ta amsa a hankali sannan ta miqen ta nufi kitchen nan da nan ta had'a mishi takai masa dining inda yake zaune ta ajiye zata juya kenan ya riqo hannunta. "Zauna kema" ya umarce ta, batayi musu ba ta zauna be sake ceda ita komi ba as se cin abincinsa yake seda ya gama yayi nak sannan ya miqe "tashi muje mu kwanta."
  "Kaje bana jin bacci" ta amsa a hankali.
  "Muje nace karki 6atan rai" bata mai musu ba ta bisa izuwa d'akin. Hijabin jikinta ya rage mata duk anan bata ce dashi k'ala ba, daga nan ya kashe musu wutan d'akin kamar wacce batada feelings kuma baibiya haka tayi mai a daren ranan duk abinda yace tayi yitake ba gardama, a haka har ya samu biyan buk'atansa da ita, sede shi kanshi beji dad'in abinda ta riga mai ba sekace wacce batada feelings? Hijabinta taja ta 6urma sannan ta miqe ta dim light ya ga miqewanta "ina zakije?" Ya tambayeta.
   "D'akina I guess amfani na ya qare anan" bece mata komi ba tafice ta ja mai k'ofa. Tana isa d'akinta ta jefa kanta bisa gado ta shiga aikin kuka.





*MIEMIEBEE.      Team #YGC!*
  Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄

17 comments:

Unknown said...

hahaha zeezee kenan ki koma ki nemi gafarar Baba duk da shima da laifin sa

Unknown said...

Wayyo zee zee,

Unknown said...

Sister mungode, Allah ya kara basira

Sabiyyah Affandi 🌹 said...

Ahhh lallai na auna wayyon ZeeZee na gani, ashe ba wayyo bane sakarci da sakaci da yawa ne da ita!...sorry ma co-readers, sorry Miemie but this is too way of takaici, haba dan Allah!
Can't she take any action @all as, kamar yanda shi Adeel din yayi mata da shigo shigo ba zurfi, ya cuta da ita...itama babu yanda zata iya ne?! Oh pls, to hell with fadin"no condition is permanent" already! Till when does she know this inhuman treatment from this hellish guy, gonna end! End her suffering already Miemie...honestly what ZeeZee's going through is hurting ma emotions! Though it's all a drama. Good Job�� ma Darlington��...Allah shi kara miki hazanci da dabara kici mana gaba.

Unknown said...

Sabiyyah Affandi haka ne Zeezee na shan wahala sosai har na fara tausaya mata....
Yau kuma daya muka samu, na kagu inji karshen littafin nan wallahi

Sabiyyah Affandi 🌹 said...

Yeah Bro me2...inason ganin yanda komai zai kasance in the end...but sai gani ma nake yi kamar yanzu muke karanta page1 of "Y'ar Gata"...seriously I'm running out of patience for poor ZeeZee!

Sabiyyah Affandi 🌹 said...

Son samu ne, ya zamanto a hannun Ya Al'Ameen wannan mediocre'n(Adeel), zai sha kashi da kyau! Ya dau wa matarsa(ZeeZee) fansa!...ko ya kuka ce luvly viewers? ������

Unknown said...

Sabiyyah Affandi maganar ki dutse.... bari dai mu gani ko tusa zata kurewa...........

Unknown said...

😭😭😭😭😭😭😭😭
Wayyo zeezee

Unknown said...

Gaskiya nima naso ace a hannun ya alameen zai sha kashi ungreatful human being.

Unknown said...

Gaskiya nima naso ace a hannun ya alameen zai sha kashi ungreatful human being.

Unknown said...

Ayyah zeezee

Unknown said...

Gaskiya ya kamata zeezee ace tafara rama wulakanci da Adeel kamata, gashi yanxuma harda shegiya Ruky ta shigo layi

Sabiyyah Affandi 🌹 said...

Ai kedai kyale shegiya barauniya...ai itama da nata Aim ta shigo gidan(tsiyata Adeel to nothing but rag),kwashe masa property zata yi kakaf! And ZeeZee, will be go back to her Mag-Gen,enjoying life like ever before...woooow! Abin da Adeel bai sani ba kenan(cewa ZeeZee da Mag-Gen) din ta suna mugun tare. Like wujiga wujiga. Lol.

Miemie don Allah ki ci mana gaba. Muna mugun tare da ke.

Unknown said...

its a pity on zeezee! Maganinta kenan.

Unknown said...

Wayooo Allah d pity for zeezee Has blinded me towards her mistakes..... I can't wat for ruky mama taci kaniya Adeel lyk die no pity kawai nd oir zeezee bck with maj-gen wif new steps of luv... Anyway i trust miemie u no dy carry last.... More percentage to ur ba3 luv.....LETS KIP Digging dear

Unknown said...

Jazakallahu Khairan