Tuesday, 7 February 2017

‘YAR GATA CE!

  *BY MIEMIEE*
PAGE 45
*Febuary, 2017*



Kiyi hak'uri Babe it shall come to pass one day, kiyi abinda na fad'a mikin muji me mara imanin zaice."
   "I'll try" tayi maganan tana and shassheqa.
  "Have faith nifa ba haka na sanki ba Babe keda kike abinda kika ga dama mesa kike tsoron Adeel haka?"
  "Kinsan mahaukaci ne shi ze iya illatani."
   "In shaa Allh bazeyi ba its hight time kiyi fighting wa kanki."
  "Is okay Babe I'll try my best nagode sosai."
  "Don't mention senaji daga gareki" anan ta katse. Tunanin ya zata (Zeezee) gudanar da wannan aiki take batta tsammanin zata iya abinda Lubiee ta sata dalili kuwa itama bata sani ba all she is adamant of is that she can't talk back to Adeel yadda ya kamata, agun ta ajiye wa Lubiee maganarta.
   Har yamma Adeel be dawo ba da zaman gidan ya isa Zeezee ta d'au wayarta tasa lamban Mama sannan ta kirata.
   "Assalamu Alaikum" fad'in Mama a lokacin da ta d'aga wayar.
   "Wa alaikumus salam" Zeezee ta amsa cikin sanyin murya, "ina ini Mama?"
   "Lafiya Zeezee ce?"
  "Eh nice Mama."
  "Toh wannan layi fah?"
  "Lubiee ne taban shi Adeel ya fasa waya na yakuma karya sim d'in."
  "Subhanallahi shiya sai miki ne?"
  "A'a fa tun wanda Ya Al'ameen ya saya min ne."
  "Ikon Allah wai dama yaron nan ba sonki yake ba Zeezee kika dage seshi?"
  "Mama ni kaina bansan meke damun Adeel ba gabad'aya ya canza."
  "Toh ya kuke ciki yanzu?"
   "Mama wai aure ze sake" sekuma tasa kuka.
  "Aure de? Da aurenku ya shekara ne?"
  "Kwata-kwata 8 months nefa."
  "Toh Allah kyauta ya rufa asiri"
  "Ameen Mama ya Baba don Allah ki bashi haquri on my behalf."
   "Am trying my best Zainab."
  "Toh Mama nagode, I love you so much."
   "Ba komai ki qara hak'uri kinji? Akwai Allah."
  "In shaa Allah nagode."
  "Yauwa se anjima."
  "Aha ki gaida Ya Omar."
  "Zeji" sannan tayi hanging. Bada dad'ewa ba Baba ya dawo daga d'an strolling daya fita "sannu da dawowa Alhj" tayi maganan tana zaro mai ruwa daga fridge.
  "Yauwa Hafsah ta sannu." Sede kallo d'aya ya mata ya gano abu na damunta.
  "Lafiya dai ko?" Ya tambaya.
  "A'a wallahi" ta fad'a sounding honest.
  "Toh ina jinki."
  "Alhj yanzun nan Zeezee ta kirani wallahi tana cikin damuwa sosai wai ma mijinta aure ze qara yi."
   "Nawa ze auro mata? Uku ko biyu?"
  "Haba de Alhj wai baka tausayawa 'yar nan?"
  "Ba ita tace tana sonsa ba? Har fiye da yadda takeson iyayenta ai kad'an tagani wallahi yamin dai-dai ya qaro mata uku ma yaga dama daga k'arshe ya korota."
   "Ahhh ahh " Mama ta saki baki tana kallonsa "toh Allah shi  kyauta."
  "Ameen" anan ya nufi bayi don watsa ruwa.

 ****
   Life moved on, abubuwa sun kasa daidaita tsakanin Zeezee da Adeel shi ya dage sam seta basa haquri inhar tanason su koma shiri itako she sees no reason why da zesa ta basa hak'uri after all she isn't the one at fault. Gini ake tayi mansion daya ninka wanda Zeezee ke ciki girma sai shi sure zeyi, tun abin na damunta kullum setayi kuka har ta soma rage bin abin a zuciya. Gashi anytime tace zatayi confronting nasa bata iyawa gabad'aya setayi losing courage haka shiko Adeel yake taking advantage nata kullum azaban yau daban na gobe daman.
   Yau Zeezee na zaune a d'akinta tana had'a kayan cikin wardrobe nata Adeel ya bankad'o k'ofan d'akin kaman yadda ya saba "Ke tashi ki had'a rice and stew me kyau yau Ruky zata dawo daga tafiya and she'll be visiting zatazo taga gidaanta." Yau kam bata tsammanin zata iya barinsa, "ai ba rainin hankalin daya kai wannan" ta fad'a finally cike da tsiwa. "Ina ruwana da banzar budurwarka ko karuwarka da zatazo? Wallahi kaji na rantse bazan girka ma wata shegiya abinci ba ko kaje ka siyo muku kokuwa ta zauna da yunwa" ita kanta bata tsamman zata iya gaya mai magana haka ba. Tsayuwa yayi yana kallonta lallai ma ta raina shi, raini na sosai.
   "Come again me kikace?"
  "Ai ka jini ba kurma bane kai bazan girka ma wata shegiya abinci ba."
   "Haka kikace? Zaki sha mamaki."
  "Ina qarshen mamakin da zaka bani shine ka d'auko kwarto yayi zina dani? Toh kasani Allah ya fika Adeel kuma dad'in abin bana sallah amman inhar jahilcinka yakai level da zaka bari a kusanceni ina al'ada get on with it."
   "Sa'anki d'aya kuma, ki tashi kije kiyi abinda na saki kona illata ki."
  "Bazan yiba ka illatanin kamin abinda Allah bemin ba, aini da illatanin ma zakayi daya fiyemin yadda hukuma zata tsaya min akai se an raba auren namu tunda cutar dani kake." Ganin tanada gaskiya yabar mata d'akin totally rai a daqule lallai kuwa Zeezee zatayi regretting gaya mai magana da tayi. Koda ya d'auko Ruky Mama daga airport restor ya wuce da ita direct inda suka ci abinci sannan suka biya ta gida don taga gininta, duk kalan qarya irin nata bata raina gidan ba saboda yadda ya had'u. Kasancewar itama 'yar duniyar kanta ne da Adeel bece mata ta shiga ciki su gaisa sa Zeezee ba se itama bata tambaya ba. Ta gama ganin gini Adeel yayi dropping nata a gida.
   Yawonsa ya wuce daga nan se Maghrib ya dawo gida inda yasa Zeezee frying masa doya tagama ta had'a mai kan dining. Da singlet da nickers yafito ya nufi dining se abinda ya jima be gani ba yake gani yau, Zeezee tsaye kan dining d'in tayi akinbo batare da yace da ita k'ala ba ya ja kujera ya zauna ya soma serving kansa har anan bata motsa ba bata kuma yi magana ba.
   "Ke hada haka? Taya zaki tsaya min aka while inason cin abinci?"
   "Makaranta nakeson na koma nagaji da zaman gida haka ba abinda nake tsinana wa kaina ni ba 'ya'ya ba bakuma karatu ba baze yuwu ba."
   "LOL da ai fitowa fili kikayi kikace za a auro miki masters holder kema kinason ki rufe k'ofan gori zaki fara degree naki, toh kisani ba a gidana ba tunda bakiyi karatu gidan ubanki ba bazakiyi a nawa ba kin gane?"
   "Seka hanani yi muga thank god inada kud'in da zanyi registration da komai, approve it or nah am starting school."
   "Please Zeezee koda wasa ki gwada taka k'afafunki waje ina raye kiga aiki da cikawa useless kawai."
  "Kai kuma macuci azzalimi ba" ba tare da ta tsaya jin mezece ba tayi ciki. Ita kanta tasan barazana duka kawai take amman bawai zata iya aikatawa bane tsan-tsan tsoronsa da take. Tun daren ranan bata sake sa Adeel a ido ba se after 3 days daman haka ne anytime Ruky Mama ke gari bayi kwana a gida. A kwana na ukun ne ya samu ya zo kusan da yamma haka. Alokacin nema Zeezee ke sauk'e indomie'n ta daga wuta tana rufo k'ofan kitchen tagansa tsaye a tsakar parlour. Gani tayi ya soma dosan inda take nanfa guiwoyinta suka shiga shaking amman don ta nuna masa bata tsoronsa again ta dake ahaka har ya isketa, jiran yauma yaja hannunta yaje ya biya bukatansa kamar yadda ya saba take setaji ya wabje plate na hannun nata.
  "Ya da haka Adeel? Ka miqa min abinci na."
  "Nawa ko naki ke kike siya?"
  "It doesn't matter as long as nina girka."
  "Seki amsa muga aikin banza kawai kije ki dafa wani am starving."
  "Ita karuwarkan bata iya girki bane data barka ka dawo haka bayan kwana ukun dakayi mata?" Ba tare da yace da ita komi ba ya ja kujera ya zauna ya shiga cin indomien. Yana gamawa ya nufi d'akinsa se 8:30pm ya fito alokacin Zeezee na zaune a parlour tana gyaran farce. Ganinsa tayi tsaf ya shirya da alama fita zeyi again. Da wuri ta ajiye nail cutter'n dake hannunta ta miqe "ina kuma zakaje?"
   "Ke waye da zaki tambayan inda zani? Karfa kiga ina barinki kwana biyu kice zaki raina ni."
  "Ai repect is reciprocal duk wanda be bawa kansa ba baza a basa ba, harga Allah nagaji ba yadda za ayi ace kullum baka yini baka kwana a gida nikuma ka barni da gadi."
  "Ya kika iya toh?"
  "Niko nake da yadda zan yi."
  "Go ahead then matsa min."
  "Ina nan wallahi bazaka gun wancan karuwar ba."
  "Kada ki sake kwatanta Ruky da karuwa, ke ba'a ce dake karuwa ba se ita? Inba karuwa ba wace zata na fita midnight party?"
  "Dole kamin gori ai yau, amman bayan parties da kake sani zuwan dole ka gayamin wani party ne kuma ka sake jin naje."
    "Ki dena cewa na saki cause ke kikayi niyyan zuwa saboda dama da akwai ra'ayin iskancin a zuciyanki, matsa min banida lokacin ki."
   "Wallahi ba inda zaka je ina nan, bazaka gun karuwar can ba."
   "Karki sake ce mata karuwa."
   "Karuwa na sake fad'a inba karuwa ba wace zata riqe mijin wata harna kwana uk-" bata idda maganan ba taji sauqan mari fas a kumatun ta. Wajen ta riqe da mamaki tare da d'ago kai tana kallonsa "mari?" Ta tambaya still not believing, hannunta maqale da gun. "mari? Adeel ni ka d'aga hannu ka mara yau akan karuwarka? Ni Adeel?"
   "Kad'an daga cikin abinda zan iya miki kenan muddin kika sake zagin Ruky."
   "Lallai Adeel kacika butulu yanzu akan wata banza zaka d'aga hannu ka mareni a fuska ta?"
   "Matsa min" ganin bata da niyyan matsa mai ya tunkud'eta a zuciye yayi ficewarsa. Sauqa tayi har qasa a gun a yayinda hawaye ke bin k'uncinta, kuka take na sosai Wani irin rayuwa ta jefa kanta? Koda wasa bata tab'a kawo wa a ranta Adeel ze iya d'aga hannu ya mareta ba, gaskiya ne na miji ba d'an goyo bane. Kodan yadda ta fifita sa akan iyayenta be kamata yayi mata haka ba, amman komi ya manta yana mata wulak'anci harda mari yanzu.
   Da k'yar ta iya ta tattara kanta ta nufi d'aki, sede har anan takasa dena kukan saboda yadda yakeyi mata zafi, se chan ta share hawayenta ta zauna gaban mirror tana kallon kanta, "wallahi bazaka cigaba da cutar dani haka ba, abin ya isa haka." Tayi assuring kanta.

   A waje ranan ma Adeel ya kwana se a washegari ya dawo ya nufi d'akinsa dan watsa ruwa anan Zeezee tayi sid'ak-sid'ak ta shiga d'akin inda yake ajiye keys nasa ta nufa ta zaro na kwad'on dayake rufe gate dashi tasa a bra nata sannan ta mai replacing da fake one. Da wuri ta fice, yana gama shirinsa ya fito dining yaci lunch zuwa La'asr ya shirya ya sake fita, ya kaiga bud'e kwad'on don datsewa yanemi key'n da ze shiga ya rasa ganin zai 6ata mai lokaci kawai ya fice a tunaninsa ai tasan kullum yana rufe gate baza tayi tunanin fita ba.
   Itako a ciki tanajin ficewansa ta shirya tsaf zata unguwa itama, makullin motarta ta d'auka tabi sahunsa. Gidajen friends nata data jima bata jeba ta jeta yau, yawo kam seda ya isheta ranan. Ba ita ta tashi dawowa ba se 7:40pm nan ma don bata iya tuk'in dare bane tana tsoro.

  Adeel kuwa yana fita bada jimawa ba ya dawo ranan anan yayita kiran Zeezee amman bata nan, zaune yake a yanzu haka a parlour yana jiran shigowarta. Ana cikin haka Zeezee ta shigo bayan ta miyar da k'ofa ta juyo seda suka had'a ido hud'u sannan ta kawar da kanta tahau tafiya. "Ke!" Ya kirata a tsawace sede sam yi tayi kaman bada ita yake ba hakan ba qaramin 6ata mai rai yayi ba "wallahi kika barni na sake nanata kaina zaki sha mamaki."
  "Ai ba da ke aka yanka min ragon suna ba if you wanna talk to me address me with my name."
   "Wow!" Ya tafe hannunsa, "I'm starting to like this wato finally zaki soma retaliating ko? Toh bani key'n da kika satan 6arauniya kawai."
   "Kar ka sake cemin 6arauniya."
  "B'arauniya na sake fad'a."
  "Kaima 6arawo."
  "Kikace meh?"
  "Nace kaima 6arawo kamin abinda Allah bemin ba." Ransa ne ya mugun 6aci, kaman a kyaftawan ido ya doso gabanta tare da fincikota da hannu yana me murd'awa cike da mugunt, duk zafi da azaban da takeji besa ta nuna masa ba don kansa ya gaji ya saketa. "Wallahi kar kiga ina barin ki kizata tsoron ki nake, kika cigaba da hakan belt zan d'au in baki kashi."
  "Yanzun me kake jira don ka dakeni sai meh? I am not the first woman to be beaten up by her husband neither will I be the last, get on ka daken d'in amman kasani kaima wataran wani ze daki 'yarka kaima."
   "Useless kawai" kad'ai yace da ita sannan yabi gefenta ya wuce har ya kaiga shiga d'akinsa ya dakata, "kuma maza ki wuce kitchen na siyo kaza pepper soup nakeso." Yi tayi kaman bata jisa ba ta shiga tafiya "dake fa nake!" Ya fad'a a tsawace.
  "Senace maka eh naji ne tukun zaka san na jikan? Mschww!" tana kaiwa nan ta nufi d'akinta bayan ta idar da Sallah ta canza kaya ta fito ta sarrafa masa kazan tana gamawa ta d'ibi nata, cinya d'aya da wasu parts masu kyau k'waya biyu again tasa, ragowan tasa a flask takai masa. Kafin yafito harta cinye nata ta kora da ruwa.

   Fitowan Adeel ya nufi dining cike da zumud'insa ya bud'e flask d'in in search  of cinyoyinsa biyu don yaci, sede ya gama dubansa amman d'aya kad'ai yake gani haka daya gwada neman other parts d'inma duk d'ai-d'ai yake gani. Danqaree!
  "Ke Zeezee! Zeezee! Ina kike?" Seda ya kirata kusan sau biyar sannan ta fito batare da ta amsa ba.
   "Ina kika kai min sauran parts d'in?"
  "Cikina."
  "Cikinki? Naki ne da zaki cinye? Kokuwa ni na baki?"
  "Ko d'aya amman naga hak'k'i na ne dole inci tunda ni na girka."
   "B'arauniya ba, toh kisani kinci haramun."
  "Kanka akeji." Tana kaiwa nan ta koma d'akinta. Later during the night Zeezee ta fito sanye da bombshot da vest tana latsa wayar da Lubiee tabata. Zama tayi kan kujera tare da kunna power button tana kallon TV tana chatting. To 10:30pm Adeel ya fito sanye da pajamas nasa zasa d'auko ruwa a fridge. Tsayuwa yayi yana kallonta, yayi hakan na mintuna biyu ya kad'a kai ya wuce dining ya d'auko bottle na ruwa duk anan Zeezee bata san da halitta tsaye gun ba. Har ya kaiga shiga d'akinsa yaga baze iya hak'ura ba, "Ke a ina kika samu wannan wayan?"
   "Sata nayi ina ruwanka tunda ba kai ka siya min ba?" tana gama amsa sa tasa dariya da alama da chatting da takeyin ne. Hakan ba qaramin 6atawa Adeel rai yayi ba shi bayison yaga tana walwala yafison yata ganin ta cikin hawaye kullum "Kuma da wa kike chatting?"
   "Wai kam ina ruwanka? In kana waya da Ruky kowa take na ta6a yimaka magana ne? Please kadena cikamin kunne."
  "Ajiye wayan kizo." Ya fad'a more like a command.
   "Nazo kamin meh?"
  "Kizo nace dont let me repeat myself."
  "Bazan zoba in fad'an abu zakayi say it ina jinka."
  "Kizo haqqi na nakeso."
   "Lallai ko kayi 6atan kai in haqqin ka kakeso kana iya zuwa gun ita karuwar taka ta baka amman kasani bakada haqqi akaina."
  "Zeezee karkisa na miki na k'arfi."
  "Kayin ai dama abinda ka saba yi kenan." Fusata yayi lokaci guda wai ita waye da zece yanason haqqinsa tace bazata bada ba, goran ruwan ya ajiye ya nufi gabanta, ko tsorata bata yi ba hannunta yaja seda ya miqar da ita daga kan kujeran "ina ayi ta dad'i bakiya so?"
  "Ka sakemin hannu mugu azzalimi kwai let me go." Janta ya shiga yi, ganin haka ta sulale k'asa "ki tashi nace!"
  "Ai wallahi na gaya maka bazaka sake samun wani abun aguna ba, I belong to Ya Al'ameen."
  Haka kikace? Bale ma shi Ya Al'ameen d'in me zeyi da wacce bata haihuwa? Mschww!"
  Eh ka fad'i koma me, bashi zesa na baka kaina ba."
   "Ajinki ko anan bazan iya yin abinda nakeso bane?" Sauk'a k'asan shima yayi ya had'e hannayenta biyu a sama yana wani erin shunshuna wuyanta wane ze had'iyeta "Adeel stop it banaso! Stop it already." Ko sauraranta beyi ba, dabara ce ta fad'o mata, ta seta k'afanta dai-dai kan abin nasa ta gullesa. Take yabar abinda yaken tare da sakar da wani mugun k'ara abin nasa ya riqe yana matse ido anan Zeezee ta samu ta tashi tareda rugawa d'akinta a guje.
   "Wallahi you won't get away with this" yace da ita lokacin da take sa lock jikin k'ofar tata. Yafi minti biyu tsugune agun sannan finally ya miqe ya nufi d'akinshi.
 
  The following day, ba yadda Adeel beyi da Zeezee ta fito daga d'akinta ba tak'i, wanki ya loda mata bakin k'ofan yau harda iron "gashi in kika fito ki wanke min su duka kuma ki goge wallahi in bemin ba zaki sha mamaki." Yana kaiwa nan ya fice seda ta tabbata ya fita sannan ta fito baki ta sake ganin yawan kayakin da kaman bazata wanke ba sekuma ta tuna da abinda ta mai jiya muddin ta bari ta sake yimai wani abin yau yana iya zaneta sabida tsab ze rina. Kamar wacce zatayi kuka ta tattara kayakin nasa ta wanke mai suna bushewa tabisu da guga, bayanta wane ze 6alle. Seda ta gama mai nasa sannan ta shiga yin nata itama, se tunawa take time da take gidan Ya Al'ameen da zaran wankinta ya taru shi da kansa yake sawa a wanke akuma yi mata guga. She can't tell how much she is missing him.

    _Few months later..._
   ***
   Maganan aure fa ba fashi, gini har an kammala an soma jere, ba aikin Zeezee yanzu se kuka kullum, bazata iya zama da kishiya ba, kishiyan ma wai wacce taji boko fiye da ita. Tunanin kalan rayuwan da zata shiga muddin ta bari Adeel ya auro Ruky Mama kawai take tasani tamkar baiwa ze mai da ita, she can't take it.

   Yau da misalin k'arfe d'ayan rana Adeel ya shigo gida da almajiri biye dashi yana riqe da akwati na tsakiya k'waya d'aya. A parlour ya umurci yaron ya ajiye mai sannan ya sallemesa. Anan ya shiga k'walla wa Zeezee kira "Ke Zeezee! Ina kike ki fito da Allah kina 6ata min lokaci."
   Tana kwance bisa gado tana aikin kuka ta miqe tazota, da k'afa ya tura akwatin side nata "gashi wannan naki ne kayan fad'an kishiya kome ake kira." K'arisowa tayi a nitse ta tsuguna ta bud'e akwatin dududu befi atamfofi biyar ciki ba nan ma ba super ko makamancin haka ciki, seda wasu local inner wears k'waya biyar da shampoo na 'yan N350 guda d'aya aciki se dubu biyar a gefe. Kai ta kad'a sannan ta miqe tsaye tana kallonsa "Adeel koda tinkiya ce zaka auro mata wata bazaka kai mata wannan abu ba bale ni mutum. Meh wannan yanzu? Kana ganin kamin adalci kenan? Akwatuna nawa ka kai gidansu Ruky Mama 24 am I right? Amman ni dake ka miyar dani tamkar wacce ba haifanta akayi ba zaka kawo min wannan tsummakaran, Ahaka ne kake tunanin zakayi adalci tsakani na da wacce zaka auron?"
   "LOL bakisan wani abu ba wannan d'inma banyi niyyan kawo miki ba, mutumin danayi siyayya a shagonsan ne yace lallai sena kawo miki wani abu, kuma tun wuri is better kidena had'a kanki da Ruky kinga na farko ita ba sadaqarta za'ayimin ba, da kud'i na zan aurota unlike ke da aka wulla min ke na biyu Ruky tafi minke tunda ita masters holder ce ke kuwa ko degree bakida, na uku garau take at any moment tana iya d'aukan ciki ta hihu ba kaman ki da bakida amfani ba, kinga ko anan ma zakisan matsayinku ba d'aya bane. Ki taimaka wa kanki kibar comparing d'in ku."
   "Haka kace?"
  "Haka yake ma so ni zan koma."
  "Dan tsaya" ta buk'acesa. Kitchen ta nufa da wuri bayan second counts ta fito riqe da galon na kero da ashana. Baki ya saki yana kallonta lokacin da take bulbula keron akan kayakin, seda ta tsiyaye tas sannan ta kyasta ashana ta wulla akai balbal ya soma ci.
   "Kasani koda a sadaqa ka sameni ba a wahala ka tsintoni ba da zaka kawomin k'ananun zannuwan dubu uku kayi tsammanin kuma zansa su."
  "Ke!" Anan ne bakinsa ya bud'u "asaran dukiya zakiyi min? Dama inba zanin dubu uku-ukun ba ki gayamin wani zanin ne yafi cancanta da 'yar sadaqa?"



  *MIEMIEBEE       TEAM #YGC!*
  beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄

14 comments:

Sadiya said...

Weldone our meimei Allah ya biya

Unknown said...

Allah sarki wallahi ta fara ban tausayi

Unknown said...

God job zezee ci uban dan kaniua dai dai iyawarki

Anonymous said...

thank you sister

Haleemah said...

Tnx sis.... duk da nasan zee zee bata kyauta ba amma wannan punishment din yayi mata yawa....ya kamata a bata courage din da xata ci uban adeel kuma ta samu su baba suyi forgiving dinta...ta koma kuma gidan mag-gen

Haleemah said...

Tnx sis.... duk da nasan zee zee bata kyauta ba amma wannan punishment din yayi mata yawa....ya kamata a bata courage din da xata ci uban adeel kuma ta samu su baba suyi forgiving dinta...ta koma kuma gidan mag-gen

Sabiyyah Affandi 🌹 said...

Yeah fcourse she'll be 4given...but what she's going through comes from her! Thanks so much Miemie, for haven shining our eyes to the fact that(not what one always luv more than one's own life, are Good). This lesson,i have been taught well...Allah shi yi miki albarka Cos not only are u creating a story but also, saving millions of gurls who value their Boyfriends more than their very own lives,Daga irin wannan kangin da Zeezee ta tsinci kanta a ciki...more ink to ur pen~

Unknown said...

Yo ai punishment din is not that much compared to her crimes nd babanta ma yakamata yafi haka shan wahala coz shine silar komai. Kudos miemiebie. More ink to pen nd more ideas to ur brain

Unknown said...

No my dear.there shudnt be any courage for retaliation. Her punishment shud be more dn did coz her crime was way too much

Unknown said...

Weldon Allah ya kara fasaha

Unknown said...

U ar amazing dr. Bravo to u keep it up

Unknown said...

Pls muna jiran nx page aturo dayawa

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Unknown said...

Enx sis.... Mehn!!!! Am just pitting zeezee lyk die buh luving ur moves lyk crazy Miemie. Kudos to u, more strength to u nd ur fingers dear, u'r1 in a trillion....