*BY MIEMIEBEE*
PAGE 44
*Febuary, 2017*
Ciki ya dosa da wuri hankalinsa gabad'aya a tashe yake, d'akunan ya soma bi yana qolla mata kira amman ko ina shiru ba Zeezee bakuma alarmarta. D'akin data koma da zama ya duba last har cikin bayi bai ganta ba. Wardrobe da take adana kayanta ya bud'e yaga wayam bakomai ciki kasancewar ita dama tayi shirin guduwa ne gabad'aya Lubiee ce ta hanata, danqaree! Ya furta a ransa “ta gudu!” dining chair yaja ya zauna akai yana nazarin dawa take communicating har tasamu tayi escaping. After a while ya zaro wayansa ya kira Lubiee sanin how intimate they are. Itama seda ta gama ja mishi ajin duniya sannan ta d'aga nan ma don bata son yayi suspecting nata ne.
“Ya da kira na kuma Malam?”
“Ina kika kai min matata? Ina kika kai Zeezee?“
“What rubbish are you talking about?”
“Dont play dumb Lubiee nasan da bakinki a wannan lamari.”
“Kaga Malam gidan biki nake kuma wallahi inhar wani abin ya samu Zeezee bazan ta6a yafe maka ba tunda you are too careless over your possessions har ka bari matarka ta 6ata.” Bata jira jin me ze sake fad'i ba ta katse wayar. Hankalin Adeel ne ya sake tashi matuqa da kalan kalamun Lubiee. “Yanzu ina zan shiga neman wancan me kunnen qashin? After telling her not to ever step a foot outside taqi jina abee? Allah dawo dake kokuwa Allah had'amu koda akan layi ne.”
****
Zeezee bazata iya tuna when last tayi walwala kaman na yau ba, gabad'aya harta manta da problems nata se cashewa suke tayi and ko kad'an Lubiee bata nuna mata Adeel called her ba gudun tashin hankalin da take iya jefata. 5:48pm Zeezee ta kira Lubiee gefe “Babe mu tafi yanzu please inason in leqa su Mama koda they won't let me in amman susan I care about them and that am missing them.”
“Toh Zeezee mu wuce barin yiwa Meela sallama” nan da nan taje ta dawo suka d'au hanyn gidansu Zeezee. Gaba da gidan kad'an Lubiee tayi parking nan Zeezee ta sauk'e ajiyar zuciya, “should I follow you?” Lubiee ta tambaya calmly.
“You don't have to nasan da k'yar ma su barni.”
“Have faith kinji best franndd?” With a nod Zeezee ta fice daga ciki chan nesa tayi sallama har sau uku sannan Omar ya fito sanye da singlet da wandon jamfa, murza idanunsa yayi don tabbatar da abinda suke gane mai ”Zeezee?” Yayi exclaiming unbelievably.
"Na'am Ya Omar.”
"Kece?"
"Nice Ya Omar, ina uni?" Ta sauqa har qasa abinda bata ta6a mai ba ta gaishesa. "Lafiya tashi abinki, kina nan dama?"
"Ina nan Ya Omar Mama fa tana gida?" Kai ya gyad'a mata yana mamakin yadda ta rage haske takuma rame tabbas yasan tana cikin damuwa "shima Baba haka?"
"A'a bayi nan ya fita." Ajiyan zuciya ta sauqe, "Ya Omar dan Allah alfarma nakeso kayi wa Mama magana don Allah tafito na ganta koda bazata min magana ba."
"Naji ina zuwa. "
Ciki ya nufa ya tarar da Mama na karatun Qur'an kamar yadda ta saba every evening. Sallama yayi wanda bata amsa ba seda ta kai qarshen ayan datake karantawan.
"Wa'alaikumus salam Babana hira kazo min ne?"
"Mama Zeezee ce tazo fah."
"Toh wata Zeezee kuma?"
"Zeezee autan mu."
"Zainab!" Tayi exclaiming tare da zaro reading glasses nata. "Zainab fa kace Omar?"
"Eh Mama tana waje wai don Allah kije ku gaisa."
"Kace mata ina bacci." Dan kuwa kwata-kwata Zeezee ta fita mata a rai yanzu.
"Mama please karkiyi haka kema, yarinyan nan tana cikin damuwa wallahi bakiga yadda tayi duhu takuma rame ba."
"Omar-"
"Please Mama" ya katseta a nitse. Seda ta d'au tsawon mintuna biyu tana nazari sannan tayi making up mind nata ta miqe "muje" tace dashi. Labule ya d'aga mata ta wuce sannan yabi bayanta. Tsugune yadda yabar Zeezee suka tarar da ita. Ganin Mama kad'ai yasa ta zubda hawaye sosai bata zata tayi missing home as this ba, so take tayi hugging Mama and feel her warmth again amman kuma tsoro takeji karta hanata. "Mama" ta fad'a a hankali abin tausayi hawaye na tsiyaya daga idanunta. Se kallonta Mama take a yayinda zuciyarta ke mara mata kode wani cutan zamanin ne da Zeezee yadda ta rame haka. "Zeezee?"
"Mama!" Ta amsa tana kuka sosai batasan lokacinda taje ta fad'a jikin Mama ba tana kuka me mugun tsuma zuciya, matseta tayi gagam jikinta tana kuka itama Mama tuni zuciyarta ta kariya da k'yar ta iya ta danne kukan dake neman qeto mata, sede har a yanzu ta kasa hugging Zeezee back, don kanta (Zeezee) ta gaji tayi breaking hug d'in sannan ta sauqa har qasa tana me cigaba da kuka. "Mama don Allah kiyi hak'uri, kiyi hak'uri ki yafemin abubuwan dana miki please indeed nayi regretting komi, I shouldn't have took my boyfriend over my family dan Allah kuyi hak'uri, Ya Omar a so sorry please..." hak'urin ta cigaba da basu duk seda ta basu tausayi.
"Shikenan Zainab tashi ya isa haka" Mama ta fad'a finally "tashi kukan is okay."
"Mama ki yafemin please badon hali na."
"Naji tashi ki tsaya" a nitse ta miqe sannan Mama ta qura mata ido "meke damunki Zeezee?" Ta tambaya finally.
"Babu Mama banda missing naku da nake ba komai again."
"Are you sure? Karki min k'arya."
"Mama bab..." se kuma ta rushe da wani irin kuka da k'yar su Mama suka samu tayi shiru sannan Omar ya shimfid'a musu darduma suka zauna duka akai. "Ina jinki gayamin meke damunki kika rame kika kuma yi duhu haka."
"Mama tabbas duk d'an da bai jin maganan iyayensa kokuwa iyayensa suke baqin ciki dashi yana cikin babban had'ari. Mama ko baki fad'a ba nasan ke da Baba are extremely angry at me fushinku ba qaramin abu bane agareni, Mama nayi nadaman qin jin magananki dana Baba, inda nasan haka halin Adeel yake da ban auresa ba. Mama banda bak'in wahala ba abinda nake sha a gidan Adeel ko fita yau ma seda nayi dagaske na samu na fita kaman kazan poultry haka ya rufeni gida bana zuwa ko ina ko waya banida yanzu azaban yau daban na gobe daban, wulak'anci ba wanda baya d'uramin nasani alhak'in ku dana Ya Al'ameen ne ke bina abinda kad'ai nakeson ku sani shine na tuba kuma nayi nadaman komi gafararku nazo nema nasan koda zan had'a sama da k'asa Baba baze ta6a yafemin ba amman Mama nasan ke ba haka kike ba haka Ya Omar ma don Allah ku gafirceni."
Dogon nishi Mama taja ta sake sannan tace, "bakomai Zeezee ni na yafe miki kaman yadda nasan Omar ma ya yafe miki ko Babana?" Kai ya gyad'a as yes. "Sauran 'yan uwanki ma zan musu magana kekuma Allah ya kawo sauk'i cikin lamarinki zan tayaki da addu'a nima. Inda za'a bi ta nawa ko komawa gidan Adeel bazakiyi ba amman nasan Babanku baze ta6a yarda ba shiyasa nakeson ki k'ara hak'uri no situation is permanent okay?"
"Hakane Mama nagode sosai Sakillahu khairan Ya Omar nagode zan koma, idan Baba yazo ku gaishesa."
"Toh Zeezee sannu ko se haquri" ta miqe kenan suka jiyo k'aran security switch na motan Baba, wani irin ruwa cikin Zeezee ya d'au ba ita kad'ai ba harta su Mama. Kafin suce zasuyi wani qwararren motsi har ya shigo ciki inda yana shiga sukayi ido hud'u da Zeezee. Tsayawa yayi yana tantancewa shin Zeezee ce 'yarsa da yayi disowning kokuwa me kama da ita don shi kansa kamanninta yaso 6ace mar.
"Baba" ta fad'a hawaye na cikowa a idanunta.
"Hafsah me wannan take min a gida?" Ya tambaya a fusace. Shiru Mama tayi, "dake nake magana fa kai Omar meya kawo wannan gida na? Se naja Allah ya isa tukun zaku shiga taitayinku ko? Maza!" yayi nuni da Zeezee "fita kibar min gida." Kuka take sosai tana neman tsugunawa don basa hak'uri "ki fita nace!" Ko sena sa polisawa sun min waje dake? kuma kika sake taka min cikin gida ke koda gate kika tab'a zanyi filing police report." Volume na kukan nata ne ya dad'u jin yadda wannan kalamu ke fita daga bakin mahaifinta cike da tsana zallah. One more look tayi wa su Mama sannan tace, "kayi hak'uri Baba inhar hakan ze farinta maka rai bazan sake zuwa nan ba kayi hak'uri farin cikinka ya fiyemin komi, Mama, Ya Omar na tafi anan" ta fice. Ita kanta Mama despite kalan abubuwan da Zeezee tayi mata bataji dad'in abinda Baba yayi ba more especially ma dataji halin da Zeezee ke ciki wai nan ma don Zeezee bata gaya mata lalacewar da mahaifarta yayi ba duk sanadin Adeel.
*~ *~ *~
Acikin mota ba abinda Lubiee ke se tambayar Zeezee meya faru dan ko bata ga shigan Baba ba as tun fitar Zeezee take ta chatting a wayarta.
"Zeezee kin min shiru? Kiji koda Mama basuyi accepting apology'n kiba eventually they'll kede ki dage da addu'a kinji?" Kukan ya isa please. Kanta ta d'ago finally daga kan cinyanta, "Lubiee Mama tace ta yafemin but Baba? Ko bani chance beyi ba he is still angry at me wallahi nayi nadaman komi."
"Is okay kinji one day all shall be well mu tafi?" With a nod Lubiee taja mota suka fice. Dai-dai gaban gate ta sauqe Zeezee "lets go in." Ta sanar da ita.
"Kaman ya?" Zeezee ta tambaya with bewildered looks.
"Muje namai explaining komi in naga abun banayi ba kid'au akwatinki mu tafi gidan mu zanyiwa Abba da Unmie bayani."
"No Lubiee please duk beyi zafi haka ba, kinga banason Adeel yasan ke kikayi helping d'ina out we don't know what he is capable of ki tafi kawai duk abinda akwai I'll let you know."
"Are you sure Babe?"
"Yes karki damu" tayi forcing smile out. "Toh ga wannan" tasa hannu a pocket dake kujeran baya tare da fito dawata samsung J1 "ga wannan ki riqe incase ya d'auke landline d'in semuna waya tanan ki qara hak'uri."
"Lubiee thank you so much" nan tayi hugging nata "you are just like a sister to me Allah yabar zumunci."
"Ameen best frandd."
"Toh se anjima" anan sukayi sallama seda Lubiee taga shigewar Zeezee ta fice itama.
***
Tafi minti biyu tsaye a entrance door amman ta kasa shiga da k'yar at last ta bud'e ta shiga kafin ta miyar da k'ofan taji footsteps na Adeel a bayanta nan fa ta shiga shaking tama kasa juyawa ta fuskancesa. "Seki juyo aiko?" Cewar Adeel tad'au almost a minute sannan ta juyon kanta a qasa. "Sannu ko kinyi qoqari, wato ke ba wanda ya isa ya gaya miki magana kiji, ko da shike dama wacce bataji maganan mahaifinta ba taya zata ji na mijinta? Menace miki akan fita unguwan? Bance miki baza ki jeba ba?" Shiru tayi har anan "dake fa nake magana ki daina maidani mahaukaci when ever am talking to you." Ji kawai take kaman ta cakka mai wuqa ta huta don haushin dayake bata maganan ma ta fasa bazata masan ba.
Gefensa ta gwada bi zata fice nan ya wani fincikota seda d'aurinta ya kunce "ina miki magana kina tafiya irin ga mahaukaci na ihu ko?" Waina hannun nata ya shiga yi da mugun qarfin dayake ji dashi cike da mugunta, tun tana iya daurewa ta soma kuka. "Adeel ka sakemin hannu please da zafi."
"Ina kikaje nace?" Ganin bata da niyyan magana ya sake murd'a hannun nata. "Adeel please you are hurting me" ta fad'a a wahalance tana kuka. "You are not ready to talk kenan nasan maganinki" janta ya shigayi izuwa d'akinsa.
"Adeel me zaka min let me go, ka sakeni don Allah." Ta qare maganan cikin kuka.
"Ina ni zaki mayar mahaukaci ina miki magana?" Jefata yayi kan gado ya haye kanta nan ta qara volume na kukan nata, k'ok'arin rabata da kayanta ya shiga yi se ihu take tana had'asa da Allah.
"Don Allah kabari banaso, ka dena please am begging you Adeel please, stop it already please" Ko sauraranta beyi ba yayi ripping mata kaya tas haka cike da mugunta da wulak'anci ya sake biyar buqatansa da ita yau, ba abinda Zeezee ke se kuka seda ya gamsu sannan ya tashi ya koma gefe yana binta da wani pathetic look "next time kika sake crossing d'ina zaki sha mamaki wallahi" yana kaiwa nan yaja trousers nasa ya bar mata d'akin. Kuka take wane don shi aka turota duniya wannan wace erin rayuwa ne? Lallai ashe iyaye ba abin wasa bane duk wanda ya bari d'aya daga cikin iyayensa kokuwa duka sukayi mai baki ko kuwa suke fushi ko baqin ciki dashi toh tabbas baze qarasa da duniya lafiya ba.
Sam ta kasa sauqowa daga kan gadon don azaba, seda tayi dagaske sanan ta samu ta tashi ta miyar da kayanta tabar mai d'akin. A parlour ta tarar dashi yana kan waya da Ruky Mama.
"Hold on Babe please" yace da Ruky Mama sannan ya miyar da kallonsa kan Zeezee, "ke kije ki had'a min dinner am starving" yace da ita yana wani mata mugun kallo. Shiru tayi tsaye gun "bazaki amsa ba sena kira wani qato a waje yayi abinda yaga dama dake ne ko kuwa?" Da mamaki ta d'ago kai tana kallonsa lallai Adeel yanzu har tunanin ya d'au matarsa yabawa wani k'ato yayi lalata da ita yake tunanin yi? Gaskiya ne ya tabbata bashida imani bayahude ne shi.
"Kina kallo na kina ganin bazan iya bane? Don amfaninki kenan for sex and cooking zaki min dinner'n ne ko sekinga aiki da cikawa?" Sanin sarai ze iya ya kira wanin kuma tana ji tana gani yayi amfani da ita tunda har ya fad'a da bakinsa yasa ta gyad'a kai "zan girka maka."
"Da ko kinsha mamaki." da hannu yayi dismissing nata sannan ya cigaba da wayansa. D'akinta ta nufa ta d'aura towel sannan ta nufa bayi donyin wanka, kuka ta shigayi kaman lalacaccen famfo yanzu abinda take gani a american films shi Adeel keson kawo mata gida? Wani irin rashin kishi ne da zaisa mutum ya d'au matarsa ya bawa wani wai yayi duk abinda yakeso da ita? Shin anya ma kuwa Adeel musulmi ne? "Wani irin rayuwa na jefa kaina ciki?" Kuka tata yi seda ta godewa Allah sannan ta idar da wankan da alwala ta fito tayi Sallah. Ba tare da 6ata lokaci ba ta had'a mai dinner yana ci ya d'au wanka koba a tambaya ba ansan gun budurwa zasa. Kukan zuci ta soma ita sede yayi biyan buqatansa da ita ba godiya babu dad'ad'd'un kalamu sema tunanin bawa wani la'ananne ita yake amman gashi zasa gun budurwa yanzu yaje yana gaya mata love and soothing words. "Ya Al'ameen don Allah ka yafemin abubuwan dana maka, I can't tell how much I miss everything about you." D'akinta ta nufa ta taqure kanta gu d'aya kan gado tana me kuka sosai.
*GIDAN ALHJ ISMA’EEL YUSOUF*
Tsaye Mama take jikin wardrobe nasu bayan ta ciro wa Baba kayan baccinsa ta miqa mai tare da sauqe ajiyar zuciya. "Alhj" ta kirasa a hankali.
"Na'am Hafsah." Waje ta nema ta zauna gefensa "Alhj don Allah badon niba ka saurareni."
"Toh Hajiya Hafsah wani magana kuma kikeson min haka?" Yayi maganan yana canza kayan nasa.
"Batun Zeezee ne." Ta fad'a tana shakkansa.
"Banason jin wani maganan daya shafi wancan 'yar iskan."
"Subhanallahi Alhj 'yarka cefa."
"Kada ki sake sa Zainab cikin jerin 'ya'yan dana haifa."
"Alhj-" katseta yayi da wuri "ya isa Hafsah inba wai fad'a kikeso muyi ba ki ajiye maganan nan ni na gaya miki."
"Naji zan ajiye amman kasani 'yar ka na wahala sosai gidan yaron can kaima kasani kaga yadda ta rame ai."
"Aini bazan ta6a sanin tana wahala ba senaji ya kasheta kowa ma ya huta annoba kawai."
"Haba mana Alhj-"
"Ya isa Hafsah in kinsan maganan da zaki tayi kenan zan bar miki d'akin" yana kaiwa nan yayi pulling trousers nasa ya fice zuwa guest room inda ya kwana can ranan. Duk yadda yayi a daren ranan dan kawar da tunanin Zeezee daga k'wak'walwansa ya kasa saboda shi kansa ta basa tausayi amman idan ya tuna da kalan abin kunyan da tamishi gaban uwar Maj-Gen seyaji ya sake tsananta.
****
The following day tun 7am Adeel yazo ya tayar da Zeezee kan ta had'a mai breakfast yanada gun da zasa which is none other than gun Ruky Mama. Haka ta katse baccinta ta had'a mishi breakfast kamar yadda ya saba ba godiya ba sannu haka yauma yaci abincin yabar plate d'in gun. Ya kaiga fita wayansa ya shiga buzzing a lokacin Zeezee na tattara dining table, "Halo Babe gani nan zuwa ki qara hak'uri kinji? I love you."
I love you d'in banza Zeezee ta furta a ranta meye amfanin ayita soyayya a waje in anyi aure kuma a miyar da mutum kashi banza? "ba haka Ya Al'ameen yake ba" ta fad'a a fili sede be jita ba kasancewar ratar dake tsakaninsu. Yana ficewa takai plates d'in kitchen tayi wanke-wanke sannan ta dawo d'akinta ta baje kan gado.
"Shikenan ni yanzu ina ji ina gani Adeel ze auro min wata?" Ta tambayi kanta, nan ta shiga rera kuka a hankali duk kalan rashin hankalin da take yiwa Ya Al'ameen koda wasa be ta6a ambaton kishiya mata ba amman wannan wanda besan darajan d'an Adam ba, ba abinda bata mai duk bayi gani shi aure ze k'ara. Hannu ta miqa dan d'ago landline ta kira Lubiee taga babu, nufi kenan Adeel ya d'aga ya 6oye. Har ta shiga yin sabon kuka seta tuna da wayan da Lubiee ta bata da wuri ta miqe ta d'auko daga inda ta adana. Bud'ewa tayi taga 3 missed calls tana dubawa taga lamban Lubiee take tayi calling nata back and hopefully ta d'aga.
"Gosh Babe you made me worried sick na d'au ko beast d'in can ya ta6a mana lafiyarki."
"Lubiee am tired bazan iya d'aukan abubuwan Adeel ba anymore wai fa shirin aure yake."
"Aure?!" exclaimed Lubiee.
Wallahi wai aure zeyi gashi har ya d'aga gini a gefe kuma site nata yafi nawa girma. Ina ni ina zama da kishiya dan Allah ina ma ace yana sona ne kuma yanada adalci da bazan damu chan ba amman wallahi nasan banda boyi-boyi ba abinda Adeel ze maidani."
"Subhanallah! Kinsan wacce ze auro makin?"
"Ban santaba amman de wai sunanta Ruky Mama-"
"Ruky Mama!" Lubiee ta sake exclaiming fiye dana d'azu.
"Kinsan tane?"
"Niko nasan Ruky Mama, ke wallahi da biyu Adeel keson auro miki ita kinsan kuwa she is a university graduate?"
"Babe don't tell me please. "
"Wallahi kuwa naji tana yin masters nata ma yanzu haka a ATBU, wallahi karki yarda ya auro miki 'yar boko kut! Wallahi Adeel shege ne." Kuka kawai Zeezee tasa saboda she is totally out of idea tasan ko had'a sama da k'asa zatayi Adeel baze fasa auren ba danko bayi magana biyu se in dagangan.
"Toh kuma kukan meh?"
"Lubiee na cuci kaina a rayuwa wallahi 'ya mace kar ta ta6a auran wanda takeso sede wanda yake sonta. Right from the start nasan nafi son Adeel shikuma he took it for granted words can't tell how much am missing Ya Al'ameen if only I can meet him once more to apologize to him and tell him just how much I love him" ta qare maganan tana kuka sosai.
"Is okay Babe we can't reverse time ki dena tunanin Ya Al'ameen sake tsanan kanki kawai zakiyi 6arna kam kin riga da kinyi sede ace Allah kiyaye aukuwan na gaba. Kina jina?" Kai ta gyad'a wane Lubiee na gabanta sannan ta bisa da "eh" tana share hawayenta.
"Shiru-shirun da kikeyi ma Adeel should end this moment ki k'wato 'yancinki da kanki its the only way you can escape."
"Kamar ya kenan Lubiee? Ban fahimce kiba."
"I mean confront the bastard ki gaya masa ke lalle school zaki koma yanzu."
"Wallahi nasan he'll never agree to it shi d'inda ko unguwa bayi son bari na inje bale school."
"Allah se ya barki bayan nan kuma kice masa ya za6i either ke ko ita Ruky'n don ke bazaki zauna da kishiya ba"
"Hmm Lubiee kema kinsan ita zece tunda baya sona yanzu, I mean nothing to him."
"Kema kin fad'a in yace ita seya sallameki don wallahi zaman zawarci yafiye zama da miji irin Adeel."
"Hmm Lubiee kina magana nan ma don ban gaya miki sauran abubuwan ba kinsan there was a night ya taho min gida a bige yayi taking advantage d'ina tun daga ranan ya miyar dashi abinyi without my concent yake kusanta ta da naqi dana so, to cut the story short sex machine kawai Adeel ya miyar dani."
"Wa iyya zubillah!" Abinda kad'ai Lubiee ta iya fad'a kenan.
* MIEMIEBEE TEAM #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
πππππ
2 comments:
Allah ya kara basira
Lol. Ya'r Gata anashan Shit! Serves her damn ryt...cos idan na tina kawai irin bakar wahalar da ta bai wa Bawan Allahn nan(Ya Al'Ameen)kawai sai naji bana tausaya mata...Gobe kusa!
Post a Comment