Thursday, 23 February 2017

‘YAR GATA CE!

    *BY MIEMIEBEE*
*PAGE 52*
   February, 2017



Tun wajajen 7am Mrs Mukhtar taji rasuwan Baba wanda Mama ta sanar da ita ta broadcast mssg da aka yiwa kowa, amman ta rasa ya zata fara sanar da Zeezee. Da k'yar ta samu tayi gathering courage bayan k'arfin guiwan da mijinta ya bata ta shiga d'akin Zeezee tare da yin sallama.  Alokacin har Zeezee tagama shirinta tsaf sauran tafiya kawai take jira don taje ta duba lafiyan mahaifinta. "Wa'alai kumus salam. Ina kwana Aunty?" Ta gaisheta cike da ladabi.
  "Lafiya Zeezee har kin shirya ne?"
  "Eh, Aunty."
  "Bazaki karya ba toh?"
  "A'a sena dawo zanje naga lafiyan Baba tukunah." Nan fa Mrs Mukhtar ta sake jin bazata iya sanar da Zeezee ba mutuwan mahaifinta but tasan she have to.
  "Zainab." Daga yadda ta kira ta yasa gaban Zeezee fad'uwa danko bata ta6a kiranta da Zainab ba sede Zeezee.
   "Na'am Aunty?"
  "Zeezee..." sekuma tayi shiru.
  "Zeezee kinsani cewa duk me rai mamaci ne ko? Kowa a duniyan nan ze mutu wataran ya koma ga mahallicinsa ko ba haka ba?" Dum! Gaban Zeezee ya sake fad'uwa sede sam bata kawo a mind nata wai rasuwa mahaifinta yayi ba.
  "Aunty me kike nufi?" Kad'ai ta iya furtawa tana kad'a kai a yayinda hawaye ke forming rapidly a idanunta wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.
   "Zeezee you are no more a child ya kamata in sanar dake gaskiya, Baba lokaci yayi, Allah yayi mai cikawa yau da daddarre wajajen k'ar-" bata kai da idda maganan ba kawai taji rigijib! Fad'uwan abu a k'asa. Da gudu ta yo kan Zeezee only to find her fainted (a sume.)

   "Innalillahi! Zeezee! Zainab!" Bangida ta nufa ta ibo ruwa ta yayyafa mata sede ko motsawa Zeezee batayi. "Mukhtar! Mukhtar!" Tashiga k'walla wa mijinta kira wanda ya fito a gigice.
   "Mukhtar! Zeezee, Zeezee please do something."
   "Jeki d'auko key da wuri" ya buk'aceta a yayinda ya cinci6i Zeezee se asibiti suka yo inda akayi emergency ward da ita. Taimakon gaggawa aka shiga bata a yayinda hankalin Mrs Mukhtar ya kasa kwanciya. Cikin ikon Allah Dr's suka samu suka farfad'o da Zeezee sede gabad'aya bata cikin hayyacinta banda "Baba, Baba" da take ta furtawa.

   "Dr how is she?" Mrs Mukhtar tayi saurin tambayan Dr'n hankali a tashe.
   "She'll be okay in shaa Allah amman kome ya sameta?"
  "Dr rasuwa akayi mata, mahafinta ne ya rasu. In the process of breaking the news to her seta yanki jiki ta fad'i."
  "Ohh ayyah, Allah yaji k'anshi da rahma."
  "Ameen" both suka amsa.
  "Shi dama mutuwa haka yake but karku damu in shaa Allah zata samu sauk'i. She is just psychologically affected wanda hakan is normal."
  "Toh Dr mungode" cewar Mukhtar.
  "Zamu iya shiga ganinta?" Asked Mrs Mukhtar.
  "Sure please, excuse me" Dr'n ya amsa tare da ficewa. Nan suka shiga d'akin Zeezee inda take nan kwance bisa gado tamkar wata zararriya ta koma, se ambaton "Baba, Baba" kawai take. Duk kalan suratai da sannu da Mr and Mrs Mukhtar suke mata ba jinsu take ba.
   "Ku kaini gun Baba, Baba be mutu ba inya ganni ze tashi ya koreni saboda ya hanani taka duk inda yake. Ku kaini gunsa please nasan be mutu ba."
   "Zeezee bakida lafiya, kibari zuwa anjima idan kika d'an ji sauk'i." Mrs Mukhtar tayi explaining calmly.
   "Ku kaini gun Baba don Allah ku kaini wajen shi" kuka take sosai me tsuma zuciya. Ganin yadda take kuka sosai yasa dole Mr Mukhtar yama Dr magana akayi discharging nasu. A sannu a sannu Mrs Muktari tasa Zeezee a mota suka nufi TH inda su Mama suke.
   A lokacin da suka isa ma su Mama da sauran dangi suna shirin komawa gida ne da gawan Baba don cigaba da kar6an gaisuwa achan. Ko ta kan Mama Zeezee batayi ba da gudu taje ta rungume gawan Baba dake a lullu6e kan gado.

   Kuka take wane don shi aka kawota duniya, ba wanda yace da ita k'ala illa ma kallonta da suke suma suna kukan.
  "Baba nasan baka mutu ba, nasan kana jina, please say something you can't die, we need you alive. Baba bazeyi ka mutu ban nemi tubanka ba, please come back Baba. I need you to forgive me please come back. Baba ni ya kamata in tafi saboda kasamu kasha iska, ba kai ka tafi ka barmin duniyan ba. Please come back" ta k'are maganan tana jijjiga gawan Baba.
   Ihu ta rushe dashi ganin be mata magana ba har yanzu assuring her he is gone forever no coming back. Matse jikin Baba tayi a nata tana hugging nasa sosai. Mariam ce tayi k'arfin hali tace da Mama, "Mama ki fad'a mata Baba ya yafe mata please." Ita kanta Zeezee ta bata tausayi, itan da sukayi sharing happy moment with Baba ma kenan kafin lokacinsa, bale ga Zeezee da Baba ke fushi da ita for a very long time. A nitse Mama ta miqe ta nufi kan Zeezee tare da patting bayanta.
  "Zeezee ya isa haka kinji? Taso yi hak'uri."
 
  "No Mama don Allah kar ku fita da Baba wallahi be mutu ba yana jina, ku tsaya kuga ze tashi yace in fita mishi daga d'akinsa. He is not dead listen to me please."
   "Zeezee kibar magana haka da rungumar k'addara aka san musulmi. Baba lokaci yayi amman jiya ya bani wasiha na fad'a miki. Yace _ya yafe miki duk abubuwan da kika masa duniya wa lahira, da 6oyayye da kuma bayyananne. Yace min yau in Allah ya yarda ki koma gida ki cigaba da zaman ki achan, chan ne gidanki. Yace min he wants you to know that you'll forever bs his little sister and daughter and that he loves you so much Allah ya miki albarka ya baki 'ya'ya na garin da zasu kula dake ya kuma baki miji nagari and lastly kema ki yafe masa abubuwan da ya miki._" Mama ta k'are maganan cikin kuka sosai wanda seda yasa duk wani mahalukin dake gun kuka banda kaman Zeezee. Within seconds kuma se aka ji kukan nata ya d'auke. "Zeezee?" Mama tayi saurin tapping nata only to found her fainted body. Sumanta na biyu kenan, nan da nan akayi next room da ita inda aka shiga bata taimakon gaggawa ciki harda drip da aka samata saboda low water and sugar level data samu a safiyan yau, bayan nan ga yunwan da yaci jikinta wanda ke neman haifar mata da gastric ulcer. Alluran sa bacci aka yi mata, seda Dr ya tabbatar wasu Mama she'll be alright hankulan su yad'an kwanta. Mrs Mukhtar da Mariam aka bari akanta a yayinda sauran duk suka nufi gida don cigaba da kar6an gaisuwa achan.

   ******
   One hour sleep Zeezee ta samu sannan ta tashi da gaggaramin yunwa. Fuskan Mariam ne ya soma mata sallama, da wuri ta share hawayenta tare da mata "sannu" sede wani irin kallon da Zeezee keyi mata. Kafin ta hankara kawai taga Zeezee na neman 6alla connection na drip da aka sa mata. Da wuri Mariam ta haneta da yin hakan. "Ki sakeni Adda Mariam."
   "Zeezee What are you trying to do?"
   "Rayuwa ta bata da sauran amfani Adda Mariam I can't bear the thought that ni na kashe mahaifina."
   "Inji wa ke kika kashe Baba?" Mariam tayi maganan still not letting her go saboda yadda Zeezee keta faman k'watan kanta.
  "Ni na kashe shi Adda Mariam, nice silar rashin lafiyan dayayi sanadiyar mutuwarsa, I killed my own father Adda Mariam" ta rushe da kuka sosai.
   "No you didn't Zeezee, Baba lokaci yayi ba abinda muka isa muyi, rashin lafiya kuwa Allah ya riga ya k'addara masa shi tun kafin ya shigo duniya so stop blaming yourself kinji?"
  "That's not true, that's not true Adda Mariam just go leave me in kashe kaina nima yaso naje na sameshi achan lahira in nemi tubansa."
  "Wani tuba kuma again Zeezee bayan Baba yace ya yafe miki?"
   "That's still not true kawai Mama ta fad'a ne don kar hankalina ya tashi nasani Baba be yafemin ba nikuwa bazan iya cigaba da rayuwa da hak'k'in Baba akaina ba I'd rather commit suicide."
   "Get your senses together Zeezee, Baba ya riga ya yafe miki shike neman yafiyarki kema."
   "Meya ta6amin da ze nemi yafiya na?" Ta ce tana kuka sosai.
   "Kede kice kin yafe mishi saboda muma duka kafin... kafin" sekuma ta rushe da kuka "kafin lokacin sa yayi seda ya nemi tuban mu don haka nakeson kice mishi kema kin yafe masa."
   "Tunda Baba yake raye ban ta6a farinta mai ba, banda asara, bad luck da ciwon zuciya ba abinda na jawo mishi Adda Mariam, I know I am his worst daughter and child I can't ever forgive myself gani nake my hands are stained with his blood. Inhar abinda Baba ya buk'ata kenan kafin ya tafi ya barmu, toh ni na yafe masa har abada."

   Hugging nata Mariam tayi inda suka cigaba da kuka sosai. Tsan-tsan yunwa ko tsayuwan minti d'aya Zeezee ta kasa, wai ahaka ma don da taimakon drip da aka bata. Ba yadda Mrs Mukhtar batayi da ita ba taci abinci tak'i. Da k'yar suka samu tasha black tea se kuka take tana su kaita gida gun Babanta. Ta gama kur6e tea'n suka d'au hanyan gida.
   Dam gidan nasu yake cike da mutane da k'yar suka samu gu sukayi parking, da k'yar Zeezee ke tafiya ahaka ne har suka k'arisa ciki suka cigaba da aikin kuka.

***
   11:40am su Yasmeen suka iso a yayinda su Ibraheem suka iso wajajen 12::50pm. Kuka de ba babba ba yaro. Tabbas iyalan Late Alhj. Isma'eel Yusouf sunji wannan mutuwa na sosai sabida tun da suka taso wani na kusa dasu be ta6a mutuwa ba se akan mahaifinsu wanda suke matuqar sonsa fiye da yadda suke son kawunan su, its indeed a great lost to them, Allah ya jik'an Baba ya kai rahama kabarinsa, Ameen thumma ameen.
   K'arfe 01:20pm aka zo fita da gawan Baba wanda yake ajiye akan makara a d'akinsa inda aka fito dashi tsakar gida aka ajiye don bawa iyalansa daman yimai kallo da kuma addu'a na k'arshe. Hajiya Mama, mahaifiyarsa ce ta soma fitowa da taimakon k'annen Baba aka kaita gaban gawan d'anta. Banda kuka ba abinda takeyi. Da k'yar ta iya ya ta yaye laqafanin izuwa wuyansa sannan a sannu a sannu ta aza hannunta kan fuskarsa tana shafawa in a soothing yet pathetical manner "Allah ya ji k'an ka d'ana, har a kullum ina alfahari da kai ban ta6a nadaman haifanka ba. Na yafe maka dukannin abubuwan da kayimin na 6oye da bayyananne, ko da gan-gan ko rashinsa. Allah yayi maka rahama ya dubi kalan alkhairun da kayimin a rayuwa ya saqa maka da mafificinsu, ya d'aukaka darajarka a cikin shiryayyun bayinsa kuma ya maye maka bayanka a cikin wad'anda ka bari, yasa mutuwa hutu ce a gareka, ameen." Add'uan da akeyiwa mamaci ta biyosa dashi wanda duk gun suka amsa da "ameen."

   Mama was tha next person, itama guiwa ba k'arfi ta k'arasa gun da gawan ke shinfid'e. Kuka take sosai itama ta yaye fuskar nasa, nan fa sabon kuka ya sake fin k'arfinta. Addu'o'i sosai tayita yiwa Baba akan wanda tayi mai d'azu bayan data gama yimai addu'an ta had'a musu hannunsu se kuka kuma, ta tashi daga gun ma ta kasa seda su Mariam ne suka d'agata. Ibraheem ma kuka yake sosai ya k'ariso gaban gawan tare da yaye liqafanin, kuka yake sosai wane d'an yaro daga k'arshe yayi mai addu'a shima sannan ya tashi ya koma. Next was Mariam itama se kuka, duk according to their ages suka rik'a fitowa suna kuka sosai suna yiwa mahaifinsu addu'a. Kasancewar Zeezee ce auta, ita aka buk'ata last ta tako zuwa gaban gawan ma takasa, Yasmeen ce tayi assisting nata. Zubewa tayi a wajen se kuka tama kasa ta6a gawan bale tayi mai addu'a. Hannunta 6ari yake sosai ta d'aga da k'yar ta iya ta yaye liqafanin, nan fa ta sa wani irin kuka me tsuma zuciya. Hugging nasa tayi sosai "Baba I cannot live without you, you need to come back nasan baka mutu ba kanaji na, please say something inason inji da kunnuwa na ka yafemin, I want to be in your arms one last time, please come back you can't die. I want to make you happy one last time, nasan tunda aka haifeni I've been nothing but bad luck to you, Baba don Allah ka dawo nayi alk'awari to make you happy and proud. I'll never go against your command not even your wish, please Baba come back" ta sake sa wani erin kuka.
   "Mariam kuje ku d'agota" cewar Mama ganin kukan Zeezeen bana k'arewa bane. Guiwa ba k'arfi Mariam ta miqe ta nufi gun Zeezee tare da jan hannunta "tashi Zeezee yi hak'uri Baba ya riga ya yafe miki muma duk mun yafe miki."
 
   "Thats not true, ki sakeni ki barni dashi don Allah."
   "Zeezee ya isa please za'a fita dashi yanzu." Ganin abin ya gagari Mariam, Yasmeen ta shiga taimaka mata sede ina sun kasa d'ago Zeezee daga jikin Baba don yadda ta matse sa gagam a jikinta. Kuka take sosai na hak'ik'a tana sunbatu. Daga k'arshe seda Mama tasa Ibraheem daya je ya d'ago Zeezee. Shima seda yayi dagaske ya samu ya d'agata nan fa ta tada bori ita subarta a jikin babanta. Wani abin ma seda aka zo d'aukan gawan Baba za'a fita dashi.
   "Baba! Don Allah ku dawo min da mahaifina wallahi be mutu ba, karku tafi dashi don Allah I'm begging you guys please don't take him away." Idanunta da suka canza launi da komi ta d'ago tana kallon Ibraheem daya rik'eta gagam pathetically.
   "Ya Ibraheem nasan kana son Baba please don't let them take away Baba from us, ka musu magana su dawo mana dashi I beg of you please." Kuka yake har anan ya kasa ce mata komi nan ta kewayo da kallonta kan Mariam da keta faman kukan itama.
   "Adda Mariam, I know you love Baba so much please don't let them take him away." Anan datayi maganan har mutanen sun kai ga fita da gawan waje, wani irin ihu ta k'urma wanda tuni Ibraheem ya sake ta nan tasa gudu. Ta kaiga iskesu wasu maza suka samu suka rik'eta nan Omar ya kar6eta daga hannunsu. Se bori take tana ihu a dawo mata da Babanta. "Mama don Allah karki bari su fita mana da Baba wallahi be mutu ba." Da k'yar Omar yaja ta tare da zaunar da ita gefen Mama, ganin tana da niyyan tashi su Yasmeen suka danne ta. Sahun gawan su Ibraheem suka bi domin samun sallatan mahaifinsu.

   Tunda aka fita da gawan Baba, Zeezee ta tabbata fa yanzu shikenan Baba ya riga ya tafi ko shadow'nsa bazata sake gani ba bale taji muryansa kokuwa dariyansa, ya tafi kenan har abada no coming back. Nan ta fita daga hayyacinta gabad'aya, gatanan a zahirce a gidan amman hankalinta bayi nan ko kad'an. Ta had'a wani tagumi se hawaye kawai take zubarwa wane lalacaccen famfo.

    ***
   Cikin yardan Allah aka sallaci Baba a Gwallaga Central Mosque inda ya samu thousands and thousands of people da suka sallacesa suka kuma rakasa makwancinsa. Ibraheem da Omar akayi susa gawan Babansu a kabari amman ina sun kasa tsan-tsan tausayi da kuka. K'annensa biyu suka sa sa tare da yimai final addu'a sannan aka bisine sa. Allah yaji k'ansa ya kyautata k'arshen namu muma, ameen.

****
   Gida se cika yake ba ko inda mutum ze sa k'afa. Dangi from other states gabad'aya sun samu zuwa se aikin kuka ake ba babba ba yaro, inda wasu ke hirar mamaci. Dayawa ke cewa Zeezee ce silar mutuwan Alhj Isma'eel tunda a sanadin ta ne ya soma kamuwa da ciwon zuciyar da har yayi leading to mutuwarsa, a inda wasu kuma ke cewa itance ma ta kashe sa kawai. Wannan maganganu su suketa yad'uwa har a cikin gari. Daga k'arshe fita Zeezee tayi daga gidan da gudu gabad'aya ta nufi gidan Mrs Mukhtar dan kunnenta bazasu iya cigaba da jiye mata wad'ancan munanan kalamu ba na cewa ita ta kashe mahaifinta. Kallon hannunta kawai take se gani take wai ga jinin Baba nan kwance jina-jina akai. Hak'uri Mrs Mukhtar keta bata. Tun daga wannan lokaci Zeezee bata sake sanin inda take ba.

   A washegarin rasuwan ne Adeel yajiyo rasuwan Babansu Zeezee wanda ya mugun tausaya mata sosai har hawaye seda ya zubar mata, tuna yadda take jijji dashi even before suyi aure. Koda yace tayi abu se tace ita Babanta fa, har ma yake neman tasokanarta da 'Daddy's girl.' Gani yake he is partially to blame shima saboda shi yasata ta bijire wa mahaifin nata wanda yayi causing masa wannan cutar da tayi sanadin mutuwarsa.
  Tsaf shida Ruky Mama suka shirya suka zo yin ta'aziyya, hannu bibbiyu aka kar6esu duk da sanin komi started with Adeel. Bayan ya gaishe da Mama yayi mata ta'aziyya ya buk'ci ganin Zeezee inda Mama ke sanar dashi cewa bata gida a haka ma yanzu batada lafiya. Still yayi insisting yana son ganinta a tunaninsa kawai hanasa ganin Zeezee Mama keson yi. Seda Mama ta fayyace masa gaskiyan al'amari na cewa koda zeezee ta gansa yanzu ba gane shi zatayi ba saboda condition da take ciki. Ko jiya da Mama ta aika aje a duba mata ita chan gidan Mrs Mukhtar bata gane su Mariam ba, sede tayita kallon mutum tana kallon hannunta amman ba kalman k'ala.

   Wani irin tausayawa Zeezee ya sakeyi if only there's something he can do. Fatan lafiya yayi wa Mama sannan ya ajiye carton na maltina biyun daya kawo musu suka koma da Ruky. Itama Ruky gabad'aya ta tsorata da mutuwan Baba tuna fa alhak'in Zeezee na sharrin data yi mata na kanta har yanzu, dole ta nemi tuba.

   Al'ameen kuwa a sadaqan uku ne Mama Babba ke sanar dashi rasuwan Baba. Sosai ya tausayawa Baba dakuma iyalansa most especially ma Zeezee da har yanzu take da gurbi a zuciyansa.  Dukda auren da Mama Babba keson had'asa da wata 'yar uwarsa Murjah, hakan besa ya dena son Zeezee ba ya kuma fara son ita Murjan. Infact her love increases in him every single heart beat. Auren biyayya kawai zeyi saboda shi har yau bega mace ba bayan Zeezee, sonta a jinin sa yake despite abubuwan da tayi mai he still loves her like so much.

   A ranan da yaji rasuwan ba tare da 6ata lokaci ba ya kira Mama yayi mata ta'aziyya, yaso ace yana gari don ya samu daman expressing masu condolences nashi. Layin Zeezee itama ya buk'ata don yimata ta'aziyyan saboda ya gwada wanda ke gunsa it aiint going through.
    Anan ne Mama ke sanar dashi halin da Zeezee ke ciki. Sosai masoyin hak'ik'an ya sake tausayawa Zeezee. If only there's something he could do.
    Abu fa kaman wasa se worsening condition na Zeezee ke tayi, se kaman neman zarewa take ne oho, abun kaman hauka. In anji sautin muryarta toh tana kuka ne. Magana ma tabar yi, ko bayi takeji in bawai anyi timing nata bane an kaita sede tayi a jikinta, cin abinci, sallah komi nata ya tsaya kat! Abu kaman wasa-wasa har akayi sadak'an bakwai Zeezee bata san inda take ba gata nan ne kawai se yadda akayi da ita. Bayan sadak'an bakwai ne lokacin da mutane suka gama watsewa, wanda suka rage befi a k'irga ba. Se a nan ne hankalin Mama da sauran yaranta ya dawo jikinsu akayi wur-wur aka d'auko Zeezee daga gidan Mrs Mukhtar aka kaita asibiti. Bayan dogon nazari da bincike da Dr yayi ya nuna musu cewa ba abu neba na damuwa saboda hakan is normal ga duk wanda mutuwa ya ta6a sa sosai, she is psychologically and even mentally affected at her own case, but in shaa Allah bayan d'an wani lokaci she'll be back to normal. Wanda kafin nan ya zama dole a kullum ana karanta mata labarai masu dad'i masu sanya nishad'i dakuma kaita leisure places saboda yayi erasing bad memory'n dake lingering akanta na cewa ita ta kashe mahafinta. Har izuwa ga wannan lokaci kuwa koda wasa kar a mata furucin da bashida dad'i. A haka ne su Ibraheem suka dawo da ita. The next day Ibraheem da iyalansa harma da Yasmeen suka juya, inda suka ajiyeta a KD sannan suka zarce Abj. Mutuwan Baba har a yau kaman sabo yake a memory'nsu, they shall never forget about their beloved father.



 *MIEMIEBEE.        Team #YGC!*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄👄

5 comments:

Unknown said...

Eyaaa zeezee Allah ya kara Sauki, enx sis more ink to ur pen.... Missing baba lyk neva b4. Allah ya jikan wanda suka riga mu Ameen.

Unknown said...

Eyyaa zeezee Allah BAKI lpy... missin Baba lyk never b4 .tanx sis

Unknown said...

ayyah zeezee baba's pet allh bata lpy weldon sis mariam

Unknown said...

Tnx sis, Allah ya kara basira, zeezee Allah ya baki lfy.

Unknown said...

wlh I pitty ha amma am happy tunda ha true love na santa haryanxu