Tuesday, 21 February 2017

‘YAR GATA CE!

  *BY MIEMIEBEE*
Page 51
 *FEBRUARY, 2017*

Blog readers how are you guys coping with this version? Lemmi know your opinions please, ILY'all❤


     "Eh Alhj" nan da nan Mama tayi placing Ibraheem on the line. A lokacin wayan nasa na a hannun Hafsah 'yarsa wacce suke kira da Maamah tana game. 'Yar tasa sak shi ba abinda ya rabasu, haskensa ne kawai bata gama ibowa ba ta d'an had'a da duhun mahaifiyarta. Ganin hoton Mama yayi displaying akan screen d'in tayi saurin kai wa Ibraheem da Fateemah da suke zaune a d'akinsu wayar.

  "Daddy! Daddy! Maman Daddy is calling you."
   "Dagaske? Kawo in gani toh Maamah na."
  "O'o Daddy ina game."
  "Yi hak'uri muna gamawa zan baki."
  "Ni o'o."
  "Yi hak'uri Maamah ki basa kinji?" Cewar Fateemah dake lullub'e cikin bargo da alama laulayi ke damunta.
  "Zan baki nawa."
  "Ni banashon naki."
  "Yi hak'uri kiban ze yanke, ga chan ice cream naki a fridge jeki d'auko."
  "Yeyy!" Kai mai wayan tayi da gudu sannan ta nufa fridge ta d'au ice cream d'in ta shiga sawa a armpit (hammatarta) hakan ba k'aramin dad'i yake mata jin sanyi-sanyin. Fateemah na kallonta aman batajin zata iya mata magana saboda tasan 6ata lokacinta kawai zatayi dan kuwa ba jin magana Maamah ke ba, halinta sak na Zeezee dukda taka mata birkin da Ibraheem ke, gado ba gwaninta ba.

  Kasancewar wayar ta yanke yayi calling Mama back.
   "Assalamu Alaikum Mama."
  "Wa'alaikumus salam Babana ina wuni?"
  "Lafiya Mama ya gajiya? Kin kira wayan na hannun Maamah tak'i bani."
  "Takwaran nawa ko? Ya jikin Fateemah kuma?"
  "Alhamdulillah da sauk'i" ya amsa yana kallon Fateemar, daga nesan tamai whispering "kace mata ina gaisheta and ta gaida Baba da jiki." Nodding yayi sannan yace, "tana gaishe ki da Baba da jiki, ya jikin nasa?"
   "Toh alhamdulillah de shi yace in kiraka ma yanzu yana son kuyi magana."
  "Allah sarki ki bashi toh."
  "Yauwa" a speaker phone ta danna sannan ta matso wa Baba da wayar kusa dashi "ga Ibraheem d'innan Alhj."
  "Aina?" Ya tmbaya nan Ibraheem ya amsa "gani nan Baba sannu ko? Allah baka lafiya."
  "Ameen Ibraheem Babana, Allah yayi maka albarka."
  "Ameen Baba gobe in shaa Allah zan shigo in duba ka."
  "Toh Allah ya kaimu Baba na nace ka yafemin rashin adalcin danayi a tsakaninku tunda kuke yara, Baba yayi kuskure ka yafe mishi kaji?" Jin haka Ibraheem ya d'au k'afa ya fice daga d'akin nan Maamah ta shiga binsa tana kiransa da wuri Fateemah ta tareta tare da dawo da ita cikin d'akin. Dining chair yaja ya zauna gabad'aya jikinsa yayi sanyi, "Baba wani irin magana kuma kake haka?"
  "Yi hak'uri ka yafemin Babana."
  "Baba nifa ba abinda kamin, ni yakamata in nemi tuba a gareka ba kai ka nema a guna ba."
  "Bazaka iya yafemin ba Baba na?"
  "Baba inhar yafiya na kakeson ji toh ni na yafe maka duniya da lahira, Allah baka lafiya kaji? Gobe da sassafe zan shigo in shaa Allah."
  "Nagode d'a na Allah maka albarka ya baka ikon yin adalci a tsakanin 'ya'yayenka nan gaba."
  "Ameen Baba nagode, sannu kaji?"
  "Yauwa ina Yasmeen kuna kusa?"
  "A'a tana Kaduna bari incewa Mama ta had'aku."
  "Toh Babana nagode."
  "Sannu Baba, Allah baka lafiya" nan Mama ta d'aga wayar tare da cireta daga speaker phone. "Hello Ibraheem?" Cikin wani irin murya cike da tashin hankali dakuma tsoro da fargaba Ibraheem yace, "Mama what is wrong with him? Jikin nasa yayi tsanani haka ne?"
   "Ibraheem se addu'a."
  "Innalillahi! Mesa baki sanar dani ba tun d'azu ko a yau d'in in shigo? Mama mesa Baba yake magana haka?"
  "Ibraheem I don't know also" ta amsa hawaye na ciko mata a ido chan bakin k'ofa ta nufa tace, "Dr yace min chances na rayuwansa be kai 30% ba I don't know what to do Ibraheem." Shima Ibraheem besan a lokacinda idanunsa suka cike da hawaye ba "why didn't you tell me he is in a critical condition like this?"
  "Banason hankalinka ya tashi kai kad'ai na sanar wa hakan k'annenka duk basu sani ba."
   "Allah bashi lafiya Mama please take care of him."
  "I'll Ibraheem sekun shigo goben ka gaishe da Fateemah" anan ta katse wayar tana me share hawayenta. "Hafsah? Hafsah ina kike?"
  "Gani nan Alhj" tayi maganan tana dosan gabansa. "Hafsah Yasmeen fah? Ki had'ani da ita itama."
  "Toh Alhj" ba musu ta shiga trying line na Yasmeen sede sam bata samunta saboda d'anta bayi bar mata wayarta kullum cikin siyan sabuwar waya take dan kuwa sede Suleiman be gani ba seya jefata cikin ruwa. Atlast dana mijinta ta kirata anan ne ta same ta haka itama Baba yayi ta neman gafararta a yayinda take ta zuba kuka cikin wayan da k'yar ta iya fad'i mai ta yafe mishi itama. Tana ajiye wayan ta fad'a jikin mijinta tana kuka sosai, hak'uri yayi ta bata yana assuring nata in shaa Allahu Baba ze samu sauk'i and first thing tomorrow morning zasu wuce Bauchi.
   "All is going to be alright kinji Queen? Bar kukan haka ko kina son kisa Abba shima?" Kai zallah ta kad'a masa.
   "King Baba bashida lafiya I don't want him to die."
  "Subhanallah! Kiyi istigfaar wayace miki Baba ze mutu? Ze samu waraka in shaa Allah just have faith kinji?" Nan ma kai ta gyad'a mai. Pecking forehead nata yayi "tashi mu kwanta zuwa anjima mu tashi muyi Sallah mu rok'i Allah wa Baba koh?"
  "Thank you My King, I love you."
  "I love you more Queen tashi mu kwanta toh."

****
  Ibraheem kuwa tun gama wayansu da Mama ya kasa komawa d'akin se hawaye yake zubdawa tsili-tsili. Ahaka har Fateemah ta kwantar da Maamah sannan ta fito ta tsince shi zaune kan kujerar. A nitse ta k'arasa gunsa tare da kwantar da kanshi a dai-dai cikinta tana shafa gashin kansa to and fro. "Everything is going to be alright in shaa Allah Baba ze samu sauk'i Daddy'n Maamah lets just pray for him kaji?" Da k'yar ya iya mata nodding kai "he is in a very critical condition Momy'n Maamah ina ji ajikina bazan sake sa Baba a ido ba."
  "Shhh! Daddy'n Maamah please kadena fad'in haka, Baba ze warke in shaa Allah have faith okay?" Kai ya gyad'a da k'yar "tashi muje mu kwanta gobe da safe se mu wuce in shaa Allah."
  "Bakida lafiya, you aiint going."
  "Baba is like my own father, dole zan bika I love him as much as you do."
  "Thank you Fateemah I love you."
  "I love you also Daddy'n Maamah tashi muje mu kwanta na ciro maka kayan baccinka." A hankali ya miqe tare da kwantar da ita a jikinsa a haka suka isa d'akinsu suka gama shiri suka kwanta sede sam Ibraheem ya kasa bacci haka Fateemah ma ta zauna awake with him har lokacin da bacci yazo ya saceta. Gyara mata kwanciya da Maamah yayi sannan ya miqe yayo alwala ya shiga yin nafilfili yana taya mahaifinsa da addu'a.

*****
    Mama na gama shirin kwanciyar ta ta shimfid'a darduma a k'asa ta hau shirin kwanciya ganin haka Baba ya kirata, "na'am Alhj kana buk'atan wani abu neh?"
  "Ruwa nakeso Hafsah." Tashi tayi ta d'au masa Faro sannan ta rigingina kansa jikin gadon ta sa mai a baki tas ya kur6e ya sake neman k'ari.  A karo na biyun ma shanyewa yayi yana me sake neman k'ari. Hakan ba k'aramin tsoro ya sanya Mama ba saboda sau dayawa tana jin ana cewa wasu idan suka zo mutuwa ruwa suke sha kaman ba gobe. Batasan a lokacinda kuka ya ku6uce mata ba.

     "Hafsah ta kuma kukan me kike?"
  "Babu Alhj" ta fad'a da k'yar duk yadda taso hana kanta kuka ta kasa. Kanta ta d'aura a k'irjinsa "Alhj kasani ina sonka sosai, no matter what kaine mijina na nan duniya dakuma lahira, bazan ta6a mancewa da kai ba."
  "Masha Allah Hafsah ta nagode sosai kuma kisani nima ina sonki sosai daga ke har yaranmu ina sonku duka." Kukan ta cigaba dayi tama kasa amsa sa "toh kibar kukan haka mana, ko so kike nima inyi?"
   "A'a Alhj Allah baka lafiya."
  "Ameen Hafsah ina... ina Zeezee?"
  "Zeezee?!" Tayi exclaiming tare da d'ago kanta da jikinsa cike da mamaki.
  "Eh ita ina take?"
 "Tana gidan Mrs Mukhtar k'awata."
   "Gobe in Allah ya kaimu kice mata ta koma gida ta cigaba da zaman ta achan kinji?"
  "Alhj kana nufin ka yafe mata kenan?"
  "In shaa Allahu Hafsah, na yafewa Zeezee dukkanin abinda tamin nima inaso zuwa gobe idan suka zo duka dasu Ibraheem in nemi gafararta saboda itama ba laifinta bane Hafsah ni na 6ata mata tarbiyya. Su Mariam da ban 6ata nasu ba ai basu ta6a yomin abin kunya ba, itama Zeezee da ban 6ata nata tarbiyyan ba da dukkanin abinda suka faru basu faru ba. Da itama yanzu tana d'akin mijinta, meya fiye mata wannan? Ki ce mata tayi hak'uri ta yafemin don ni na yafe mata komi da bayyananne da 6oyayye duniya wa lahira kice mata I missed being with her, tell her she'll forever be my sister, I love her so much." Wani sabon kukan Mama ta sake rushewa dashi "in shaa Allah Alhj, gobe da kanka zaka fad'a mata hakan Allah ya kaimu kawai. Nasan ba wanda ze kai Zeezee jin dad'i a duniya gobe, saboda batada abinda ya fiye mata yafiyanka a gareta."
 
  "Naji dad'i na faranta mata, Allah yayi ma rayuwarta albarka ya bata 'ya'ya nagarin da zasu zo su kula da ita nan gaba ya bata miji na gari da kuma ze riqe ta amana ya rabata da sharrin dukkanin me sharri."
  "Ameen ameen Alhj nayi farin ciki matuk'a tun ba yau ba nake jiran rana kamar ta yau, ranar da hak'k'in iyaye ze tashi daga kan Zeezee." Murmushi kawai ya iya ya mata "Allah baka lafiya kaji Alhj? Kasani Zeezee na sonka sosai kuma tayi nadaman what she've made you gone through."
  "Ameen Hafsah nima ki gaya mata inasonta sosai."
  "In shaa Allah Alhj"
   "Masha Allah, baki k'aramin ruwan ba Hafsah."
  "Alhj gora uku be maka yawa ba?"
  "Beyi ba Hafsah k'ishi nake ji." Tana hawaye ta k'aro wani ta basa, rabi ya kwankwad'a sannan da kansa yace mata ya k'oshi. Gyara mai bargo tayi sannan ta miqe zata koma kan dardumanta da wuri yace, "Hafsah mu kwana tare anan." Cikin sautin kuka tace, "Alhj ai gadon nan baze d'auke mu ba kuma kaga bakada lafiya."
   "Karki damu ki taho mu kwanta tare kinji? Inason mu kwanta tare yau." Bata sake mai musu ba taje ta kwanta a gefensa a tak'ure.
  "Nagode Hafsah ta Allah miki albarka ya biyaki dukkanin abubuwan da kikayimin da gidan Al~Jannah."
  "Ameen Ameen Alhj."
  "Yauwa karki manta saqo na wa Zeezee fah? Kice mata Babanta ya yafe mata inason ta kuma ta koma gida da zama."
  "In shaa Allah Alhj ka kwanta kaji?"
  "Toh Hafsah Allah bamu alkhairi."
  "Ameen" ta amsa. Da mintoci kad'an Baba ya samu yayi bacci banda Mama da bacci ya k'aurace mata kwata-kwata. Imagining life without mijinta kawai take...

   MARIAM**** @11:40pm
   Wayarta dake ajiye a gefen tane ya shiga ruri wanda tana dubawa taga 'Dear' na flashing akan screen d'in, ba tare da 6ata lokaci ba ta d'aga "hello Sweetheart."
  "Na'am Dear" ta amsa tana sobbing.
  "Baki bar kukan ba har yanzu? Kiyi hak'uri kinji? We are in this together, in shaa Allah Baba ze samu sauk'i muna ta kan mai addu'a gobe in shaa Allah nima zan dawo."
  "Allah yasa, meetings naka fa?"
  "Nayi cancelling nasu already lafiyan Baba ya fiye mana komi."
  "Thank you Abban Ramlah I love you."
  "I love you more my princesses mother, ki samu ki huta kinji? Sena shigo goben."
  "Toh Allah ya kaimu."
 "Ameen, su Ramlah sun kwanta?"
  "Eh tun d'azu."
  "Kema ki kwanta kinji? I don't want you worried Baba will get well soon in shaa Allah."
  "Thank you ka huta gajiya."
 "Kema Sweetheart seda safe" anan ya jira ta katse.

   ZEEZEE**** @01:48am
  Juyi take tayi akan gadonta a yayinda taketa kuka kaman ba gobe. Tunanin mahaifinta kawai take, don kuka har sara kanta keyi mata tana gani dishe-dishe. ganin ba mahalicci se Allah kawai yasa ta miqe da k'yar ta d'auro alwala sannan ta shafa robe akanta don rage mata ciwon kan da takeji ta shiga yin nafilfili.

   *^*^*
  Sallah Ibraheem yayi tayi har pass 01 pm inda Fateemah ta farka tare da shafa gun kwanciyarsa taji wayan, hakan yasa ta miqe zaune anan ta gansa yana takan sallah. Itama alwalan taje ta d'auro tare da tada kabbara tayi joining nasa, hakan ba k'aramin farin ciki ta sanya Ibraheem ba.
 
  *^*^ Yasmeen ma haka k'arfe biyun dare mijinta ya tayar da ita sukayi alwala yajasu sallan nafila inda suka yita roqon Allah wa Baba.
   On Zeezee's side and Mariam ma haka ne sallan suke suma ba wasa.

•^••^•••^
    Yau Juma'ah k'arfe hud'u dai-dai Allah yayi wa Baba (Alhj Isma'eel Yusouf) cikawa, wanda mutuwarsa tazo masa cikin sauk'i a hankali a hankali Mala'ika ya d'au ransa wanda Mama dake gefensa tana bacci ma bata ji komi ba.
   Asuban fari Mama ta tashi ko ganewa gawan Baba ne a gefenta batayi ba saboda be wani kumbura ba cikin ikon Allah, murmushi ne kwance fal a fuskarsa. Bayan ta samu ta miqe ta miyar basa da bargon sannan ta zarce bayi tayi brushing tayi alwala sannan ta fito. Tana sanye da hijabi ta nufi kan gadon tare da zama a gefe "Alhj" ta kira sunansa a hankali.
  "Alhj tashi kaji tashi in taimaka maka kayi alwala kayi Sallah Asubah tayi." Shiru nan ma.
  "Baccin ne yayi nisa haka?" Ta tambayi kanta. "Alhj?" tapping nasa ta shigayi, ba k'aramin razana tayi ba ganin ko motsawa Baba baiyi. Hakan yasa ta matso da kunnenta dab da hancinsa dan jin futan nishi amman shiru takeji ba numfashi ba alamansa. Hannunta ta aza akan heart nasa cike da tsan-tsan tashin hankali don feeling heartbeat nasa, hukuncin da zuciyarta ta gama yanke mata na cewa Allah yayi wa mijinta, uban 'ya'yayenta cikawa ne ya mugun sa kanta ya sara. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta tana hawaye sosai. "Alhj! "Ta k'wala mai kira "Alhj! Don Allah kar ka tafi, innalillahi!" rungumesa tayi ta shiga sunbatu tana kiran doctors da nurses da muryan da Allah ya bata.

   Ahaka ne har wata nurse tazo ta sameta, da wuri ta je ta kirawo Dr'n daya duba Baba jiya, da k'yar nurses suka samu suka fita da Mama waje inda take ta leqe ta window tana kuka sosai. Dr na duban Baba ya kad'a kai ba amfanin basa pulse saboda har ya gano d'an kumburin da Baba yayi, tests kad'an suka yi akansa dan gano time of death nasa which was exact by 4:02am today being Friday (babbar ranar da Allah ke yafewa dukkanin bawansa da ya rasu a ranan tambayoyin kabari, Allah yasa Baba yayi mutuwar shahada, yasa k'arshen wahalarsa kenan. Allah ya dubi girman tuban da yayi ya yafe mai k'urak'uransa yabasa gidan Al~Jannah ya kyautata mana k'arshen mu yasa mun d'au darasi daga rayuwan Baba mu bawa 'ya'ya'yen mu tarbiyya na gari, AMEEN.)

   Tun da Mama ta hango ana rufe fuskan Baba da k'yalle tasani shikenan Baba ya tafi ya barta. Wani irin kuka ta sa tana sauk'a k'asa a haka Dr ya fito ya tarar da ita. Kansa a k'asa yace, "am so sorry Ma'am theres nothing we could do, mijinki ya riga ya cika tun wajen k'arfe hud'un dare, fatan mu Allah yasa ya cika da imani ku kuma Allh ya baku hak'uri, verily every soul shall taste the pain of death, I'm sorry" yana kaiwa nan ya fice. Nurses d'inma one by one sukayi wa Mama ta'aziyyah sannan suka fice. Ta d'au about 10 minutes a wajen tana kuka sannan daga bisani ta miqe ganin kukan batada wani amfani, ta koma cikin d'akin ta idar da Sallanta cikin natsuwa, tagama tofe addu'o'inta sannan ta ja kujera ta zauna kusa da Baba tare da yaye k'yallen da suka rufe mai fuska dashi. Hawaye ta soma a hankali se ji take kaman idan tayi mai magana ze amsa ta, ya kira sunanta kamar yadda ya saba. Wani irin zafaffun hawaye ta shiga kwararowa "ina sonka Alhj, amman nasan Allah ya fini sonka shiyasa ya d'auke ka ya kaika kusa dashi, Allah yasa mutuwa hutu ce a gareka, kasani ban ta6a nadaman kasancewa dakai ba, Allah ya had'a fuskokinmu a gidan Al~Jannah ya tura rahamarsa kabarika, Ameen"

    Mama ta d'au mutuwar Baba as k'addara ta kar6esa hannu bibbiyu, sam batayi irin haukan nan da wasu keyi idan anyi musu rasuwa ba, suna suratai suna cewa sun mutu sun lalace. Kukan zafin rabuwa bayan an zama d'ayan daya zama dole kawai tayi bayan nan tayi masa Addu'an da akeyiwa mamaci sannan ta biyosa da dukkanin addu'o'in data sani akanta ta tofe masa. Bayan nan da kanta tayi mai wanka ta suturcesa, har anan ba wanda yaji rasuwan Baba.

   Ibraheem Mama ta d'aga waya ta soma kira, lafiya sumul suka gaisa inda yake sanar da ita yanzu haka ma sun gama shiri zasu kama hanya.
   "Ibraheem ina son ka saurareni da hankali a matsayin ka na babba cikin yarana da musulmin da aka sani da tawakalli, kasani cewa duk wani me rai mamaci ne." Tun anan jikin Ibraheem yayi sanyi jira kawai yake yaji Mama ta furta mai abinda ransa ke ta raya masa.
   "Ibraheem Allah yayi wa Babanku cikawa yau da daddarre wajajen k'arfe hud'u."
   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya furta a hankali a yayinda idanunsa suka kad'a sukaji ja zirrr lokaci guda.
  "Mutuwa abu ne me zafi amman yazama dole muyi tawakalli mu rungumi k'addara, dukkanin me rai mamaci ne kaman yadda Babanku ya tafi muma wataran turn namu zezo. Sekun shigo, da sallan juma'ah a nan Gwallaga za'a sallace shi, Allah yasa mutuwa hutu ce a gareshi."
  "Ameen" kad'ai ya iya furtawa tare da yasar da wayansan a k'asa. Hakan yayi dai-dai da shigowar Fateemah don sanar dashi breakfast is ready sede ganin idanunsa ta gane cikawa mahaifinsu yayi. Itama take idonta suka cike dam da hawaye da gudu taje ta samesa tare da hugging nasa nan suka fashe da kuka sosai abin tausayi ba na miji ba mace.


  Hajiya (maman Baba) next Mama ta kira ta sanar da ita inda itama tayi salati tare da sa kuka sosai. Yasmeen ta gama yima Suleiman wanka ta shigo dashi riqe a hannu sannan ta ajiye sa kan gado ta kira sunan mijinta dake maqale da waya a kunne da "King, Wankan fa sauran kai." Kasa juyawa ya kalleta yayi bayan sanar dashi mutuwan Baba da Ibraheem yayi. "Abban Suleiman?" Ta sake kiransa "zamuyi latti fa." Yana kaffa-kaffa ya juyo a hankali emotion dake fuskarsa kad'ai says it all.
  "Abban Suleiman is something wrong? Why the face?"
  "Yasmeen" ya kirata a hankali tun anan jikinta ya bata Baba ya rasu ne kai ta shiga kad'awa "no no don Allah kar ka cemin Baba ya rasu please don't" gudu tasa zata bar d'akin sede kafin nan mijinta yayi sauri ya jata tare da forcing nata ta kwanta a jikinsa.
    "Sshhh he is in a better place in shaa Allah." Kuka take sosai tana sumbatu "he can't die please ka fad'amin wasa kake be mutu ba."
  "Yasmeen kiyi hak'uri Baba lokaci yayi Addu'an mu yake buk'ata ba kukan nan ba kiyi hak'uri." Ai kaman sake tunzirata yake ta kasa barin kukan ganin haka Suleiman ma ya sa kuka.


  Mariam ta gama shirya Ramlah school, Ummie kuma day care text message from Ya Ibraheem ya shigo wayarta tana kai dubanta taga biggest suprise of her life salati kawai ta saki sekuma aikin kuka, makarantar da yaranta basu jeba kenan ranan. Ko kiran da mijinta ke mata ma ta kasa picking se kuka kawai. Hakan yasa Ramlah da Ummie ma kuka, se hak'uri me aiki ke bata amman ina abin ya gagara.
 
   Zeezee was the last person to come to know about thier father's death.






* MIEMIEBEE.      TEAM #YGCπŸŽ€*
   Beeenovels.blogsot.com
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

9 comments:

Unknown said...

Inalillahi waina ilaihirajiun wif lost of tears rolling down my cheeks nd hrt full of emotion may ur soul rest in jannah baba luv ya. Enx sis, buh we prefer the other version, anyway dat nt it we will talk more abut dis version after mornin baba. Enx once more sis

Unknown said...

Innalillahi wa Inna'ilaihi Raji'un
kamar gaske haka na dunga kuka da hawaye ina namiji dani na manta cewar labari ne ba gaskiya ne ba.

Unknown said...

😭😭😭wlh harda kukana
Wayyoo baba

Unknown said...

eyyah allah sarki ban zee zee even we readers hv missed uh alot tnx miemie allh kara basirah

Unknown said...

miemie plz move forward i just wanna knw zeezee's action i pity her lot

Unknown said...

Ayyah, It's a pity on zeezee for her to hear this sad story. Please Miemiebee were not coping well with this new version, we'll rather prefer the older version that normally shows each post separately. Thank you, more ink to your pen.

Mahmah said...

Oh my goodness, zeezee will never forgive herself, she will blame herself for her father's death, i was crying as if though ni akawa mutuwa. Thanks alot miemie keep it up. 😒😒😒

Unknown said...

yes@zainab abbakar we prefer d old version

Unknown said...

Wayyo baba Allah ya jikanka da rahama, zeezee will blame her self for this death. Tnx sis, I prefer the old version