BY MIEMIEBEE
PAGE 41
Febuary 2017
_One week later..._
Da dawowan su Zeezee from Florida one week kenan. Tun dawowansu Mami ce ta d'auki nauyin kai musu breakfast, lunch and supper, tayi haka na sati na marmari wato itama ta gaji.
Yau da safe bayan su Zeezee sunyi wanka fes sun shirya sukaji shiru fa yau ba alaman Mami zata kawo abinci ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga kitchen ta musu frying chips da omalet komi yayi suka karya. Sun gama breakfast Adeel ya fita ya rage Zeezee kad'ai a gida, chatting suke da Lubiee ganin Lubiee nason cika mata kunne yau ma da zancen da bayi wuce na bata kyautawa Ya Al'ameen ba ta kashe datan nata ma gabad'aya. D'an goge-goge tayi sannan ta sake wanka tahau jiran dawowan Adeel. Bata aza girki ba a tunaninta in Mami bata kawo musu ba shi Adeel ze siyo a hanyan dawowa gida shiko Adeel tunda Mami bata kawo breakfast ba it shows that ba lunch kenan dole Zeezee zata yi musu girki don shi ya gaji da cin abincin waje he is fade up with it. Kusan 2:15pm ya dawo gida as always tayi welcoming nasa da kisses and hugs. Kasa 6oye mar yunwan da takeji tayi ta tambaya a hankali "Very Own baka siyo mana lunch ba?"
"Sayan lunch kuma? Baki gaji da cin abincin waje ba kullum nikam am fade up, Mami bata kawo ba?" Kai zallah ta kad'a mar. "Wow meaning ta gaji kenan so da kikaji shiru you didnt cook anything for us? Am hungry."
"I didn't, I thought zaka siyo mana its what Ya Al'ameen normally does" ta fad'a a hankali ashe kuwa ya jita.
"What?!" Yayi maganan a fusace "Ya Al'ameen kowa kika ce?"
"Very Own calm down" ta gwada rik'e hannunsa ja yayi da k'arfi "seki je ki samu Al'ameen d'in tunda shi haka yakeyi bullsh*t kawai a gidana kina kiramin sunan wani mschww!" A fusace ya miqe ya shiga d'aki tare da shutting door d'in gbam! Hawaye ta shigayi a yayinda take binsa da kallo. Share hawayenta tayi tabi sahunsa "thank god" ta furta a ranta jin besa lock ba, miqe kan gado yana fuskantan ceiling yana chatting ta samesa wanda yana ganinta yawani juya mata baya. Har gabansa tajeta ta zauna bakin gadon sede banza da ita yayi tamkar besan da halitta gun ba.
Da abun ya isheta a maraice tace, "Very Own am sorry please don't be mad I didn't mean it in a bad way" har anan be tanka taba "am sorry kaji I can't take it you being mad it wont ever happen again kayi hak'uri" anan ne yayi gefe da wayan yana kallonta "pleaseee..." tayi pleading se anan yayi magana "its okay" yace da ita. Dad'i taji sosai wanda koda Allah yi miki albarka Mama tace mata baza taji kalansa ba "you are no more mad?"
"Am not" ya amsata cike da ji da kai. Kwanciya tayi a jikinsa "I love you so much Adeel."
"I know Babe and I love you too." Sun jima a haka sannan ta d'ago a hankali "so me zakaci?" Seda yad'an 6ata lokaci yace, "spaggetti da minced meat akai." Anzo wajen tace a ranta tunda take bata ta6a girka jollof na spaghetti ba ina ma fari yace seta masa heating stew na jiya so take tace masa zata dafa musu fari amman tasan halinsa yanzu seyace ta raina sa tana gaya mai abinda zeyi. "Kinyi shiru Babe am starving."
"Uhmm I was carried away by something don't worry gimmie an hour" pecking nata yayi lightly a lips sannan ta miqe ta fice.
A kan centre table dake parlour ta d'aga wayarta tare da kiran Lubiee dan guiding nata kan ya ake dafa spaghetti.
Seda Lubiee tamata iskancin duniya sannan tayi agreeing zatayi helping nata out haka da prescription and describtion na Lubiee ta samu ta dafa sede gardaman da tayi mata, Lubiee ta bata amount na maggi da amount na red sauce sam tak'i ji ta k'ara nata akai abincin yayi wani irin d'an banzan zak'i da yaji seda ta sauk'e ta d'ana taji tukun "omg!" Ta fad'a tare da kiran Lubiee.
"Babe am dead I should have listened to you wallahi abincin yayi zaqi da yaji over what am I gonna do?"
"I told you."
"Shut up and give me a solution" ta katseta a fusace.
"Jimin mata nina 6ata miki girki ne kike neman had'iye ni sede kuci haka kokuwa ku hak'ura."
"Awww ma haka zakice good!" kafin Lubiee tayi magana Zeezee tayi hanging. Eating up nails nata ta shigayi totally out of idea ta zubar ne ta girka sabo? "Kai! It will take long Adeel can't wait for long me zan yi to?" Ba kalan karkataccen shawaran da bata bawa kanta ba amman duk it aiint working daga k'arshe tace kawai zata zubar ta girka sabo zat using ruwan heater. Ta kaiga d'aukan tukunyan kenan Adeel ya fad'o kitchen yunwa yaci maza mehn!
Firgita tayi har tana neman cin tuntu6e "Babe easy!" Yayi exclaiming "abincin beyi bane? am starving" yayi maganan hannunsa rike da cikinsa.
"Uhm... Ermm..." Ta shiga kame-kame next abinda taji kawai hannunsa akan nata yana neman amsan tukunyan kafin tayi wani k'wararren motsi har ya amsa ya aza kan cooker ya bud'e. A ido abincin soo yum! Yum! Gabad'aya yawunsa ya tsinke ga k'amshin curry'n dake tashi. Fork kawai yayi grabbing shi bek'i yaci a tukunyar bama.
"Ade-" kafin ta qarisa kiran sunansa harya kai baki within seconds count kamannin face nasa ya sauya, kansa ya juya ya zubar dana bakin nasa a sink sannan hurriedly ya nufi dispencer ya tsiyaye ruwan sanyi ya kora yajin dashi duk anan binsa Zeezee ke da kallo tana kakkarwa tana jiran masifa kawai. Seda ya kora yajin hankalinsa ya dawo dai-dai tukun ya nufi gabanta "what is this?" Ya tambaya a tsawace. Shiru tayi danko batasan na cewa ba
"Yes... Am talking to you what is this? Dagangan kikayi kome? Saboda you weren't in the mood to cook, is that it?"
"No Adeel ba-"
"Then yayane?" yayi saurin katseta still a tsawace, tana shaking hawaye na forming a idonta tace, "am sorry ban iya girkin bane this is my first time." Dala-dalan idanunsa ya zaro waje unbelievably "like seriously?" ya tambayeta still not believing. Kai tayi nodding a hankali. Dariyan rainin hankali ya saki "LOL baki iya girki ba? And you call yourself a lady? How is that even possible? Me amfanin auroki danayi then if you cant make me a dish inci?"
"Ver-"
"Shhh!" Ya katseta "dont Very Own me kingannin nan bana wasa da cikina you know that inhar you cant make me a meal to eat then bazamu shirya dake ba inada mata I can't depend on buying meal always a waje its two of one, its either ki koyi girki or I should figure out what to do with you." Tana share hawayenta tace, "like how figure out what to do with me Adeel?"
"Yes Zeezee you give me no choice how can I depend on buying food always bayan I have a wife?"
"To da ban iya bafa?"
"Seki koya its never to late."
"Adeel in cire kud'i ne baka sonyi I have lots of money zan na saya mana."
"Owww haka kuma table d'in yayi turning into? Ni zaki nunawa kinada kud'i? You mean to say banida kud'i kenan right? Saboda kinga kina hawan wancan so called Ford jeep ko? For a record kisani Genesis G80 na yafi naki taada way much its just the size, you've got some nerves you know" ya k'are maganan yana watsa mata harara. Gabad'aya hankalinta ya tashi se hawaye kawai take "omg! Adeel yaushe nace haka? Thats not what I mean believe me."
"Oh you're even asking me again? Kin kyauta bravo super woman" be sake jiran jin me zatace ba ya fita yabar mata gidan gabad'aya. Har k'asa ta sauk'a tana kuka gun tafi minti ishirin se tuna time da Mama zatace mata tabi Yasmeen kitchen tana ganin koda abinda takeyi ne amman haka zata ki ga irinta ai yanzu girki nason shiga tsakaninta da Adeel nata, kukan ta cigaba dayi seda tayi me isarta ta sake aza sabon tukunya tana cikinyi ta manta wani step again ta kira ta tambayi Lubiee kuma bataso ta 6ata mata rai d'azu haka tayi kwa6an ta shima bayi cuwuwa. Tana kuka ta zuba duka a leather bag ta zubar a dustbin sannan t had'a golden morn tasha.
Har 5pm Adeel be dawo ba, wayarta taja ta shiga kiransa haka har ta tsinke bai d'agawa haka ta rufe kanta a d'aki ranan ta yini tana kuka. Abu fa kaman wasa har 8-9-10 kai har 12 na dare Adeel be dawo b gashi yanzu ma kwata-kwata kashe wayan nasa yayi. Ba inda Zeezee batasa kanta ciki ba gabad'aya baccin dake idonta ya watse tayi kuka har ta godewa Allah. A parlour bacci ya risketa se 6:30am ta tashi nanma bataga Adeel ba. Ta shiga d'akinsu donyin alwala taji kaman motsin mutum a bathroom in seconds count k'ofan ya bud'u revealing Adeel, binsa da kallo ta shigayi ma'ana ya dawo ya wuceta kwance a parlour be damu ya tadata ba koya d'agota ya kawo ta ciki ba kenan. Ganin kallon bana k'arewa bane ya d'aga towel dake a wuyansa ya shiga goge gashin kansa ahaka har yazo ya wuceta ya nufi wardrobe yana neman kayan sawa. Guiwowi suna kakkarawa ta juyo direction nasa sannan cikin wani erin murya me nuni da tsan-tsan damuwa tace, "Adeel ina ka kwana jiya?" Banza da ita yayi yana me cigaba da harkan gabansa.
"Adeel am talking to you" yanzu kam ta soma hawaye.
"Somewhere better than here" ya amsata in an I-dont-care tone.
"Baka fa kwana a gida ba Adeel, I waited for you for so long har kusan 1am baka shigo ba."
"Ke kika so dan ni bance ki jirani ba" anan ya ciro kayan da zesan ya juya kenan da gudu Zeezee taje ta fad'a jikinsa tana wani irin kuka me tsuma zuciya, hugging nasa gagam tayi se kukan take, kayan nasa ya wulla kan gado amman yak'i hugging nata back. Tana kukan ta soma cewa;
"Adeel am sorry, am so sorry dan Allah kayi hak'uri that wasn't my intention please stop being mad in girki kakeso na koya I'll but stop staying mad please I beg you..." Ta k'arasa da kuka kaman bazeyi hugging nata ba sekuma ta basa tausayi shi kansa yasan punishment daya bata yayi tsauri, a hankali ya d'aga hannayensa ya zagayesu a bayanta tare da sake kwantar da ita a jikinsa "its okay stop crying am sorry also just dont try it next time okay?"
"I wont, ever."
"Shikenan toh bar kukan" a hankali ya samu tayi shirun sannan y d'agota daga jikinsa tare da share mata hawaye "is okay, kinyi Sallah?" Kai ta kad'a as a response.
"Jekiyi toh."
Zaka sake fita ne?" Ta tambaya a hankali cike da damuwa.
"I was amman na fasa yanzu" with a nod ta nufi toilet tayi alwala tafito tayi sallah. Koda Adeel ya koma bacci ita ta kasa as tana tunanin ya za'ayi ta koyi girki daga k'arshe ta yanke hukuncin registering online cookery class.
****
By 10:30am su Zeezee suka gama breakfast yauma chips tamusu frying da scrambled egg. Suna zaune a parlour Adeel na kallon sports whereas ita tana chatting tayi focusing sosai se murmusawa take da alama tana enjoying chat da take. Catching her always for 3 times tana murmushi Adeel yayi deciding daya tambayeta dawa take chatting.
"Babe who are you chatting with?"
"Its no one" ta amsa a takaice chan tace "just a friend."
"Gender?" Ya tambaya a take.
"Oh calm down Adeel childhood friend d'ina nefa kawai."
"Amman ban hanaki chatting da maza ba?"
"Ad-"
"Yes or no?" Yayi cutting nata off.
"No I mean Yes but-"
"Pass me your phone" ya buk'aceta "Adeel this isn't fair kaima fa kana chatting da female friends naka amman ni just this once ma bazaka barni ba" tayi explaining a nitse.
"Owww you're comparing us kenan pass me your phone nace" kaman bazata miqa mai ba kawai ta basa ta tashi ta bar mai parlourn ma gabad'aya a zuciye ta nufi d'akinta. Warning ya kashe wa friend natan sannan ya goge contact nasa daga wayar tata gabad'aya. Seda Azahar ya lek'a d'akin nata yaga tana bacci, wayar kad'ai ya ajiye mata kan dressing mirror sannan ya k'arasa yayi positioning nata tare da pecking nata ya fice yawonsa.
Da La'asr da Zeezee ta tashi bayan tayi Sallah ta leqa waje as expected bata ga motansa ba. Ita ta rasa ina yake zuwa kwana biyu kullum bai gida. White macaroni da sliced carrots and peas ta dafa musu sannan tayi heating stew na Mami ta had'a dining table. Ganin har 4:30pm be dawo ba ta d'iba nata taci, ba Adeel ya dawo gida ba se Maghrib. Sun idar da Maghrib in a soothing manner ta tambayesa yadda baze fusata ba "Very Own nace d'azu ka fita baka sanar dani ina zaka ba."
"Yeah na shiga naga kina bacci, I visited a friend." D'an sanyi kad'an taji a ranta "ohh okay then" dining suka nufa sukaci abinci suna hira, sun gama Adeel ya nufi bayi ya watsa ruwa se gani tayi ya ciro kaya da alama fita yake da niyan yi. Zama tayi a bakin gado tana binsa da kallo tana ganin supras da ya zaro ta gano party zasa. Zuciyarta ne ya mugun fad'i yanzu Adeel yana nufin da igiyan auranta akansa zena fita midnight party? Yaushe Al'ameen ya ta6a yi mata haka? Shin da ba kyautata masa ma take ba. Yana gama turare jikinsa ya doso gabanta tare da pecking nata a cheeks "Babe zan d'an fita I'll be late so sleep early, I love you ahh! Meds naki" nan da nan yaje ya 6allo ya bata sede tak'i amsa.
"Sweetest Love kina 6atamin time fah I'll be late, kar6i mana."
"Late? For the party?" Kaman da ze mata k'arya sekuma ya fad'a mata gaskia "yes."
"Very Own yanzu party zaka fita da daren nan baka ma san lokacin da zaka dawo ba kana ganin ka kyautamin kenan?"
"What gibberish are you saying Babe? Its not as if I'll be gone forever zan dawo zuwa gobe ina?"
"Nikuma hak'k'i na a matsayi na na matarka fa?"
"In hak'k'in ki kikeso ai akwai gobe sena baki gobe take ur meds please."
"Bazan sha ba." Ta fad'a in a low tone.
"Kikace?" Sanin ta sake nanata abinda ta fad'a suna iya yin fad'a kaca-kaca tace, "nothing" tare da amsa ta had'iye haka tana ji tana gani ya fita yabar gidan. Jin moisture kawai tayi akan fuskanta, tana ta6awa tajiyo hawaye. Kuka ta shigayi sosai Allah sarki seta tuna Al'ameen inhar baya gida toh yana office ne in ba haka ba kullum yana gida dukda bawai farinta masa rai take ba amman hakan besa kullum yana fita waje ba. Seda tayi kukam me isarta sannan ta watsa ruwa finally ta kwanta da k'yar bacci 6arawo ya sace ta.
**
6:34am the following day Adeel ya dawo gida sid'ak-sid'ak ya nufi d'akinsu ya rage kayan jikinsa sannan ya haura gado ya sameta suka kwanta se pass 9 ta tashi ko da ta gansa a gefenta batayi ta kansa ba. Wanka tayi ta had'a musu breakfast bata jirasa ba tayi nata. Se pass 12noon Adeel ya tashi yayi wanka yafito parlour inda ya tsinceta tana goge TV stand. Idanunsu na had'uwa tayi saurin kawar da kanta daga direction d'in danko har yanzu bata sauk'o daga abinda ya mata jiya ba. Shima d'an rainin hankali ignoring nata yayi ya nufi dining ya karya wanda yana cikin yi yaga Zeezee ta nufi d'aki bayan mintuna kad'an ta fito all dressed up. "Ni zan fita zani gidansu Lubiee."
"Kuma da izinin waye?"
"Kaman ya da izinin waye? Am letting you know." Ganin ranta fa a 6ace yake ya tashi ya nufi inda take tare da patting both shoulders nata. "Are you still mad Baby?" Banza dashi tayi, gyalen data ruhu dashi ya cire a hankali ya ajiye a gefe sannan jakar nata "kin fasa kar6an hak'k'in kine?"
"Nafasa banaso you are wasting my time please." Ta fad'a ba tare da ta kalli direction nasa ba, hannunsa ya aza kan face nata yana rubbing in a romantic way "haba mana Sweetest Love it was a friend's birthday I can't miss it for the world amman trust me I didn't touch any girl there." Se anan ta kewayo da idanunta kansa "how do you expect me to believe that?" Wani mayen kallo yake mata yana lasan lips nasa, "like this" ya amsata kafin ta gane me yake da niyyan yi kawai taji ya d'agata sama a hannunsa just like a bride. "Keep me down Adeel banas-" her last word was crashed on his lips. Kissing nata ya shigayi wanda tun tana neman turesa seda tayi giving in atlast. D'akinsu ya kaita tare da direta kan gado anan nikuma na basu privacy.
****
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa, Adeel da Zeezee basu ta6a yin good two or three days basuyi fad'a ba as yakasa dena zuwa midnight parties, abinda Zeezee tafi tsana kenan fiye da komi. Ita kuwa ko gidansu Lubiee tace zata se yayi ta mata corner-corner at last ya hanata zuwa. Rayuwar aurenta de yabar mata dad'i a takaice, ita she is trying her possible best to make him happy amman it aiint working. Ga massive improvement a girkinta duk don su zauna lafiya amman abu ya gagara, kuma ita harga Allah ta gaji yanzu is like sex machine Adeel keson maidata kullum baya gida da zaran ya dawo kuma har ya sake fitan yana kanta, tagaji ita shikenan batada wani amfani mai se desire or need nasa ya taso abin yafara isarta.
Yau ma kaman kullum bayan Adeel yagama biyan buk'atansa da ita ya tashi yashiga bayi ita tana nan miqe kan gado har yanzu. Few minutes afterwards Adeel ya fito da towel d'aure a waist nasa yana goge gashin kansa. Mutum d'aya ne ya fad'o mata a rai which is none other than Al'ameen, se tuna how muscular and builded up his body is take, packs gasunan a fili har shida, she misses staring at his naked body.
"Tunanin me kike haka?" Adeel dake neman zama akan stool yayi maganan da man shafawansa rik'e a hannunsa. Kai ta kad'a da wuri "babu" tamai k'arya "you seem carried away."
"Erm Adeel nace da bikin mu how many months now ya kai six?"
"Six I guess, yes six months... One week... Three days exactly today."
"Kana ganin lafiya kuwa?" Tayi maganan not sur of her words.
"As in?" Ya tambayeta da sauri.
"Very Own its been six months amman ko 6ari ban ta6a yi ba." Ita dariya ma tabasa wai dama bayan magunan da yake bata take ta sha ba fashi how can she get pregnant?
"Adeel you are laughing." Ta fad'a da mamaki.
"Yes I am" ya amsa confidently within laughter.
"Its no joking matter Adeel, matarka maybe cannot concieve kai kuma kana dariya?"
"Not so fast wai ke dama you are ready to be a mother ne?"
"What are you talking about Adeel? Daman meye amfanin auren badon a haifafa bane?"
"To some not to all." Yana kaiwa nan ya miyar da man ya nufi wardrobe yana fiddo da kayan da zesa.
"What do you mean Adeel?"
"I mean am not ready yet to be a father am still young for God's sake Zeezee am just 26 going to 27."
"Adeel wani irin magana kake haka? 'Yan 20 ma sukayi aure suka haihu bale kai? You mean to say you are happy that maybe I cannot concieve kenan?"
"Your words not mine" yasa kayansa sannan ya nufi gaban dressing mirror yana taje gashin kansa yana cikin yi wayansa dake kan side drawer yahau buzzing. Kasancewar Zeezee na akan gado tayi saurin leqawa sede kafin tagama karance wake kiran fyayi sauri ya d'auke wayar.
*MIEMIEBEE*
www.beeenovels.blogspot.com
๐๐๐
23 comments:
thanks alot dear
Tnxs....dear Nice piece.Buh u av twisted d whole thing am nt enjoying it....Y adeel nt al'ameen....istandwidal'ameen...LoL
Welcm back dear....thats like our miemiebee๐
Godia muke sis Allah ya kara basira,
Hmmmmmmm...,daman rayuwa haka take, tana maka sakayya ne da son ma ranka what u damn think is gud for ya! Later will u come to realise u're making a huge mistake in ur life... Hmmmmmmm,"Ya Allah, ka danne mana zukatarmu ta farken son ma kanmu ba dai dai ba a rayuwa! Ameen". As for Zeezee, saidai Kawai mu taya ta da Adu'a, Allah shi rabata da wannan rayuwar da tayi masa daurin Infinity Gele a kanta,da bayi da niyar kufce mata.
Ameen!!! ��i'm sad though,for all that "'YAR GATA"is going through! Duk da cewa bata kyauta wa fmly dinta ba, akwai fa tausayi yanzu ma Zee... Thumbs up��and a 5star for this novel, quite one of the best novels of Miemie i liked. Allah shi k'ara maki Hikima da Basira ki ci gaba mana with the story. Ameen
Wlh zeezee tausayinta nafara yanzu
Allan yasa halayen adeel ya a idonta tasan wane shi and bana mata fatan tama samu ciki dashi gara takoma wurin maj-gen
Amma b4 then gara adeel yamata kaca kaca tasan meta aikata a baya was all wrong and pls kada asa alameen yayi aure gara yajira zeezee aftr taji jiki wurin Adeel
Wallahi dai nima haka nake son komai ya kasance...By then ta tuba. Allah shi ganar da ita dai
Eh wannan ma yayi daidai da ita...ai daman sai masara yaji wuta yake ihu��. Yanda adeel keyi mata daidai kenan, serves her damn ryt... Gobe kusa! Da koda an nuna miki(Zeezee) adeel a lahira ba zaki ji ki so shi ba.
Yauwa yar gari
anayi muna jin dadin anzo gurin labari ya fara mun dadi
..Ni kam ba haka naso ba....naso ace saki dayan da maj-gen ya mata ta gasu a gida amma ba ta auri Dan kwalta ba....thou dae itama yar kwaltar ce....Lol
Nd by the way kudos...to ya Sis u re doing damn well.....
Ai gara da ta auri adeel bagashi har ta fara sanin muhimmanci iya girkiba, gidan adeel ne daidainta.........Allah ya kara basira muna jira nxt plsssssssss
Ai gara da ta auri adeel bagashi har ta fara sanin muhimmanci iya girkiba, gidan adeel ne daidainta.........Allah ya kara basira muna jira nxt plsssssssss
Gaskia ne wannan
Yar kaniyar uwa๐น๐น๐น an gaya mata gayu da daukan shit ne
Haka Kuwa Maganarki Take
Baes...u funny..Hhhh
Muna jira sis
Wallahi
Wallahi
Post a Comment