Sunday, 5 February 2017
‘YAR GATA CE!
*BY MIEMIEBEE*
*PAGE 42
*Febuary, 2017*
_I'm hereby honouring this page to none other than my *BLOG FOLLWERS AND READERS* thank you for making it a lit๐๐พthere, it was impossible before but with you its now possible. Thank you so much for your inspiring comments, love and care! Am proud to have and know you guys, I love y'all oceans and galaxies❤❤❤ #OneLove❤_
“Kekuma mena leqa min a waya?” Yayi maganan yana duban wake kira.
“Inga wake kira is it a crime?”
“It is banason shisshigi“ zata sake magana ya aza hannunsa bisa lips nasa nufin tamai shiru, shirun tayi tana kallonsa. A nitse yayi picking call d'in “Halo?” Ya fad'a cikin sanyin murya. K'ure kunne Zeezee tayi donjin muryar ta mace ce kona miji aikuwa taji a lady's voice. Take gabanta ya fad'i sede ta kasa jin me matar ke fad'a and after a while Adeel yayi responding da “okay am on my way, see you” tare da hanging. Dnqaree!
“Who is she?” Ta tambaya zalla cike da kishi
“A friend koda me kikeson ji?”
“Adeel you are lying wacece ita?”
“A friend ha'a nifa banason tak'uri dayawa sekace wata Boss d'ina kina asking d'ina questions.”
“Da kyau, yanzu bayan ka gama biyan buk'atanka dani zaka barni kaman kayan wanki kaje ka samu 'yan matanka a waje right?”
“Kanki akeji ni banida time na small talks d'innan” bata sake cemai komi ba har yagama feffeshe jikinsa da turare ya fice dan kuwa Adeel mamaki yake bata yanzu. Hawaye kawai taji yana bin k'uncinta she have to find out ko Adeel dagaske ne yayi budurwa a waje amman kafin nan meyake nuf'i d'azu dayace "am not ready to be a father?"
“Oh God no!” Tayi exclaiming cike da tashin hankali “what if... What if... No it cant be possible Adeel baze ta6a bani abinda ze cutar dani ba.” Degree of rolling tears nata ne ya k'aru “what if he did?” Hannu tasa ta miyar da gashinta baya tare da jan vest nata dake kan gadon tasa sannan ta miqe all confused. Wardrobe nasu ta nufa ta bud'e side nashi, ita kanta batasan me take nema aciki ba amman haka tayita searching tana duba cloth after cloth chan a last counter ta zaro kwalayan maguna guda biyu sunan ta karanta ta sake miyarwa.
After a while ta sake zaro su tare da jan stool ta zauna, jikin kwalin ta shiga karantawa to her biggest suprise tagano maganin hana d'aukan ciki ne. “Innalillahi wa inna ilaihi raji'un this can't be true” fito da capsules d'in tayi har 6ari hannunta ke don tabbatar da zarginta aiko tana 6alla d'aya ta tabbatar shine maganin da Adeel yayi ta bata for the past 6 months ba fashi.
Hawaye kaman lalacaccen famfo se fitowa suke ba makawa. Kuka tayita yi abin tausayi what have she ever done to him to deserve this? Mesa be fito fili ya gaya mata bayason haihuwa ba yaso seta fara family planning amman yayita d'ura mata maganin da she is sure yanada side effects. Ashe dama back then daya ta6a ce mata suyi eluding suje suyi aure and have their own kids was all a lie, tabbas na miji ba d'an goyo bane. Yanzu shikenan ita bazata ta6a ganin jininta ba kenan? “Ashe Adeel never loved me he was just after my body and thats all, how could you Adeel?” Ta tambayi kanta cikin tsan-tsan takaici da nadama. “I regret it, I regret every single bit of it, I shouldn't have gave my pride to you Adeel, ba kai ka cancanta ba Ya Al'ameen ne ya cancanta. Why didn't I thought of all these before? Adeel was never my true love Ya Al'ameen is nasan komin meye nayi wa Ya Al'ameen baze ta6a 6ata min rayuwa as how Adeel did ba. Shi d'inda ban ta6a kyautata masa ba, ban ta6a yimai abinda yakeso ba amman dai-dai da rana d'aya be ta6a cutar dani ba, hasali ma kyautata min yake akan wulak'anci da zagin da nake sak'a mishi dashi. Oh! Allah na tafka babban kuskure na auran Adeel, Ya Al'ameen please forgive me nasan alhak'inka ne yake bina” ta k'are maganan tana kuka me tsuma zuciya. Tafi minti ishirin zaune gun tana kuka sannan daga bisani ta nufi bayi tayi wanka cikin k'ank'anin lokaci ta shirya tsaf cikin doguwar riga tad'au kwalin maganin ta fita dashi.
Asibiti direct ta nufa ga layi kaca-kaca amman haka tayi zaman jira har seda turn nata ya iso that was around 3:12pm. Takai ga shiga ganin Dr wayanta dake rik'e a hannunta ya shiga ringing tana kai dubanta taga Very Own na flashing akai, wani haushi da tsanansa taji na running through her veins inhar dagaske abu ya samu mahaifarta bazata ta6a yafewa Adeel ba. Kashe wayar tayi gabad'aya ta miyar jaka sannan ta shiga d'akin bayan sun gaisa da Dr ya tambayeta meke damunta. Kwalin maganin ta zaro daga jaka ta miqa mai “Dr please I need all information about this drug” amsa yayi ya duba sunan “are you married?” Ya soma tambayarta.
Kai ta gyad'a a hankali.
“Ke kike sha?”
“Yy... Yes” tayi stammering.
“But why? Yanada side effects sosai in haihuwa ne bakiso nan kusa you should have simly gone for one out of the numerous family planning methods, this is a bad idea for how long kike sha?”
“Dr for about six months now” ta k'are maganan moisture na filling a idonta.
“What!” Ya zaro ido. “Are you serious? 6 months fa kikace?”
“Yes Dr nima ban ta6a sanin shi nake sha ba se yau mijina ne yake bani dan Allah tell me what damage it has done to me already.”
“Am sorry Ma'am but I fear it has destroyed your womb.”
“Inna lillahi wa inna ialihi raji'un!” Ai seta hau kuka gun ba yadda beyi da ita ba tayi shiru tak'i seda tayi me isarta sannan tad'an yi pausing. “Calm down okay? Karki tada hankalinki zamuyi scanning mu duba mugani miracles happens, tunda ke bakiyi niyyan sha ba baki ake Allah na iya duban niyan ki ya miyarwa mijinki da aniyansa just pray Allah yasa be miki damage da muke gudu ba.”
“Dr nasan damage kam has already been done dan ko 6ari ban ta6ayi ba for six months after marriage, abu d'aya nakeson sani Dr please tell me the truth” ta tsaya ta sharr hawayenta.
“Ina jinki Ma'am.”
“Yanzu koda na bar sha daga baya bazan zo in iya concieving ba?” Shiru yayi nad'an tsawon lokaci. “Please Dr just tell me mahaifata ta 6aci kenan kwata-kwata?”
“Gaskiya to be frank with you tunda har kince for six months kike sha zeyi wuya ace zaki iya concieving baby saboda ko bamuyi scanning ba I know ya riga ya miki damaging womb cause there was a lady also data sha for just a month, mahaifarta ta b'aci gabad'aya daga k'arshe surgery akayi mata aka cire aka yasar dan ya zama ba amfani. Amman kinsan kowa da yanayin jikinsa maybe naki baya jin magani da wuri.”
“Innalillahi! Yanzu Dr kana nufin bazan iya ta6a haihuwa ba kenan?” Kasa tare hawayen tayi se zuba suke.
“Zeyi wuya to be frank Ma'am amman kinsan akwai miracles, babu abinda yakai ikon Allah mamaki saboda ba yadda Allah baya abinsa kisa a ranki wataran zaki haihu kema kuma ki dage da addu'a in shaa Allahu you wont be disappointed.”
“Shikenan Dr nagode.” Tayi managing ta fad'a.
“Bakomai sauran muyi scanning muga shape na mahaifar naki ko?”
“No please, bazan yi ba banason inji nima se an yanke min nawa koda ya 6aci ne abarmin shi a jikina.”
“But Ma'am yakamata kiyi scanning d'in still.”
“A'a wallahi Dr tashin hankalin danake ciki ma kad'ai ya isheni damuwa basena k'ara wani akai ba thank you” tana kaiwa nan ta miqe se soaking with tears tissue'n hannunta yake “Ma'am! Ma'am!” Dr ya shiga k'olla mata kira, kasa amsasa tayi ta fita da sauri inda ta nufi motarta ta zauna ta bud'e sabon dandalin kuka.
Takasa tayi shiru, hawayen har kaman so suke su k'are ga d'an banzan yunwan da takeji. Babu abinda yafi bata takaici kaman in ta tuna batada gatan iyaye yanzu, da ace auren mutunci akayi mata da albarkan Baba da Mama aciki da hankali kwance zata je ta irga musu komi da yardan Allah kuma suyi mata tsaye akan case d'in se an k'wato mata 'yancinta. Amman yanzu fah? Ba yadda ta iya haka zata hak'ura kokuwa taja Allah ya isa.
Se 4:36pm Zeezee ta isa gida alokacin har Adeel ya gaji da trying number'nta, jira kawai yake ta dawo ya hauta dan kuwa ya hanata fita bale wai yau bada izininsa ba. Ta bud'e k'ofan parlour ta tarar dashi zaune bisa sofa da remote rik'e a hannunsa. Bata bari idonsu ya had'u ba ta kawar da kanta da wuri. Ji kawai take kaman ta d'au wuk'a ta cakka mai for what he did to her.
“Ina kikaje? Ma tukun ban hanaki fita ba?” Ya tambayeta cike da tsiwa. Ko d'aga kai ta kalli direction nasa batayi ba, hakan ya sake k'ullar dashi. “Zeezee am talking to you, are you deaf?” Nanma shiru hannu ta zira a jakarta ta ciro kwalin maganin sannan ta nufi har gabansa ta ajiye akan centre table. Mamaki ne karara ya bayyana a fuskansa be tsamman zata iya tatso magunan ba a inda ya 6oye don haka jikinsa yayi sanyi, “a ina kika samu wannan?” Ya tambayeta finally.
“Wow! Abinda kad'ai zaka iya tambaya kenan? A ina na samu? Ba dogon surutu nakeso ba just tell me menayi maka a rayuwa da ka za6i daka 6atamin mahaifa Adeel, mena maka?”
“What are you saying?”
“Don't play dumb sarai kasan maganin nada side effect amman dake you are a beast a horrible one you proceeded on and kept me taking it wallahi kasani bazan ta6a yafe maka ba for what you did.” Miqewa yayi ya tsaya, “look at you daman nace ki yafemin ne? Please don't ever forgive me, am not ready to be a father and that was the only decision to make.”
“Ashe maqaryaci ne kai ban ta6a sani ba, waya ta6a cemin we should elude muyi aure and have our own kids?”
“Don na fad'a doesnt mean I meant it and koda wasa karki sake referring d'ina da maqaryaci I wont let it go.”
“Mene inba maqaryacin ba? Me zakamin? Kasheni? I wouldn't be suprised tunda har ka iya ka kashemin mahaifa hakan na nufin zaka iya kasheni nima mugu kawai.”
“ENOUGH OKAYY!!” Ya tsawata mata amman ko firgita batayi ba “its not enough until I say it is kabani takardana this instant.”
“LOL” ya saki dariyan rainin hankali. “In baki takardanki? Sekuma kije ina? Ko kin manta bakida gun zuwa ne? Well if you do lemmi remind you, Babanki yayi disowning naki bakida kowa se ni gomma kin bini a hankali ‘yar sadaqa ma dake ko kin manta a kyauta Babanki yabani ke? Don haka bakida value ko kad'an a idona. Bama wannan ba ajinki akwai na mijin da ze zauna da macen da bazata iya haihuwa bane yanzu? You are nomore a complete woman Zeezee your womb is bad you can't concieve so is better ki bini a hankali nine kad'ai gatanki a duniyan nan. ”
Karyewa gabad'aya zuciyarta tayi, tabbas ba k'arya a zancensa amman sede duk abubuwan da suka faru shine sila da tun lokacin taji maganan Lubiee da Adeel bashida bakin da zai mata gori har yace da ita 'yar sadaqa. Hawaye kawai taji na forming rapidly a idanunta kafin ta hankara taji sauk'ansu kan cheeks nata. “Gomma kukan de shi ze rage miki takaici” yana kaiwa nan ya bar mata parlourn. Sauk'a har k'asa tayi gun tana kuka me tsuma zuciya, tayi nadama, tayi nadaman kawo Adeel rayuwarta.
***
Through out ranan word be sake had'ata da Adeel ba dan tunda ta shiga guest room bata fito ba seda taji k'aran engine na motansa, anan ne ta fito ita ko htl ne ta gwammaci tayi zamanta ciki kafin ta samu permanent place don batajin zata iya cigaba da zama da mugun halitta kaman Adeel, if only tasan true colour'nsa da bata aure sa ba. “Oh Allah! am missing you Ya Al'ameen please forgive me” ta furta a ranta. D'akinsu ta shiga ta had'a akwati d'aya da wuri-wuri tazo da fita ta murd'a handle seji kawai tayi a rufe, “like seriously? Rufeni Adeel yayi?” Rattling k'ofar tayita yi amman ina sam bayi bud'uwa, kuka ta shigayi amman hakan besa ta hak'ura ba seda k'arfin jikinta tas ya k'are sannan ta tattara kanta tayi guest room. Har after 9pm Adeel be dawo gida ba, yunwa ne ya korata ta nufi kitchen ta had'a oats tasha sannan ta sake komawa d'aki gabad'aya tunanin duniya ya sata gaba. A haka har bacci yayi awon gaba da ita.
Adeel kuwa se dab da Asubah ya dawo gida bayan ya idda Sallah ya koma bacci se pass 10 ya tashi yayi wanka tsaf sannan ya leqa parlour. A dining table ya tarar da ita tana had'a tea, gefenta kuwa indomie ne da sardines aciki seda fried egg a gefe, kafin ta hankara kawai taga ya d'aga plate natan “Adeel ya da haka give me back my plate.“ Tayi stating angrily.
“In ke kike siyan abincin seki amsa aikin banza kawai, ki sake girka wani am in a hurry zan fita.”
“Ina ruwana da fitanka give me back my plate.”
“Ki amsa idan kinada k'arfi mschww!” tunkud'eta gefe yayi seda ta kusan fad'i sannan ya k'arasa had'a tea'n nata yakoma d'aki. Hawaye ta soma without knowing how, a hankali ta share ta koma guest room ta baje kan gado ta cigaba da aikin kukan.
15 more minutes taji an bankad'e mata k'ofa which she is sure is no one other than Adeel ko juyawa ta kallesa ma batayi ba “Ke!” Ya kirata cike da raini da nuna isa. “Ke! Baki jina ne? Don't let me repeat myself turn around.” Seda ta d'au tsawon minti d'aya sannan ta juya a hankali tana kallonsa kayan wankinsa dake hannunsa ya zuba a k'asa “gashi do my laundry in kika gama seki girka min spaghetti for lunch, up you go.”
“Nice zan maka laundry?” Ta tambayesa in a low tone cike da mamaki.
“Baki tab'a ganin mata suna yima mazajensu wanki bane?”
“Bana d'aya daga cikin jerin matayan can don haka bazan wake komi ba, ko ka wanke da kanka kokuwa ka kai laundry su wanke maka.”
“What? Me kikace? Come again.”
“Bazan wanke ba nace ai ba 'yar aikinka ce niba.”
“LOL toh ai baki sani ba Zeezee, me aiki ma yafiki min ke k'ima da daraja a ido saboda su atleast da kud'i zan d'auko su kekuma fah? A sama fa na sameki don haka kibar 6ata min lokaci and do as I ask.” Tana hawaye tace, “bazan yiba“ isketa yayi lokaci guda zuwa kan gadon tare da fincikota da hannunta. Wani irin riqo ya mata wanda tuni k'arfin kukanta ya dad'u dan azaba. K'ok'arin kar6e hannunta take amman takasa. “Adeel ka sakeni” ta fad'a in between tears.
“In saki aiki kice baza kiyi ba?” Ya sake dandame rik'on daya matan k'ara ta saki a sanadin haka. Da zafin ya isheta tana kuka sosai tace “zanyi, zanyi ma wankin don Allah ka sakeni.”
“Repeat it again.”
“I'll wash your clothes for you ka sake min hannu please.” Ta qare maganan tana kuka sosai, se anan ya saketa wajen har yayi dark pink colour tsan-tsan azaba.
“Don't try crossing me again” yana kaiwa nan ya fice, kan gadon ta koma ta cigaba da rusa kuka sosai na haqiqa.
Seda tayi me isarta sannan ta tashi taje ta wanke mai kayakin tas ta shanya ta kuma aza mai girki. Dad'i sosai taji ganin be rufe k'ofa ba, nan da nan taje ta d'auko akwatinta sede kash tana isa bakin gate ta tarar dashi a rufe. Kulle idonta kawai tayi se hawaye suka soma fita, abin tausayi ta koma ciki ta cigaba da kuka tana cikinyi taji buzzing na wayarta, Lubiee taga ke kira amman batajin zata iya amsawa haka har ya tsinke tana gani.
*~ *~ *~
Rayuwa kuma haka ta canza, Zeezee kullum cikin kuka ba kalan azaban da Adeel bai galla mata. Ta yini a aiki takuma ta tashi da aiki gashi koda wasa ta gwada cewa bazatayi ba threatening nata yake sosai, daga yasata yimai wanki, se girki, gashi ya tashi dawowa daga yawonsa yanzu da gan-gan se ya taro ambaliyan friends nasa about 5-6 of them suci lunch. Zeezee kullum tsaye bakin gas, da iskancin Adeel ya tashi ma yace shi yabar siyan Gas d'in wai tayi tsada charcoal stove ya sai mata haka kullum tana waje tana mishi girki da friends nasa which she don't get any thanks in return. Se tunawa kawai take da bawan Allah Al'ameen. Shin ma ta ina zata soma neman yafiyansa? Dukkanin rashin hankalin da take mai dai-dai da rana d'aya be tab'a wulak'anta taba ko tsawa bayi mata a kullum cikin missing Al'ameen take se yanzu ta gano the true definition of Love and Adeel was never her true love Al'ameen is amman tasan its too late now maybe yanzu Al'ameen ma yayi aure ya manta da ita.
Abin da yafi bata takaici kuwa shine yanzu koda ta kira Mama, Mama bata picking calls nata ba ita kad'ai ba harta sauran 'yan uwan nata. Inhar ba aiki Zeezee keba toh tana kwance a d'aki tana kuka ne, cikin sati biyun nan ba k'aramin zubewa Zeezee tayi ba don har haskenta ya ragu sosai, gata nan ne kawai kullum cikin nadama take.
****
Yau da safe tana girka breakfast a waje kan charcoal ta baro wayarta a kitchen. A dai-dai lokacin da wani friend nata Imam ke turo mata saqo a dai-dai lokacin Adeel ke shigowa kitchen ganin haske yayi flashing kan screen natan yayi sauri ya leqa kasancewar iphone na reading notifications ya samu ya karanta saqon as “morning dear ya kike?” Wani banzan kishi ne ya tokaresa d'aga wayan yayi yasa a aljuhunsa wanda a dai-dai nan Zeezee ke shigowa da soyayyen doyanshi da sardine sauce. Bata cemai komi ba ta wuce dining ta ajiye ta dawo kitchen d'aukan wayarta taga babu sede kallo d'aya tama Adeel ta gano shi ya d'auka. “Kabani wayata.”
“Bazan bada ba, iskanci zaki soma kawomin gida? Waye Imam and why is he referring to you as a Dear One?”
“Ina ruwanka kai kullum da kake waya da 'yan matanka na ta6a yima magana ne?”
“Are you talking back to me?” Fuskanta ta wajen bakinta ya kama da k'arfi ya maqure, “don't you dare banason raini kina ganewa ko?”
“Let me go you're hurting me” ta iya fad'a kad'ai don azaba seda yaga tana wahala sosai ya saketa. “Mugu, azzalimi kawai Allah ze saqa min kuma ka bani wayana ai ba kai ka siyamin ba don haka you have no control over it.“
“Haka kikace?”
“Yes give it back.” Hannu ya zira a pocket nasa yafito da wayan da mamakinta taga ya tarwatsar dashi a k'asa da duk k'arfin da Allah ya basa “I guess I do have a control over it now.” Yana kaiwa nan ya fice sauqa tayi har k'asa gun tana kuka abin tausayi. Yanzu kuma a ina zata samu wani wayan tunda ko bakin gate bayi barinta ta taka. Seda taji ya fita tayi d'akinta. Landline ta d'au ta kira Lubiee tana kuka sosai gabad'aya hankalin ta ya tashi daman tasan ba lafiya ba yadda taji Zeezee shiru kwana biyu.
“Babe please calm down and tell me meya faru? Kina gida ne inzo right away?” Lubie tayi stating hankali duk a tashe. Hanci taja sannan tace, “ko kinzo ba ta inda zaki shiga locking d'ina yake baya bari na in taka koda bakin gate.”
“Subhanallah shi waye?”
“Adeel.”
“Adeel? Adeel fa kikace kunyi fad'a ne?”
“Kaca-kaca Babe ashe Adeel ba sona yake ba tunda ya ringa bani wani capsules seda na rasa mahaifata.”
”Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!” Labarin komi Zeezee ta bata wanda ya mugun bawa Lubiee mamaki bata ta6a sanin Adeel is as wicked as this ba. Ranta ya matuqar 6aci tayi hanging call d'in tare da kiransa. Se a karo na biyu ya d'aga.
*MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
๐๐๐๐๐
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
1 comment:
Hhhhh������...this is damn getting hotter��...Oh ZeeBaby��, daman haka rayuwa ta kasance miki...!? Nadamar da Yanzu kike ciki, da kin gwammace a da...da Baba ya aurar dake ma Ya Wakeel mai shago, da yanzu kina cikin Gatan cinki...It's rather unfortunate u're going through these atrocities...abinda kika shuka ne,shi kike girbawa! Hope u 'Enjoy' eating them������. Sai dai kawai mu yan kallo mu tayaki da Adu'a...Allah shi ne mafita,Maj-Gen kuma makawa. Allah shi fitar lfy. Allahumma Ameen �� ������
Post a Comment