Sunday, 8 January 2017

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 33

  *January, 2017*

   _Hummm! I can smell my birthday tomorrow☺😋_

    _This page is in honour of  *Zaynab Anka, Fiddy G Muh’d, Kabo daughter, Hamra, Ummee, Mom Nu’aym, Umm Aneesah, Maryam,* and *Maryam Wasagu* #OneLove❤_




 
       Ana gama event su Zeezee suka dawo gida gabad’aya kowa ya watse a gidan daga ita se Al’ameen se soliders kota ina suna gadi. Driver na parking ta bud’o k’ofa ta fita gaban entrance door ta tsaya tana jiran Al’ameen ya bud’e mata k’ofa har anan bata bar kuka ba wanda hakan ba mugun damun Al’ameen yake ba. Har tambayan kansa ya somayi anya kuwa Zeezee na sonsa? Da guards nasa biye dashi ya k’arisa ya bud’e mata k’ofan kai kawai tasa se a d’akinta ta tsaya ta baje kan gado tana me cigaba da rusa kuka. Bayan Al’ameen ya bud’e kazan amarchi yasa mata a plate da farm fresh a cup ya nufi d’akin nasu, sallama yayi ganin batada niyyan amsawa yasa kai ciki kawai. A kan side drawer ya ajiye “Princess?” Ya kirata a hankali cikin sark’ak’k’iyar muryansa. “Princess kukan ya isa kinji? Yi hak’uri” hannunsa ya d’aga a hankali ya aza kan bayanta, jikinta ta ja da wuri tare da d’ago kanta tana mai wani mugun kallo. “Don’t touch me Al’ameen don’t! Bak’in cikin daka jefani kad’ai ya isheni ba seka k’ara min da wani ba. Ka rabani da iyayena and above all ka rabani da saurayi na Adeel kasa yayi nesa dani kasani bazan ta6a yafe maka ba Al’ameen. Ka cuceni I wish I’ve never met you.” ta k’are maganan hawaye na bin k’uncinta.

   “Zainab what are you talking about? Weren’t you the one that agreed to thsi wedding in the first place? Dama ba sona kike ba kika bari akayi auren?” Ya tambayeta suprisingly.
  “Nayi ne saboda in farintawa Baba rai amman badon wai ina sonka ba, ban ta6a sonka ba kuma bazan ta6a sonka ba. I hate everything about you, your skin and that sweet irritating voice of yours Adeel nakeso I want you to stick that to your head and please excuse me just looking at you disgusts me.” Ta k’are maganan tare da watsa mai harara.
  Mamaki ne sosai ya cika Al’ameen da har ya zama lost of words amman be damu ba saboda gani yake har yanzu yarinya ce batasan ciwon kanta ba eventually al’amura zasu daidaita tsakanin su, he believe. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki “naji toh My Zainab amman tashi kiyi having dinner seki kwanta kinji?”
    “I am not yours and ba ruwanka da abinda zanyi tunda ba zaman ka nake ba, kuma ka tattara kajinka kayi waje dasu banaso bazan ciba.” Tana kaiwa nan ta mik’e tare da jan akwatinta ta ciro night gown nata ta nufi bathroom. Kai kawai Al’ameen ya kad’a ya wuce d’akinsa shima ya watsa ruwa, koda yafito be koma d’akin nasu ba atunaninsa bari ya bata space. A parlour ya zauna yaci ragowar kajin. To twelve (12) ya lek’a d’akin nata yana sanye da ¾ wandon soldiers zalla, hakan ya sake fiddo da how muscular and built up his body is making him worth more looking. Kwance tana bacci ya tarar da ita tana sanye da wani pink sleeping dress me hannun spaghetti da ¾ wando. Kajin data ce bazata cin bama ta cinye tas harda fasa k’ashi. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki sannan ya k’arisa d’akin tare da gyara mata kwanciya yaja comforter ya rufeta sannan ya kashe musu wutan d’akin ya hauro suka kwanta. Sam beyi niyyan mata wani abu ba a daren ranan saboda yasan koda had’a sama da k’asa zeyi ba basa had’in kai Zeezee zatayi ba she needs some space.

   12:50am Zeezee ta farka gabad’aya takasa gane meke damunta, tunda tasan kanta bata ta6a jin abinda takeji ba yau, juye-juye tahau yi kan gadon duk anan Al’ameen bacci yake peacefully besan meke faruwa ba. “Wayyo Allah na! Mama me kika samin a maganin d’azu?” Sauk’a tayi daga kan gadon tana me cigaba da juye-juyen a k’asa wani irin sha’awa kawai take jiyowa ita kad’anta ta rasa dalili. K’ara ta saki sosai seda Al’ameen ya tashi ganinta kawai yayi se juye-juye take. A hanzarce ya nufi kanta tare da sa hannunsa akan bare back nata kasancewar sleeping dress natan show me your back ne, “My Princess are you okay? Meke damunki?” Da wuri taja jikinta don d’an ta6a tan da yayi ba k’aramin affecting nata yayi ba kawai jin wasu electric sparks suna bin jikinta ta tayi a yayinda degree na sha’awan nata ya sake k’aruwa.
   “Wayyo Allah zan mutu Mama kin kasheni dan Allah karka sake ta6ani I can’t take it.”
  “Mama kuma? Me ta miki?”
  “Dan Allah kabarni in kanayi wa Allah karka sake ta6ani muryanka ma dad’a min abinda nakeji yake in kanayi wa Allah ka tashi ka fita kokuma kasa kaya.” So take ta miqe amman takasa se juyi take wajen, tuni Al’ameen yagano meke faruwa. “Tashi toh muje mu kwanta.”
  “Wai ana dole ne? Wayyo Allah na! Dan Allah ka tashi kabarmin kaina, Mama kin kasheni yau! Nashiga uku!!” Murmushi kawai Al’ameen ke ba yadda beyi da ita ba ta tashi suje su kwanta tak’i haka ya koma ya kwanta yana kallonta. Juyi Zeezee ta cigaba dayi agun ganin abin bana sauk’i bane taja pillow ta danne kanta har anan bata barjin abinda takeji ba. Ga sauk’i nan kawai taje ta samu Al’ameen amman batajin zata iya basa kanta tayima Adeel alk’awarin budurcinta. Haka tayita wahalar da kanta a daren ranan da k’yar d’in k’yar takoma normal ta haura gado ta kwanta.

   Da Asubah ya tashi yayi alwala sannan ya zauna gefen sleeping Zeezee yana k’arewa kyakkyawan fuskanta kallo then back to d’an mitsitsin bakinta me uban tsiwa. Kallonta kad’ai na sanya masa farin ciki baze iya kwatanta yadda yakeson Zeezee ba. “Zainab” yayi whispering name nata. “Zainab tashi muyi Sallah kinji? Zainab!” yayi tapping nata. A hankali ta bud’e idanunta tare da kallonsa sekuma ta juya mai baya. “Tashi muyi Sallah ko inyi nawa ni kad’ai?”
   “Ban sani ba” ta amsa a takaice ganin batada niyyan tashi ya miqe ya hau yin Sallansa. Seda ya kusa idarwa ta tashi itama tayi alwala. Koda ta idar bata gaishesa ba ta koma gadon ta cigaba da bacci. Al’ameen kuwa na gama Azkhar nasa ya fita waje ya samu men nasa ya hau training nasu har safiya be koma bacci ba.

  Amarya kuwa se 10am ta tashi, bayi ta fad’a tayi wanka tana zaune gaban mirror da towel zallah a jikinta tana shafa mai Al’ameen ya shigo ganin batada kaya yad’an tsaya gun tare da clearing throat nasa ko zata gyara. Aiko maras kunyan yi tayi kaman bata jisa ba ta cigaba da wangale santala-santalan cinyoyinta tana shafa mai. Cikin d’akin ya k’arisa tare da zama bakin gado yana kallonta a yayinda wutan so da sha’awanta ke running a veins and atteries nasa. Tana gama shafa man ta d’au inner wears nata tasa sannan kayanta ko kunyansa bataji. “good morning My Princess tunda bazaki gaisheni ba” yayi speaking up finally. Ko kallon direction nasa batayi ba tafice izuwa kitchen tana tunanin dame zatayi breakfast. Tana cikin wannan tunani idanunta sukayi tozali da take away akan counter. Ba tare da 6ata lokaci ba taja ta bud’e chips da omalet taga ciki. Ai kujera kawai taja tahau ci seda tayi nak sannan ta koma d’aki alokacin Al’ameen na gun wanka. Wayarta ta d’au taga missed call na Lubiee take ta kirata tare da barin d’akin. “Hello Babe.”
  “Matar Soja good morning.”
  “Banaso ni na gaya miki banaso.”
  “Toh yi hak’uri ya jiki-jiki?”
  “Jiki-jikin k’aniya ce miki akayi banida lafiya?”
“Kamar ya?”
  “Wai da kin d’au zan bawa Al’ameen kaina ne?”
  “Aww yanzu ko Ya d’inma babu.”
  “Bansani ba ai dana basa budurcina na gommaci na baiwa mahaukaci akan hanya.”
  “Haka kika ce?”
  “Eh mana.”
  “Amman tsaya jiya kinsha maganin da Mama tabani na baki?”
  “‘Yar iska daman kinsan abinda maganin zemin kenan kika k’i gayamun? Wallahi jiya da k’yar na samu nayi bacci.” Dariya Lubiee tasa “kinshan ne kuma shine kikeson nayi believing kan ba abinda ya shiga tsakaninki da Al’ameen?”
  “Wallahi babu pillow nad’au na tare kaina.” Nanma wani dariyan Lubiee tasa “wallahi ‘yar iska ce ke.”
  “Niba abinda ke damuna ba kenan ya zancen Very Own fah? Line nasan ya soma shiga?”
  “A’a wallahi Babe.”
  “Oh no! Na shiga uku.”
  “Babe gomma tun wuri kin miyar da hankalinki kan aurenki kina jina ko?” Nasiha Lubiee ta shiga yima  Zeezee wanda tana cikin yi Zeezee ta katse wayar abinta. D’akinsu ta koma ta tarar dashi yana shafa mai, la6ewa tayi bakin k’ofa tana kallon yadda muscles nasa suke moving in sync in yana shafa man haka kawai take depriving pleasure from staring at his naked body. Ta mirror Al’ameen ya ganta, murmushi kawai ya saki ya cigaba da abinda yake chan yayi clearing throat nasa “My Princess ki shigo mana.” Kunya taji sosai sannan ta fito daga la6en “nifa ba kallonka nake ba k’ofan ne ya kama min kayana naga kana wani murmushi.”
  “Toh ai bance kallo na daman kike ba, inma kallon nawa kike ai ba damuwa tunda am all yours.”
  “Kai kaji wajen kuma wai kai haka muryanka yake ne kokuwa iyayi ke saka magana haka?” Dariya sosai ya tsaya yi in which Zeezee find him cute “meh muryan nawa ya miki kuma?”
  “Bayamin dad’i.”
  “Nikuma naki na min dad’i sosai My Princess. ”

   “Sau nawa zan gaya maka kadena cemin My Princess? I am not yours I belong to Adeel kuma ka sa kaya banason ganin na miji other than my Adeel ba kaya, sannan kuma kasa wad’ancan useless guards nakan da suke waje su kaini gida inason inje inga Mama.”
  “Toh dama Amarya tana fita unguwa ne?”
“Wai kai baya damunka ne idan na kira sunan Adeel da baza kayi zuciya ba kace zaka sakeni?”
  “Mesa ze damen Zainab? Duk wanin da kikeso nima dole in sosa ai.”
    “Seka tayi ai wallahi da kanka zaka gaji ka sakeni, kuma ba amarya ceni ba cause as far as am concerned banida aure.” Ignoring what she said yace, “kibari ko zuwa next week ne seki fara fita kinji? Yi hak’uri.”
  “Har next week?” Tahau tsiwa, “mezan tsaya yi a wannan gidan naka har zuwa next week? In ganinka da wad’ancan useless guards d’inne na gaji dayi, wallahi ka kaini gida” tasa mai kuka. Kai kawai ya kad’a “naji toh bar kukan shirya driver yayi dropping naki nima zan d’an fita dama.” Tana share hawayenta tace, “da yafi ma kam.” Wardrobe nata ta nufa ta ciro mayafinta tare da nannad’esa a one side of her shoulder yadda ‘yan mata keyi bayan ita gata matar aure. Al’ameen na gama shiri ya kalleta “mu tafi ko?”
  Miqewa tayi tare da jan wayanta “wait haka zaki fita Zainab?” yayi maganan a hankali.
  “Ni wallahi muryankan nan...” ta zumburo baki “kuma da ya kakeson in fitan?”
  “Ki rufe jikinki da gyalen mana Zeezee na, bakiga duk gidan maza bane?” Kishin Soja ya k’osa!
  “Toh ni nace ka d’ibo gang of soldiers ka tarasu a gidanka ne? In kaga bakason kaga matar ka tana fita haka is simple seka sakeni daman niba san auren nake ba.”
  “Yi hak’uri ki gyara kinji? Yi hak’uri bakisan beautiful things are left covered ba? You are too beautiful to expose your body like this” ya k’are maganan some inches away from her. Shiru tayi tana kallonsa, hannunsa ya miqa a nitse ya d’ago gyalen daga kan kafad’arta tare da bud’ewa ya yafa mata shi me kyau sekace mace. Juyata yayi yadda take kallon kanta a mirror “bakiga kinfi kyau haka ba?”
  “Ni ka sakeni toh” taja jikinta. Murmushi ya saki sannan yace mata “lets go” ganin ya shiga tafiya ta sake bud’e gyalen sannan tabi bayansa. Soldiers d’in suna ganinsu suka hau saluting nasu wani dirty look Zeezee tashiga binsu dashi ita haushi ma suke bata yadda sukeyi ma Al’ameen sekace wani god, mschw! D’aya daga cikin prados na gidan d’ayan soldiers d’in ya bud’e mata tana shiga Al’ameen ma yashiga aka rufe sannan suka fice.

  Not long enough suka isa gidansu Zeezee. Nan soldiers na d’ayan motan suka fito tare da jeruwa ta side na Zeezee d’aya daga ciki ya bud’e mata. Tazo fita Al’ameen ya rik’o hannunta “ki gaishe da mutanan gida kinji? Da La’asr zanzo in d’aukeki.” Kaman bazata amsa ba ta gyad’a kai tare da ficewa. Mama na zaune tsakar gida ita da Omar Zeezee ta shigo.
  “Amaryar! Lafiya dai ko?” Mama tayi exclaiming. K’arisowa tayi tare da gaishesu “baki amsani ba lafiya?”
“Lafiya mana Ya Al’ameen ze fita ne shine nace yayi dropping d’ina nan gida tunda ba abinda zanyi and yace yana gaisheki ma.”
  “Kaman ya ba abinda zakiyi Zeezee girkin rana fah?”
  “Nace zanyi yace no need ya d’aukemin girki wai.”
  “Abun nema ya samu ba, dama ba son girkin ake ba.”
  “Uhm ina Baba?”
  “Ya fita kasuwa” cewar Omar.
“Ohh ni zan wuce d’akina.” Kallonta kawai Mama ke har seda ta fice “uhm su Zeezee amarya.” Omar na murmushi yace, “kede bari kawai Mama Allah sa de auren yasa tayi hankali.”
   “Ameen Omar ya ko ka fasa fitan ne?”
  “Eh zan koma d’akina kawai.”

  ****
   Yini Zeezee tayi tana trying line na Adeel da Lubiee ta turo mata sede sam bayi shiga. Gabad’aya ta rasa ina zata sa kanta se bayan La’asr Al’ameen yazo d’aukanta har anan ma Baba be dawo ba, d’aya daga cikin guards nasa ya tura yayi ma Zeezee magana kaman karta bisu takeji amman dolenta taje kada Mama tayi suspecting wani abu. Sunyi sallama da Mama ta fice koda ta shiga motan bata ce da Al’ameen ko k’ala ba shine ma yace mata sannu nanma banza dashi tayi. Dagangan dan neman magana ta bud’e wayarta ta ajiye a tsakiyansu yadda Al’ameen na lek’awa yaga pic na saurayi kan wallpaper’n nata wanda he is sure shine Adeel d’in. Kallonsa Zeezee ke a yayinda yake kallon pic na Adeel a zatonta ma zeyi magana segani kawai tayi ya kawar da kansa daga direction d’in, hakan ba k’aramin haushi ke bata ba, shikenan shi ba aikinsa se ignoring nata? Mschww tafison suyi ta yinta har seya saketa tukun, bata da burin dayafi wannan.

   ★*★*★*★
   Ahaka fa har Al’ameen da Zeezee suka samu sati biyu da aure. Ba abinda ya ta6a shiga tsakaninsu saboda ko gwada ta6ata bayi yi idan sun kwanta. Cikin sati biyun nan Zeezee bata ta6a d’aga tsintsiya ba da sunan shara banda rashin kunya da yarinta ba abinda take na Al’ameen, shikuwa duk abinda take mai overlooking kawai yake saboda uzurin yarinta dayake mata for sure yasan da tasan ciwon kanta bazata na hakan ba. Har a yau Zeezee bata ta6a hura wuta ba, breakfast, lunch and dinner kullum siyo musu yake randa yace sufita suci ma gar da gar setace mai ita batason aganta da tsoho. Rashin kunya kwando-kwando Al’ameen ke sha.

   Yau Sunday Al’ameen ze koma aiki Abj leave nasa ya k’are. Zeezee dad’i kasheta finally zata samu tafita yawo abinta. Koda Al’ameen keta had’a akwatinsa batayi yunk’urin tayasa ba as she is busy playing game a wayanta har a yau kuwa kullum setayi trying numban Adeel sede ko so d’aya be ta6a shiga ba. 1:30pm Al’ameen yagama shiri da trolley’nsa rik’e a hannunsa ya kalli Zeezee da tayi banza dashi “My Princess ni zan wuce toh ga pocket money naki nan incase need yayi arising bana nan tho duk wani abinda zaki buk’ata ma na riga na tanadar miki, anytime you’re hungry na bar miki two of my men they’ll be at your service.” Wayar nata ta ajiye ta nufi gabansa tare da d’ago bundle na d’ari biyar daya ajiye matan. “Yanzu zakayi tafiya shine d’an wannan zaka ajiye min? Nasan shekaru nawa zakayi a Abujan? Wallahi bazan yarda ba ka k’aramin kokuwa k’afanka k’afana, taya agida Baba be barni da yunwa ba kai kace zakayi hakan?”
  “Yanzu wannan ya kasa Zainab?” Ya tambayeta suprisingly yana murmushi.
  “Seka tambaya ne? Ya kasa mana me ‘yar dubu hamsin da ina iya kashewa a minti biyar zata min?”
  “Nawa kikeso toh?”
  “Double mana” ta amsa a takaice. Be sake cewa komi ba ya k’ara mata wani bundle d’in “shikenan?”
  “Eh kuma se yaushe zaka dawo dan ba zaka ajiyeni a wannan k’aton gidan naka ni kad’ai ba wallahi kai kaje chan kana mu’amala da mutane kabarni da wasu sojojinka nan.”
  “Shiyasa nace miki in kaiki chan family house a KD kika k’i.”
  “Toh a dalilin me zan zauna da in-laws haka kawai abi a sawa mutum ido.”
  “Uhm toh ni natafi ko?” Yi tayi kaman bata jisa ba “ba rakiya Zeezee?”
  “Lallai baza kayi tafiyan ba kenan inhar ni kake jira nama rakiya” ta kai da juyawa ya rik’o hannunta tare da pecking forehead nata “I love you My Peincess” freezing Zeezee tati a wajen sabida wani sparks da takeji suna tashi a jikinta, peck na Adeel be ta6a sata feeling haka ba. Kasa cewa komi tayi daya gano hakan se kawai ya mata murmushi ya fice.

   Tafi minti biyu tsaye a wajen immobile sannan tasamu ta dawo hayyacinta, hannu tasa wajen tana murzawa in an tambayeta peck nasan take gogewa. Koda Al’ameen yayi landing Zeezee bata damu ta kirasa tamai ya gajiya ba. Haka shi yazo ya kirata daga baya nanma seda ta gama jan aji sannan ta d’aga “hello My Princess?”
  “Nifa bacci nakeji.”
  “Har kin kwanta ne? Its just 9:20pm fa My Princess.”
  “Toh mezan tsaya yi awannan gida naka?”
  “Uhm toh sleep tight Beautiful, I love you.”
  “Naji” nan tayi hanging. Addu’an Al’ameen a kullum bayyafin Allah ya kawo rananda al’amura zasu daidaita takaninsa da Zeezee. Lubiee Zeezee ta kira kan tazo mata yini gobe Al’ameen bai gida.
   Washegari tun 8am kasancewar Lubiee tanada lecture free day ta iso gidan Zeezee. Ko breakfast batayi ba. Aikan d’ayan soldiers d’in Zeezee tayi ya siyo musu breakfast suna cikin karyawa Lubiee ta ta6e baki “amman Zeezee kin ta6a share gidan nan naki kuwa?”
    “Zamansa nake da zan share mai gida? Ya saken ya auro matar da zata mai kokuwa ya kawo me aiki.”
   “Oh! Zeezee fa kina jin dad’i wallahi har yau baki soma girki bakuma ko?”
  “Yo da wace boyi-boyinsa da zemai girki? Karki 6ata min rai please.”
  “Se ke matar Soja se yaushe ze dawo?”
“Ohonsa ni yaga dama ma kada ya sake dawowa ba nemansa nake ba.”
  “Hmm ma farin sojan kike ma wannan iskanci? Ma nawa ya ajiye miki tukunnah?”
  “100k ofcourse yaban 50k nak’i amsa dan dolensa ya k’are kuma inhar yakai two weeks be dawo ba seya k’aramin wani.”
  “Haba! haba! Zeezee kinajin tsoron Allah mana.”
  “Kanki akeji ni bud’en wayanki.” Ba musu Lubiee ta bud’e mata pictures Zeezee ta shiga gani suna karyawa, mistakenly hannunta yashiga call logs nan taga sunan Adeel gun as last person da Lubiee tayi waya dashi ayau. Kai ta d’ago tana kallon Lubiee da mamaki. “Ya da wannan kallo haka?”
“Kinzo kin samu numban Adeel d’in kuwa? Kinsan wanda ke waje na bayi shiga.”
  “Ermm... Uhm...” Lubiee ta shiga kame-kame “nima har yau bamu sake waya ba.”
  “Hakane? Babe k’arya kika soma min yanzu? Number’n waye wannan? Wato d’azu ma kunyi waya dashi kinsan how crazy I went looking for  his number kin samu bazaki gayamun ba, kin kyauta.”
  “Zeezee yanzu da da fa ba d’aya bane matar aure ce ke yanzu be dace ace da mijinki ba kina waya dawani. Its high time ki mance da Adeel saboda Adeel ya miki nisa.”
  “I will never forget about Adeel I believe zamu kasance tare someday and kaman ya yamin nisa? Ba a Abj yake ba?”
  “A da kenan, 4 days back ya wuce Florida achan yake yanzu kinga ko ya miki nisa just forget about him.”





  *© MIEMIEBEE    Team #YGC!*
  www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄

11 comments:

Unknown said...

Nice 1

Unknown said...

Sannu da aiki. Allah ya qara baseera. 👍

Anonymous said...

Happy Birthday

Unknown said...

Enx durln sis Nd a vry vry big happy buffdea tou lln Allah's noor its ur day dearie hv fun

Unknown said...

Awwn! 😻😻 thank you so much Hun,I Love You❤❤❤❤

Unknown said...

Thank you so much❤

Unknown said...
This comment has been removed by the author.
Unknown said...

Happy birthday sweetheart Allah karo shekaru da basira masu anfani

Unknown said...

Happy buffdea dear... wishing u Allah's noor always and forever

Unknown said...

🎂Hip📯Hip📯hurray🎂happy birthday dear 🎍🎂 wishing u LLNP

Unknown said...

sis so uh are enjoying ur day no post today am eager to read d next page