BY MIEMIEBEE
PAGE 32
*January, 2017*
Jere aka shiga yiwa Zeezee achan gidanta dake New GRA layin Sunday Awoniyi road, wannan gida shi ake kira da mansion I don’t have to go in details sanin kanku ne gidan Maj-Gen ba wasa. Ana cikin haka Zeezee takai Lubiee gidanta suka duba se yaba gidan Lubiee ke, gida sekace ba a Bauchi ba. A month to biki Mama ta d’aukowa Zeezee me gyaran jiki daga Maiduguri wacce tayi wa su Mariam da Yasmeen. Sam Zeezee tace ita bataso seda Mama tayi dagaske ta amince, magunan gyaran jiki da Mama ke bata kuma har ayau ba wanda ta ta6a sha da an bata seta wulla cikin side drawer’n gadonta.
Yau ma as usual da safe Mama ta shigo d’akin nata rik’e da roban drugs d’in “ina kwana Mama?”
“Kin tashi lafiya?”
“Eh sannu.”
“Kinga yadda skin naki ya k’ara haske kuwa? Ai kin kamoni fari yanzu koma ince kin fini, amman kice wai ke ba ruwanki da gyara? Bansani ba ko jiki kaman na k’adangare kikeson kije dashi gidan Maj-Gen. d’in yadda zeji dad’in sako ki.”
“Ai daya kyauta.”
“Kika ce meneh?”
“Eh man ai gaskiya ne wallahi shiyasa banason wannan shirmen gyaran jikin ayita miyarwa mutum fata ja sekace fuskan Ya Ibraheem.”
“Aww Baban nawa kike zaga?”
“Toh ai gaskiya ne, ayita murjewa mutum jiki sekace Aljannah za’a kai sa mschw!”
“Toh ya isa ke dama baki gaji mutunci ba, ga maganinki.” K’afa ta shiga shurewa “wai Mama kullum magani magani sekace rashin lafiya nake ni wallahi na gaji banaso.”
“Wawiya wannan ba shine ze gyara ki ta ciki ba, ko cemiki akayi gyaran waje kawai ake?”
“Nide banaso.”
“Amshi nace banason zancen banza” haka Zeezee na gunguni ta amshi maganin ganin Mama bata kallonta ta wurga goran k’ark’ashin gado. “Yauwa ni ranan ina na ajiye makullin gidan naki ne?” Mama tayi maganan tana k’ok’arin jan side drawer’n kan Zeezee wanda take tara duka magunan nata aciki. Ganin haka da wuri Zeezee tace, “Mama baya cikin chan karki b-” bata idda maganan ba Mama taja kawai gani tayi maguna suna mata sallama. Baki ta sake wide in shock totally out of words wato duk aikin banza take kullum tayita kawo mata magani tayita kashe kud’inta duk a iska, lallai Zeezee!
“Me wannan?!” Ta tambaya a fusace. Lamo Zeezee tayi zaune kan gadon tana kallon k’asa. “Magana nake miki, meh wannan? Bazakiyi magana bane?”
“Mama kiyi hak’uri dan Allah.”
“Meh wannan nace?!”
“Magunan ne.”
“Magunan dana ke baki?” A hankali ta gyad’a kai mari lafiyayye Mama ta kai mata a bare back nata seda shatin hannunta yafito nan Zeezee tasa ihu “dan k’aniyanki inyita asaran kud’i na inasai miki abinda ze amfane ki ashe duk tarawa kike ba sha kike ba? Iyye?!” Tana murza bayan nata ta kad’a kai “kiyi hak’uri kar Baba ya sani dan Allah.”
“Inba rashin wayo irin naki ba dry d’inki haka kikeso ki jewa shi Maj-Gen d’in? Ana baki abinda ze taimakeki kina shashanci? Ina wanda na baki yanzun?”
“Na shanye” tayi k’arya.
“K’arya zakimin? Ina yake nace?” Tsugnawa tayi ta zaro goran daga k’ark’ashin gado “maza bud’e kisha ina ganinki.”
“Mama wallahi banaso da Allah kiyi hak’uri.”
“Bazaki bud’e bane ko sena kira Omar ya baki kashi?” Haka Zeezee na hawaye ta kurb’e goran tas tun daga ranan Mama ke tsayawa akanta seta shanye maganin tas sannan tabar kanta.
2 weeks to bikin aure Mama ta soma batun pre wedding pics saboda yadda sisters na Al’ameen sunka k’osa kullum cikin kiran Mama suke awaya. “Zeezee! Zeezee!” Mama ke kiranta.
“Na’am” ta amsa tare da zuwa ga koran “gani.”
“Ehem kinada labarin gobe zamu wuce Abj ko? Achan zakuyi pre wedding pics nakun.”
“Har Abuja?! Kuma ma wani pre wedding? Shi baze zoba sede ni na bisa? Ni wallahi banason bidi’ancin nan ayi aure kawai ba shikenan ba.”
“Lallai kam! Keda shi waye babba? Ko bakisan he is busy bane yanzun ma squeezing time nasa zeyi bama wannan ba se in in-laws nakin suka kiraki kice musu ke baza kiyi ba nide na gayamiki anjima Omar ze amso miki d’inkunanki daga gun tailor seki had’a akwatinki.” Tana kuka ta koma d’akinta, babban tsoronta shine kar Adeel yaga pre wed’s d’in saboda tasan muddin akayi hoton dole ze gani, takira shi ta sanar dashi yanzu kuma batada courage. Ta shiga contacts neman numban Lubiee Adeel ya soma kiranta seda ta sa lock a d’akintan ta d’aga tare da clearing throat nata “hello Very Own.”
“Sweetest Love ya kike?”
“Lafiya” ta amsa sama-sama.
“Why whats wrong? Muryanki sounds not okay.”
“Bakomai kawai na buga k’afa na ne jikin gado.”
“Awcchh! Sorry Hun.”
“Its okay so ya kake?”
“Am good Sweetest Love anya kuwa buga k’afanki kawai kikayi? Something sounds really not okay.”
“Seriously...” Sekuma ta fashe da kuka. “Gosh! Did I say something wrong? Please stop crying” kukan ta tayi da k’yar ya samu tayi shiru. “Yanzu zaki fad’a mun mesa kike kuka?”
“Very Own babu.”
“So kike muyi fad’a abee? Tell me.”
“Very Own please no matter what happens know that I love you morethan words could ever tell and that I can die for you.”
“I know that Babe and I love you as much but why the sudden words?”
“Babu I just want you to know that no matter what you are the only love of my life.”
“I love you Babe, so much.”
“I love you too, what of now? In nazo gidanku neman auren ki still Baba will suspect?”
“He’ll Adeel mubari nan da months ahead haka.”
“Babe what if before then wani ya rigani zuwa fah? I can’t lose you.” Wani kukan ne yaso fin k’arfinta da k’yar ta danne sanin Al’ameen ya riga ya rigasa, batasan da wani bakin zata soma fad’awa Adeel aurenta saura sati biyu ba.
“I’ll call you later, I love you.”
“I love you too” jira tayi yayi hanging sannan ta koma kan gado ta cigaba da kuka. Da yamma kayakinta suka iso Mama da kanta ta had’a mata akwati a washegari suka wuce Abj ita da Mama achan suka had’u da Al’ameen, he couldn’t take his eyes off Zeezee dan yadda skin nata ke wani glowing. The following day best makeup artist na Zeezee wato Oshewa Beauty ta cancare mata makeup sannan suka wuce studio’n George Okoro sukayi pictures. Pictures are just lit and fire! Zeezee bataso 6ata pre wed’s nata ba saboda mutane irinsu Sumayya masu bacci da ido d’aya. Kafin ace me pictures se yawo yake a social media.
Kwana d’aya suka k’ara suka juyo ita da Mama.
3 days to biki Mama ta kawo wa Zeezee wani pepper soup na kazan daya sha had’in maganin gyaran jiki banda rashin dad’i bakomi tattare da shi. Zeezee na kai bite d’aya baki tace ita sam bazata ci ba, tsaye Mama tayi akanta da belt haka seda Zeezee ta cinye kazan tas wane zatayi amai.
****
Adeel ne miqe kan gadon d’akinsa yana viewing pics a instagram, yashiga ta explore kawai yaci karo da biggest and most shoking suprise of his life wato pre wed pic na Zeezee da Al’ameen wanda take sanye da hulansa na soja akanta sun rik’e da hannun juna suna dariya. Idanunsa ya shiga murzawa danko ya kasa believing what he is actually seeing, gashi de a zahiri Zeezee yake gani a hoton amman ya kasa believing itance. Tapping hoton yayi nan name nata da akayi tagging yafito assuring him itance ba me kamanninta ba.
“No! No! It can’t be possible it just can’t, this is not Zainab me kama da ita ne” yayi maganan yan kad’a kai still not believeing. Wani irin ciwo yaji a zuciyarsa wanda be ta6a witnessing ba wurgi yayi da samsung J7 dake hannunsan seda ta tarwatse. Wasu zafaffun hawaye ne suka soma sauk’owa daga jajayen idanunsa a yayinda kansa ke masa wani irin sara. Da k’yar ya iya mik’ewa ya ciro iphone nasa daga wardrobe ya kira Lubiee.
***
Tana shirin zuwa gidansu Zeezee ta tsaya tayi picking “hello Adeel?” Kawai jin sautin kukansa tayi “omg! Adeel are you okay?” Shiru be amsa ba “kana ina ne? Hello Adeel?”
“Lubiee tell me it aiint true kinji? Dan Allah tell me its not.”
“Whats not true? Ban fahimce kaba.”
“Z... Z... Zeezee.”
“Meya samu Zeezee kuma?!” Tayi maganan hankali tashe a cewarta ma kowani abunne ya samu Zeezee.
“Aure Zeezee zatayi?” Dum! Zuciyarta ta buga ina kuma Adeel yasamu wannan labari kode Zeezee ce ta fad’a mai? Kai No halan yaga pictures d’inne a instagram. “Answer me please pre wed nata nagani dawani soldier, itace? Is she really the one? Is Zeezee getting married to someone else? Ke kad’ai zaki iya amsa min wannan tambaya.”
“Adeel calm down okay?”
“How can I calm down Lubiee? Zeezee zatayi aure and wani zata aura for all this while she’ve been cheating on me shiyasa koda nace mata zan tura Uncle Abdul gidansu take tamin corner-corner ashe this was it, she have someone already. I should have guess.” ya k’are maganan sounding disappointed.
“Omg! Adeel stop saying all these kaima kasan kalan son da Zeezee ke maka, its not what it seems.”
“Ni just answer me itace ko ba itace ba?”
“Itace amm-” katse wayan yayi a kanta koda ta shiga gwada line nasa kuwa bayi shiga. Yini Adeel yayi ranan yana kuka indeed this is the biggest heartbreak daya ta6a witnessing a rayuwansa.
Lubiee kuwa koda ta isa gidansu Zeezee takasa fad’a mata abinda ya faru sabida batasan ta ina zata fara ba.
Da daddare Zeezee tayi trying both lines na Adeel sede switched off yake ta cemata, sanin ba halinsa bane switching off phones nasa hankalinta ya matuk’ar tashi. Lubiee takira right away “hello Babe meya samu line na Very Own bayi shiga? Inason mishi magana, its high time I tell him the truth.”
“Ermm.. Ni... Nima ban sani ba fa tun d’azu nake trying.” Sede don yadda Zeezee tasan Lubiee ta gano k’arya Lubiee ke. “Babe you are hiding something from me dan Allah ki gayamun meya samu Very Own d’ina? Yayi accident ne? Is he badly injured?”
“Zeezee enough of the panicking please ba abinda yasamu Adeel nima nayi trying line nasa it aiint going through.”
“Babe please don’t lie to me on this, I can sense it ba lafiya ba dan Allah meya samu Very Own?”
“Zeezee wallahi babu abinda ya sami Adeel just that... Just that...” sekuma tayi shiru.
“Just that what? Tell me please.”
“He has find out the truth already Zeezee.”
“Truth about my wedding? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” sekuma ta fashe da kuka “Babe how? I intended on telling him everything tonight dan Allah tell me its not true, please...” ta sake rushewa da kuka.
“Please ya isa kuka is never a solution I know Adeel he’ll calm down soon enough, if he does nida kaina zan mai explaining komi please kibar kukan haka.” Har anan Zeezee kuka take, “Lubiee na fiki sanin Adeel wallahi baze ta6a sauk’owa ba, koda zeyi ma ba nan kusa ba nikam na mutu na lalace, Al’ameen be kyautamin a rayuwa ba” tana kaiwa nan ta katse wayar. Wurgi tayi da kanta bisa gado ta shiga rera kuka tana sumbatu ahaka Mama tazo ta tarar da ita ba kalan tambayan duniyan da batayi wa Zeezee ba amman Zeezee tak’i tankata. Daga k’arshe ma kawai tayi suggesting halan kukan shagwa6an barin gida Zeezee ke.
Kwana ranan Zeezee tayi tana trying layin Adeel sede sam its not going. Washegari Lubiee itama ta gwada line na Adeel bai shiga tana gama shiri tazota gidansu Zeezee inda ta sameta se kuka take Mama na a tsaye a kanta ta zuba mata ido. “Ina kwana Mama?” Lubiee ta gaisheta.
“Barka ma da kika zo Lubabatu, shin meke damun k’awar taki? Ba kalan tambayan duniyan da ban mata ba tak’i fad’amin. Tun jiya take wannan kuka ga gida ya soma cika da mutane banason a fara k’ananun magana cewa auren dole Babanta keson mata.”
“Shikenan Mama zan mata magana kije ba damuwa.”
“Yauwa please.” Mama na ficewa Lubiee taja crying Zeezee jikinta “Babe its okay please kinga kukan nan baida amfani bashi ze dawo da Adeel ba, yau zanje gidansu in samesa in person kinji?” Take Zeezee ta d’ago kai “please kije ni ko yanzu nema kije ki samesa I need him badly.”
“I will amman sekin bar kukan nan.”
“Wallahi na bari” tasa hannu ta share hawayen nata. Sosai idanunta suka kumbura sukayi water bags a k’asa.
“Toh bari naje na same san” anan Lubiee ta fice zuwa gidansu Adeel.
Mamin shi kad’ai ta tarar bayan ta gaiaheta ta tambayi ko Adeel na gida.
“Ai Auta na baya nan Lubabatu, be fad’a miki zeyi tafiya bane?”
“Tafiya Mami?!” Lubiee tayi exclaiming.
“Eh fah.”
“Amman lafiya dai ko?”
“Toh kinsan halin Auta baya son sanar dani problems nasa, nide all I know is tun jiya ko lunch yak’i fitowa yaci yau da safe kuma na gansa fuskansa duk a kumbure yana rik’e da akwati. Dana tambayesa ko lafiya kuma yacemin lafiya kawai ze wuce Florida ne yaje ya huta achan yanzu haka yana Abuja d’azu ya kirani kan sunyi landing.”
“What?! Florida ze wuce?”
“Eh wai.”
“Toh Allah sa lafiya ya kuma dawo dashi lafiya amman Mami ya gaya miki for how long he’ll be staying there?”
“A’a gaskiya nima ban tambaya ba becika son tambaya haka ba.”
“Toh numbansa nakeso zan kirashi.” Bayan Mami ta bata layin tayi godiya sannan ta fice a bakin gate ta kira layin Adeel thankfully ya d’aga “hello Adeel?”
“Lubiee?” Ya tambaya not sure.
“Eh ni, kai haka akeyi ne Adeel? Yanzu ka kyauta kenan tun jiya Zeezee ke kuka-”
_Disconnected_ taji tana dubawa taga hanging call d’in Adeel yayi kafin tace zata sake kiransa har ya cire sim d’in ya karya. Tashin hankali! Kasa komawa gidansu Zeezee tayi. Zeezee ko tun d’azu jiran Lubiee take jin shiru ta kirata da kaman Lubiee bazata d’agaba sekuma ta canza mind nata “hello Babe I’ve been waiting for you since, ina kika shiga?”
“Uhn Ummi ce ta kirani wallahi I had to go back home.”
“Oh ayyah kinsamu kinje gidansu Adeel d’in?”
“Uhm-”
“Please don’t lie to me, komin d’acinta ki gayamin wani yanayi kika tsinci Adeel please.”
“Zeezee I’m terribly sorry, I went Adeel bai gida yana Abj as we speak now daga can ze wuce Florida for a break regarding what happened.”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! No! No! No please!!!” jefar da wayan nata tayi ta ruga aguje zuwa bayi tasa lock. Bajewa tayi k’asan toilet d’in tana kuka wane don shi aka turota. Hakan ta cigaba dayi seda hawayenta ya kusa k’arewa. “Adeel why do you have to leave me please, why? You know right I can’t leave without you please come back it doesn’t have to be this way.” Seda tayi calming kanta ta fito ta d’au wayar several missed calls na Lubiee ta tarar nan ta kirata back “thanks Gee!” Lubiee tayi exclaiming.
“Lubiee kimin sending digits na Adeel if kinada please.”
“Wallahi bani dashi sabo wanda Mamin shi taban ma yabar shiga maybe ya karya koya kashe wayan. Yanzu ba lokacin damuwa da Adeel bane it might follow afterwards kinsan fa jibi za’a fara wedding events naki inhar kikayi ruining su Sumayya sun samu abin magana akai kenan. Please ba don ni ba don Allah ki manta Adeel for now kinji? Kiyi hak’uri.”
“Thank you sekinzo gobe” nan tayi hanging. Haka koda Mama ta kawo mata maganinta yau tasha ba tare da sunyi long drama ba takoma gado ta kwanta. Mama de harta gaji da tambayan Zeezee whats her problem.
A washegari Yasmeen, Fateemah da mazajensu suka hallaro.
_PROGRAMS OF EVENT Starts..._
Da Tea party suka fara, event ya had’u iya had’uwa sede Zeezee sam ba walwala tatattare da ita su Lubiee kad’ai sukayi enjoying party’n through out the event tunanin Adeel Zeezee ke. The following day akayi English dinner Zeezee and Al’ameen nailed it a wajen ba’a cewa komi se wanda yagani, naira yayi kuka. Bayan english dinner akayi Kamu se sword crossing wanda yafi dukannin events d’in so far had’ewa. The next day which is Friday aka d’aura auren MAJ-GEN. MUHAMMAD AL’AMEEN SHETTIMA da ZAINAB ISMA’EEL YUSOUF akan sadaki naira dubu d’ari biyu.
Zeezee najin an d’aura aurenta da Al’ameen ta rikice musu a gida ranan. Kuka tayita yi wane zata cire ranta. Ita abubuwan ma sun taru sunyi mata yawa. Na farko ba wanda takeso zata aura ba, na biyu ga barin gidan da zatayi and above all rashin Adeel nata. Su Mariam sun bata hak’uri har sun gaji, haka Lubiee, Fateemah da Mama ma. Wani kukan ma seda dangin Ango sukazo d’aukan Amaryarsu. Zanin Mama ta kama k’ememe tak’i sakewa se rusa kuka take tana sumbatu tana ita ta fasa auren. Ba yadda basuyi ba a fito da Zeezee sun kasa daga k’arshe Baba aka kira tana ganinsa ta ruga aguje ta nufi kansa tare da tattara jamfansa a hannu tana kukan cire rai tana basa hak’uri dan Allah ya barta ta cigaba da zama a gida ta tuba bazata sakeyin wani rashin hankali ba. Seda Zeezee tasa idon Baba yayi ja saboda yadda take kuka sosai har se ji yake kaman yasa Al’ameen ya saketa a fasa auran amman hakan bame yuwuwa bane.
“Yi hak’uri Zeezee, everything will turn out perfect kibi su Ayshah kinji? Muma zamu taho daga baya, muna tare ai Hafsah zoki jata.”
“Baba dan Allah kayi hak’uri Mama please karku fitar dani daga gidan nan.” Haka da k’yar aka fitar da ita aka sata mota zuwa gidanta, su Lubiee se hak’uri suke bata. Not long enough aka hau shirin dinner, makeup na ranan shine beyi kyau ba saboda yadda fuskan Zeezee ya kumbura bayan nan kuma tak’i ajiye fuskan nata se kuka take. 8:30pm suka wuce Zaranda Hotel inda za’ayi program d’in. Ai ganin hotel d’in kawai ta sake tunawa da Very Own nata. Suna zaune da Al’ameen a motar ta shiga rusa mai kuka, beso mata magana ba saboda yasan theres no point doing so and koda hak’uri ya bata ma sake worsening situation d’in zeyi dan haka kawai ya zuba mata ido se aikin kukan take. Dai-dai driver yayi parking Al’ameen juya ya kalleta “My Princess all shall be well kinji? Stop crying haka, our families awaits us.” Wani wutan tsanansa ne ke ruruwa a zuciyarta ko kallonsa batayi ba, da k’yar su Lubiee suka fito da ita daga motar. Tabari ya rik’e hannunta ma tak’i haka through out the event tak’iyin murmushi bale dariya se tissue take sawa a idonta tana tare hawaye.
*™ MrAndMrsMuhammadAl’ameen.*💑
*© MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
7 comments:
Tnks dear
Enx sis ..... Cnt wait for when zeezee wil realise maj-Gen ix her beta half
Wow this is awesome pls continue
Muna jire de sis
Muna jire de sis
Pls sis don't leave us in suspense kisa mana next page din pls
Ever wanted to get free Instagram Likes?
Did you know you can get these AUTOMATICALLY AND TOTALLY FREE by getting an account on Like 4 Like?
Post a Comment