Friday, 20 January 2017

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE
PAGE 38

  *January, 2017*



   
     _09:34AM_
   Zeezee ta gama shiri tsaf sekace wacce zata gidan biki. Tana kan pancaking face nata Al’ameen yayi knocking bisa k’ofa tare da shigowa “My Princess har kin shirya ne? I thought kina bacci ai.”
  “A’a na tashi since.”
  “Jikin da sauk’i kenan.”
  “A’a wallahi kawai de na dage ne yanzu haka kaina ciwo yake min just now nayi amai ma.”
  “Subhanallah sannu ko? Muje mu karya toh muje asibitin yaso daga chan se nayi dropping naki a gida zuwa Maghrib na d’auko ki.”
   “Wai kai ka d’au yini kawai zanje inyi? Rashin lafiya fa nake” akwatinta ta fiddo daga lungu “ina kuma zakije da wannan?”
  “Gida mana.”
“Lafiya daiko?”
  “Kaman ya lafiya zanje gida Mama ta kula dani mana.”
  “Zainab yanzu sabida fever’n da be kwantar dake ba shine zaki had’a akwati zaki gida?”
  “Kamar ya be kwantar dani ba? Dan ya d’an sakeni yanzu sekace haka? Ai zuwa anjima ze dawo.”
  “A’a baza ayi haka ba, tunda ina gida i’ll take care of you yanzu muje asibitin.” Bajewa tayi k’asa gun tahau rusa kuka haka kawai ze kama yayi mata ruining plan wallahi k’arya ne. “Wallahi ni se ka kaini gida, ni Mama nakeso ba kai ba wayyo Allah!!” Ihu ta cigaba dayi wajen tana kururuwa a yayinda yayi tsaye wajen kawai yana mamakin yarintarta.

   “Is okay toh naji tashi mu kaiki gidan bar kukan haka.” Hannu tasa ta share hawayenta “anya kuwa Zainab ba faking rashin lafiyar nan kike ba?”
  “Kaman ya faking? Ana k’aryan rashin lafiya ne? Kai kanka fa kaji yadda tempreture na yahau d’azu Allah banida lafiya.”
  “Toh get well soon.”
   “Yauwa kuma ni bazan je wani asibiti bafa Mama zata kula dani.”
   “As you wish lets have breakfast” nan da nan suka karya aka fito mata da akwatinta, acikin mota Al’ameen ya kalli Zeezee daketa buga Candy Crush a wayanta sannan yace, “Princess sekuma yaushe zaki dawo?”
“Idan fever’n yayi sauk’i kaman nanda one week haka.”
  “Har one week?”
  “Wani har nema? Dan bance zanyi wata ba?” Bada dad’ewa ba suka isa gidan nasu. An bud’e mata k’ofa ta fita kuma seta k’i. “Any problem?” Ya tambayeta.
   “Yanzu na taho gida bazaka d’an bani kud’i na rik’e a hannu na ba?”
  “Yaushe ne na baki 20k Zainab?”
  “Ni ba abinda na tambaya ba kenan in kud’in ne bazaka bayar ba shikenan.”
  “Toh ni ban fito da kud’i ba” sarai da akwai kud’i a pocket nasa dakuma motar ma in whole amman baze bata ba tunda rashin kunya tasa a gaba.
  “Kar Allah yasa ka bayar d’in.” Buga masa murfin motan tayi wane zata 6alla sannan guard yabita da akwatinta ciki, binta da kallo Al’ameen yayi tare da kad’a kai.

   ****
   Koda ta shiga ciki bata tarar da Mama ba saboda ta fita unguwa ana sunan ‘yar k’awarta. Sallama tayi Baba dake shirin fita kasuwa ya fito “a’a K’anwata ya da akwati? Lafiya dai ko?”
  “Ina kwana Baba?” tayi maganan wane maras lafiya tare da tsugunawa har k’asa.
   “Amsani de tukun meya faru?” acewarsa ma sakinta Al’ameen yayi, his biggest fear.
  “Lafiya k’alau Baba nice bana jin dad’i zazza6i yasani gaba chan kuma bame bani kulawa Ya Al’ameen kullum bai gida shine yayi suggesting nazo nan nad’an huta.”
  “Toh hakane? Amman don zazza6i shine har sekin dawo gida K’anwata?”
  “Toh Baba bazan iya kula da kaina ba yanzu haka daga asibiti muke ammin allura.”
  “Wai wai har allura? Sannu K’anwata sannu, k’ariso ciki toh.” Da kansa yaja mata akwatinta (iyayen d’aure ma k’arya gindi ba.) Bada jimawa ba ya fice kasuwa nan Zeezee ta samu kanta. Waya tahau yi da Adeel kaman ba gobe. Harda La’asr ba wanda yadawo cikin su Baba. Se chan 5:46pm Mama ta dawo gida all exhausted ganin Zeezee tayi a kitchen tana soya k’wai aikin kenan kullum, kafin tace zata 6oye plate d’in har Mama ta ganta. “Zainab!”
  “Na’am Mama sannu da zuwa.”
  “Sannu de tun yaushe kike nan?”
  “Tun safiya fah Baba yace kin tafi gidan suna.”
  “Eh wallahi Fateey’n Maman Fateey ce ta haihu.”
  “Ayyah sannu da zuwa, arghh! wayyo kaina!” Tayi faking exclamation.
  “Me kuma ke damun kankin?”
  “Oh! Ban fad’a miki ba ko? Wallahi zazza6i ne yasani gaba for the past three (3) days shine Ya Al’ameen yace na taho gida zanfi samun kulawa.”
  “Ban fahimci wai kidawo gida ba wai kina nufin harda akwatinki?”
  “Eh toh achan bame kula dani.” Tafe hannu Mama tayi in suprise tana mamakin gut irin na Zeezee “yanzu don zazza6in k’aryan da am sure kika k’irk’iron shine kika dawomin gida da zama?”
  “Mama wallahi ba k’ar-”
  “Rufa min baki” ta katseta da wuri, “ni zaki raina ma wayo ko jinki bansan wannan d’an banzan halin da kuke developing bane ‘ya‘yan yanzu? Da zaran kunga kun fara aikatuwa a gidan aurenku seku d’ibo k’afa ku dawo gida da sunan wai bakuda lafiya ko ba haka ba? To ki bud’e wannan kunnuwan k’ashin naki ki saurareni da kyau wallahi ba a gidana za’ayi wannan iskanci ba kina jina ko? A da dabaki fara su shara ba ai baki ta6a cewa bakida lafiya ba se yanzu. Maza-maza ki had’a kayakinki kiyima Maj-Gen waya yanzu ya turo a d’aukeki.”
   “Mama wallahi ba haka bane Allah banida lafiya ai Baba ma yaga shigowa na kuma ya amince na zauna anan har sena samu sauk’i.”
  “Babanku kam dama ai komi ma amince miki yake tunda shi har yau be koyi darasinsa ba, maza ki kira Maj-Gen ba a gidana za’ayi wannan sakarci ba wallahi, kin ta6a ganin Mariam ta dawo gida da sunan bata lafiya ne? Koda ta haihu batace zata dawo gida ba nice naje na sameta mesa baza kiyi koyi da yayyun ki ba? Bazaki motsa bane?”
 
   Kuka Zeezee tasa gun ita a dole batada lafiya. “Wai jiranki nake ne?” Tana tsugune gun tana ta k’irk’iro kukan k’arya tace, “wallahi Mama banida lafiya ki kira Ya Al’ameen ki tambayesa abinda har allura mun d’auka min.”
  “Wato se kinji na jaki zaki tashi ko?”
  “Wallahi Mama banida lafiya dan Allah kibarni na zauna anan, ina warwarewa zan koma gida na.” Ana cikin haka Baba da Omar suka dawo suka samu su Mama in the act. “Sannu da zuwa Alhj, Omar sannu.”
  “Yauwa sannu Mama.”
  “Sannu Hafsah meke faruwa haka kikasa patient agaba?”
  “Patient? Wace patient d’in?”
  “Zeezee mana ko bata gaya miki ba tada lafiya bane?”
  “Baba wallahi na gaya mata wai sam k’arya nake.”
  “Ai k’aryan nema, rashin son aiki yasa kika gudo nan koba haka ba?”
  “Wallahi ba haka neba.”
  “Haba Hafsah! Ana k’aryan rashin lafiya ne? Kuma munyi waya da shi mijin nata ma ya shaidamin batada lafiya.”
  “Yo Maj-Gen kam ai dama haka zece maka tunda Zeezee tafi k’arfinsa amman wallahi ‘yar nan k’alau take.”
  “Allah banida lafiya.” Omar dake tsaye wajen yana kallonsu don kansa ya nufi site nasa saboda shima yasan k’arya Zeezee take.
   “Ya isa haka Hafsah tunda ba’a kanki ‘yar nan zata kwana ba, ba ruwanki musamman mijinta ya kawo ta saboda batada lafiya kice k’arya take?”
  “Nikuma kaji na rantse da Allan da raina ke hannunsa baza ayi wannan rashin hankali a gida na ba, wani rashin lafiya ne anan yarinya duk tayi kumatu saboda yadda takejin dad’i a gidan miji amman don rashin son aiki ta gudo wai batada lafiya? Wallahi bazan bari ba yanzu, yadda ka lalata tarbiyyan yarinyan nan ada kayi ma yanzu, Zainab zata koma gidanta ko tana so ko bataso ni na gaya maka.” Ta k’are maganan in a serious tone sosai tabawa Baba mamaki be ta6a jinta tana d’aga murya haka ba hakan na nuni da yadda ranta ya matuk’ar  6aci kenan.
   “Me yayi zafi haka Hafsah na? Yi hak’uri mana” yayi maganan in a soothing tone.
  “Ai ba zancen hak’uri bane ‘yar nan bazata kwana gidan nan ba.”
   “Naji toh yi hak’uri kinga Maghriba ya riga yayi yanzu kiyi hak’uri kibarta ta kwana nan yaso gobe da safe seta koma chan gidan nata. In rashin lafiyan ya sake tak’urata yaso sekije ki sameta ko?”
 
   “Har se gobe ta koma gida? A yau d’innan zata koma, yarinya sam batasan ciwon kanta ba ke bakisan da haka zakiyi creating space wa Maj-Gen. ya soma kula matan waje bane? Saboda time da ya kamata kina tare dashi baki nan as kinzo nan kina faking rashin lafiya ni na gaya miki a gobe zaki koma gidanki aikin banza kawai.” Mama na kaiwa nan ta fice, kuka Zeezee ta shigayi shikenan Mama ta rusa mata plan nata yanzu haka zata koma ta cigaba da bauta wa Al’ameen? Wayyo ita.

   Hak’uri Baba yata bata da alama har ya mance da kalan rashin hankalin da Zeezee tamai a baya be koyi darasinsa ba har yanzu. Zeezee na kwance a d’akinta se turo baki take gabad’aya ji take kaman ta gudu taje somewhere tasamu Adeel nata. Video call da sukazo sukayi da Adeel nema ya d’an farinta mata rai.
  Kafin Al’ameen ya kwanta seda ya kirata don yi mata ya jiki amman dake a cike dashi take, gani take duk laifinsa ne yasa ko d’aga wayan ma batayi ba.

*~ *~ *~
  Washegari tun 8am Mama ta kira Al’ameen da kanta ta buk’acesa da ya turo driver’nsa yazo ya d’auki Zeezee maza-maza kuma koda wasa kada ya sake bari ta baro gida inhar Zeezee batada lafiya ne dagaske nan gaba ita da kanta zataje ta zauna akanta, fad’a sosai tamai da yadena zubawa Zeezee ido tana abinda taga dama yana mata fad’a sede shi yana ganin baze iya ba, ansan soldiers da fad’a da zafi but when it comes to their loved ones they are damn sweet, calm and quiet!
   Tara saura driver’n Zeezee ya iso, sam bata so tafiya ba. Fad’a Mama tata mata kaman ba gobe.

***
     Su Zeezee suna isa gida tafito daga motar a fusace not minding ta rufe k’ofar, zaune bisa dining table yana having breakfast ta tarar da Al’ameen, wani d’an banzan harara ta watsa masa sannan ta nufi d’akinta direct inda ta baje tayita kuka kaman ba gobe. Seda tayi ta godewa Allah sannan ta nufi bayi ta wanke fuskanta tafito ta zauna bakin gado tana tunani ya zatayi tasa Al’ameen ya saketa, shin wani rashin hankalin zata mai da zesa ya rabu da ita? Gabad’aya ta shiga damuwa yanzu saboda yadda Adeel kece mata bata damu dashi ba yanzu don kuwa da tayi da tuni ta kashe auran nata (wa'iyya zubillah!) Dabara ce ta fad’o mata, wata maqirar murmushi ta saki. A ranan gabad’aya word be had’ata da Al’ameen ba saboda ko shiga d’akinta beyi ba shima.
   Washegari bayan ta k’are chores nata sun karya Al’ameen ya shirya tsaf sannan yazo yayi mata sallama kan ze fita ko ta kansa batayi ba banda dogon tsukan data ja mai. Yana fita taja mayafinta itama ta nufi gidan k’awarta Hajar datayi aure recently, bayan ta fayyacewa Hajar plan natan tayi promising nata 100k inhar tabata had’in kai suka gudanar da wannan plan, kasancewar Hajar money monger ce tuni ta amince.

   _2 days later..._
     Ana sauran kwana hud’u Al’ameen ya koma ABJ, yana zaune a parlour as usual yana kallon sports aka danna door bell yana dubawa yaga bak’in fuskoki guda biyu amman sede yana da tabbacin k’awayen Zeezee ne. Ya bud’e yayi musu sannu da zuwa sede meh? Take Hajar tahau sa da tsiwa “ina matar taka take? Wallahi ta fito ta biyani kud’ina ai ba haka mu kayi da ita ba, kota ban kud’i na kona kai k’aranku duka police station tunda kaine mijinta.”
  “Wait, wait what is going on here guards!” Take suka mammatso “kunsan wannan faces?” ya tambayesu in an authoritative voice.
   “No Sir sunce mana de k’awayen Madam ne.”
   “And mena ce muku about letting strangers in?”
  “We are very sorry Sir but they told us they are friends.”
  “It shouldn’t repeat itself, am I clear?”
  “Yy.. Yes Sir thank you” sukayi saluting nasa tare da ficewa.
  “Baiwar Allah kode kinyi 6atan kaine?” yadawo da kallonsa akan Hajar dake ta admiring kyansa ita bama wannan ba muryansa ne ke tafiyar mata da imani, me bawan Allan nan ya rasa da Zeezee ke neman ya saketa? Ai ita wannan ma ya fiye mata Adeel wallahi, dake wa tayi;
  “Ba wani 6atan kai ko ba nan bane gidan Maj-Gen Al’ameen me mata Zainab?”
  “Nan ne nine ma maigidan.”
  “Good so nake ka fito min da matarka ta biyani kud’i na wallahi.”
   “Kud’i you mean kina bin Zainab bashi? Since when?” yayi maganan damn suprised.
  “3 weeks back.”
  “Subhanallah, nawa kuma?”
  “500k.”
  “What?!” yayi exclaiming jaw dropped.
  “Ai ka jini de kuma ba sharri nake mata ba wallahi tafito taban kud’i na ace babban mutum kaman ka amman kabari matarka tana cin bashi awaje Allah wadai wallahi, nide aban kud’ina konayi kururuwa in tara maku jama’a.”
   “Ko kinsan a gidan soja kike kike wannan batu? And how can you accuse my wife?”
  “Aww ma tambaya kake? Zainab!” ta shiga k’wala wa Zeezee kira “Zainab kifito nan.” A farko Al’ameen yayi niyyan yasa guard nasa suyi mai waje da Hajar da k’awarta amman ganin yadda ta dage kan sam wallahi da akwai bashinta gun Zeezee ya shiga duhu shin har yaushe Zeezee taci bashin 500k besani ba? Wani irin kud’i ne bai bawa Zeezee da zata nemi ta tozarta sa a idanun jama’a da girmansa da komi zata mai haka meya mata? A gaban k’ananun soldiers nasa bujakai wanda basu kai sun kawo ba sun tsaya suna gaya mai magana gaskiya abin Zeezeen kuma ya soma yin yawa “ina zuwa” kad’ai ya iya ce dasu sannan yaje yasamu maqirar zaune kan gado, yi tayi kaman bata da masaniya kan abinda ke faruwa.

   “Zainab?”
  “Meh? Menayi kuma yanzu?”
  “Shin dagaske ne kin ranta bashin 500k gun k’awarki baki biya ba?”
   “Sosai ma kuwa anyi haka.”
  “Sabida mesa?”
  “Kaman ya sabida mesa? Baka bani kud’i ishasshiya ba ba dole naci bashi ba.” Magana ya soma a fusace sabida ransa ya matuk’ar 6aci, bayason abinda ze ta6a masa suna.
   “What nonsense Zainab? wani irin kud’i ne ban baki ba? White gold naki be 6ata ba kince ya 6ata na sai miki sabo, I heard you the other day on the phone kina ciniki zaki siyar da shi duk ban miki magana ba, yanzu kuma seki nemi tozartani ki 6atamin suna agari ace babban mutum kaman ni nabar matana tana cin bashi a gari?”

  “Wow! Wow!” Ta tahau yin tafi “I like where this is going finally kafara fighting back ai da hakan kakeyi tunda a baya da warhaka mun tarwatse, bakason sunan ka ya 6aci a agari? Fine and good seka bani takarda na yanzu-yanzun nan ko minto d’aya kada ka k’ara aikin banza kawai baka bani kud’i ba ya kakeson nayi? Ko ka ta6ajin Baba yace maka naci bashi lokacinda nake gidan shi ne? Kai ka d’aukoni ka kawo ni nan dole kayi hak’uri da dukkanin abinda zan maka kuma believe me this is just the start wallahi I will never rest until da hannunka ka d’au takarda na ka miqa min mschwww!”
  “Haka kikace?”
  “Ai hakan nema, ko ka biyasu kud’insu kokuwa ka sakeni Baba na ya biya min tunda ba matsiyaci neba shi.”
  “Ya miki kyau” kad’ai yace mata sannan yaje ya rubuta wasu Hajar cheque na 500k tare da basu hak’uri on behlaf of Zeezee.

   Su Hajar suna isa gida tama Zeezee waya “Babe ga cheque nan fa har Ogan naki ya bamu.”
  “Aikinki yayi kyau gobe zan taho miki da 100k d’inki.”
  “Toh ya yanzu? Yace ze sake kin?”
  “Wannan mayyen? Ai inba maqora na kaisa ba, baze ta6a saka na ba.”
  “Toh amman Zeezee meyasa kikeson rabuwa da miji kaman Maj-Gen.? Bawan Allan nan banga abinda ya rasa ba ga kyau ga hankali most of all ga sweet voice.”
Allah ko? bari Ahmed (mijin Hajar) ya jiki ba ruwa na.”
  “LOL but seriously.”
  Toh ni duk feautures d’in ba burgeni suke ba, Adeel kawai nakeso.”
  “Allah baki shi toh sena ganki goben.”
  “Ameen bye!” nan tayi hanging yau ma kaman jiya word be sake had’ata da Al’ameen ba ko duba ta da Asuba beyi ba saboda abinda ta masa ya mugun 6ata mai rai.

   ****
  A washegari kaman yadda ta saba fita bada izininsa ba da sassafe ta tashi ta gama ayyukanta ta karya sannan ta fice yawonta. Ba Al’ameen ya tashi ba se to 10am nan yayi wanka shima jin ba motsinta yasan tafita yau ma, breakfast ya aika aka siyo mai yana cikin karyawa wayansa ya shiga ringing yana kai dubansa kuwa yaga Hjy Sadeeyah, batare da 6ata lokaci ba ya d’aga “halo Big Sis.”
   “Na’am Little one kana gida?”
  “Eh ban koma aiki ba tukun se jibi.”
  “Oh to gamu da Mama mun yanko kwanan gidanka.”
  “You mean kuna Bauchi?!” yayi exclaiming.
  “Yes gamu nan ma a bakin gate yanzu.” Mumunar fad’i gabansa yayi yasan halin Sadeeyah sarai ba shakka taje ta irgawa Mamansu halin da yake ciki ne Mama ta ibo k’afa all the way from Kaduna ta taho nan. Tunanin me zeyi ya soma wanda beyi nisa ba Sadeeyah ta danna doorbell. Jiki na k’yarma ya miqe ya bud’e musu. Salati kawai Mama ta saki ganin yadda fuskan Al’ameen nata yad’an fad’a ba shakka Sadeeyah batayi k’arya ba matar Al’ameen na basa wahala saboda ta samesa shiru-shiru bayi magana.  Al’ameen mutum ne da abubuwa basu cika damunsa ba inhar ko aka soma ganin damuwa tattare da shi to abu ya 6aci ne kwata-kwata ba kanta.

   “My Only Son?!” Mama datayi ageing about 67 tayi exclaiming tana shafa fuskansa pathetically.
   “Ai na gaya miki Mama, kinga yadda ya rame kuma believe me wallahi time dana zo bekai haka rama ba.” Hannun Al’ameen taja suka shiga ciki suka zauna kan kujera d’aya a yayinda Sadeeyah ke zaune oppsite them. “Al’ameen Babana meke faruwa? Meke damunka?” Hannunta ya sauk’e da k’yar daga fuskan nasa, “babu Mama” sannan ya maida kallonsa kan Sadeeyah, “Hjy me kikaje kiga gayawa Mama kika sa tazo all the way from Kaduna, bakisan its bad for her health bane?”
   “Akwai abinda yakai min rashin kwanciyar hankalinka tashin hankali ne Al’ameen? Yanzu ace da raina amman bazaka sanar dani halin da kake ciki ba sede a bakin Sadeeyah? Itama da Allah be kawo taba sede rana d’aya inji matar taka ta sa maka ciwon zuciya ka fad’i ka mutu?”
   “Mama what are you talking about? Bafa abinda ke faruwa ki kwantar da hankalinki please ni banason abinda ze tayar miki da hankali.”
   “Ai ka ajiye kalman kwanciyar hankali a gefe, ina matar taka take?”
  “Uhm... Erm-” katsesa Sadeeyah tayi da wuri “ta fita yau ma kaman kullum ba? Ai na gaya miki Mama, wallahi kullum da safe seta fita yawo kuma karki manta ba breakfast take ajiye mai ba sekuma Magrib take dawowa.”
  “Thats not true Mama karki jita, Hjy enough please” yayi defending kansa.
  “Aww nice nake k’arya Lil Bro? Well lets see” dining space ta nufa sega take away nasa dayake having breakfast with, kai ta kad’a ta d’ago ta kai wa Mama, “ba gashi ba aikin kenan kullum cikin siyan takeaway, bata ta6a mai girki ba Mama meye amfanin wannan auren? Wallahi ina raye wancan shegiyar bazata wahalar min da k’ani ba, I just let her go kwanaki but not now not ever.”
  “Barni da ita Sadeeyah, haka kawai tasa min Only Son a gaba sabida taga baya magana? Ina matar taka take nace?”
  “Sekin tambaya ne Mama? Ofcourse ta fita yawon banzan data saba mana.”
  “Ina take Al’ameen answer me.”
  “Mama bata gida ta fita amman da izini na ta fita.”
  “Al’ameen yanzu ni zakayi wa k’arya? Ka kalli cikin idanu na kamin k’arya?”
  “Mama please...” Sekuma yayi shiru.
  “Da izinin ka tafita koko a’a? Karka min k’arya am damn serious.”
  “Bada izini na ta fita ba but pl-” katse sa Mama tayi “Sadeeyah d’au waya ki kira min iyayen yarinyar both baban da maman now! Za’a yita ta k’are yau.”





   *© MIEMIEBEE   ™YGC!*
   www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄

35 comments:

Anonymous said...

gsky hankulanmu sunyi matikar tashi kasancewan baki taba shuru hakaba
kullun muna tambayan kanmu meyake faruwa amma bama samun amsa saedai munata miki addua da fatan Alkhairi gareki
fatan Allah yasa kina lpy aduk inda kike kuma Allah ya albarkaceki.
muna tare da ke kuma muna farin ciki da ke Allah Ya kara baseera

Unknown said...

Kai sai yanzu hankali ya kwanta, Allah ya kara basira. Fatan alkhairi gareki

Unknown said...

Alhamdulillah tunda komai lfy. Da ftn kin dawo lfy

Unknown said...

Enx sis,Alhamdulillah d lng awaiting tym has com, May Allah be wit u nw nd always... More maiko to ur Elbow

Unknown said...

Alhamdulilllah!!! thank Allah ki na tare da mu yanzu. Allah ya kare mana ke ya kuma kara basira ameen.

Unknown said...

Alhmadulillah that you are back, may Allah SWA guide you every where you are, we missed you so much

Mzz Hajjo said...

yeppie 💃💃 my favorite girl is back. ....... all the best

Unknown said...

Alhamdulillah kina tare da mu haka zalika muna tare dake,da fatan kin dawo lafiya?mun gode da kokari, Allah ya kara baseera. Muna jiran cigaba plssssssssssssss

Unknown said...

Alhamdulillah kina tare da mu haka zalika muna tare dake,da fatan kin dawo lafiya?mun gode da kokari, Allah ya kara baseera. Muna jiran cigaba plssssssssssssss

Unknown said...

Alhamdulillah kina tare da mu haka zalika muna tare dake,da fatan kin dawo lafiya?mun gode da kokari, Allah ya kara baseera. Muna jiran cigaba plssssssssssssss

Unknown said...

Munata baza ido dai

Unknown said...

Miemiebee, we're still waiting for your next post please

Unknown said...

Kitaimaka kina mana posting pls

Unknown said...

Gaskiya na dauki kinshi kindawo daga tafiya,kina ja mana rai sis tunfa Friday.

Unknown said...

Gara kina sa mana tym pls instead of muyita dubawa bamu da tabbacin kinyi sabon post

Unknown said...

Enter your comment...
gaskiya wannan novel in yanada Dadi sede naga 2days bakya posting hop de Lfya kalau

Unknown said...

Sis u novel so amazing
Dan Allah ki cigaba we cant wait

Unknown said...

Miemie !!!!!!!!!!!!!!!! We ar waiting oo, if nt we will arrest u for kipin us in suspense.........

Unknown said...

Allah ya sa kimana posting yau dai.... Ai sai mu manta labarin ma

Unknown said...

Ai kuwa de

Unknown said...

Gaskiya kam

Unknown said...

Gaskiya,nikam har na gaji

Unknown said...

Gaskiya,nikam har na gaji

Unknown said...

Enter your comment...munji shiru kwana 2

Unknown said...

Enter your comment...munji shiru kwana 2

Unknown said...

Wlh dande bayanda ka iya ne kaika saka kanka amma wlh hkan babu dadi yakamata ki duba yar uwa bai kamata sbd zamu karanta book dinki ba sai kina ja mana rai irin haka ba inda wani matsala ne ki posting issue din once and for all saimu sani basai muna damunki ba muma

Unknown said...

Wallahi shatu kamar kinsan meke zuciyata
gaskiya kia ma dan gaya mana cewan mu Dan baki time kinga sai my daina damun kanmu,amma shuru ba magana.

Unknown said...

Wallahi shatu kamar kinsan meke zuciyata
gaskiya kia ma dan gaya mana cewan mu Dan baki time kinga sai my daina damun kanmu,amma shuru ba magana.

Abusuhaylarh said...

nice novels ........

Unknown said...

Sis Maryam Plz If U Dnt Av Tym 2 Post At Least Reply Our Cmmt Is't Bcos We Love Ur Novel U Ar Doin Dis 2 Us

Unknown said...

Mu hakura kawai kila tadaina ne

Unknown said...

Hmmmmmmmmmm

Unknown said...

Wynta ne ya baci

Unknown said...

Salam sisto....dix suspense z killing us oooo...Lol

Unknown said...

plz do reply for us to know dat u re in a gud condition....luv ya