BY MIEMIEBEE
PAGE 28
*January, 2017*
_I dedicate this page in honour to each and every *special member of my group, MIEMIEBEE NOVELS GROUP.* Sorry for enticing you guys yestarday๐
๐ I just couldn’t help it, how you guys are so eager to see Baba cutting off Zeezee’s head. Mugaye kawai!๐ That aside I love you guys so much, thanks for your maximum supports #OneLove๐_
“Dan Allah bayin Allah ku rufa min asiri karku kaini gida wallahi kasheni zeyi, kuji k’aina dan Allah” kuka tayita musu a motan tana had’asu da Allah amman kota kanta basuyi ba suna isa bakin gate driver yayi parking suka fito da Zeezee neman kwanciya tayi a k’asa amman haka d’ayan ya d’agata chak se cikin gida inda Baba, Mama, Mariam da Omar suke tsaye. Wani sabon kukan ta rushe dashi ganinsu, “aikinku yayi kyau nagode, you may leave” cewar Baba.
“Godiya muke” suka amsa almost a tare sannan suka fice. Taku d’ai Baba yayi ta direction na Zeezee dake zube a k’asa tana kuka Mama tasha gabansa, “Alhj dan Allah karka tab’ata” tunkud’eta yayi a zuciye sekace ba Hasfsar saba da wuri Mariam taje ta tari Mama kafin ta gama fad’i. Hannun Zeezee yaja seda ta mik’e tsaye ko kallon cikin idanunsa ta kasa. Mari lafiyayye ya sakar mata tas! Wani irin rikicaccen ihu ta saki a yayinda take hango stars, kafin ta farfad’o daga marin ya k’ara mata wata, Mama dake zaune a k’asa Mariam na tsaye a kanta tace, “Omar kaje ka karb’i Zeezee dan Allah karya kasheta.” Omar na nufan wajen Baba ya bud’e masa ido “wallahi Omar ka matso nan kaji na rantse maka zan tsine maka.”
Jin haka Omar yaja baya, hannun crying Zeezee Baba yaja zuwa d’akinsa yasa lock “Baba dan girman Allah kayi hak’uri na tuba” dorina me baki biyu taga ya ciro daga wardrobe nasa nan tasa ihu tana had’asa da Allah. Kir6ata ya shigayi, mutum na iya rantsewa ba mutum Baba yake daka ba. Ya gwara ta da bango, yayi ball da ita ya nausheta ba abinda beyi da ita ba, “Mama dan Allah kizo ki taimakeni Baba ze kasheni!” Su Mama dake tsaye bakin k’ofar se bubbugawa suke suna bawa Baba hak’uri amman se kaman sake tunzira sa suke, ya zabga mata bulalan yayi ball da ita sekace ba Zeezeen’sa ba. Amai Zeezee ta shigayi amman hakan besa Baba ya barta ba, tun tana ihu har yazamo hawaye kawai take.
“Alhj! Alhj! Dan Allah ka rufa mana asiri karka kashe yarinyan nan, Omar me kake jira ka b’alla k’ofan mana!” Mama tayi maganan tana jijjiga k’ofan.
“Ba gomma na kasheta na huta ba, ni zatayi wa abin kunya? Kasheki zanyi na huta ina adda na?”
“Adda?! Alhj kayi me dashi, dan Allah ka rufa mana asiri, Omar me kake jira ka b’alla k’ofar mana.” wardrobe nasa ya nufa ya shiga neman addansa shi a dole se ya yanka ta ya huta. Da k’yar Omar ya samu ya b’alla handle na k’ofan sukayi ciki da gudu Mama tayi kan Zeezee dake ta kwararo amai dai-dai nan Baba ya sami addan nasa, gaban Mama data tare Zeezee yasha “ki matsa Hafsah kona yanka ku tare.”
“Sede ka yanka mu taren kashemin ‘ya kakeson kayi? Meye amfanin haka?”
“Ki matsa nace!”
“Wallahi ba inda zanje.”
“Baba dan Allah kayi hak’uri she’ve had enough” cewar Mariam calmly.
“Kufita nace! Kubari na gama da ita kowa ya huta tunda ita iskanci ta d’au wa kanta” hannu yasa ze finciko Zeezee daga hannun Mama amman dan yadda Mama ta damk’eta ajikinta ya kasa. “Ko ke kad’ai ce ‘ya a gareni na yafe ki Zeezee-”
“Subhanallahi! Alhj karka zo kayi abinda zakayi nadama dan Allah kayi shiru haka ya isa kayi hak’uri.”
“Na fad’a na yafeta taje ta nemi wani uban, shi saurayinki da kika fi jin maganarsa akan nawa sekije ki samesa na baki nan da minti biyu ki tattara ina-ina ki kibar min gida konasa ‘yan sanda su baki d’ankaren duka.” Ganin har yanzu crying Zeezee bata motsa ba ya sake daka mata tsawa “bada ke bane?!” har a yanzu dan yadda ta daku lik’is takasa motsawa “wallahi ba inda Zeezee zata je, kai bakasan yin hakan sake ta6ar6arar da al’amarin bane? Wallahi k’afarta k’afata, muddin ka kori Zeezee nima sede ka nemen a gidan nan, Zeezee nada laifi amman kaine sanadin komi.”
“Hafsah stay out of this kina jina koh? Ke bazaki tashi bane sena kira ‘yar sandan ko ya? ‘yar iska karuwa kawai.”
“Baba dan Allah kayi hak’uri haka, Omar kabashi hak’uri” cewar Mariam.
“Ku fita daga d’akin nan ko dukanku na tsine muku albarka, ku fita nace!” A sanyaye suka bar d’akin.
“Tashi kibarmin gida ‘yar iska kawai, saurayi zaki fifita akaina ni ubanki? Yasmeen da Mariam ba yara bane? Ki tashi nace!”
“Alhj dan Allah kayi hak’uri” ganin har yanzu Zeezee bata motsa ba yasa hannu da force ya fincikota daga jikin Mama yahau janta Mama na binsu a baya tana had’a sa da Allah, dasu Mariam sunce zasu motsa Baba yace ze tsine musu har bakin gate suka kai yakaiga bud’ewa Mama ta sha gabansa da k’yar “Alhj don Allah nace, dan darajansa kayi hak’uri wallahi yanzu ka kori yarinyan nan sake lalacewa zatayi, think mana! Yanzu da muke kanta ma ya ta k’are bale ace ta wayi gari bame hore mata kayi tunani please.”
“Ina k’arshen iskanci shine karuwanci? Tou ta zama fiye da karuwa bare damen ba tunda na yafeta ban san da zamanta ba again, barin zauna a gari k’aramar k’waro kaman Zeezee ta b’ata min suna ba.”
“Alhj listen to yourself, koran yarinyan nan baida fa’ida wallahi sake lalata wannan al’amari zamuyi kamata yayi yanzu kasa mata ido.”
“Ki matsa Hafsah kokuwa a bakin auren ki.”
“Shikenan zan matsa amman wallahi kasani Zeezee na barin gidan nan nima zan bari kaji na rantse” Mama tayi stating in a serious tone.
“Haka kikace?”
“Eh wallahi haka nace ai kaji na rantse.” Kallo ya galla wa Zeezee dake neman sulalewa k’asa a hannunsa sannan yayi wurgi da ita tamkar kashi a gun seda ta buga kanta jikin gate, d’akinsa ya nufa a fusace. Nan su Mariam sukayi kan Zeezee, Omar ya cinci6eta se asibiti sukayi inda aka duba Zeezee aka kuma yi mata treating minor injuries. Se da Azahar suka dawo gida har alokacin Adeel bebar trying number’n Zeezee ba amman ba response, tsoronsa kuma kar yaje gidansu Zeezee ya sake making things worse than they already are.
Gabad’aya Mama haushi da tausayin Zeezee take a d’akinta ta kwantar da ita har a lokacin bata bar kukan ba kanta gabad’aya an zagaye da bandage dan yadda Baba ya faffasa mata shi. One last kallo Mama ta k’are mata cike da takaici sannan ta fice izuwa d’akin Baba. Mariam ce ta matso kusa da Zeezee tana kallonta pathetically “yanzu kin kyauta wa kanki kenan? Me amfanin hakan Zeezee? Look at the state of yourself kin kyauta wa kanki kenan?” Da k’yar Zeezee ta iya ta kad’a kanta.
“Toh kukan ya isa mana da uban wa yace kifita kik’i kwana a gida? Ashe ma this is not your first time me kike nema a duniya Zeezee? Kyau ne Allah ya baki, kinada iliminki daidan gwargwado mesa bazaki kare mutuncin ki kiyi aure a mutunci ba? Ajinki yanzu shi saurayin da kike bin ze yarda ya aure kine bayan ya riga ya sanki a waje?”
“Adda Mariam wallahi ni ban tab’a sanin wani d’a na miji ba.”
“Then mesa kike kwana a waje?”
“Sabida koda alokacin da aka gama party’n nace zan dawo gida k’ofa a rufe ne.”
“Hmm amman ‘ya musulma dake me zai kaiki attending midnight party? Bakida hankali ne?” Nasiha da fad’a sosai Mariam tayita wa Zeezee a yayinda Mama kecan d’aki tana yi wa Baba nasiha shima dan sam yace Zeezee bazata kwana gidansa ba yau ya yarda Maman ta bita su tafin. Ganin haka Mama tayita basa hak’uri da k’yar d’in k’yar ta samu ta shawo kansa ya hak’ura da Zeezee ta cigaba da zama a gidan amman she is not his responsibility.
“Kije kice mata ta kawo min wayan da suke communicating ita da d’an iskan saurayin nata.”
“Wani erin waya kuma Alhj? Tanada wani wayan ne bayan wanda ka fasa mata?”
“Da dame kika d’au take communicating dashi? Kije kice tabani dan wallahi inhar bata kawo ba zata bar gidan nan this very instant.”
“Naji zan mata magana” da wuri tayi d’akin Zeezee ta sameta zaune bakin gado se rusa kuka take, harara Mama ta watsa mata sannan tace, “bani wayan, kika min k’arya kuma wallahi zakisha mamaki.”
“Mama wani waya?” Tayi speking up finally.
“Aww k’arya zakimin? Inbar Baban naku ya sake miki dukan da yafi na d’azu ya koraki ko?”
“A’a dan Allah kiyu hak’uri.”
“Then kawo.”
“Zeezee bada inhar akwai” wayar cewar Mariam. Hannu tasa a bra nata ta ciro samsung d’in cike da mamaki Mariam ta tsaya tana kallonta amsar wayar Mama tayi tana k’are mai kallo sannan back to Zeezee.
“Zainab me yaron nan ya miki? Mesa zaki fifitasa kan iyayenki? Shin wai damu dashi suwa sukafi daraja a idon ki?”
“Mama wallahi na tuba dan Allah kuyi hak’uri.”
“A’a ki amsani damu dashi suwa sukafi daraja?”
“Ku Mama dan Allah kuyi hak’uri.”
“Kin kyauta” tana kaiwa nan tafice takaiwa Baba wayar rugu-rugu yayi da wayan sannan ya karya sim d’in. Bayan da Baba ya tabbata duk sun fita sunbar d’akin Zeezee itace kad’ai ragowa yajesa. Tana ganinsa ta hau 6ari “Baba dan darajan Allah kayi hak’uri karka sake ta6ani, wallahi bazan sake ba” hannunta yaja a fusace se ihu take tana kiran Mama da Adda Mariam. Yana kaiwa store room yayi wurgi da ita ciki tare jan k’ofan ya datse kwad’o ta waje sannan yasa makullin a aljihunsa. Buga k’ofan tashiga yi seda su Mama suka fito “ya haka Alhj? Bade rufeta kayi cikin d’akin nan me window d’aya ba? Dan Allah kayi hak’uri ka bud’e kasheta kakeson yi?”
“Mama! Mama dan Allah ki taimakeni kice ya bud’emin k’ofan.”
“Alhj dan Allah kayi hak’uri ka bud’e mata.”
“In kinga na bud’e k’ofan nan toh gawanta za’a cire kuma duk wanda ya bud’e Allah ya isa ban yafe ba.” Yana kaiwa nan ya fice yabar gidan. Kuka Zeezee tayita rusawa tana bubbuga k’ofan, wani erin bak’in duhu ne da d’akin saboda d’an window d’ayan ma ba haske yake kawowa ba. Ita kanta Mama batasan a lokacinda ta fara kuka ba da k’yar Mariam ta samu tayi shiru.
*~ *~ *~
Bayan Sallan La’asr Baba yadawo cikin kuka Mama ta samesa tana had’asa da Allah da ya bud’ewa Zeezee k’ofar ko Sallah ne tayi taci abinci amman haka Baba yak’i. Rok’onsa tayita yi har Sallan Maghrib yak’i bud’ewa, haka Zeezee tayini cikin d’akin takuma kwana ciki tun tana hawaye har hayayen nata suka k’are ya zammana ta nemi waje kawai ta zauna tana jan numfashi.
***
Ta fannin Adeel ma hankalinsa ya matuk’ar tashi jin line na Zeezee bayi shiga har yanzu, Lubiee ya kira ya buk’aceta da ta kira Mama taji daga gareta bayan Mama ta mata bayanin komi Lubiee tayita kuka itama sannan ta kira Adeel ta irga masa komi tana me blaming komi akansa. Sosai shima ya tausayawa Zeezeen’sa, ji yake inama ace ze iya ceto ta right now su gudu suje somehwere far away and start a new life, a daren ranan beyi bacci ba shima tunanin Zeezee ya hanasa.
Washegari ma da rok’an Baba Mama ta tashi amman sam yak’i jinta daga k’arshe Kaka ta kira tata mata kuka, koda Kaka tasa baki k’in bud’e k’ofan Baba yayi. Around 10am Lubiee da Ummi sukazo abin tausayi sede a leqa Zeezee ta window, take away da Mama tabata ma na can a gefe bata ta6a ba, rabuwanta da abinci tun breakfast na jiya. Ba yadda Lubiee batai da Zeezee ba ta taso ta ganta amman Zeezee tak’i haka har su Lubiee suka tafi bataga idon Zeezee ba. Se bayan La’asr da Kaka tata had’a Baba da Allah ya amince ya bawa Mama key taje ta bud’o Zeezee.
Kuka tasa tare da rungumota, tanayi Zeezee nayi. A hankali ta d’agata ta kaita d’akinta tasata yin wanka da biyan sallolin ta sannan taci abinci.
★*★*★*★
Tun rana me kamar na ranan rayuwan Zeezee ya soya, gabad’aya Baba ya hana duka friends nata visiting nata harta Lubiee. Ba inda take takawa daga toilet se d’akinta, kullum cikin kuka take ba safe ba dare, uwa uba kuma ga rashin jin murya ko motsin Adeel nata a kusa da ita, hakan ba k’aramin rama yasa tayi ba a sanadin haka Baba yace sam se anje anyi mata pregnancy test waya sani ko ciki take dashi, duk yadda ta rantse musu kan ita bata tab’a sanin wani na miji ba Baba yak’i yarda hasali shi yanzu ko muryan Zeezee ma bayason ji. Sunje sunyi test result ya nuna ba ciki, ita kanta Mama se anan hankalinta ya kwanta sabida rama erin wanda Zeezee tayi itama ya tsorata ta.
Ta fannin Adeel shima hauka ne kawai beyi ba kullum yana gidan su Lubiee yana roqarta tasan ya zatayi ta had’asa da Zeezee. Rana d’aya Lubiee ta kira Mama bayan sun gaisa ta buk’aceta da ta had’ata da Zeezee. Kasancewar Baba ya hana yin hakan da k’yar ta samu Mama ta bawa Zeezee wayar ta fice.
“Hello Zeezee.”
“Na’am Lubiee” tayi maganan wane maras lafiya.
“Ya kike? I missed you.”
“I missed you, ya gida da kowa sa kowa?”
“Lafiya qalau Zeezee Adeel ne ya dameni wai yanason ku gaisa.” Kuka kawai Zeezee tasa, jin haka Adeel ya wabje wayan “hello Sweetest Love.” Da k’yar ta iya ta amsa sa “na’am Very Own.”
“Sweetest Love I can’t tell you how sorry I am, only if I knew all this would happen da bakije party’n ba, da banyi bama gabad’aya.”
“Its not your fault I was the one who insisted on going so stop blaming yourslf please.”
“what now yanzu? Baba ya hak’ura?”
“Ko murya na baya sonji bale yaso ganin fuska na, Very Own am afraid I might lose you sabida Baba yace aure zemin with whomsoever.” Kai ya shiga kad’awa “no... No it can’t be possible Babe, you belong to only me please don’t accept the marriage.”
“Very Own danasan anyway possible dana bi dan kub’ucewa aukuwan wannan aure but I can’t.”
“There has to be away, bazaki iya escaping ba?”
“Bazan iya ba 5pm ake rufe min d’aki gakuma masu gadi har biyu da suke gadi kullum a waje theres no way out.”
“Damn it!” ya buga hannunsa jikin bango “I can’t lose you, I can’t” jin an murd’a handle na d’akintan tayi saurin cewa, “Mama is here” tare da katse wayar. “Har kun gama wayan ne?” Mama ta tambayeta
“Eh” ta amsa tana share hawayenta.
“Dama nazo fad’a miki Babanku ya dawo ne.”
“Nagode Mama.”
“Toh ni zan wuce d’akina” tayi maganan tana kar6e wayanta “seda safe.”
“Allah tashemu” Mama na ficewa Zeezee ta bud’e sabon chapter’n kuka 5pm on the dot Baba yazo yasa kwad’o a d’akin nata as always. The next day Baba A’ee tazo gidansu Zeezee ba shiri bayan jin labari da tayi a gari kan ga abinda ke faruwa a gidan Alhj Isma’il. Mama na a kitchen ta fito tayi mata sannu da zuwa.
“Yauwa Hafsah, karki gayamin abinda naji a gar-” bata k’are maganan ba Mama tace, “gaskiya ne ba k’arya ko d’aya aciki.”
“Zeezeen!” Ta dafe k’irji.
“Ita de Baaba amman dekam bawai taje ta kwana da na miji bane kamar yadda mutane ke fad’i party ta fita har sau biyu bata kwana gida ba.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Duniya ina zaki kaimu? ‘Yar Zeezee? Kinga irin abinda nake gaya mikin tun a da ko? Kingani ko?”
“Toh Baaba ya kikeson inyi?”
“Keko kike da yadda zakiyi, alokacinda abu basu 6aci haka ba na miki magana kan kidena cewa ke ba ruwanki da tarbiyyan Zeezee, ke ce uwarta tarbiyyan ta a hannunki yake ba ana Alhj ba, komin ya Alhj yake da Zeezee da kin tashi dagaske kika nuna masa kefa wannan tarbiyyan daya d’aura ‘yarki akai gur6arcacciya ce bakiso wallahi daya tsorata shikansa ya dena. Amman haka kika zauna kina zuba mai ido ga irinta ai yanzu, ‘yan unguwa ba Alhj kad’ai suke zaga ba har dake tunda kece mahaifiyarta.”
Shiru Mama tayi saboda ba shakka dukkankin abinda Baaba ta fad’a gaskiya ne shiyasa take kira ga iyaye mata masu zubawa mazajensu ido suna lalata musu tarbiyyan ‘ya’yansu suce su ba ruwansu ciki da tun wuri suyi hattara su dena sabida abubuwa suna ta6ar6arewa ba uban kad’ai za’a zaga ba, harda su matan tunda iyaye mata dama aka sani da aikin bada tarbiyya.
“Gaskiya ne Baaba kinyi gaskia nima da hannuna acikin lalacewar tarbiyyan Zeezee, da a lokacin nama Alhj wuta sosai na nuna masa ba’a gidana za’ayi haka ba da tarbiyyan Zeezee be lalace haka ba.”
“Aikinga irinta yanzu, abinda nake gudu muku kenan ranar dana sani.”
“Tabbas Baaba nayi kuskure nima amman haka mu ‘yan Adam muke ajizai ne mu, nayi alqawari daga yau koda akan titi na tarar da yara masu kalan halin Zeezee zan tsaya na musu gyara se a inda k’arfi na ya k’are itama Zeezee yanzu zan sa mata ido sosai fata na Allah ya shiryar min da ita.”
“Ameen da hakan kikayi ada da duk haka be faru ba, Allah shirya mana Zeezee toh.”
“Ameen Baaba nagode sosai”
“Ba komai ai D’A NA KOWA NE (Bebeelo) ina Zeezeen take itama?”
“Tana d’akinta Baban ya rufeta.”
“Kamar ya?”
“A kullum k’arfe biyar na yamma nayi yake sa kwad’o k’ofar d’akinta ko abincin dare ta window nake mik’a mata.”
“Toh Allah ya kyauta in Alhj yazo ki gaishesa ni na tafi.”
“Bazaki jira dinner ba?”
“A’a nagode”***
★*★*★*★
Several weeks and months passed by. Matar Ibraheem Fateemah harta haihu ta samu ‘yarta Hafsah itama takwaran Mama. Koda Mama ke shirin tafiya ta rok’i Baba daya bari Zeezee taje itama amman sam yak’i, haka Mama ita kad’ai ta tafi ta dawo. A rashinta na sati Zeezee ji take kamar an cire wani gab’a ne daga jikinta, d’an waya da suke da Adeel jifa jifan ma babu shi yanzu. Bada jimawa ba admission nasu Zeezee ya fito duk friends nata sun soma registration amman banda ita, tayi kuka har seda ta godewa Allah Baba ya hak’ura ya barta ta cigaba da karatu yak’i, Mama tasa baki ta rok’esa amman yak’i ji ya riga ya yanke hukunci Zeezee bazata koma school ba se inde a gidan mijinta. Gashi har yanzu al’amura basu daidaita tsakaninta dashi ba dan ko zata mutu tana mai magana ba amsata ze ba, muryanta ma ba son ji yake ba.
Shikansa Baba abin ba k’aramin damunsa yake ba acewai ga abinda Zeezeensa ta koma, shi kansa ya d’an rame dan yadda yake bin abin a zuciya. Ana cikin haka wata rana wani friend na Baba yazosa gidansu Zeezee.
*© MIEMIEBEE TEAM #YGC!*
๐๐๐๐
wwww.beeenovels.blogspot.com
No comments:
Post a Comment