Sunday, 23 October 2016

HEEDAYAH!


                  2⃣4⃣
   written by miemiebee👄

     Bayan like 30mins da tafiyan barayin, nanny tadan lumshe ido da taimakon table dake tsakiyan kitchen din ta riqe ta miqe da hannunta riqe da cikinta tana ma kitchen din wani erin kallo nan ta tuna meya faru sunan alhj kawai takira da karfi ta ruga a guje dakin daddy tagansa bayya motsi salati ta hauyi jiki na qyarma ta kira mummy a waya tana kuka "mummy ki zo gda, kizo gda, gda ba lafya barayi sun shigo sun mana fashi, alhj baya motsi" ta fashe da kuka... Mummy tace "what!?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kasa daukanta kafafunta sukayi ta sulale qasa salati kawai take ta nanatawa har na tsawon mituna uku sannan da kyar ta tashy tabar office dinta a guje key kawai ta dauka ta fice, Allah ne kawai ya kawota gda lafya dan wata erin wawiyar driving da takeyi a bude wangalau tasamu gate na gdanta daidai bakin kofar parlour tayi packing ta fito ko rufe kofar batayi ba hasali ma a kunne ta barta ta shigo ciki da saurin gaske abinda tafara cin karo dashy shine ba TV'nta, tana kai ido kan showglass taga du an kwashe abinda ke ciki hannu kawai tasa kan bakinta ta karasa dakin daddy tasamu nanny a gefe ta rike ciki tana kuka, daddy kuwa na kan wheelchair nasa a sume wayarta ta gwada lalima taji ba alamarta nan ta tuna tabar wayar a office ta kira sunan nanny, nanny tadago jajayen idanunta "mummy har kin iso ki kira likita...wayyo cikina" mummy tace bani wayarki ta karisa ta amsa Allah yaso ma ta haddace numban family dr din, nan da nan ta kirasa ya iso ya duba daddy da nanny yabasu immediate care ba abinda mummy ke shararawa se kuka, shide dr yamata jaje yakuma bata hkr sannan ya fice. Haka har lokacin daukan heedayah yayi mummy bata sani ba se kuka take shararawa can bayan 30mins da tashinsu heedayah ta tuna gashy barata iya fitaba dan haka ta kira driver da wayan nanny kan yaje ya dauko heedayah frm sch batare da ta gaya masa dalili ba, driver kuwa a hanyan dauko heedayah wasu barayi suka tsare sa ni miemie nace wannan barayi sunyi kalan wanda suka kai fashy gdan alhj s.u daxu, suka ma mal idi tsinannen duka sannan suka kwace motarsa suka kara mai, da kyar mal idi yasamu ya lalimo wayarsa upon all dukan da suka masa ahaka yayi karfin hali yakira numban mummy har yagama ringing bata daga ba yakuma mata wata missed call din sannan ya kirata da numban nanny nanne ta daga, ahankali yake maganar "haj..i..ya yan ta'ada kije ki dauko heedayah" mummy tace "whaat!???" Kana ina? Da kyar ya iya cemata "hotoro" tace "toh keep calm, ga ni nan zuwa" nanny tana tambayar ta meke faruwa amman bata ko amsa taba tafita a gigice se hotoro can ta hango mal idi a kasa ta karasa yasamu ya tashy da kyar mummy take tambyarshi ze iya kaiwa har a dauko heedayah? Ya amsa da "eh" amman de da anga condition nasa an san bare iya ba dan jikinsa duk yoyon jini yakeyi sbd gardaman da yyi wa barayin suka shasa sosai, reverse kawai mummy tayi sukayi asibiti akayi emergency dashy tace wa dr din zataje dauko 'yarta a makaranta ta fice, heedayah har tagaji da jiran mummy tafara kuka, tana cikin raira kukanta a hankali mummy tace "am so sorry my little princess yi hakuri am late kinji?" Ta dagota ta riko mata jakarta suka kama tafiya, maimakon su wuce gda se heedayah taga mummy nabin wata hanyar daban dan haka ta tambayeta "mummy ina zamuje?" Mummy tace "asibiti heedayah, barayi sun tsare idi a hanya sun masa duka sun kwace motarki" heedayah tazaro dara daran idanunta tace "mummy! Prado dina?" Mummy tace "eh heedayah, ke akan ki tambayi jikin idi ma motarkice ta dame ki?" Heedayah ta maraice sannan tace "toh ya jikin mal idi?" Mummy tace "bari mu karisa asibitin muji" nan da nan suka isa aka tabbatar mata da cewa mal idi beji internal injuries ba kawai external ne nd anyi treating nasu, nanne mummy ta sauke a jiyar zuciya tabiya kudin treatment nasa da kudin magani sannan suka dawo gda, tun isarsu bakin gate heedayah da mal idi suka sake baki mal idi yace "hajiya meke faruwa?? Gate a bude kuma ba motoci a gdan" mummy bata ce masa komi ba dan haka yaja bakinsa yayi tsit, heedayah kuwa har yoyon miyau bakinta yafara ahaka mummy ta nemi gu tayi parking suka fiffito, mummy tashige ciki dan takaici heedayah kuwa da mal idi se kallon gdan kowan nensu keyi ko zasu ga motocin amman ina! Heedayah ta nemi gu ta zauna can inda ake parking motoci shikuma mal idi ya shiga ciki, hawaye a hankali heedayah ke zubarwa kaman daga sama taga hannu daga dakin me gadi wata ihu ta sakar duk su mummy suka fito suna tambayarta mene? Dakin me gadi kawai take nuna musu da 'yatsarta mal idi ya karasa yaga mal musa me gadi kansa du yana zuban jini salati ya sakar, su mummy sukayi kansa da heedayah mummy na salati mal idi nayi**** Alhj lawal da alhj ismail suna zaune a gdan shi alhj ismail se dariyan mugunta sukeyi ana cikin haka wayar alhj lawal tayi qara ya duba...

No comments: