Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 25
BY MIEMIEBEE


“Hello” tace a hankali.
    “coffee nakeso.” Ya fad’a authoritatively.
       “Sir amman ai yau saturday ne ba’a aiki a weekends.”
     “In Boss naki yace se kinyi kuma fah? Can you say no.”
     Can k’asa k’asa tace, “a’a.”
    “Good, meet me at my paint house...” Nan yamata kwatance kafin tace, “okay” ya katse wayar.
 
     “Meh yace wai?” cewar Afrah dake d’aura kai.
     “Wai coffee yakeson sha inje in samesa a paint house nasa.”
  “Ranan Asabar d’inma?”
    “Humm! sekace bakisan Mr. Fauzi ba? Haka yake d’an ra’ayi ne.”
    “Kina nufin yanzu bara muje gidan Haleeman ba kenan?”
    “Zamuje mana ai had’a coffee kawai zan masa within 2-3 minutes nagama semu tafi yanzu kiyi ki gama shirinki muje tare.” Da “toh” Afrah ta juya ta gama d’aurin ta sannan sukayi sallama da Mami daidai gaban paint house na Anas kamar yadda ya mata kwatance suka tsaya bayan ta sallame me napep d’in suka tsaya admiring gidan dududu barefi 2 bedroom flat bane ciki fari ne tas gidan ya k’ure kalman kyau.

        “Ya Fannah wannan ne motarsa?” Tana nuni da yatsa.
    “Wai ba” cewar Fannah.
    “Wow! Wow!”
   “Ke kin fara ko? Nikam kizo mushiga”
   “Wa? ni? In shiga? Saboda ya koreni kimin dariya? Kefa kikace baida mutunci a dalilin me zan biki ciki? Nide kiyi sauri ina jiranki nan.”
    “Amman Afrah bakiyi ba wallahi ai da sekice min baraki shiga ba, da bamu sallami me napep d’inba.”
     “Oho sorry zamu samu karki damu, kiyi sauri kar muyi latti.”
     “Afrah da Allah mu shiga wallahi bansan shiga ni kad’ai.”
     “Ya Fannah dan Allah kibar had’a ni da Allah dan wallahi barin shiga ba. Off you go” ta mata gwalo. Baki Fannah ta murgud’a mata sannan tayi hanyanta ciki.

     Door bell data gani bakin k’ofar ta danna zuciyarta se bugawa yake tana jiransa. Bayan kamar minti d’aya k’ofar ya bud’u. Anas tagani tsaye jikin k’ofar ko singlet babu jikinsa bale kaya ¾ wando ne na soja jikinsa, da alama yanzu yafito daga wanka danko gashin kansa a jik’e yake kad’an kad’an ruwa na d’iga a k’asa, ga wani kyan da skin nasa yayi a jik’e har shining shining yake. Blue eyes nasa kuwa sun sake shiga ba k’arya yayi kyau sosai ga body kam masha Allah very muscular ta kasa dena kallonsa kamar yadda shima yake kallonta and for the first time bada wata manufa ba. Be tab’a ganinta da shiri irin na yau ba, kullum cikin hijabi take banda gyalen data yafa yau ga d’an kwaliyan datayi wanda be tab’a gani tayi ba. Sosai ta canza kamanni, ga yadda Afrah ta yafa mata gyalen, ta d’an bar kad’an daga cikin k’irjinta dake a cike dadai ‘yar budurwa a waje. Za’a iya ce miki kinyi kyau ya fad’a a zuciyarsa.

     Kusan a tare suka kawar da ido daga kan junansu gyalen dake wuyanta ta d’aga ta yafa kai tare da rufe k’irjinta dashi. Kad’an ya matsa gefe “come in” yace da ita a hankali ta shiga ta tsaya ba daga nesa ba “ga chan kitchen d’in” ya nuna mata da yatsa k’ok’ari tayi kar ta sake kallonsa kafin ya silleta. Kai ta giad’a nan take ta tuna dokokinsa tace, “okay.” A sanyaye tabi direction daya nuna mata ta shiga kitchen d’in komai tsatsaf ba datti ba wari. A gefe guda ta hango coffee machine gefe guda kuwa fridge. Wajen fridge d’in ta nufa ta bud’e as expected taga bottles na giya jere daban daban kai kawai ta kad’a taciro abinda zata buk’ata ta nufa wajen coffee machine d’in ta ajiye cupboards d’in tabi tana bud’ewa har tasamu na cups and spoons. Sosai ta mayar da hankalinta gu d’aya gudun kar ta fasa masa d’aya daga cikin fancy cups nasa yasata biya. Bayan ta gama had’a masa ta d’auka da hannu bibbiyu shes very careful ta bud’e k’ofar a hankali  ta rufe tana juyawa kawai taga mutum tsaye gabanta gashi har yanzu besa kaya ba ¾ wandon ne. Tsorata tayi sosai iya tsoro dayasa tayi b’arin coffeen saura suka zube a jikin Anas dako singlet baida saura kuma jikinta saura a k’asa. Da cup da plate data d’aura kai dakuma spoon d’in duka suka fashe a k’asa.

    K’ara sosai Anas yasaki dan zafin coffeen ita bata ma damu da kanta ba, batasan ma yatayi taciro gyalenta ta soma goge masa jikinsa ta cikinsa dashi ba “sorry sir, I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri” duk ta rikice. Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki tab’a masa jiki ma take, lallai kuwa. Alokaci d’aya kuma ta tsaya cak! A kunyace ta d’aga hannunta daga jikinsa ta d’aga kai suna had’a ido tayi sauri ta kawar da kanta. “I’m sorry” tace kallonta ya tsaya yi, besan meke damunsa ba, shi d’inda ko matan turawa kan bikini (pant and bra) ma basu masa ba mesa yake kallon Fannah toh? Me take dashi? Jik’ak’en mayafinta ta bud’e zata yafa ya kama karap! A razane ta d’ago kanta tana kallonsa alokaci d’aya tana k’ok’arin fisgan gyalen sede k’arfinsu ba d’aya bane.

   Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta d’aura hannayenta biyu tana tare k’irjinta da kanta k’asa har yanzu Anas be motsa ba kallonta yake sosai sosai da ta d’aga kai seta ga ita yake kallo. Da k’yar tayi gathering courage ta bud’e baki zatace masa “kabani mayafina” kawai ya juya ya fice da gyalen zuwa wata d’aki. B’ari sosai Fannah take, shikenan tabar Anas yaga jikinta duk laifin Afrah ne da hijabinta ne da asirin ta a rufe. Ido ta d’aga sama “Ya Allah ka yafemin astaghfirullah astaghfirullah.”
     Daidai lokacin Anas ya fito daga d’akin da wani leather a hannunsa baya ta juya take tana kare k’irjinta seda yagama matsowa kusa da ita ta tuna kayan tan ma show me your back ne sanda tace wa d’an iskan tellan su kar ya mata yak’i ji.
    Kallon spotless bayan ta yake da gashi kad’an kad’an kwance luf akai uban gashinta kuwa an kama sa a tsakiyar kanta wanda dan uban yawansa still sanda yafito daga d’an kwalinta. Sanda ya k’are mata kallo tukuna ya bud’o leather’n har yanzu Fannah bata juya ta kallesa ba ita alhamdulillah tunda be tab’a ta ba. Ta gommaci ya kalli bayanta dayaga k’irjinta.

     Zuciyar ta kuwa se bugun d’ari d’ari yake. K’aran leather tajiyo a lokacin dayake ciro gyalen daga cikin leather’nsa wani tsoro tasakeji ya ratsa ta se addu’o’i take ta suburbud’owa idanta gagam ta rufe. A hankali taji sauk’an gyale ajikinta a razane ta juya tagansa tsaye a bayanta kwata kwata distance dake tsakaninsu befi inchi uku ko hud’u bane. Da sauri ta rufe jikinta dashi dukda kuwa gyalen shara shara ne amman yafi babu, gashi kuwa yayi kalan me tsada sosai gashi kuma sabo gal. Stepping back tayi “nagode” tace tanasan tambayansa ina gyalenta sekuma ta fasa.

    Tsugunawa tayi zata tattara broken glasses d’in ya cafko ta da hannu “so kike ki sake yankewa kimin kuka anan? Ko an fad’a miki inasan tab’a jikin ki ne?” Wai ace mutum yanzu ya gama showing kindness wa mutum kuma yana zaginsa, wani hali sena Anas. Fannah tayi tunani a ranta.
     Hannunta take k’ok’arin fisga dan zafin rik’onsa amman ta kasa, yana noticing haka ya sake ta. “Wuce ki sake had’a min wani coffeen akoi flask akan counter d’in ki cika min shi in kin gama ga kud’inki” ya nuna mata bundle ma N100 kan dining table. Fat zuciyar Fannah ya buga bade korarta daga aiki zeyi ba saboda ta fasa masa cup.
     “Mr. Fauzi I’m sorry dan Allah don’t fire me ba da gangan na fasa maka cup d’inba ka fad’a min nawane kud’in I will pay you but kar ka koreni please.” Ita ba komi ke damunta ba inbanda kud’in magunan Baba gashi sun kusa k’arewa.

    Kallonta yake wani eri “and waya gaya miki kinada kud’in da zaki iya biya na kud’in cup d’innan. Humm!” Ya d’an yi murmushin rainin hankali. “Incase clueless mind naki na ce miki firing naki zanyi to ki kwantar da hankalinki wannan kud’in saki aiki ranan saturday ne becareful karki fasa min wani cup d’in saboda zan iya saki biya ko inyi pressing charges.”

       “Nagode” tace masa tana kallon farin cikinsa dayayi turning ja saboda zafin k’onuwan amman ko kad’an Anas bai nuna yaji zafin k’onar ba. Duk laifinta ne yanzu ta k’ona masa ciki.
      “Kibar kallo min jiki haka.” Haushi da kunya taji duk lokaci d’aya ita bawai kallonsa take saboda he is hot ba tausaya masa take dan ta k’onasa.
    “Sir ni bawai kallonka nake saboda inajin dad’in hakan ba, I’m concerned saboda ni na k’ona ka, ka shafa vaseline awajen dan hanasa tashi.”

     “Kuma se akace miki kina da right na tausaya min kokuma na fad’amin abinda zanyi? Jiki na ne ba naki ba, kawoki gidan nan nayi ki had’a min coffee bawai kizo kina kallo na kina fad’amin abinda zanyi ba, banasan shisshigi.”
   Mamaki ne yacika Fannah shi da ya tsaya yana kallon k’irjinta da bayan ta d’azu batayi magana ba se shi. Ji take kamar ta sissile sa amman tsoro takeji kar ya koreta.
    “Allah baka hak’uri” tace kanta a k’asa tare da juyawa kafin ya sake cakka mata wata bak’ar maganar. Bayan minti shida tafito daga kitchen d’in tare da tsallaka fasassun glasses d’in ta ajiye flask d’in kan dining sannan ta koma ta d’au cup d’in taje ta ajiye masa kan side tables na kusa dashi a parlour. Ko kallonta beyi ba wani magani ne a hannunsa yana shafawa kan inda ta k’onasa.

    Ba tare da tace masa komi ba ta wuce ta d’au jakarta tare da sa kud’in daya bata cikin jakarta tazo fita kenan ya tsaida ta. “Wajen kuma ni zan share?”
     Baki na rawa tace, “a’a.. A’a” komawa tayi ta ajiye jakarta “ina tsintsiya da moper’n suke?”
    “Nima bansani ba” ya bata amsa “just go zan kira masu giara su share kafin ki sake min wata b’arnan tunda you are too clumsy”
      Danne zuciyarta tayi “Nogode” tace masa sannan ta fice. Afrah har ta gaji da jiran Fannah ba sak’e sak’en da batai ba a zuciyarta.
   “Ya Fannah ya kika jima haka? I thought kince minti hud’u ma yayi yawa.”

    “Da wannan mutumin?” Ta nuna gidan Anas da yatsa. “Ai aikin minti uku seya sa mutum yayi minti ishrin.”
   “To mayafin ki fa?” Cewar Afrah “Ina yake waya baki wannan?”
    “Ke dogon zance muje gidan Haleemar tukunnah zan miki bayanin komai bayan mun isa gida.” Wani kallon tsiya Afrah ta soma mata wanda tuni ta tand’e k’eyarta sanda ta tsaya ta giara d’aurin sannan suka fice.

   *© miemiebee*

   

No comments: