Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 26
BY MIEMIEBEE


Bayan Anas ya gama shafa maganin kan ciwonsa ya kurb’e coffeen sa hankali kwance. Yana gamawa yasa kaya yaja motarsa zuwa gida. Amal na tsaye bakin k’ofa tana jiransa. Ko gama fitowa daga mota beyi ba tayi kansa tana masa oyoyo a garin haka tad’an fama masa k’onuwansa. K’ara yasaki kad’an.
    “Ya Anas kaji ciwo ne?”
    Murmushi ya mata “a’a angel ba ciwo bane.”
    “Toh Ya Anas kayi ihu fa, mugani.” Tana k’ok’arin d’aga mai T-shirt. Hannunta ya rik’e “don’t worry angel ba ciwo bane.”
     “Toh Ya Anas ina mayafina daka ce ka siya min zaka taho min dashi.” Nan ya tuna mayafin nata ya bawa Fannah. “Ya Anas kayi shiru ko dama wasa kake baka saya min ba.”
    “Angel na saya miki mana, naga bashida kyau ne shine na kyautar ma wata mata akan layi but don’t worry zan k’ara saya miki wani kinji?”
   Kai ta giad’a a hankali tana turo baki.
    Ganin haka yace da ita, “dauk’o mayafin ki muje mu siyo miki wani yanzu, infact shopping ma zan kaiki ki saya duk abinda kikeso.”
    “Yeyy! Ya Anas!” dagudu ta shiga ciki ta d’auko mayafinta suka fice.

    ****

    Afrah kuwa ta k’osa Fannah tabata labarin abinda ya faru cikin tsakaninta da Anas d’azu, tun a hanya take ta damun Fannah sanda suka iso gida Fannah ta labarce mata komi. Ido wuru-wuru Afrah ta zaro. “Ya Fannah wallahi Mr. Fauzi na sanki irin wanga kallo haka?”
    “Kefa akuya ce” cewar Fannah “Mr. fauzin yasoni? Impossible tense kenan! bakiga uban rashin mutuncin dayake suburbud’a min bane wallahi.”
     “Ke baraki gane irin san bane-”
   Katse ta Fannah tayi “ni banasan ji sekace baki san banida martaba ba aiko da ace ma sonan yake bare aureni ba muddin yaji labarina kamar yadda nima baran auri masifaffen mutum kamar Mr. Fauzi ba. Kinga tashi ki rakani muje mu siyo wa Baba magunansa tunda mun samu kud’i.”
     “Amman Ya Fannah a gani na ba sekin bar aiki da Mr. Fauzi ba.”
   “Kamar ya Afrah? Ke bakisan Mr. Fauzi bane wai? Ai barin aiki dashi consider it done monday monday’n nan zan fara nema in Allah ya taimakeni nasamu ai na huta.”
   “Tunda haka kikace, Allah sa hakan yafi alkhairi.”
   “Ameen” Fannah tace sannan suka je suka siyo wa Baba magunansa.

      Wahsegari ma haka ya kirata kan taje ta had’a masa coffee a paint house nasa tun 8:00AM ya kirata amman se kusan to 9:00AM ta isa saboda ta raka Mami kai Baba ganin likita daga can ta biya gidan Anas tare da mayafin daya bata, ta wanke sa harda guga. Hijabi har k’asa take sanye dashi yau. Bayan ta danna door bell ta tsaya jira shiru dan haka ta sake dannawa nan ma shiru, yin haka sau uku taga ba motsin mutum gidan ta d’au wayarta ta kirasa alokacin da ya soma ringing kuwa wayan na hannun Amal tana game.

    “Ya Anas coffee maker na kiranka” kafin yace, “mik’a min” ta d’aga “hello coffee maker.” Ido wuru wuru Fannah ta zaro wato ma da coffee maker yayi saving lambarta, Allah shirya toh. “Hello Amal” Fannah ta gaisheta.
    “Laaa kinsan suna na taya ya?”
   “Bani wayar Amal” cewar Anas.
    “Ya Anas gashi ta kira suna na wacece ita?” Nan ta dawo kan wayar “Hello coffee maker ya sunanki?”
    “Fannah ce Amal.”
   “Laaaa! Fannah!!” ta daka ihu “ya kike?”
   “Lafiya, kefah?”
   “Amal kawo wayan nan.” Nan ya mik’e da nufin ze karb’a ganin haka ta mik’e a guje kafin tace me ya kamata ya k’wace wayan.
 
    “Yes? Kud’inki ne baki gani ba komeh?”
  “Mr. Fauzi gidan a rufe ne.”
   “Kin gwada bud’e k’ofar ne kika ga a rufe?”
  Nan tasa hannu taga a bud’e a kunyace tace, “a’a.”
    “Good kud’inki na kan dining table don’t call me again.” Kafin tayi magana ya katse wayar. Kallon wayar ta tsaya yi lallai ma wannan Mr. Fauzi wallahi da girman kai na kisa da ka juma da mutuwa. Tsuka taja sannan ta shiga ciki...

****
     “Ya Anas shine kace min bakasan wace Fannah ba ranan dana tambayeka.”
   Kallon Amal ya tsaya yi yana tunanin wani k’arya ze mata can yace, “eh mana ban santaba, ni banma san asalin sunan ta ba se yanzu, bakiga da coffee maker nayi saving number’nta ba.”
    “Toh Ya Anas mesa ta kiraka?”
    “Aiki zatamin.” Ya amsa ta a takaice.
  “Toh Ya Anas bani lambarta inasan muna waya da ita.”
   “A’a Amal, Fannah is not a good person bana san kuna zumunci da ita.”
    “Mesa Ya Anas?”
   “Just trust me kinji Angel?”
   “Okay Ya Anas” ta masa murmushi “bani wayar in cigaba da game d’in toh.” Ba gardama ya mik’a mata “zan d’an fita in kin gama ki had’amin a charging kinji?” Kai ta giad'a “and also karkiyi recieving min calls, Angel am serious.”
    “Ya Anas barin yi ba seka dawo.”
   “Yawwa Angel!” Be zarce ko inaba se paint house nasa alokacin kuwa Fannah har ta gama had’a masa cikin flask ta ajiye kan dining ta tafi. Dad’i yaji dan ba san ganinta dama yake ba sesa ma yace tazo time da bayya nan. Tun jiya daya ganta ba mayafi ya riga tunaninta wanda ya mugun basa haushi. Nutsuwa yayi ya sha coffeen sa sannan ya taho da flask d’in da ze dawo gida.

      ****

     Fannah na zaune ita kad’ai a d’aki tun dawowarta take zaune shiru kasancewar Afrah ma ta tafi yawonta, su Mami kuwa basu dawo ba. Dadai zata d’au wayarta dan buga game kenan wayar ta soma ringing ganin sabuwar lamba ta tsaya nazarin kowaye amman sam bata san lambar ba sanda ta kusan tsinkewa ta d’aga nan ma batace komi ba, familiar voice taji “Fannah” aka kira sunanta.
   “Na’am Amal ce?”
    “Kin gane ni kenan?”
          “Eh!” Fannah ta fad'i cike da mamaki. “Ina kika samu number na?”
    “A wayan Ya Anas karki fad’a masa munyi waya fa kinji? Besan na d’auka number’nki ba.”
    “Toh Amal barin fad’a masa ba. Mesa kika kirani?”
    “Kawai I want you to be my friend.”
    Cike da mamaki Fannah tace, “toh nikuma? Ai na miki babba.”
  “To ki zama big sis d’ina” Amal ta fad’i tana turo baki.
   “To Ya Anas fa bare miki magana ba?”
    “Ai bare ma sani ba dan ni ba fad’a mai zan ba, kamar yadda kema baraki fad’a masa ba koh?”
    “Sosai” Fannah tace tana dariya “toh little sis barin fad’a masa ba.” Hira sosai suka sha suka riga tambayan juna questions akan rayuwarsu suna amsawa se can sukayi sallama.

    Washegari...
     Kasancewar yau Monday Fannah ta tashi tayi shirin zuwa office tare ta taro credentials nata dan daga can tana san ta wuce neman aiki. Takwas da ‘yan mintuna aka ta isa office bayan tayi knocking Anas yace, “come in.” Kanta sunkuye tashiga ta gaishesa be amsa ba bale ya kalleta, matsowa kusa da shi tayi alokacin ne ya d’ago kai yana kallonta.

        Jakarta ta bud’e taciro gyalen daya bata kafin ta ajiye kan table d’in ya dakatar da ita. “Wannan kuma fa? Kar ki ajiye min kan table” Ya tambayeta.
        Cak! Ta dakata “Sir mayafin daka bani shekran,jiya ne thank you, shine zanyi returning maka yanzu.”
          “Inada ido ai, banaso, bana buk’ata. Ko ki cigaba da ajiyewa wajenki ko kuma ki jefar ya rage miki. Make me coffee.” Mamaki ne yacikata bata ce masa komi ba ta mayar cikin jakarta sannan ta ajiye ta wuce ta had’a masa coffee bayan ta ajiye ta kallesa “Sir excuse me zan d’an fita but in shaa Allah zan dawo kafin azahar.”

    Yana sipping coffeen sa tare da duban wasu files “wannan kuma keya dama, iyaka in bakizo on time bane inyi firing naki” ya fad’a mata ba tare da ko ya kalleta ba. A ranta tace ka kwantar da hankalinka ina samun aiki zanyi resiging a nan. Jakarta ta ja ta fice neman aiki ta tayi amman ba sa'a kafin azahar ta dawo ta sake had’a masa coffee.
 
    Haka de tun daga ranan Fannah ta shiga neman aiki ba wasa. Mayafin kuwa ta adana sa gu d’aya dukda bata da niyyar sake sawa. Anas kuwa be canza ba baya shiga harkanta amman ko d’an k’aramin mistake tayi ze balbaleta ya tsawa ta mata, kuka take sosai duk sanda ya masifeta sam takasa sabuwa da masifar Anas, shiko kukanta sam  be d’aga sa bale ya nana sa a k’asa. Shak’uwa sosai yashiga tsakanin Fannah da Amal wanda har yau Anas be sani ba. A yau wata d’aya da sati biyu kenan tana masa aiki.

     Yau ranar ta kasance Wednesday, dawowar Fannah daga aiki kenan idanunta duk sunyi ja saboda kuka.
    “Fannah ya haka?” Mami dake fitowa daga kitchen ta tambayeta.
    Kare fuskarta take “ba komai Mami dutse ne yashiga min ido amman yafita karki damu.” tamata k’arya.
    “Are you sure?”
   “Eh Mami ina Aiman da Afrah?”
   “Sun shiga nan mak’ota.”
  “Okay barin watsa ruwa toh” nan tayi hanyan d’akinsu. Bayan tafito daga wanka tajiyo alert a wayarta tana dubawa taga message daga d’aya daga cikin ma’aikatan datayi applying FCB ltd. Tsalle ta daka ganin aiki suka bata kuma akan abinda ta karanta finally zata samu tayi amfani da ilimin data samu a jami’a.
   Afrah na dawowa ta labarta mata komi sosai Afrah ta mata murna. Ga albashi me kyau daidai N50,000.

       Bayan ta sa kaya taje tayi printing resignation letter’n da zata kaiwa Anas gobe. A hanyar dawowarta gida Amal ta kirata bayan sun gaisa take fad’a mata kan tabar aiki a Enterprise na Anas tasamu aiki. Amal ta mata murna kam sede bataji dad’in barin aikin Fannah gun Anas ba. Sau dayawa tana zuwa office na Anas ita da Fannah su fita suje suta hira ba tare da sanin shi Anas d’inba.
   
     “Ya Fannah amman mesa zaki bar aiki da Ya Anas? Ya miki wani abu ne?”
    Murmushi Fannah tayi sam halin Anas da Amal ba iri d’aya bane, kamanninsu ne kawai d’aya. “Ba abinda yamin Amal kawai nasamu better job ne.”
   “Yanzu shikenan bara mu sake had’uwa ba?” ta fad’a kamar zatayi kuka.
       “Nima banso hakan ba Amal, amman ai zamu na waya ko?”
   “Eh amman its still not enough ko zaki na zuwa gidanmu?”
    Danqaree Fannah tafe a zuci. “A’a Amal bareyi inje gidanku ba saboda Ya Anas.”
        “Ba abinda Ya Anas ze miki dan Allah kinji?”
    K’arya ta mata “naji zanzo in shaa Allah. Ina kan hanya bari in na isa gida zan kiraki.” A haka sukayi sallama.

     Washegari Fannah tasha baccinta a cewarta ta bar masa aiki se lokacin data ga daman zuwa office zata takai masa resignation letter’nta. Da misalin k’arfe 9:30AM Fannah ta iso building na Anas. A first floor ta had’u da Yusuf ta sanardashi great news na aikin data samu sosai yaji mata dad’i kuma ya mata murna. “Barin haura inkai wa Mr. Fauzi resignation letter na ina zuwa.” Da “toh” ta shige elevator. Zuciyarta fal da farin ciki ba me sake sata kuka yanzu dan ta tabbata ba worse Boss kamar Anas. Knocking d’aya tayi a bakin k’ofar yace, “come.” Cike yake da ita wato yau se 9:34AM Fannah taga daman zuwa masa office, she will get it from him.

        Bayan ta k’ariso ciki ta gaishe sa ko amsa ta beyi ba kallo ya watsa mata wanda yasa k’afafunta shaking. Ya bud’e baki ze soma suburbud’o mata masifa kamar an turosa kawai k’ofar office d’in ya bud’u wanda ba kowa ke shigowa haka ba illa Amal. “Ya Fannah!” tayi ihu ganin Fannah tsaye da gudu ta nufa wajenta tayi hugging nata. Baki wangalau Anas ya bud’e yana kallonsu. Wato Amal bata je school ba yau, bama wannan ba yaushe suka san juna da Fannah har suka shak’u haka? Tambayoyin da yayi wa kansa kenan.

     “Ya Fannah yanzu dagaske kike zaki bar aiki nan? Dan Allah kiyi hak’uri.”
     Kunnensa ya bubbuga ko halan ruwa ya shiga yau da yake wanka, barin aiki Fannah zatayi zuwa ina? Ta samu wani aiki ne? Coffee na fa? Bece dasu komi ba sanda suka gama hoge-hogensu. Bayan Fannah ta ciro letter’n ta matso kusa da table na Anas. “Mr. Fauzi wannan resignation letter na ne. Thank you for giving me the oppurtunity to work for you.” Letter’n ya d’aga yana k’arisa masa kallo sannan ya d’ago blue eyes nasa yana kallonta “are you really sure about this? Na barin aiki a nan?” ya tambayeta ba tare da ya nuna damuwa ba dukda kuwa ya damu sosai.

      Kai ta giad’a a hankali. “Kin samu wani aiki ne?” Nanma kai ta kuma giad’awa. “A ina?”
    “A FCB ltd.” ta amsa sa.
   “Ohhh, nawa ne salary’n naki?”
   K’arya tayi masa “nima bansani ba tukunah.”
   “Yayi kyau zaki iya tafiya.” Amal dake kallonsu ne tace, “Ya Anas ka hana ta tafiya ka k’ara mata salary se kar ta tafi.”
    “A’a Angle barta ta tafi. Ni ban hanaki alak’a da ita bama?” Ya tambayeta ba alaman wasa a tattare dashi.
    “Ya Anas kayi hak’uri.”
    “Zan hak’ura if only kika dena alak’a da ita, kingani ai barin aiki tayi.”
  “Mr. Fauzi-” cewar Fannah be saurareta ba ya daka mata tsawa “just go, leave, bana san sake ganinki.”
   “Amal na tafi” nan ta juya.
   “Ya Anas-” itanma tsawa ya daka mata for the first time. “Enough Angel kije ki samu Yunus yakira Shettima yazo ya d’auke ki.”

    Ita kanta tsoro taji sosai bata tab’a ganin mood na yayanta haka ba. Wajensa ta nufa tayi hugging nasa “Ya Anas I’m sorry, bansan me Ya Fannah tayi ka tsaneta haka ba, tanada kirki fah but tunda baka sona tare da ita, I’m sorry.”
     Bayanta ya shafa “is okay je gida ki huta nima I'm sorry for shouting at you.” Bayan Amal ta fice Anas ya d’au resignation letter’n Fannah ya yayyaga into pieces, zuciyansa se tafasa yake. Yarasa me ke damunsa mesa ma nake damuwa dan wata wai ita Fannah tabar min aiki? Nawa suka fi ta komi kuma na koresu, toh se meh dan kin bar min aiki? Mschww dama dan coffee ne kuma akoi masu neman aiki anan dubu. Wayarsa ya d’au ya kira Ahmad. “A buga a news ina neman masu aiki wanda suke da degree inma da hali har da masters kan had’a cofee.” Cike da rashin fahimta Ahmad yace, “Boss coffee kuma? Anayin course akan coffee ne?”
    A fusace Anas yace, “in baka aiwatar da abinda na saka kayi ba a yau a bakin aikinka.”

    Tuni Ahmad ya amsa “yes ofcourse Boss”  “Good, kuma ka turo cleaners suzo share wannan gabbage” yana nuni da resignation letter’n Fannah daya yayyaga “and also ka turo min number’n manager’n FCB ltd”


*© miemiebee*

No comments: