TANA TARE DA NI... PAGE 87
BY MIEMIEBEE
“Yauwa Habeebi nace ya labarin Moosa ne? Har yanzu shiru ba’a samesa ba?” yatsunsu yayi interwining;
“D’azu munyi magana da police sunce suna kan investigating har yanzu, kinsan Farouq shege ne Allah kad’ai yasan inda yakaisa.”
“Allah sa a samesa a raye Habeebi nasan danni Ya Farouq ya masa duka haka saboda yak’i shigo dashi ciki.”
“You are right Flower in shaa Allah zamu sam-” besamu daman k’arisa maganan ba sakamakon ringing da wayar sa yasoma ganin number’n Inspector General yayi saurin d’agawa.
“Hello Inspector.”
“Yes Mr. Fauzi I will like to congratulate you.”
“Yes... About what Sir?” Yayi maganar cike da neman k’arin bayani.
“Mun samu Moosa your driver achan Mongunu wai gidan Bad Boy achan Farouq ya kaisa ya b’oyesa.”
“Alhamdulillah, Alhamdulillah this is indeed a great news.”
“It is kuma shima Bad Boy d’in yana a hannu yanzu according to record babban drug dealer ne partner in crime na Farouq kuma dan da miliyan biyar nasa akayi bailing Farouq a prison 2 weeks ago.”
“Okay... Thank you Sir ina Moosan yake yanzu?”
“An kaishi asibiti dan duba lafiyarsa I guarantee you ba abinda suka masa.”
“Ina godia Sir zamuyi magana anjima.” Nan ya katse wayar tare da juyo da kallonsa kan Fannah dake kallonsa fuskarta d’auke da tambaya. Kafin tayi magana ya aza yatsansa kan lips nata “nasan me kikeson tambaya, an samu Moosa? Ko ba haka ba?”
“LOL eh haka please an samesa?”
“Yes sweetheart an sami Moosa yana asibiti yanzu as we speak yakamata inje in duba sa, I will be right back.” peck ya manna mata a goshi kafin ya miqe ta riqo shirt nasa. “Habeebi nima zanje.”
“Zakije ina?” ya tambayeta disbelievingly.
“Asibitin mana nima in duba sa kasan fa nice sila.” Kai ya kad’a mata “inaaa! you are going nowhere ko kin manta kema yau aka sallamoki? Bafa kida lafiya ki zauna ki huta barin d’au lokaci ba zan dawo kinji Flower?”
“O’o” ta shakwab’e fuska.
“Flower please kiyi hak’uri ki zauna zan isar masa da saqon gaisuwanki bareyi ki bini ba.” Badan tana so ba ta gyad’a kai wearing a sad face.
“Flower ba goodluck kiss?”
“Eh babu” ta fad’a ba tare da ta kallesa ba.
“Oh common! Flower.” Alokaci d’aya ta d’ago fuskarta tana mai murmushi “Habeebi na gabad’aya ze fita barin basa goodluck kiss ba? Impossible!” a hankali ta had’a musu lips tare da kissing nasa a passionately. “Off you go take care okay?”
“I will and you too Flower, in shiga dake ciki ko zaki iya?”
“Don’t bother zan iya I love you”
“I love you too Flower.” har ya soma tafiya ta tsayar dashi “wait wait tsaya in d’aukemu selfie so I can be starring at my husband’s handsome face kafin ka dawo.” Murmushin jin dad’i ya saki tare da dawowa baya ta d’aukesu sannan ya fice, anan yashiga ya fito da key’nsa ya fice itama bada jimawa ba tashiga ciki.
*****_3:10PM_
Daidai nan Anas ya dawo gida rashin ganinta a parlour ya tabbatar masa a d’aki take aiko yana shiga d’akinsu ya sameta zaune kan dressing mirror se sosa cikin gashinta take da comb tsantsan k’aik’ayi.
“Flower” ya kira sunanta anan ne tasan da shigowarsa ta juyo tana kallonsa cike da so da k’auna “sannu dazuwa Habeebi.”
“Thank you, me kikeyi haka?”
“Wallahi kaina k’aik’ayi na kwana biyu ban wanke ba, ya jikin Moosa’n?”
“He is okay alhamdulillah.” Yayi maganan yana dosowa gabanta.
“Toh masha Allah, aha! Mami ma ta kira tana gaisheka” tacigaba da sosa cikin gashintan.
“Ina amsawa” yace tare da karb’e comb d’in daga hannunta. “Habeebi bani please k’aik’ayi” ajiyewa yayi kan mirron tare da rik’o hannunta “muje in wanke miki kan Flower.” Dariya sosai ta tsaya yi wanda sakamakon haka Anas ya tsaya kallonta yana admiring nata, dariyan sa na mugun kashesa.
“Habeebi baraka isheni da kayan dariya ba, yaushe kazamo hair dresser da zaka wanke min kai?”
“Aww bakisani ba Flower? I can be anything fo you, Dr, hair dresser, cooku, servant komi da komi ma, muje.”
“A’a please kabari.”
“Flower banason dogon surutu” hannunta ya sake ya shiga cikin wardrobe ya ciro mata vest tare da miqa mata “sa muje in wanke miki” anan shima ya rage kayan jikinsa ya ragar da singlet se ¾ wando zallah.
Ba musu ta cire T- shirt d’in tasa vest daya kawo mata acikin jacuzzi ta zauna ya karkato da kanta direction guda. “Welcome to FAHNAS beauty salon how can I help you Mrs. Fauzi?” Dariya sosai take “thank you, wash and set nakeso.”
“You are at our service.” Daga farko seda yayi combing dogon sumanta sannan ya wanke thoroughly da ruwa sekuma da shampoo, a hankali yake mata massaging kan wanda ke mata dad’i sosai cikin d’ank’ank’anin lokaci ta nemi k’aik’ayin ta rasa. Bayan daya gama wanke mata ya d’aure mata kan da towel sannan ya miqa mata babban towel ta nannad’e jikinta dashi. Gaban dressing mirror ya ajiyeta ya ciro hand drier ya kunna sannan yasoma drying mata gashin bayan ya gama ya mata oiling sannan yayi mata packing gu d’aya harda style na donurt.
“Wow! Habeebi you are amazing!” tayi maganan tana duban kanta cikin mirron. “Wai nikam ya akayi ka iya komai neh?”
“LOL!” yasoma feeling. “Kin manta inada sister ne?”
“Thank you so much for making my hair.”
“Always Flower.” Yayi maganar yana mata murmushi miqewa tayi tare da pecking nasa a both kunatunsa, sekuma tip na hancinsa kafin ta kai kan lips nasa ya dakatar da ita. “Uhn-uhn Flower I know where this is going.” Murmushi cike da kunya ta saki “then let it happen.”
“A’a Flower kin tuna meh Dr. Yace? Cemana yayi kina buk’atan atleast 3 months na hutu before you can get pregnant again.”
“Toh ai hutun d’aukan ciki yake nufi bawai totally mubar yin...” Sekuma tayi shiru “ai ka gane me nake nufi.” light red lips nasa yayi pouting “ban gane ba” yayi maganar da gira d’aya a d’age. Bugi cike da shakwab’a takai masa a hannu “wallahi qarya kake ka gane.”
Dariya yake sosai “toh naji na gane but even still Flower muyi hak’uri.”
“Toh baby ba semuyi using protection ba.” Kai ya girgiza mata “I don’t trust in that, saboda sometimes suna bursting kuma kinga zaki iya samun ciki if that happens which is very harmful to your condition” ya tab’a tip na hancinta. Baki ta murgud’a masa “ina ni kayi rejecting yau Mr. Fauzi nima sena rama.” Hannayenta ya gwada rik’ewa da wuri ta fisge ita a dole tayi zuciya. Daidai zata juya masa baya kenan ya zagaye hannayensa a waist na tare da pulling nata closer to him. “Haba Mrs. Fauzi matar Anas, the mother to my awesome kids in shaa Allah. Taya zanyi rejecting the perfect woman I’m lucky to call my wife? Kema kinsan hakan k’arya ne, Flower ni kaina ina missing naki like hell I miss us on bed amman kinga lafiyarki ya fiye min komai, koda na shekara da shekaru akace inyi avoiding naki zanyi inhar hakan ne ze sama miki lafiya balle ma na d’an months, bawai nayi rejecting naki bane understand kinji? I’m sorry my sugar lips”
Kafad’a ta buga uwar zuciyar har yanzu bata sauk’o ba. “Flower meh kikeso in miki ki hak’ura?”
“Muje mu kwanta.”
“Zamu kwanta amman ba abinda ze shiga tsakaninmu its a deal.”
“O’o toh na fasa hak’uran.”
“Sena sauk’a akan knees d’ina zakiyi?” Ganin yasoma sauk’a tayi sauri ta hanasa. “A’a please baby don’t na hak’ura but can I kiss you atleast Mr. Fauzi?” Murmushi yamata “ofcourse Mrs. Fauzi” sannan yayi owning lips nata da kansa yasoma kissing nata.***
****
Tun daga ranan rayuwan masoya biyu ya cigaba da kasancewa kamar yadda ya saba da a baya ko inche fiye dana da ma, ba fad’a kullum cikin farintawa juna rai suke, ga uban lovely suprises da Anas yake cikin bawa Flowersa a kullum. A kullum wutan soyayyan junansu dad’a ruruwa ya ke a birnin zuqatansu.
★★★★
_6 months later..._
_Monday, 6:20AM_
Tsaye Fannah ke a kitchen da shiganta kusan minti uku kenan yanzu amman takasa tsinana komi ciki dan wani irin zazzab’in da takeji wanda ya fara mata tun jiya da daddare amman sam tak’i nuna wa Anas saboda batasan sasa cikin damuwa ‘cause ta lura aduk lokacinda batada lafiya Anas yafita damuwa. Tsugune take gefen sink takasa koda miqewa, tafi minti biyar ahaka sannan da k’yar ta miqe sanadiyar amai da yazo mata, cikin sink d’in ta riga kwararo amai wane zata harar da hanjinta seda tayi emptying cikinta kap sannan ta wanko bakinta, wane k’adangare tabi jikin bango har izuwa d’akinsu.
A kasalance ta miqe agefen Anas dake ta bacci hankali a kwance.
“Habeebi” ta kira sunansa ko motsawa beyi ba se a karo na uku yayi groaning “uhmmm Flower.”
“Habeebi ka tashi kaji? Yau Monday akwai office.” A hankali ya bud’e idanunsa kallo d’aya yama Fannah yagano batada lafiya she is looking so pale. Cike da tashin hankali ya shafa fuskarta “Flower are you okay?” Kai ta girgiza masa “Habeebi I’m sick ko breakfast na kasa had’a maka, I’m sorry.”
“Subhanallah, shhhh! Haqurin me kike bani?” body tempreture’nta ya tab’a yaji ya hau sosai yayi zafi. “Omg! Flower kinji tempreture naki kuwa? Ya kikeji?”
“Zazzab’i Habeebi sau biyu nake amai yau ko miyau ban iya had’iye.”
“Omg! Flower mesa baki fad’amin ba?” I’m sorry kinji?” Kai kawai ta girgiza masa dan batajin ma zata iya magana.
“Arghhh!” Ta saki wani irin k’ara hannunta rik’e da gefen cikinta, cike da tashin hankali yakai yana dubanta “Flower wani abu ne?”
“Habeebi ciki na tanan, wayyo!”
“Sannu Flower ina zuwa” bayi ya fad’a a gurguje yayi wanka sannan ya had’o mata black tea tare da b’allo mata meds. Duk’unk’une cikin bargo ya tarar da ita “Flower tashi ki zauna kisha magani kinji?” Da k’yar ya miqar da ita tare da jinginata jikin gadon, magunan ya miqa mata sam tak’i karb’a.
“Flower kiyi hak’uri kisha if not baraki warke ba.” Kai ta kad’a masa nufin barata sha ba.
“Why?” Ya tamabayeta.
“Habeebi kasan meh?”
“A’a meh?” yayi maganar ba alaman kwanciyar hankali tattare dashi.
“I think I’m pregnant gani nake kamar ciki ne dani” Bright blue eyes nasa ya zaro waje “Flower you are what?!” Yayi exclaiming cike da k’in yarda dan yadda jin dad’i ya mamaye masa fuska da zuciya.
“I’m pregnant again Habeebi kaga ko bareyi insha kowani irin magani ba it may harm our baby.” Tsantsan jin dad’i har a yanzu Anas yakasa believing. Besan a lokacin da ya ajiye tean a gefe ya rungumo Fannah ba.
“Flower we are soon going to be Daddy and Mammy again, I love you!” Hugging nasa back tayi dukda ba dad’in jikinta takeji ba. “Yes Habeebi” breaking hug d’in yayi tare da riqe hannayenta biyu cikin nasa “Flower dagaske kike you are pregnant?! Omg! Akwai little Fauzi achan? Ko inche akwai HANAN namu a chan?” murmushi tamasa tana gyad’a kai, hot kisses yahau peppering mata a fuska yana sauqowa kan wuyanta tasa hannu da k’yar ta iya ta shuresa “Habeebi please kadaina, kabari banaso.” Cike da mamaki yake kallonta “bakiya son sugar lips naki yau?” Kai ta gyad’a tana turo baki.
D’an murmushi ya saki another symptom yace a ransa “I know this attitude cikin nema dake amman your last pregnancy ai bakiya hanani kissing naki wannan kuma ko kiss d’inma bakiya so?” Nanma kai ta gyad’a.
“Humm! Akwai babban aiki Flower ‘cauae I can’t stop kissing you, yanzu kisha black tea d’in seki kwanta zuwa 10 haka se muje asibiti.” Kai kawai ta gyad’a masa shida kansa yabata tean bayan data gama sha ya kwantar da ita. “Habeebi kaifa baraka je office ba?”
“Mom Hanan bata da lafiya inje office inyi meh? barinje ba zan sanar da Kacallah.” Kai kawai ta gyad’a masa “thank you.”
“Always Baby Machine” yayi pecking nata a kumatu. Hannu tasa ta goge “Habeebi banaso.” D’an murmushi ya saki sannan ya koma d’ayan side d’in ya kwanta tare da janyota zuwa chest nasa ahaka suka koma bacci.
10:30AM Anas ya tashi banda Fannah data kasa bacci tun d’azu se juyi take ajikinsa. Jikinta yayi zafi tamkar wuta shi kansa Anas seda ya razana. “Flower” ya kira sunanta cike da tausayi. “Na’am Habeebi” tayi maganan tana kakkarwa. Kodaya gwada d’gata daga cikinsa sake kankamesa tayi not letting go.
“Flower sannu kinji? D’agani mu shiryaki muje asibiti.”
“Habeebi mubari anjima ban tsammanin zan iya tashi.”
“Sorry kinji? Yi hak’uri” da k’yar ya d’agata ya kaita bayi cikin 30 minutes suka shirya zuwa asibiti achan aka duba Fannah aka tabbatar wa lovely couple cikin sati uku ne d’auke da ita. Murna gun Mr and Mrs Fauzi kam baya misantuwa Anas promised to protect his child with his life wannan karan.
****
Tun isowarsu gida Fannah keta tufar da miyau, ga kuma amai a asibiti ma seda tayi dawowansu ma haka, Anas is so worried ko kad’an bara’a had’a laulayin cikinta na farko da wannan ba, bata iya cikakken minti biyu a tsaye se jiri ya kwasheta. Sede bataji k’amshin turare ba in bahaka ba setayi amai na turaren wutan daya mamaye mata gida ma haushinsa takeji. Sallan Azahar ma sauran a zaune ta k’arisa, lunch da Anas yayi musu ma kad’an ta iya tachi shima ta harar.
Hankalin Anas yayi matuqar tashi zaune yake akan kujera a gefenta, damuwa ne karara a fuskarsa, ayayinda take kan gado lullub’e da bargo se zufa takeyi. Hannunsa dake akan bayanta ya d’aga dan irin zafin da jikin nata yayi sannan ya share mata zufan.
“Sannu Flower, you’ll be fine in shaa Allah I’m here for you.” Moderate cold water ya nemo da towel yana mammatse mata jikin ko ze d’an sauqar mata da body tempreture cikin ikon Allah kuwa zafin jikin nata ya ragu sede bada jimawa ba ya sake rising. Tausayin Fannah duk yabi ya mamaye Anas sam bayason ganinta ba lafiya haka fa suka kwana cikin wannan zazzab’i ba wanda yayi bacci cikinsu se jinyarta Anas yake gabad’aya hankalinsa yabi ya tashi wani irin pegnancy sickness ne haka?
_Washegari..._
Rashin lafiyar yau yama fi na jiya ko meh taci seta harar banda black tea tun Anas na iya jurewa har ya kasa Dr. Mansoor ya kira yazo ya sake duba Fannah har ruwa seda aka sa mata, cikin kwana biyu Fannah tazamo abinda tazama ko k’wararren motsi batta iya yi. Maminta Anas yakira ya sanar da ita halin da ake ciki aiko ba tare da b’ata lokaci ba taje tasamu Afrah dake miqe kan gado se hirarta take sha da dearheart nata.
“Ke katse wayar” cewar Mami dake tsaye akan Afrah dako noticing shigowar Mami batayi ba. A firgice ta katse wayar, hannunta dafe kan k’irjinta “kai Mami dan Allah yaushe kika shigo? Kinfa bani tsoro.”
“Bansani ba kinsa soyayya agaba ina zaki sani dama, mschw! Yarki ba lafiya amman ko a colar rigarki.”
“Fannah?!” Tayi maganam ido a waje.
“Eh mana yanzu Anas yakirani yake sanar dani. Maza maza tashi muje mu dubata wai har ruwa aka sa mata.”
“Oh! Allah sarki Ya Fannah kode wani cikin ne Mami?”
“Mukaje ma sani oya tashi kishirya.”****
*_GWS FLOWER, MOM HANAN😔_*
*Ina me baku hak’uri and inason ku k’ara hak’uri da irregular posting kwana biyu, somethings came up so se harkoki suka min yawa*
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
9 comments:
Thanks miemie
Thanks Dear
thank you mrs. writer God bless you ...
Sanu da kokari
Thanks
Yeh am so happy for de lovers
Pls sis we re expecting de next episode cus latey u haven't been posting.... ....... ..... We can Wait for de sweet ending of ur book....
Well done Jimmie.how is your hand
Well done Jimmie.how is your hand
Post a Comment