Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 02
BY MIEMIEBEE


Tafiya suke a sahu d’aya, tsayin nan nasu na nan d'ai da kad’an Anas ya d’ara Shettima inba wai ance ya da k’ani bane za’a zata agemates ne. Daidai lokacin da suka yanko wata corner kenan Anas yasa hannu a aljihu yaji wayam ba komai, cak ya tsaya hakan yasa Shettima tsayawa shima. “Ya maza lafiya?” “Ba lafiya ba, go ahead I'll catch up nayi mantuwa.” cewar Anas. Shettima ya tsaya ya k’are ma d’an uwan nasa kallo sannan yace, “bade blessing d’in ba.”

      Anas ya kallesa da gira d’aya d’age sannan yace, “toh meh? Kadega yadda su Kashim suka sani tono maganan chan definately nasan ciwon kai ze kamani and despite that, yadda akayi ruwan saman nan I'm gonna enjoy sleeping.” tare da d’anyin murmushi wanda ya sake bayyano da kyansa tare da lotsar da dimple nasa dake kumatun dama. “Kona yau baraka hak’ura ba?” Shettima yasake tambaya. “Se in na amso karka sha” cewar Anas.

       Dariya kad’an Shettima yayi “zan d’an tab’a mana, naji ance da akoi dad’i cikin tea.” Anas ya dafe kafad’arsa “lets go?” Da d’aga kan da Shettima yayi suka juya suka dawo gun Kashim da Baana. Suna iso wurin nasu, Anas yace, “maza bani!” Baana yaci fuska “ban gane baka ba, mezan baka?”  “Wai me ka maidani ne? Give me!” Anas ya fad’a a little bit pissed. Dariya Kashim yayi “basa please kaga har yafara losing temper.”

     Nan Baana yasa hannu a aljihu yaciro wata leda ya raba into two saidai d’aya yafi d’aya yawa sannan ya mik’a wa Anas kad’an din. “Are you serious? Naga fa wannan abu ni nasaya da kud’ina so kabani me yawan ko in hanaka duka.” Baana yace, “haba! Anas namu na kanmu, kap qauyen nan fa kai kad’aine me blue eyes yi hakuri mana. Aikasan da inada kud’i dana siya nima.”  “Toh ni na hanaka yin noma ka samu kud’i? Abeg give me and stop wasting my time.”  “Dan Allah fa nace” Baana yafad’a pleadingly. “Okay naji talaka kawai semun had’u a masjid then.”

      Daidai sunkai ga shiga corner'n gdansu kenan wata budurwa tafito daga wani gida, sanye take da hijabi iya guiwarta, dududu barata fi shekaru 15-16 ba. Idanunta suna sauk’a kan Anas ta sakar dawata murmushi. Tsuka Anas yaja yasa qaninsa a gaba yana tunkud’esa dan suyi sauri subar gun shiko Shettima daya gano haka tuni ya rage saurin tafiyarsa dukda tunkud’in da Anas kemasa.

     Se k’arisowa wajen nasu wannan budurwa ke. “Anas kamar kayi bak’uwa ko? Wannan ba Aisha bace? Ka tsaya kaji me zatace mana.” Cewar Shettima yana murmushi. “Wallahi in bakayi shiru ba zan mareka, kuma barakayi tafiya bane?” Daya wani tunkud’a gaba Shettima besan sanda yasoma matching dasauri sauri suka bar wurin ba.

     Isarsu gidah keda wuya suka tarar da Ummee a tsakar gidah tana tsince shinkafa. Da sallama suka shiga ta amsa da fara'arta. ‘yar dattijuwa ce wacce barata fi shekaru 45 a duniya ba, tanada haske sosai amman bara’a kirata da fara ba, ga kyau daidan gwargwado masha Allah!. “Ohhh mazan nawa sun iso ne? Sekuma ruwa ya tareku a hanya ko?”  “Eh Ummee” cewar Anas yana k’arisowa wajen da take. “Me kikeyi haka?”

     “Tsince nake baba na, tuwon shinkafa Abuu keson ci gashi har ruwan ya tafasa ban gama ba.”  “Toh Amal fa mesa bata tayaki ba? Anyways kawo in tayaki Ummee.”  “Kai Baba na kaide Allah shi maka albarka” ta d'ago kai tana kallon Shettima dayayi kamar besan ma me suke fad’i ba. “Kai yanzu Shettima koda aiki ze taru ya kasheni ba ruwanka da bari ka tayani ko? Baka ganin wanka ne?”

    “Toh Ummee fisbailillahi ina aka san maza da tsintar shinkafa.” Baki wangalau ta bud’e tana kallon Shettima dududu shekarunsa sha shida ne fa da abu aka yake wannan tsiyar bayan ga wansa Anas me shekaru sha takwas bece komi ba. “Ehh hakane, sannu fa” tafad’i cike da gatsine. “Oyoyo Ya Anas” cewar wata kyakkyawar yarinyar da baratafi 8years ba fitowarta daga wata d’aki, ba shakka itace sistersu da suke kira da Amal, kyakkyawace sosai kamar sauran yayun nata bata gama kai Anas fari ba amman tafi Shettima. Su uku kap kamanninsu d’aya.

          (Bayan tafiyar mahaifiyarsu daga gdansu da wata takwas ta turo da Amal da wasiqa na cewa tabar gidan da cikin Amal ga ’yarsu nan ta haifota, kwanan ta d’aya a duniya kenan) sanadin haka Anas yake mutuwar san Amal duk rashin kunyarta bata masa saboda duk fitar da zeyi seya siyo mata abun k’walama unlike Shettima da cikinsa kawai ya sani thats the reason why basu shiri da Amal kullum cikin fad’a sukeyi duk sanda Anas yazo kuma seya bata gaskiya, wani sa’in har taran dangi suke masa.

     “Oyoyo my angel” yafad’i tare da bud’e hannunsa tazo da gudu tayi hugging nasa. “Ina sweet d’ina ya Anas?” kafin ya amsa mata ta zira hannu cikin aljuhunsa taciro ’ya’yan wiwin da Anas ya amso gun Baana sekuwa idan Ummee yakai kai. “Baba na meh wannan!?” Ta tambaya tare da zaro idanu waje. Nanfa Anas yasoma kame-kame can yace, “laaa Shettima kalli wannan abin da abokin Baanan can yace na rik’e masa” yama Shettima ido. Shettima yace, “ohh yamanta be karb’a ba kenan?”

      “Gashi anan kuwa!” Cewar Anas. “Anyways meh abun nema?” ya amshi daga hannun Amal. Ummee tace, “maza ka mayar masa wannan abu shaye shaye akeyi dashi, mayar masa maza!”  “Toh Ummee amman bansan ina gdansu ke ba, agidansu Baana muka had’u.”  “Nide koma me ka mayar masa.”  “Toh Ummee bari in muka fita Maghrib zan bawa Baana ya mayar masa.” Anas yafad’i a hankali
“Toh” tace tare da numfasa. “Ya Anas to ina sweet d’ina toh?” Cewar Amal.

      “Angel bansamu na saya miki ba, shops d’in duka a rufe I promise gobe kinji?” A hankali ta giad’a kai tare da turo baki. “Tsaya kiji wani batu” nan ya daidaita tsawonsa yakamo nata tare da rad’a mata wata magana a kunne aikuwa tahau tsalle suna ido hud’u da Shettima ta galla masa harara. “Wallahi Amal niba sa’anki bane wa kke harara? Maras kunya kawai.” Kafin Ummee ta masa magana Anas yace “ah’ah karka zagarmin k’anwa now go inside okay? Anyi ruwa kar mura ya kama ki.” Tana tsalle takoma ciki.

     Ba tare da b’ata lokaci ba Anas yataya Ummee suka gama tsince shinkafar banda Shettima daya tsaya kansu yana kallonsu cike da mamaki yarasa meke burge Anas a aikin kitchen bama aikin kitchen kad’ai ba. Bayasan ganin abinda ze tab’a Ummee ko Amal, he is so protective of them, duk abinda zeyi zeyi inhar it will keep them save and happy.

   *****

        Bayan sunfito daga masallaci iyayensu sukayi gaba a yayinda Shettima, Anas, Baana da Kashim suke tafiya a bayansu suna tattauna warsu ta maza. Wata budurwa ce ta b’ullo gabansu, dakatar dasu. “Ina wuni?” ta gaishesu duk suka amsa illah Anas dake neman any chance yabar wajen. “Anas ina wuni?” tasake fad’i cikin wata anniyar murya ganin shine be amsa ba. Shiru yamata, “Shettima ko nama Anas wani abu ne baimin magana?”

      Murmushi k’adan Shettima yayi sannan yayi k’arya “ko kad’an Hafsah mura yake saisa bai iya magana.” Wani kallo Anasa ya watsa masa wanda shi Shettima yamayar da murmushi. Kafin yace wani abu Hafsah tace, “dama zuwa nayi na tayaka murna ne kan scholarahip daka samu cewa nanda ‘yan kwanaki zaka London shine na had’o ma wannan pepper soup sekuma gashi kana mura I'm sure ze d’an wassakar maka da muran ma. Gashi please ka amshi”

        Ganin Anas baida niyan karb’a Shettima yasa hannu ya amsa “kai sannu Hafsah kamar kinsan mura na damunsa kika kawo wannan.” Shettima ka tabatta Anas yasha please ze taimaka masa sosai.”  “Aii karki damu” cewar Kashim “consider it done, zamu tabbata yasha.”
 
      Da murmushi a fuskarta tace, “toh nagode seda safenku.” Sanda ta sake kallon Anas sannan ta fice. Nan Anas ya finciko Shettima tare da kama masa kunne ya murd’a da iya k’arfin da Allah ya basa. “Awchhhh!” Shettima ya sakar da k’ara. Karb’e kulan abincin Anas yayi ya soma tafiya. Baana yace, “ya haka kuma? Nad’au ai baraka ci ba.” Duk suka k’yalk’yale da dariya. Bece dasu komi ba yacigaba da tafiya, “anji kunya” cewar Shettima nan ma be tankasu ba. Yana isa gida ya tarar da Ummee tana ‘yan wanke-wanke kafin ya b’oye flask d’in har ta riga ta gani.

       “Baba na me wancan kake k’ok’arin b’oyewa?” Cewar Ummee da murmushi fal a fuskarta. “Oh wannan!” Ya d’ago flask d’in sama “erm... Erm... Na-”

      “Iyye baba na manya har ‘yan matan naka sun soma kawo maka abinci ne, to yayi kyau. Me aciki?”

    Kamar ya mata k’arya sekuma ya fasa, “pepper soup ne nakawo wa Amal ko kema zaki tab’a?”  “Noo haba! Budurwa takawo wa Baba na kaji kuma se inci je kaci abinka.”  “Kai Ummee da Allah bafa budurwata bace.”  “Hehe!” tayi dariya sosai “yanzu uwar taka kake jin kunya?”  Rashin sanin me zece mata yasa ya wuce ta kawai ya kira Amal suka wuce d’akinsu ya bud’e masu suka sha pepper soup nasu. Ni miemie nace Anas ba kunya yanzu sha yake!? Lol

       Sun ci kusan rabin kazan Shettima yashigo senishi yake da alama gudu yayi ya iso nan. “Yanzu Anas cinye kazan nan zakayi da wannan maras kunyan baraka d’an bani ba nima?”  “Eh bara'a bayar ba” cewar Amal “Ya Shettiman nan shegen kwad’ayi wallahi ko Ya Anas?” Ta sake p’antarar kazar ta kai baki. “Sosai ma Angel” Anas ya amsata. “Wallahi Amal ki kiyaye ni” gwalo ta masa sanin in Anas na gefe da ita ba abinda Shettima ya isa ya mata.

          “Ka kwantar da hankalinka bari mu fita sallan Isha har gidansu Hafsah zanje in fad’a mata ka cinye kazan kap ko k’ashi baka bari ba.” Murmushi kad’an Anas yayi “to ai ko ka fad’a mata ba yadda zatayi ba saboda ban bata fuska ba.” Haka ya dake sanda suka cinye kazan tas shida Amal, pippike da wuya suka ragar sannan Anas ya ceda Amal ta mik’a ma Shettima da yawunsa ke d’iga k’asa.

      Itako ta d’aga ta ajiye mai “gashi Ya Shettima.” Hannunta ya rik’e tare da danna mata nank’washi aiko tasaki kuka harda na munafirci take Anas ya k’ariso ya rama mata.

     ***

     Haka ma da suka dawo sallan Isha Aishar d’azu ta tsaresu tare da masu sallama kap suka amsa illa Anas. Sak batun da Hafsah tayi haka Aisha ma tayi sede nata chips da omalet ne, itama na taya Anas murnan samun scholarship da yayi. Anas na jiran Shettima ya amsa kamar na d’azu aikuwa yak’i. “Dan Allah kayi hak’uri ka karb’i Anas ni badan kasoni na kawo ma ka ba, consider it as a friendship gift please.”

      D’ago blue eyes nasa yayi ya kalleta ciki ciki wanda tuni ta soma shaking tare da kawar da kanta. Ajiye flask d’in tayi a k’asa “dan Allah ka d’auka se da safenku.” Aiko tana shigewa cikin gdansu ba kunya Anas ya d’aga yakama tafiya. Baana yace “andeji kunya” haka suka ta masa tsiya amman ko a kolan rigarsa, duk yasan so suke suci kuma bayarwan ne bareyi ba. Nanma dashi da Amal ne suka cinye wannan karan ko ragowar ma ba’a baiwa Shettima ba.

    ****

        Da misalin k’arfe goman dare bayan kowa ya kwanta a gdan. Anas da Shettima suna kwance kan seperate gadonsu bayan sun gama shan wiwinsu cikin tea. Shettima daya zura wa Anas kallo na kusan mintuna yace, “tunanin me kake haka?”

      “Anas?” Nanne ya dawo hankalinsa “yes! kace me?” Shettima ya kuma nanata kansa “nace tunanin me kake?”

     Murmushi sosai Anas yayi wanda yasa dimple nasa lotsewa sosai, kad’an daga cikin fararen hakwaransa suka bayyano. “My dreams are about coming true.”  “Wani dream kenan?” Shettima ya tambaya tare da tasowa ya zauna kan gadonsa tare da jingina bayansa a jikin kan gadon.

      “Don't tell me bakasan dreams d’ina ba! Ofcourse to be a billonaire se in samu inyi breaking hearts na thousand of women by then kaga na ramawa Abuu abinda mamarku ta masa.”

    “Wai wace erin magana kakeyi Anas? Wai yanzu kana ganin in Abuu yaji wad’annan munanan kalamu daga bakinka zeji dad’i? Haba mana kai baka yafiya ne?”

      “Yafiya! Har yau bansami defination na word d’in a dictionary ba plus in wa’azi kakeson yi kaje masallaci kayi, kagannin nan? Banasan jin wannan wa'azi allow me to get some sleep yadda nasha ’ya’yan wiwin nan.” Nan yaja bargo tare da rufe kansa ciki a hankali bacci me nauyi ya daukesa.

*© miemiebee*

No comments: