Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI...PAGE 41
BY MIEMIEBEE

Haka har da aka tashi Anas be sake neman Fannah ba. So yake ya nisantar da kansa daga gareta as possible enough as he can, saboda ya soma ji kamar maganganun Shettima gaskia ne. Saboda when it comes to Fannah he is weak abubuwa dayawa take masa wanda yaci ace ya koreta koya hukunta ta amman seyaji bare iya mata komai ba. Yasoma yarda eh he is feeling something for Fannah amman ba love bane tausayi ne kawai, yana tausayawa mata sede ko daya tambayi kansa tausayin me take basa yakasa answering. Fannah is his weakness.

Fannah kuwa dad'i taji da be sake nemanta ba dan da wannan kayan kunyan da tama kanta na masa shisshigi harda karance diary'nsa bata san da wani idan zata sake kallonsa ba. Ita abinda yafi bata mamaki ma shine yadda Anas yabata hanky wai ta goge hawayenta bayan abinda ta masa, shin meke damunsa yau? Ta d'au atake zeyi firing nata kokuma ya mata wani abu makamancin haka amman seyayi sab'anin abinda take expecting. He is acting wierd yau, bata tab'a ganinsa haka ba shida yake fad'in kukanta bai damunsa segashi yau bayasan ji.

Hanky'n ta ninke tasa cikin jakarta sannan ta mik'e tare da rufo k'ofar ta dan ganin lokacin tashi yayi. Ta rufe k'ofar office nata ta juya kenan sega Anas shima yafito suna had'a ido tayi saurin kawar da kanta. Public elevator tabi a yayinda Anas ke binta da kallo so yake yace mata ta zo su shiga elevator'nsa amman kuma girman kansa bare bar sa ba, wai mesa ma yakesan su shiga elevator'n sa bayan abinda ta masa d'azu? Sanda ta b'ace sannan ya nufa nasa ya shiga shima, kafin ya sauk'o kuwa tuni Fannah ta k'ara mai. A d'an wani shago ta tsaya tare da yima family'nta d'an siyayyan kayan k'walama. Isarta gida keda wuya.

Mutane biyun data gani tsaye cikin gidansu ne suka mugun razana ta. Ido wuru wuru ta zaro tare da dafe k'irjinta tana me salati a zuci. "Baffah Khaleel?! Ya Farouq?!" Kai tasoma kad'awa danko bata yarda da abinda idanunta suke gane mata ba. Mami dasu Afrah dake tsaye gefe guda suma fuskarsu d'auke yake da damuwa.
"Mami dan Allah kice min basu bane, tell me idanu na wasa suke min."

"Fannah manyan gari wato har gidan TV ake nuna ki, 'yan matan nawa fa duk sun girma sosai tunba Fannah surikata ba." Cewar Ya Khaleel yana wani murmushin mugunta.
"Kai Farouq baka ga matarka bane da baraka mata magana ba? Jeku gaisa mana." Wani tantirin dariya ne a fuskar Farouq a yayinda ya soma takowa gaban Fannah. Baya tayi take ganin haka "Fannah mata ta ya haka kuma? Mijinki ne fa ni, bekamata kina min haka ba, matso mana mu gaisa." Sosai Farouq ya sake girma yazama cikakken na miji yanzu kyansa ya sake fitowa, sede iskancin nan nasa daya saba har yanzu yana yi be bari ba.

"No don't touch me." Kamar kyaftawan ido Mami tashigo tsakaninsu, "Ya Khaleel meh amfanin haka dan Allah? Nasan kai da d'anka kunfi k'arfin mu dan Allah kuyi hak'uri ku koma inda kuka fito. Fannah bata san Farouq Ya Khaleel kayi wa Allah ka hak'ura da kai da d'anka dan Allah."
"Maman Aiman kenan, in kinga mun koma Bama toh wallahi da Fannah ne. Wace karuwar 'yarkun ma wacce ko martaba battada, dan ni da Farouq zamu rufa mata asiri zaku wani tsaya kuna mana tsiya yau shekarunta nawa takasa yin aure, ba d'a na mijin da ze amince ya auri Fannah inba Farouq ba."

"Baffah Khaleel dan Allah kayi hak'uri ka rufa min asiri banasan sake komawa Bama, banasan Ya Farouq ni na rungumi k'addara zan gama rayuwata duka ba aure dan Allah kar ka aura min Ya Farouq." Fannah ta fad'i hawaye na gangarowa kan kumatun ta abin tausayi. Tajima bataji tashin hankali kamar na yau ba. Ta riga da ta ajiye past nata a gefe mesa su Baffah Khaleel zasu dawo su hargitsa mata komai??

"In baki son shi to shi yana sanki sakariya kawai, aure tsakaninki dashi kuma farillah ne nan da 'yan watanni, gomma tun wuri ku fara shiri, karatu ne Farouq yayi. Yanada diploma'nsa dakuma aiki me albashin da ze iya rik'eki. Kinga ko wannan karan ke zakiyi kayan d'akinki tunda kema kinada aiki. Abinda ya kawo mu dama kenan, bayan biki zaki bi mijinki Bama ku fara zama acan, in qaninan ya tashi ku gaishesa. Farouq mu tafi."

"A'a Baba ni ba yanzu ba semun gaisa da matar tawa tukuna."
"Karka damu akoi gobe ai, gobe zaka dawo har girki seta maka tunda matar kace, mu tafi." Nan suka fice. Kuka me k'arfi Fannah ta rushe da. Mami na bata hak'uri haka Afrah da Aiman ma. "Mami ni shikenan Ya Farouq zan aura? Duk inda mukaje se sun tsakuro mu. Mami dan Allah do something wallahi banasan Ya Farouq mugu ne, azzalimi banasan sa Mami." Ta k'ara shigewa jikin Mami tana kuka me tsuma zuciya.
"Yi shiru Habibti in shaa Allah baraki auri Farouq ba kamar yadda Allah ya k'wato ki kwanakin baya haka ma ze miki yanzu mu dage da addu'a kawai."

"Ya Fannah kiyi hak'uri zamu tayaki da addu'a" cewar Afrah cike da tausayi. Kuka sosai Fannah takeyi haka yadda taga rana taga dare ta kasa bacci. A ranan kowa hankalinsa tashe yake basu san kuma ina zasu sake zuwa ba, basu san ko in sun bar Maiduguri akoi inda zasuje Fannah tasamu aiki me kyau kamar na nan ba. Baba ya tausaya wa 'yarsa sosai ba kuma abinda yafi bak'anta masa rai kamar in ya tuna ba abinda ze iyayi ya cheto 'yarsa daga halaka. Dan auren Farouq halaka ne yaron da besan darajar mace ba ko kad'an, d'an giya d'an iska.
Daga Fannah ta rufe ido seta soma mafarke mafarke ganin ba mahilicci se Allah ta tashi tayi alwala tariga nafilfilu har seda k'arfinta ya k'are sannan tayi zaman istighfaar. Da safe ta tashi tana shirin office sanyi sanyi kamar wacce k'wai ya fashe ma aciki duk Afrah na kallonta takasa koda ce mata uffan dan tausayi. Mami ce tashigo ta tarar da ita tana sa kaya bayan gaisuwa Mami ta tambayeta cike da tausayi "Fannah ba se kinje office ba yau ki huta"

"Mami gomma inje saboda zama anan ba abinda ze haifar min inbanda bak'in ciki jiya Baffah Khaleel yace Ya Farouq ze dawo yau, bana san ganinsa Mami na gwammaci naje office."
"Toh shikenan Fannah Allah kare kicire damuwa daga ranki kinji? Muna nan muna kan miki addu'a."
"Nogode Mami ni na tafi." "Allah kare" both Mami da Afrah suka mata sannan ta fice.

8:01AM daidai ya mata a office na Mr. Fauzi kanta sauk'e a k'asa ta gaishesa, sama sama ya amsa. Jakarta ta bud'o tare da ciro hand kerchief daya bata jiya ta ajiye kan table nasa. "Gashi, nagode." D'gawa yayi ya sake mik'a mata "na baki keep it."
"But Sir-" katse ta yayi "I said keep it" yace a hankali. Amsa tayi tare da masa godiya ta mayar cikin jakar ta.
Har yanzu basu had'a ido ba dan kanta a sunkuye yake.

"Ina schedule d'ina na yau?" Ya tambayeta yana danne danne a laptop nasa.
"I'm sorry bansamu na had'a ba excuse me yanzu zanje in had'a maka."
"Mesa? Me kikeyi tun jiya da baki had'a ba?" Ya tambayeta cike da tsiwa.
"I'm sorry" tace nan ma bata d'aga kai ba sede daga yadda take maganar Anas ya gano wani abu na daminta ya tambayeta meneh kuma girman kansa bare barsa ba. Kallonta ya tsaya yi kusan na minti biyu amman sam bata gwada yunk'urin d'ago kai ba bale ya kalli cikin idanunta ma. "Miss Aleeyu" ya kira sunanta a hankali.
"Yes Sir" ta amsa ba tare da ta d'ago kai ba. "Make me coffee" ya fad'i. A sanyaye ta juya ta nufa wajen machine d'in sede hankalinta ko kad'an baya jikinta tayi nisa tunanin abubuwan da suka faru jiya she actually can't believe Baffah Khaleel da d'ansa Ya Farouq sun dawo suna san maida ita Bama da bata sake tsammani zata koma wataran ba.

Bayan ta gama had'a jagual-gualenta ta juyo dan ba coffee ba sunan abinda ta had'a. D'an k'usa ne ya kama mata hijabi agarin cirewa tayi b'arin coffeen duka ya zube a k'asa cup d'in kuma ya fashe. Kid'imewa tayi a lokaci guda batasan lokacin da ta tsuguna ba dan tattarawa. "Don't Miss Aleeyu karki ki tab'a" Anas yayi warning nata da ihu chak ta maida hannunta. "I'm sorry" ta fad'i hawaye na cikowa a idanta. "I'm sorry please" ta sake basa hak'uri.
Toh kuma kukan meh? Ai be tab'a taba, bekuma mata masifa ba kodan d'an ihun dayayi dan kar ta tab'a glass d'inne ya sata kuka? Tasowa yayi daga mazauninsa ya nufo gabanta har yanzu tana tsugune "get up" yace mata. A hankali ta mik'e kanta sunkuye se hawaye takeyi side bag nata ya mik'a hannu yaja a hankali, batace masa komai ba, bud'ewa yayi ya ciro handkerchief daya batan "wipe off your tears" amsa tayi ta na gogewa sede the more tana gogewa the more kukan yake k'aruwa harda me sauti da k'yar ya zaunar da ita.

Besan me ba se kawai yaji ya damu da ita bayasan ganin ta tana kuka. "Miss Aleeyu mesa kike kuka na miki wani abu neh?" ya tambayeta a hankali. Kai ta kad'a masa da nufin a'a tana me cigaba da kukan.
"Toh mesa kike kuka? Sabida glass cup da kika fasa min ne? Don't worry I have lots more."
Kukan take har yanzu ba makawa hasali se k'ara volume na kukan nata ma take. "Miss Aleeyu what is it?" Kai kawai take kad'a masa chan ma ta tashi ta ruga office nata a aguje kan table nata ta baje sekuka take shark'af shark'af abin tausayi. Anas nason bin bayanta amman girman kai irin nasa bare barsa ba. "For goodness sake what is wrong with me? Mesa nake damuwa da Fannah? She is not my responsibilily so let her be, duk abinda ke damun ta ita taji wajen." Mik'ewa yayi tare da zama kan kujerar sa yana me cigaba da abinda yakeyi. Sede inaa mind nasa gabad'aya yana wajen Fannah. What if har yanzu kuka take? Me aka mata ko daga gida ne aka b'ata mata rai? Wayarsa ya d'ago dan kiran Mami se in ya soma shiga se ya katse haka ya kasa kirarta dan tambayen meke damun Fannah. Meeting dayake dashi ma yau shi kad'an sa yaje saboda yasan there will be no point yaje da Fannah tunda haka ta taho yau tana kuka. Shi kad'ansa yaje though shima duk hankalin sa na kan Fannah bayan da meeting d'in ya k'are as usual driver ya wuce dashi hotel dan cin abinci.

Ga abincinsa a gabansa amman yakasa chi, dududu sau nawa suka chi abinci da Fannah amman yaji yau inba ita bare iya chi ba kuma bawai fa baya jin yunwa bane kawai seda ita ze iya chin abincin. Kacallah ya kira kan ya sanar da Fannah driver ze zo d'aukanta yanzu dan bayasan ya kirata da kansa ta raina sa, hakan kuwa akayi bayan 20minutes aka kawo Fannah hotel d'in tana shiga tagansa zaune dan bata masan nan za'a kawo ta ba ce mata kawai akayi Boss na nemanta. Idanunta sun kumbura sunyi ja dan kukan datasha a hankali ta k'arisa gaban table nasa ta tsaya ba tare da tace uffan ba.
"Sit" yace mata hakan ko tayi bada jimawa yasa aka kawo mata abinci sak irin na jiya. Nan ma "eat" yace mata.
"I'm not hungry" ta masa k'arya dan kuwa ko breakfast batayi ba yunwa takeji amman batada appetite na cin abincin saboda damuwar dake kanta kad'ai ya isheta. Spoon biyar yakai yaga ko yunk'urin tab'a abincin ta batayi ba.
"Miss Aleeyu bakiya so ne akawo miki wani daban?"
Kai ta kad'a masa. "Then why are you not eating?"
"Sir I'm sorry bana jin yun-" bata k'are maganar ba cikinta yayi wani irin kuka.
"Yes kinajin yunwa eat." Nanma kai ta kad'a masa. "Kichi kokuma in baki 500 papers kiyi correcting nasu" ya gwada taorata ko dan haka zata chi. "Okay I'll do it in muka isa office d'in." Mamaki sosai amsarta ya basa itan da kullum take had'asa da Allah in ya bata aikin yau ita ke fad'in zatayi kai tsaye? Toh meke damun ta?

"Miss Aleeyu meke faruwa? Meke damunki? Tell me." Ya tambayeta cikin sanyin murya dan duk yashiga cikin damuwa ganin Fannah a damuwa."
"Babu Sir thanks for your concern, zan jiraka a waje in ka gama se mutafi in fara correcting papers d'in da wuri saboda in gama on time."
"Barakiyi correcting komi ba, I don't mean it kawai kichi abincinki kinji? You are sick har yanzu zama da yunwa won't help, eat." A hankali ta d'aga spoon nata ta soma ci sede ba hab-hab kamar yadda ta saba ba. Anas ko da jimawa yagama cin nasa yayi zaman jiranta saba'anin yadda ya saba. Dududu quarter kawai taci tace ta k'oshi. "Are you sure?" Ya tambayeta kai ta gaid'a masa. Bayan ya biya kud'in suka fice.

Shigarsu mota Anas yace da driver "ba office zamu wuce ba gidansu Miss Aleeyu zaka kaimu." Cike da mamaki ta d'ago kai se yanzu suka had'a ido dashi tun had'uwansu yau. "Gidan mu kuma Sir? Mesa?"
"Saboda inji meke damunki." Yabata takaicaccen amsa.
"No Sir please don't ba abinda ke damuna kawai fad'a mukayi da Afrah" tanasa k'arya
"Ban yarda ba" ya bata amsa yana duban agogon sa.
"Sir I'm serious." Ita tsoronta kar in sunje su had'u da Baffah Khaleel kamar yadda ya saba kiranta da karuwa ko karya ya kirata gaban Anas. "Sir please mu juya na bar wayana a office I need to get it." ta masa k'arya ko ze canza mind nasa.
Resting kansa yayi jikin kujerar "karki damu zansa Ahmad ya kawo miki."
"Sir-" hannu ya aza kan lips nasa "shhh! Banasan surutu dayawa." Ahaka har suka iso gaban gidansu Fannah zuciyarta se bugun d'ari d'ari yake. Driver na parking Fannah ta fito da sauri dan duba ko su Baffah Khaleel suna gida takai da shiga k'ofar gidansu kenan kawai suka ci karo da Ya Farouq kafin tayi wani k'wak'waran motsi ya cafko ta da hannu daidai lokacin Anas yake fitowa daga motan shima, idanunsa basu tsaya ko ina ba se kan hannun Farouq rik'e dana Fannah se k'ok'arin k'wata take amman ta kasa. Wani erin mahaukacin kishi yaji ya bugesa inba wai kashe koma waye mutumin yayi ba yana ganin bare samu sukuni ba.

A fusace ya k'ariso wajen. "Matata me haka dan na kama miki hannu? Ke wai bakiyi missing d'ina bane? Ko d'an shafaki bara ki bari inyi ba?" Cewar Farouq dawani shu'umin murmushi fal a fuskarsa.
"Ya Farouq ka sake min hannu niba matar ka bace let me go" ta fad'i tana hawaye tare da k'ok'arin k'wace hannunta.
"Ka sake mata hannu!" Anas ya fad'a cike da isa. Fannah da Farouq tare suka juya suna kallon Anas. "Waye kuma wannan baturen?" Farouq ya tambaya.
"Mr. Fauzi please ka tafi, don't involve yourself in here."
"Kinsan sa kenan" Farouq ya sake tambaya. "Bade shima saurayin ki bane kina kwana dashi, kinsan sana'a sa'a." Anas be san lokacin daya kai wa Farouq naushi a fuska ba da zobobin azurfa a hannunsa. Take hancin Farouq ya fashe gefen bakinsa yasoma na d'igan jini.


*© miemiebee*

No comments: