Saturday, 3 September 2016

TANA TARE DA NI...

TANA TARE DA NI... PAGE 40
BY MIEMIEBEE


Shettima na gama share wajen kamar yadda Anas ya umurcesa ya wuce d’akin Anas. Knocking yayi Anas naji yasan shine “Shettima kashigo d’akin nan zan sab’a maka.”   “K’yal k’yal k’yal” Shettima ya shek’e da dariya kafin Anas ya tashi yasa lock a k’ofar inaaa har Shettima ya bud’e ya shiga.
   “Fita toh” Anas ya fad’i yana nuna masa k’ofa.
     “Ai wallahi ban fita se munyi magana.”
    Punch ya kai masa a saman hannu “ai dama maye ne kai seka cinye d’akin zan koma parlour ko guest room.” Vest nasa Shettima ya kama “please mana Ya Anas I’m serious we need to talk.”
    “Wai akan meh? Ha’ah!” Anas ya fad’i a fusace.
    “Akan Fannah, Fannan office naka.”
     “Me zakace a kanta? In ma so kake kace ina santa to wake up you are dreaming ni bana santa har yau banga macen da zance ina so ba, ba’a yita ba. Fine, are you okay now? Zan iya tafiya?”

      “Ya Anas kenan bakasan meh soyayya ba wallahi, kana feeling abu amman baka sani.”
    “Toh love expert seka je inda akeson jin bayaninka kamusu amman ni banaso, sake min shirt.” Jansa Shettima yayi da k’arfin gakse da vest nasa sanda ya fad’o kan gado. “Toh Ya Anas bari kaji, inhar kana experiencing wannan abubuwan da zan lisafo whenever kana *_TARE DA_* da Fannah to you are in love. Na farko;”

        Ya numfasa, “Duk lokacin da kuke tare zakaji kansan kata kallonta, you can’t take your eyes off her.” Shiru Anas yayi yana nazari kamar d’azu kawai yaji yanasan yana kallonta har da d’aukan popcorn yanaci yana kallon Fannah, kuma ko a meeting d’in d’azu yakasa dena kallonta.

       “Na biyu, zakaji ka damu da ita, the moment abu ya sameta you’ll just be there for her, zakaji kanasan kana protecting nata from kowani erin harm da zezo mata.” Nanma nazarin yake kamar d’azu da batada lafiya kawai yaji yanasan ya taimaka mata yayi protecting nata.

      “Na uku, za kana kishinta daga ka ga na miji na mata managa ko na tab’a ta sekaji kanasan kashe koma waye shi a lokacin.” Nazarin yake kamar ranar daya kira Yusuf yake ce masa suna tare da Fannah, dakuma yau da Moosa yayi yunk’urin tab’ata da kuma d’azu da Shettima yace masa yana san Fannah.

     “Na hud’u, du-” katse sa Anas yayi “banaso! banaso!” Kunnuwansa ya rufe da hannayensa yana kad’a kai “No! No! No! No! It can’t be! I can’t love Fannah. No! No! Shettima get out please.”
      “Ya Anas ina sanka ne saisa nake fad’a maka duk wad’annan abubuwa. Tunda har Allah ya bud’e maka zuciyar ka accept it, kana san Fannah there is no denying in that. Change your life Ya Anas now is the time, ka manta da pass naka and move on.”

    “No! No! Absolutely no just get out please, I need to think.”
      “As you say” yana kaiwa nan ya fice. Pillown dayake rungume dashi ya wullar sanda ya fasa wani had’adden flower vessel a d’akinsan. “I can’t fall in love, bangama mission dana fara na breaking zuqatan mata guda d’ari ba guda 50 nayi sauran rabi, I can’t fall in love. Bareyi Fannah kizo ki b’ata min plans ba, I have to send you farther away from me, bareyi in so ki ba, ni ba’a haifeni dan inyi soyayya ba an haifeni ne dan in d’au revenge, in kuma koya wa mata lesson a life. No way!”

    *****
      _Washegari..._

     8:00AM yama Fannah a office for the first time, bata k’ara ba bata kuma rage ba. Knocking tayi bakin k’ofar office nasa. “Enter” yace hannunsa biyu rik’e k’ark’ashin hab’ansa da alama tunani yake tun d’azu. Yana ganinta se kawai yaji damuwansa sun soma gushewa, sanye take da pitch hijabin daya mugun mata kyau tare da amshe golden skin nata, besan sanda ya fara kallonta ba yakuma kasa hana kansa kallonta, shi yarasa me yake kallo ma wajen Fannah. Is not as if tana shirin batsa ne bale ace ko jikinta yake gani, kullum cikin hijabi take amman inya kafa blue eyes nasa kanta baya iya d’agasu. Bebar kallonta ba seda ta k’ariso gaban table nasa. “Good morning Mr. Fauzi” ta gaishesa, dan takaici ko amsa gaisuwan ma beyi ba, files na gabansa da Kacallah ya kawo masa jiya yaja ya soma signing, abinda ya kamata yayi tun a jiyan amman tunanin Fannah ya hana sa.

    Fannah kuwa ganin baida niyan amsa gaisuwarta ta bud’o side bag nata tare da ciro jotter’n ta “ga schedule naka na yau Sir, inda akoi abinda za’a giara let me know. Zan koma office d’ina.” Bece mata komai ba ganin haka ta juya har ta kai da bakin k’ofa ya kira sunanta a hankali “Miss Aleeyu.” Cak ta tsaya “kar ki tafi.”
      Ido ta zaro wurur wuru bambarak’wai tajiyo kalamun kamar ya kar ta tafi, a hankali ta juya “eh? Sir?” Ta tambayesa. Kansa sunkuye yana kallon files na gabansan yace, “kar ki tafi office naki yau sit here” a hankali kamar ba shi ba. Bata d’au maganar dawata manufa ba kuma yanzu, dan yadda ta karanchesa yau seta ga kamar yana cikin damuwa ne maybe a gida aka b’ata masa rai dande a office kam ba wanda ya isa. A sanyaye ta koma ciki ta zauna kan cushion tana wasa da yatsunta. A hankali ya d’ago blue eyes nasa yana kallonta koda idanunsu ya had’u beji kunya ba kallonta ya cigaba da yi, take ta kau da kanta. Tsikan jikinta har tashi suke dan yadda blue eyes na Anas suke kallonta.

     Da kallon ya isheta se kawai ta mik’e be ce da ita komai ba illa binta da kallo da yake, wajen coffee machine ta nufa ta had’a masa sannan ta kawo ta ajiye kusa dashi. “Sir it seems kamar yau wani abu na damunka take this, it might help.”,Ita Fannah acewarta tunda in ita batada lafiya yana nuna ya damu itama bari ta mayar masa da kulawan in return sede kamar yadda tace ba’a gane halin Anas.

    “Banaso!” yace da zafi. “Jeki zubar banaso!” Ya fad’a a tsawace dayasa ta firgita. Me tayi ne da Mr. Fauzi baya san coffeen ta yanzu?
     “Mik’o min bottle d’aya a fridge.”
    Shaye shaye again! Ita abinda bata so kenan, mesa Mr. Fauzi zena shaye shaye. “Mr. Fauzi shan abunnan baida amfani please kadena”
     “Bakida right na fad’a min abinda zanyi pass me a bottle.” Bata ko motsa ba “now!” Ya daka mata wani irin tsawa bata san lokacin da ta je ta d’auko masa ba. Hawaye take sosai, ganin ya bud’e bottle d’in kawai ta juya bayanta shima koda yakai baki seya kasa sha ya rasa dalili. “Damn it!” Ya fad’i a fusace tare da wurgi da kwalban tatas! Ya fashe a k’asa. A firgice Fannah ta juyo ganin kwalban ya fasa taji dad’i sosai a ranta.

       “Sir take the coffee please” d’agawa tayi daga kan table d’in ta mik’a masa kallon cup d’in yake yana nazarin ya karb’a ko kar ya karb’a. “Ka karb’a please.” Hannu ya sa ya amsa tare da kaiwa bakinsa, kurb’i daya yayi kawai seyaji duk damuwansa sun gushe, abinda ko giyansa ma be tab’a masa ba. Atleast in giyan ne seya d’au kamar minti uku daga baya ma yazo seya kusan minti goma saboda yadda jikinsa ya saba dashi. He really missed her coffee like crazy be cire daga bakinsa ba sanda ya kurb’d duka.

      “Should I make you another?” Ta tambayesa kai ya kad’a mata.
      Amsar cup d’in tayi taje ta ajiye kan fridge sannan ta kama hanyan fita. “Miss Aleeyu ina zakije?” Ya tambayeta cikin sanyin murya kamar bashi ya masifeta yanzu ba.
   “Zanje in d’auko mop ne daga janitor’s closet (inda ake ajiye tsintsiya, mop da sauran kayan share dotti) in yi mopping wajen chan.”
     “Leave it cleaners zasu yi taking care of wajen just don’t go.”
     Wai meke damun Mr. Fauzi ne yau? Mafarki yayi ne yake tsoron a barsa shi kad’ai ko meh? Dawowa tayi ta zauna kan kujera duk lokacin data d’aga ido se suyi ido hud’u da Mr. Fauzi kallonta yake ko kyafta ido baiyi. Bata kuma d’aga ido ba se chan, tana d’agawa kuwa taga har yayi bacci kan table d’in. Through out jiya beyi bacci ba as se tunanin abinda Shettima ya fad’a masa kan Fannah yake ga kuma a gida ya kwana bareyi yayi shaye shayensa ba.

    A hankali ta mik’e ta nufa wajen nasa biron dake hannunsa ta karb’e a hankali yadda barata ta dashi ba tare da arranging kan table nasan tasa komai in place kamar ranan yau ma taga littafin data soma karantawan. “Mr. Fauzi” ta kira sunansa. Bacci yake me k’arfi ko jinta beyi ba. “Mr. Fauzi da ka tashi kaje d’aki ka kwanta, kwanciya anan ze iya haddisa maka ciwon baya.” Nanma shiru be amsa taba. Hannu ta gwada waving a fuskarsa taga ko motsawa idanunsa basuyi ba alaman bacci yake me k’arfi kenan. Littafin ranan ta kuma cirowa takai kan page data tsaya ranan se b’ari take amman kaman aikin dole takasa ajiyewa karantawa ta soma dukda tasan yin hakan haramun ne.

    _From the day Ummimi left us, my family was turn apart. You made me your son a drunker. Why do you have to leave? Why must you choose another guy over your family? Why will you have to bring back Angel (Amal) 8 months after leaving? Exactly a day after birth. Why are women cruel? Ummimi I’ve loved you but not now again, I’ve cared for you but not now again. I will never set my eyes on you again, God bless Ummi for caring for us just as her own kids. I hate you! Don’t ever come back. I promise to avenge for my family and I for what you did to us on all women of your kind. I promise to cause heart break and attack to 100-200 women so they will feel exactly how it feels to be abondoned. Only these three women I promise not to hurt, Ummie, Amal and the girl from the other night._

     Mamaki ne da tausayi ne yacika Fannah. Allah sarki Mr. Fauzi ashe ba laifinsa bane duk abinda yakeyi yau, laifin mahaifiyar sa ce, mesa to zata barsu? Ashe saisa yake san Amal kamar ya mutu saboda bata sha d’umin mahaifiya ba. Allah sarki, gaskia duk sun bata tausayi, su nasu ba tafiya Baba yayi ba rashin lafiya ne amman seji suke duk ba dad’i time da jikinsa yayi worse bale nasu suna ji suna gani mahaifiyarsu ta tafi ta barsu. So wannan ne dalilin dayasa bayan ko wani kwana uku-hudu yana breaking up da ‘yan mata ashe ramawa yake. Shine dalilin da yasa baya mutunta mata kona misqala zarratun, amma dukda haka da besa shaye shaye aciki ba, ba abinda shaye shayen ze masa in banda sake b’atar dashi da yayi hak’uri ya rungumi k’addara.

    Next page ta juya zata karanta a yayinda Anas yaja wani dogon numfashi hannunta na b’ari ta mayar ta ajiye se bugu zuciyarta yake. Dudum! dudum! Sede Anas ya ganta lokacin da take mayarwan amma be gane me take ajiye wa ba ko files ne ko littafi be sani ba dan daga bacci ya tashi.
     “Me kikeyi anan?” Ya tambayeta.
   “I... I.. I” tama kasa magana. “I’m sorry” tace daga k’arshe.
     Idanunsa ya sake mayarwa inda yaga tana ajiye abu seyaga diary’n sa wajen, take mood d’insa ya canza danko Shettima da Amal bai barinsu su karanta.
   
    “Diary na kika maranta?” Ya tambayeta daga jin muryarsa a san he is angry. Shiru tayi se b’ari take. “I’m talking to you!” Ya fad’a a tsawace.
Bata san lokacin data fara hawaye ba. “Sir I’m sorry.”
    “How dare you! Ke bakisan ba kyau karantawa mutum sirrinsa bane?” Kuka harda me sauti take dan yadda yake magana a fusace a kuma tsawace.
    “Am talking to you! Mesa zaki karanta min diary?”
    “Sir I’m s.. So..” Bakin ta b’ari yake tama kasa magana. Ita kanta tasan itace da laifi batasan wani gulman yasata karanta masa diary ba, kodan halan ta damu dashi ne tadamu da shaye shayen da yakeyi, tana san ta gyara masa gurb’arcacciyar rayuwar dayake living zuwa daidaicacciyar hanya. Batasan taga Mr. Fauzi na shaye shaye musamman ma data karanto kad’an daga cikin sirrinsa.

        Kuka take sosai wanda har ya soma damun Anas. Sekace ba shi ba, in akoi me san ganin Fannah na kuka be wuce Anas ba amman banda yanzu, bayasan jin kukanta. Sekuma yaji ba dad’i mesa ya sata kuka? “Me aciki dan ta karanta diary na, maybe tausayi na fara bata and she wanted to help, the problem is banasan help nata banaso.” Handkerchief yaciro daga aljihunsa tare da mik’a mata. Kukan take bar yanzu ba makawa, “wipe off your tears” yace ba tare da ya kalleta ba. Amsa tayi a hankali tayi kamar yadda ya buk’ace ta sede har yanzu bata bar raira kukan ba.

     “For goodness sake kukan ya isa. You passed the line banasan ana min shisshigi kema kin sani.”
    “I’m sorry” tace a hankali.
   “Ya isa you can go.” Hak’uri ta sake basa sannan ta fice. “Huh!” Numfashi yasaki “God what is wrong with me? Koda Amal ce ta karanta min diary nasan zan mata worse than this, firing Fannah ya kamata inyi amman nakasa, koda banyi firing nata ba yakamata in bata punishment na intruding min datayi amman nakasa, se wai ma taban tausayi naji banasan kukanta. Naji wai ma nine da laifi dan sata kukan danayi. Oh God no! I’m not in love I’m not.”

 
*© miemiebee*

No comments: