BY MIEMIEBEE
PAGE 18
July, 2018
****
"Alhj?" Ummi dake zaune a kan gado ta kirasa.
"Na'am" ya amsa yana me karkato da kallonsa a gareta.
"Nace ba ina laifin mu fara samun iyayen ita Amal d'in kafin mu nemi Abdul nake ga hakan ze fi fasali."
"Ko meyasa kika ce haka?"
"A tunani na hakan ze fi tunda de ita Amal da bakinta tace mun Prince kaman d'an gida yake a gurinsu and kaga ze fi sauk'i mana ma idan har iyayen nata ne zasu sanar da Abdul d'in halin da ake ciki zefi d'aukan maganan shima da muhimmanci."
"You have a point."
"Thank you so mey kace?"
"We'll do it your way gobe in shaa Allahu se muje gidansu Amal d'in."
"Yauwa toh Allah kaimu."
"Ameen" kammala abinda yake yayi sannan ya k'ariso ya kwanta tare da kashe masu wutan d'akin.
Gari na wayewa wajajen k'arfe goma Abdul yasa Maamah a gaba suka wuce gidan su Amal. Kiranta ya tayi amman tak'i d'aga wayar, haka ma da ya gwada da lamban Maamah still tak'i picking don haka ya buk'aci Maamah da ta shiga ta tabbatar masu meke faruwa. Shigan Maamah taci karo da Mami se suratai take ita kad'ai da ta kasa kunne kuwa seta gano regarding Amal ne tana cewa "yarinya tun jiya ake tambayarki meke damunki amman kink'i kiyi magana se aukin kuka ki tayi"
"Assalamu Alaikum" tayi sallama hakan yasa Mami kewayowa had'e da amsawa.
"Wa'alaikumus salam, a'ah! Maamah?"
"Na'am Mami ina kwana?" Ta tsuguna ta gaisheta "Lafiya k'alau ya kike ya makaranta?"
"Alhamdulillah Amal na gida kuwa?"
"Ga ta chan tana d'akinta tana kuka ki k'arisa ciki halan ke ta gaya miki meke damunta." Ba gardama ta k'arisa ta tsinci Amal nata kuka kaman yadda Mami ta fad'a gabad'aya ta fita daga kamanninta fuskan nan ya kumburo tum idanunta sunyi ja suma sun tara ruwa a k'asa. Hugging nata kawai tayi tsananin tausayin da ta bata, kukan ta cigaba dayi yayinda Maamah ke bata hak'uri da k'yar tasamu kukan nata yad'an lafa sannan ta shiga tambayarta meke faruwa sede Amal tak'i bata amsar komai. Ba yadda Maamah batayi da ita ba amman banda hawaye ba abinda Amal takeyi. Abdul da ya gaji da jiransu a waje ne ya kira Maamah don jin ko lafiya inda take irga mai ai Amal d'in tak'i sanar da ita komai. Abdul be san lokacinda zuciya ta d'aukesa ba ta diresa a cikin gidansu Amal ba shiri. Sallama yayi da wuri Mami taja hijabinta daga kan igiya ta sanya jin muryan na miji sannan ta amsa tana jiran ganin kowa. Bak'on fuskan data gani tsaye bakin k'ofan ne ya sanyata ja da baya kad'an. Se kuma taga tsananin kama tsakaninsa da Maamah to kode wanta ne? Ta tambayi kanta. Tun daga bakin k'ofan ya durk'usa har k'asa ya gaisheta.
"Tashi don Allah tashi kaji?" Amman yak'i seda ta amsa sannan ya mik'e. "K'ariso ciki, wan Maamah kake ko?" Mamakin daya bayyana a fuskansa ne ya sanyata murmushi "Bade mamakin ya na gano kake ba?" Dukda mugun halin da yake ciki hakan be hanasa mayar mata da murmushin ba "Sosai Mami" ya amsa.
"Yo ai kama kuke wane an tsaga kara marabanku de hasken data fika shikenan lale k'ariso ciki barin yi mata magana ta fito."
"Toh nagode amma dama wajen ki nazo" ya sanar da ita. Da mamaki ta tsaya kallonsa "Gu na kuma?" Ta tambaya.
"Eh Mami I'm sorry please."
"Ba komai bismillah k'ariso." Tabarma ta shinfid'a masa ya zauna sannan tayi hakan itama har anan Maamah da Amal dake cikin d'aki basu san meke faruwa ba.
"Toh gashi ban ma san sunan ka ba."
"Abdurrahman" ya sanar da ita.
"Toh Abdurrahman meke tafe da kai?" Gyaran murya yayi tare da dukar da kansa "Mami a farko de ina son in fara da baki hak'uri, dan Allah kiyi hak'uri na shiga gonan ki da Papi da nayi na sace flawanku ba tare da sanar daku ba, I'm sorry." Sosai Mami ta shiga duhu "Baba na kayi hak'uri amman ban fahimce ka ba."
Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yace, "Sama da wata shida kenan muna tare da Amal amman keda Papi ba kuda labari, what's worse is ko izinin nemanta banyi ba daga gareku which I know is very wrong of me amman ku gafarceni. Banida niyyan lalata Amal, ina sonta ne so na tsakani da Allah so na aure idan har zaku bani izini. Sau dayawa nakan gwada rok'an kanta da tabani dama in turo magabatana koda formal introduction ne ayi don asan juna amman hakan ya gagara kullum excuses da take bani daban amman ina da tabbacin tana da k'wak'waran dalilin dake sata hakan. Toh kuma se gashi tun jiya na kasa gane kanta, muna cikin waya kawai ta rushe da kuka tun wannan lokacin bata sake d'aukan kira na ko na Maamah ba. Yau na turo Maamah don ta tabbatar mana da me ke faruwa amman shiru Amal tak'i magana dalilin daya sa nayi wannan zuwan bazata kenan amman kiyi hak'uri sam ban so hakan ba nima da magabata na naso fara tako k'afa na cikin gidan nan, my sincere apologies please."
Shiru Mami tayi tana assimilating kalamunsa wato har na kusan wata shida suna tare amman shine Amal bata ta6a bud'an baki koda wasa tace mata gashi ba? Sau dayawa takan jita a waya amman kota tambayeta da waye ne setace da Afzal ne ashe saurayi tayi a bayan idonsu.
"A gaskiya Abdurrahman bazan 6oye maka ba banji dad'in cewa se yau nakejin wannan batu ba ace na tsawon wata shida kana neman 'yata amman ba tare da ka nemi izini gun d'aya daga cikin iyayenta ba?"
"Nasan ban kyauta maku ba Mami and I'm gravely sorry bana son hakan yasaki tunanin da wata manufan nake neman Amal wallahi my intentions are pure ina son Amal ne tsakani da Allah."
"Kuma da ba don halin da ta fad'a d'inba bakada niyyan bayyana mana kanka yanzu ko ba haka ba?"
"Mami bazan gaji da baki hak'uri ba saboda nasan ni me laifi ne amma kisani wallahi nima ba haka naso abunnan ya kasance ba. My apologies please, and ko a yau kukace in turo magabata na zanyi hakan saboda bana son abinda ze rabani da Amal, inason ta sosai."
"Naji bayanunka Aburrahman kuma na gamsu dasu idan Papinta ya dawo daga tafiya zan mai bayani duk abinda akwai zan sanar da kai."
"Nagode sosai Mami kuma ina sake baki hak'uri."
"Ba damuwa karka damu."
"Se kuma batun Amal ko zan iya sanin meke damunta? Nayi nayi ta sanar dani amman tak'i bazan kuma 6oye miki ba hankali na ya matuk'an tashi banason ganin Amal cikin damuwa."
"Wallahi bazan 6oye maka ba, yadda baka da masaniya akan halin nan da take ciki nima haka ne, tak'i sanar dani matsalarta se kuka kawai. Yanzu haka jiran Papinta kawai nake shi kad'ai take jin maganansa." Ya bud'e baki zeyi magana kenan sega k'ofan d'akin Amal ya bud'u Maamah na fitowa bayanta kuwa Amal ce ta rik'e k'ofan tana shirin rufewa. Idanunsu na had'ewa gabanta yayi mumunan tsinkewa barin ma ganinsa da tayi tare da Maami. Yau shikenan ya gama da ita, tasan she's in a big trouble idan Papi yazo.
"Amal!" Ya kira sunanta da sauri ta mayar da k'ofan kai zallah Mami ta kad'a wai kode aljanu ne suka shigeta? "Kafa kwantar da hankalinka yau Papin nata ze dawo koma mey ke damunta zata sanar dashi ko ta fad'a miki abu ne Maamah?" Ta juyo tana kallon Maamah.
"A'a wallahi tak'i sanar dani komai."
"Toh Mami zamu koma nagode sosai da k'aramcin da kika nuna mun Allah sak'a da gidan aljannah."
"Ameen Abdurrahman ba komai gashi har zaka tafi ko ruwa ban baka ba."
"Haba daga gida nake karki damu mu tafi ko Maamah?" Yayi maganan had'e da mik'ewa har waje Mami ta rakasu sannan ta dawo ta nufi d'akin Amal tare da bankad'e k'ofar. "Ai Papinki ze dawo wai shin a ina kika koyo wannan d'abi'ar iyye? Har kiyi saurayi ba wanda ya sani a gidan nan? Abinda kikeyi a makarantar kenan ko?" Shiru Amal tayi mata don bata jin ma tana da energy'n yi mata bayanin komi.
"Sa'an ki d'aya wallahi yaron nada hankali wato har iyason turo magabatansa amman kike hanasa saboda ke bakison ku gina abinda kuke da shi akan addini ko? Kuma kiji ni kukan nan ya isa haka, ba dukanki akayi ba ba fad'a aka miki ba kawai kibi ki ta da wa mutane hankali haka a banza? Dubi yadda hankalin yaron nan ya tashi da safen nan kika d'agosa duk da hakan kin gansa kin kasa k'arisowa ki gaishesa toh ki cigaba Baby" tana kaiwa nan ta fice. Wani sabon kukan Amal ta rushe dashi a gun haka ta cigaba dayi har izuwa dawowan Papi. Bayan ya d'an huta Mami ta zaunar da shi ta labarta masa ababen da suka faru bayan tafiyansa ta ke kuma yabawa hankalin Abdul. Turata yayi da ta kira Amal bayan sun k'ariso Amal ta tsuguna daga waje-waje tana mey tare fuskarta da hijabinta.
"Mama na?" Ya kirata
"Na'am" ta amsa.
"Daina kukan haka kinji? Ya isa goge hawayenki." Ba musu ta shiga share hawayen nata "Gaya mun meke faruwa?"
"Papi babu."
"Nace ki gaya mun meke faruwa."
"Babu komai."
"Kode se kinji bugu ne?" Fad'in Mami.
"A'a beyi zafi haka ba zata fad'a da kanta gaya mun kinji keda waye ne?Keda Abdul d'inne?" Kai ta kad'a a hankali "Toh waye?"
"Yaya" ta furta chan k'asa-k'asa.
"Afzal??" Papi ya tambaya da mamaki yayinda Mami ta bud'e baki tana kallonta itama cike da mamaki.
"Meya samesa? Wani abun ya miki?"
"Ba shida lafiya, likita yace yana iya rasa ransa."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" both shi da Mami suka sa salati. "A dalilin mey?!" Mami tayi exclaiming cike da tashin hankali Allah sarki ashe shiyasa kwana biyu baya zuwa kuma bayi ko kiranta ita ko Allah be bata ikon kiransa ba dukda cewan yana ranta ashe beji dad'i bane.
"Meya samesa?" Papi ya tambaya finally.
"Ya kamu da ciwon zuciya." Nan ma wani salatin suka kuma sawa. "Allah sarki d'an halak shine baki fad'a mana tun wuri ba Baby? Sede kiyita kuka amman baza kiyi magana muje mu dubasa ba? Haka akeyi ne aka ce miki?" Mami ta kurareta.
"Tun yaushe yake jinyan?"
"Ya d'an kwana biyu Papi" ta amsa tana share hawayenta.
"Ya isa kukan haka in shaa Allah ze samu sauk'i ba wanda ze mutu kinji?" Kai ta gyad'a a hankali "Zamu shirya kuma duka muje mu dubasa kukan ya isa haka."
"Nagode" bata kai ga mik'ewa ba ya dakatar da ita.
"Se kuma batun Abdurrahman ko?" Yayi maganan yana kallon Mami.
"Waye shi?"
"Wan k'awata Maamah ne."
"Mey a tsakaninku?" Shiru tayi ba amsa. "Meyasa baki ta6a sanar dani ko Maminki batu akansa ba? Haka aka ce miki akeyi?"
"Papi I'm sorry kayi hak'uri."
"Baki amsa tambaya na ba meyasa?"
"Papi kuskure ne amman kayi hak'uri."
"Da yakeson turo magabatansa kuma meyasa kike hanasa?"
"Papi ba hanasa nayi ba."
"K'arya Mamin ki take kenan?" Kallon Mamin tayi sannan ta kad'a kai. "Toh meye dalili?"
"Na d'au idan akayi hakan zaku hanasa kula ni ne."
"A ganinki kula shi da kikeyi ba tare da izinin mu ba shine abinda ya kamata?"
"A'a" ta amsa tana kad'a kai.
"Tun yaushe kuke tare?"
"About 6 months now" ta amsa chan k'asa-k'asa.
"D'an gidan waye ne?"
"A Zarma na bakin layin polo."
"A Zarma me masallacin juma'ah?"
"Eh shi."
"Kina sonshi kuma?" Shiru tayi ta kasa amsawa. "Ke fa Baby kina son shi?"
"Eh Papi" ta amsa murya a ciki kallonta Mami tayi had'e da turo baki.
"Idan nace ya turo magabatansa zaki amince ki auresa?"
"Eh Papi."
"Toh shikenan tashi ki fice amman nan gaba karki sake yin wannan rashin hankali duk wanda kuka had'u dashi ya nuna yana sonki kiyi masa kwatancen gidan nan kice yazo ya gana da Papinki kinji? Bawai kuje chan kuna sha'aninku ba bawanda yasani kin ji?"
"Naji Papi nagode kuma ka sake yin hak'uri kema haka Mami."
"Shikenan ta shi ki fice" da haka ta mik'e ta wuce d'akinta.
"Ban yarda wai saboda rashin lafiyan Afzal take wannan kuka ba" fad'in Mami.
"Ko?"
"Sosai ma kuwa Baba kasan tun yaushe take wannan kuka? Da akwai 6oyayyan al'amari a tattare da yarinyar nan."
"Nima nayi zaton hakan amman kinga koda k'arya take anjima idan mukaje asibitin zamu tabbatar da gaskiyar al'amarin."
"Toh shikenan Allah kaimu."
****
Nazeefah ce tayi knocking bisa k'ofan d'akin Afzal sannan ta bud'e ta shiga yana ganin itace ya kawar da kansa. K'arisowa tayi da basket na lunch nasa ta ajiye akan table "How're you feeling? Kana iya d'aga hannun?"
"Tukunna amma da sauk'i" ya amsa.
"I cooked your favorite Rice and stew" ta sanar dashi tana me bud'e hulunan. Bayan tayi serving nasa ta taimaka masa ya zauna sannan ta zauna a gefensa itama da shirin basa abincin.
"Ahhh" ta buk'acesa.
"I can manage karki damu."
"Come on Afzal open up."
"Nace karki damu zan iya ci da kaina."
"I know laifi ne don nayi feeding naka? Besides you're still not fit." Da k'yar ta samu ya amince ta shiga basa abincin har seda ya k'oshi. Godiya yayi mata sannan ta tsiyaye masa ruwa ya had'iye magunansa yake tambayanta Ina Ummi tun jiya be sake ganinta ba.
"Nima tun jiya da na ganta tsaye dasu Sultan da Ummah tace zata masu rakiya ban sake ganinta ba." Haka kawai seyaji gabansa ya tsinke bade wani d'anyen aikin suke shiryawa a bayan idonsa ba ya tambayi kansa.
"Wayyo!" Yasa ihun k'arya.
"Lafiya?" Tayi saurin tambaya.
"Get my Dr! Hurry! Washhh!"
"Keep still ina zuwa" a guje ta fice neman likitansa inda ya ciro wayansa ya kira Sultan. A karo na farko ya d'auka.
"Sultan meke faruwa?"
"Kaman ya? Lafiya?"
"I don't want to believe ka sanar dasu Ummi batu akan Amal ka tuna ka d'au alk'awarin bazaka fad'a musu komi ba."
"Sekuma akace maka na sanar dasu wani abun?" Ya mai k'arya.
"I just have a strange feeling."
"Ka kwantar da hanaklinka ni ban sanar dasu komai ba."
"Yauwa thank you."
"Ya jikin naka?"
"Alhamdulillah zuwa anjima ma zasu sallameni."
"Toh madallah ko kun sake waya da Amal?"
"Nah bata kirani ba nima ban kirata ba."
"Alright sena shigo de."
"Okay you take care." Da haka sukayi sallama. Dawowan Nazeefah da Dr seyace ai daya sha ruwan sanyi yaji sauk'i, dubasa sama-sama likitan yayi sannan ya fice.
Wajajen k'arfe biyu da rabi Ummi da Abba suka isa gidansu Amal. Sallama suka yi a bakin k'ofar seda aka amsa suka shiga, Ummi ce ta soma sa kai.
"Lale sannu da zuwa" cewan Mami lokacin da taga Abba a bayan Ummi ne tayi saurin mayar da hijabinta. "Sannunku da zuwa" dadduma ta shiga ciki ta dau ta shimfid'a musu sannan suka gaisa. "Baki gane ni bako?" Ummi ta tambayeta.
"Eh toh wallahi" ta amsa da fara'a.
"Ummi ce, mahaifiyar Afzal na gefena ko mijina na ne Abban shi."
"Wai wai wai ashe manyan bak'i mukayi lale lale sannunku da zuwa bari in kawo muku ruwa."
"A'a karki damu daga gida muke" cewan Abba.
"Ya jikin Afzal d'in se yau Baby ke sanar damu wai beji dad'i ba."
"Jiki Alhamdulillah da sauk'i" ya amsa.
"Toh Allah k'ara masa lafiya muma muna shirin zuwa dubasa dama da Kakan Baby."
"Ayyah ba komai ko shi kakan nata na gida?" Abba ya tambaya.
"Eh barin yi mishi magana."
"Yauwa toh" da haka ta shiga ciki ta kira shi yayin da ta lek'a d'akin Amal don tazo ta musu sannu da zuwa sede ta ga d'akin nata ba kowa ko yaushe ta fita ba tare da ta sanar da ita ba? Papi na fitowa suka gaisa da Abba sannan Ummi inda Papi keta sawa Afzal albarka yana fad'a masu irin hidiman da yakeyi wa Amal yake kuma godiya. Sosai shi Abba da Ummi suka ji dad'in halin taimako irin na Afzal.
"So Alhj Muh'd ba tare da 6ata lokaci ba bari in sanar da kai meke tafe damu" cewan Abba had'e da yin gyaran murya "Munzo ne batun Afzal."
"Toh ina jinka Alhj."
"Kaman yadda Amal ta fad'a muku be ji dad'i ba, hakan yake likita yayi gwaje-gwajensa an gano ya kamu ne da ciwon zuciya."
"Tabbas haka Baby tace Allah k'ara mai lafiya ya kuma yaye mashi wannan ciwo."
"Ameen ya Allah" duka suka amsa sannan Abba ya cigaba. "Sanadin wannan ciwo daya kama sa se kan kowa ya d'aure mun rasa sababin ciwon, ba irin tunanin da bamuyi ba amman ina mun kasa gano dalilin da ze sanya masa ciwon zuciya a k'arancin shekarun da yake da ita. A fari munyi tunanin ko rashin jituwar dake tsakaninsa da matarsa ne kasancewar auran biyayya duka sukayi amman da bincike yayi bincike se muka gano ba hakan bane ciwon son 'yarku Amal ne da ya kasa furtawa kowa."
"Ciwon son Baby?" Shida Mami suka nanata cike da k'in yarda.
"Tabbas na tsawon lokaci Afzal na son Amal amman ya kasa samunta ko ku ya fad'a muku wanda har izuwa yanzu bamu san meyasa ba, kwatsam kuma kawai sega wannan shi Abdul ko?" Ya juya ya kalli Ummi inda ta gyad'a masa kai "Yauwa shi Abdul ya fito yace yana sonta har ya zamanna sunyi nisa da ita Amal d'in, toh wannan ne sababin rashin lafiyan nasa. Ganin su da yake kullum tare kuma ba yadda ya iya, gashi yana ganin lokaci ya riga ya k'ure masa se ya zammana ba aikinsa kullum se tunani, yana mey tak'ura wa kansa yana bin abun a zuciya har wannan ciwo yayi nasara akansa. Sau biyu kenan yake samun attack gashi likitansa yace muddin ba a magance masa wannan matsala ba yana iya rasa ransa idan ya cigaba da samun attack d'in."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mami ta sake sa wani salatin.
"Jiya ina nan ma ai na samu Amal nakeyi mata maganar inda ta tausaya wa halin da Afzal ke ciki ta kuma nuna min zata iya yafe komai saboda ceto ransa dukda cewan bata 6oye mun tsananin soyayyan dake tsakaninta da shi wannan saurayin nata ba amma tace muddin ku iyayenta kun amince ita me iya yafe farin cikinta saboda na Afzal ne. Tabbas mun san Afzal me laifi ne na hadissa duka wannan matsalar, da tun farko ya sanar daku komai da shi Abdul baze ma samu daman shigewa zuciyan Amal ba amma abinda ya faru ya riga ya faru sede ayi tunanin magance ta yanzu haka as we speak Afzal ma ba shida masaniya akan zuwan mu nan. Yanzu haka be ma san mun gano sababin rashin lafiyan nasa ba ma sabida wa amininsa Sultan kad'ai ya fad'awa damuwansa ba yadda bamuyi da shi ba ya fad'a mana meke damunsa amman yak'i da k'yar muka samu abokin nasa ya bamu had'in kai ya kawo mu gidan naku." Nauyayyar ajiyar zuciya both Papi da Mami suka sauk'e as suna mamakin wannan al'amari ashede kukan da Amal ta yini take tayi kenan tun jiya na zafin rabuwa da masoyinta ne, hak'ik'a tana son Abdul. Shi ko Afzal har yanzu sun rasa dalilin da ya hanasa sanar dasu cewan yana son Amal bayan yasan ba wanda ya cancanci soyayyarta sama da shi kodan hidimomin da yake mata. Sau dayawa Papi kan zauna yayi tunanin nan na cewa anya ba son Amal yake ba shiyasa yake mata wannan hidimomi sede tun yana sa ran wataran Afzal zeyi masa maganan Amal har ya dena saboda koda wasa Afzal be ta6a d'auko masa zancenta ba. Toh meyasa? Meya hanasa? Ko gani yake ko da ya furta masu kud'urina zasu hanasa Amal d'inne? Ai shima yasan baza a ta6a yimasa haka ba toh meya hanasa sanar dasu?
"Shine muke neman alfarma a gareku, ku kad'ai keda ikon ceto mana ran d'annan idan har Allah ze baku iko, shi kad'ai ne garemu bama son mu rasa sa kuma munsan yadda tambayan hakan agareku ya nuna tsan-tsan san kanmu amman ina da tabbacin duk iyayan da suka tsinci kansu acikin halin da muke ciki haka zasuyi suma" Ummi ta sake fad'a.
"Tabbas haka yake Ummin Afzal" Mami ta nunfasa "Nima koda nice na tsinci kaina acikin halin nan da kuke ciki bazan fasa ba har se inda k'arfi na ya k'are. Abu d'aya ne ya d'aure mun kai, dalilin da ze hana Afzal sanar damu k'udurinsa akan yarinyan nan bayan yasan baza a ta6a hanasa ita ba kuma a fari ita kanta Baby nasan bazata k'i sa ba, yanzu gashi tun tafiyanki jiya ta kulle kanta a d'aki tana ta aikin kuka ko ni tak'i sanar dani meke faruwa harta Papinta ma ce masa tayi babu da aka tak'ura mata ne se take ce mana wai Afzal ne bashida lafiya likita yace yana iya rasa ransa dalilin da ke sata kukan kenan amman dukkanmu ba wanda ya yarda da hakan saboda kukan yayi yawa. D'azu shi Abdul d'inma ya shigo kuma ya nuna a shirye yake da ya turo magabatansa anytime aka basa daman hakan, a gaskiya ban san ya zamu 6ullowa al'amarin nan ba. Yaran nan sunyi nisa ba adalci bane mu raba su, ta fannin Afzal kuwa ya cancanci komi a garemu ko saboda halaccin da yayi mana ko duniya yake buk'ata inde muna da ita ya zamo dole mu basa." Sosai Ummi suka ji dad'in maganan Mami suka shiga yi mata godiya.
"Toh yanke hukunci de ba namu bane" cewan Papi "Mude zamuyi k'ok'ari muga mun karkato da hankalin ita Baby da Abdurrahman d'in idan sun amince zasu iya yin shahada su ceto mana ran Afzal walillahil hamdu amman nikam bazan iya tilasta Baby auran wanda bata so ba, shi auren dole ba shida amfani kuma kun sani."
"Wannan haka yake Alhj Muh'd" cewan Abba "Kuma a hakan ma muna godiya sosai and we pray for nothing but the best Allah sak'a muku da gidan aljannah."
"Ameen wa iyya kum" ya amsa.
"So zamu wuce duk abinda akwai dan Allah ga number na" yayi maganan had'e da zaro card nasa daga aljihunsa ya ajiye a gaban Papi "Ka min waya."
"Toh toh shikenan Allah sa mu dace."
"Ameen ameen" da haka suka musu rakiya.
"Ai dama na fad'a miki iyayen Afzal ne" fad'in Amal dake la6e jikin k'ofansu Falmata tare da ita Falmatan. Tuntuni taso komawa gida amman cin karo da tayi da motar seta fasa gashi kuma kamar yadda ta fad'an ne su Ummi ne.
"Yanzu har sunzo sun sami su Papi kenan? Amal ki hak'ura da Ya Abdul kawai nasan da k'yar ki kasance tasa."
"Falmata I love him I can't do without him."
"Ya Afzal fa? Kina nufin duk halaccin da ya miki da butulcin nan zaki sak'a masa kenan?"
"Falmata ban sani ba sun tafi barin k'arisa gida duk abinda akwai zan sanar da ke."
"Toh se anjima." Tana isa gida Papi ya kirata ta k'arisa ta zauna a tsakankaninsa da Mami. "Uwata ina kika shige?"
"Na jeni gidansu Falmata ne."
"Toh tafiyanki iyayen Afzal suka zo suka kuma sanar damu dalilin kukan da kika kwana kinayi a gidan nan tambayata itace meyasa? Meyasa kika k'i sanar dani ko Maminki halin da kike ciki kika gwammace kisha wahala ke kad'anki?"
"Papi I'm sorry ban san ya zan fara sanar daku bane shiyasa."
"Ko tunani kike zamu bada ke ga Afzal d'in ko kink'i ko kin so?" A hankali ta gyad'a kanta. "Ko kad'an Baby se wanda kike so zaki aura kinji? Alk'awari na d'auka tunda Maminki ta haife ki na cewa zan kula dake tamkar nine mahaifinki kuma bazan bada ke ba se ga wanda kikeso."
"Papi ina son Ya Abdul bana son rabuwa da shi" ta fad'a yayinda ta shiga kuka.
"Shi ko zaki aura in shaa Allah kinji? Se wanda kikeso zaki aura ki kwantar da hankalinki."
"Toh Papi Yaya kuma fah? Ya zamuyi da shi? Kana ganin munyi mai adalci kenan bisa ga duk ababen alkhairin da yayi mana a gidan nan? Ace buk'atansa ya tashi amman mun kasa biya masa saboda son kai namu?"
"Uwata meke tafe a k'wak'walwarki? Kina son Abdul?" Kai ta gyad'a take "Ba kiya kuma son Afzal ya rasa ransa?" Nanma kai tayi saurin gyad'awa "Amma kinsan bazaki iya auran maza biyu ba ko? Dole cikinsu d'aya ya hak'ura koba haka ba?"
"Hakane Papi."
"Toh wa zamu ba hak'uri? Dan ni se abinda kikeso zanyi miki."
"Papi ban sani ba nima I don't want to lose them both."
"Amman ya zama dole Baby, hungo Jamila ku shiga daga ciki duk hukuncin da kuka yanke shi zamuyi aiki akai." Yace da Mami ba gardama taja hannun Amal suka yi ciki kaman yadda Papi ya buk'ata sede banda kukan da Amal keyi ta k'i cewa komi. Daga k'arshe de Mami ta yanke hukuncin Amal zatayi istikharan kwana uku duk za6in da Allah yayi mata shi zata bi. Amal batayi musu ba ta amince da shawarar cikin dare yau ta fara.
2 days later...
"Assalamu Alaikum" Mami ta fad'a tare da sa kai cikin d'akin Amal. Hawayenta ta shiga sharewa da wurwuri sede ina Mami ta riga ta ganta. K'arisowa tayi ta zauna a gefenta had'e da kiran sunanta. "Na'am" ta amsa sama-sama.
"Yau kika kammala istikharan ko?" Kai ta gyad'a a hankali.
"Wanne cikinsu yafi kwanciya miki a rai?"
"Mami..." sekuma ta rushe da kuka, rungumota tayi tana shafa bayanta tana bata hak'uri har seda kukan nata ya lafa. "Waye ne ki gaya mun kinji?"
"Mami it can't be Yaya it just can't! What of Ya Abdul? Bana son in rasa sa" ta kuma rushewa da wani kukan.
"Afzal?" Mami ta ambata da mamaki "Shi hankalinki yafi kwanciya da?"
"Mami zan sake yin wani istikharan what of Ya Abdul? Me ze sameshi? Waze aure shi?"
"Baby za6in Allah shine mafi alkhairi idan har hankalinki yafi kwanciya da Afzal toh shine za6in da Allah yayi miki ya zamo dole ki hak'ura da Abdul nakin."
"But Mami I can't, I love Ya Abdul wallahi ina son sa kuma banjin zan iya rayuwa ba shi dan Allah karki fad'awa Papi wannan za6in zan sake yin wani istikharan."
"Baby ai ba ayin istikhara sau biyu akan matsala d'ai kuma ina da tabbacin koda kin sake d'inma still Afzal Allah ze za6a miki."
"Mami dan Allah ki bari in sakeyi please don't tell Papi."
"Baby-"
"Mami please" ta rushe jikinta tana kuka, sosai Mami ta tausaya mata daba don za6in Allah yafi ba da se suyi ma Papin k'aryan cewa Abdul ne yafi kwanciya mata a rai a shafe zancen Afzal. "Shikenan bar kukan haka zan sake baki kwana uku ki k'ara yin wani istikharan tunda abinda kikeso kenan."
"Thank you Mami."
"Shikenan toh kukan ya isa haka" tayi maganan tana share mata hawayenta. Bayan fitan Mami sega Ya Abdul na kiran Amal, hawayenta ta share ta gyara muryanta sannan ta d'aga.
"Halo my princess?"
"Na'am my Baby good morning."
"Morning ya kike?"
"Lafiya k'alau ya office?"
"Alhamdulillah baki fita school bane yau?"
"Eh."
"Baby why?"
"Gobe zan fita in shaa Allah."
"Toh Allah ya kaimu, Baby har yau bazaki bani date in turo su Baba ba? Ni ko formal introduction akayi I'm satisfied, bana son wani yazo yayi mun awuf dake."
"Bayan kasan ni kai kad'ai nakeso?"
"Even still my Princess, du da hakan inason iyayena suzo su sami su Papi."
"Ya Abdul kad'an k'ara hak'uri kad'an kaji? In shaa Allah very soon zan kasance mallakar ka kaji?"
"Promise?"
"In shaa Allah Ya Abdul."
"Thank you my Amal, I love you so much."
"I love you even more you take care."
"You too, bye" da haka sukayi sallama. Kwanciya tayi akan wayan yayinda wasu zafaffun hawayen suke shiga gangarowa akan kumatunta. Tasan 6ata lokacinta kawai take koda ta sake yin wani istikharan still Afzal Allah ze sake za6an mata but why not Ya Abdul? Ta fi son Ya Abdul akan Yaya a tunaninta kodan wannan Allah ze za6an mata shi akan Yaya but why?? Why Yaya? Kuka ta shiga yi a hankali.
****
Kwana biyar kenan yau su Abba suna sa ran kira daga gun Papi amman shiru, gabad'aya shida Ummi sun k'osa a fari ma shikam cewa yayi ko zasu sake komawa gidan nasu ne amman Ummi ta ce su k'ara hak'uri su bari zuwa gobe ko jibi idan har basu kirasu ba se su san nayi. Afzal kuwa har yau besan me ake ciki ba, lafiya k'alau suke zama da Nazeefah a gida. Kasancewar be fara fita office ba kafin ta fita school take shirya masa breakfast da lunch idan rana yayi se yayi heating a microwace yaci.
Washegari...
Tun shigowan Mami da tayi taga Amal ta baje kan sallaya tana kuka kawai ta yanke hukunci. K'arisawa tayi tare da hugging nata tana bata hak'uri "In shaa Allah Afzal shine za6i mafi alkhairi a gareki hak'uri ya zama dole kinji?"
"Mami Ya Abdul fah?" Ta d'ago daga jikin Mami tana kuka sosai idanun nata sun kunburo sunyi ja wur. "Shikenan shi ko wacce budurwa yayi ta ringa tafiya tana barinsa kenan? What if shima ciwon zuciyan ya kama sa fa? I'm sure idan ya gano for all these while I've been deceiving him ze kamu da ciwon zuciya kokuwa yayi hauka."
"Wa yace deceiving nasa kikayi Amal? K'addarace ta rabaku bawai ke kika yi niyyan barinsa ba saboda haka ki kwantar da hankalinki in shaa Allah shi Abdul d'in ze miki kyakkywar fahimta."
"No Mami no matter what karku sanar da Ya Abdul zan auri Yaya banason ya rasa hankalinsa a sanadin hakan dan Allah kar ku fad'a mishi."
"Toh ya kikeson ayi Baby? Ayita yaudararsa kenan? The earlier the better."
"I know amman karku sanar da shi direct I don't care how you do it amman karku fad'a mishi cewan zan auri Yaya wallahi ina gudun abinda hakan ze iya haifarwa."
"Shikenan zan yima Papinki bayani za'a san yadda za'a sanar da shi amma kibar kukan haka kinji?" Kai zalla ta gyad'a. Isan Mami d'akin Papi ta sanar da shi halin da ake ciki da kuma alfarman da Amal ke nema na cewa kar a sanar da Abdul direct bata son wani abun ya samesa. Dabara ce ta fad'o wa Papi bayan ya kira Abban Afzal ya sanar da shi outcome da suka samu bayan istikharan da Amal tayi Abba yayi ta godiya yace zuwa anjima ko gobe ma zasu shigo. D'akin Amal ya nufa ya buk'aceta numban Abdul inda take sake rok'ansu da komin yaya ne ita kar a sanar da Abdul direct cewa Yaya zata aura. Kwantar mata da hankali Papi yayi akan ta bar masa komi yasan yadda ze 6ullowa al'amarin. Bayan ya amshi lamban nasa ya kira sa tare da masa bayanin shi waye, bayan gaisuwa yake ce masa yana son ganin mahaifinsa idan da hali har ita mahaifiyarsan ma.
"In shaa Allah zanyi musu magana duk abinda akwai zan sanar da kai Papi nagode."
"Nine da godiya Abdul Allah yima albarka."
"Ameen" ya amsa "Toh se anjima." Isanaa gida can yamma ya watsa ruwa yad'an huta bayan sallan Isha ya samu mahaifinsa a site nasa yake sanar da shi halin da ake ciki. Sosai mahaifin nasa ya masa murna tun ba yau ba yake jiran wannan rana da Abdul ze ce masa gashi ya samu wata se gashi nan Allah ya k'addaro masa da ranan ashe da rabon zega auran d'ansa. In shaa Allahu gobe nida mahaifiyarka zamu je gidansu yarinyan kaji?"
"Toh Baba nagode."
"Yauwa d'an albarka ko 'yar wace gida ne?"
Ba 'yar babban gida bane Baba amman she's from a well respected home."
"Madallah, zamu je gobe in shaa Allah ko akwai wata matsalar?"
"A'a shikenan." Da haka yayi masa seda safe ya wuce 6angarensa. Amal ya kira yake ta faman yi mata godiya a tunaninsa gabad'aya wai ita tabada daman ayi wannan formal introduction. Itako bata nuna masa komai ba, hira suka shafa kad'an tayi masa seda safe akan gobe tana da school. Washegari iyayen Abdul sukayo gaggarumin shopping na kayan abinci yadda al'ada ya kawo suka iso gidansu Amal har da shi Abdul d'in. Bayan gaisuwa da hiran da suka d'an ta6a Abdul yayi tunanin basu waje su tattauna dan haka ya fito waje ya shiga mota yana jiransu. Anan ne Papi ya samu daman yin magana.
RANA D'AYA
#RD
Love... King Miemiebee👄✨
11 comments:
Yaay,u such a durlyn.tnx alot
May Allah bless hardwork dear! Tanks a mil we cnt wait 4 d next update
tnks a lot Mimi Allah ya kara basira
Thanks dear
You're welcome dear
Ameen you're welcome 😊
Ameen you're welcome
You're welcome
Thanks.. We need more please
Later today in shaa Allah
Tab papi dai is going to break abdul's heart gaskiya dan ya riga ya gama sa rai... Allah ya kawo basira i love your novels
Post a Comment