BY MIEMIEBEE
PAGE 21
_Big sis🗣 (Maman Fadeel) where are you? I just want you to know that I'm devoting this entire page to you. Thank you for always trying to put a smile on my face, for treating me as if I'm one of your true little sis, know that your Lily loves you so much. XX 😘_
Kasancewan jikin Nazeefah a gida Afzal yayi sallah ya jasu tare, bayan sun idar da sallan ne ya shiga shirin office inda tace zata had'a mishi breakfast. Take ya hanata akan ta kwanta ta huta tunda bata da lafiya, he can manage. Haka ya shirya ya had'a breakfast nasa ya ci sannan yayi mata sallama. Kaman yadda ya saba kiran Amal ko wani safiya haka nan ma yayi yau sede har yanzu Amal bata sakewa dashi sama-sama suka gaisa sannan ya katse.
Da yamma bayan Amal ta dawo daga school ta la6e a d'akinta se hira suke a waya da Abdul not knowing Mami na la6e tana sauraronta tun d'azun. Ashe de har yau bata fasa waya da Abdul ba, shin wai meke damun Amal? Ta tambayi kanta, ace mutum an bada shi ma wani amma ya zauna yana hira da wani na daban? Bata yi mata magana ba ta koma ta cigaba da aikin dake gabanta. Bayan dawowan Papi ne ta zaunar dashi take fad'a masa abinda ke faruwa. Amal d'in ya kira bayan ta k'ariso take mai sannu da zuwa.
"Yauwa Mamana ya makaranta?"
"Alhamdulillah."
"Nace yaron nan Abdul ai baku waya yanzu ko? Kuma kin canza sim naki kaman yadda iyayensa suka buk'ata?" Shiru Amal tayi dan ko k'aryan da takeson yi d'inma ta gagara, kum taji bakinta ya kullu.
"Baby?" ya kirata.
"Na'am Papi" ta amsa.
"Baki jini bane? Kode har yanzu kuna waya ne dashi?" Nan ma shiru. "Ba magana ake miki bane Baby?" Mami tasa baki.
"Eh Papi" ta amsa murya chan ciki-ciki.
"Haka kukayi da iyayensa? Ke bakisan cin amana kike ba yanzu Baby? Taya bayan an bada ke ma wani amma ki tsaya kina hira da wani na daban? Kina ganin kin kyauta wa shi Afzal d'in kenan Baby?" Shiru tayi ta kasa cewa komai yayinda take nazarin rabuwa da Ya Abdul.
"Iyye? Kina ganin kin kyauta masa kenan?"
"A'a" ta kad'a kai a hankali.
"Toh kije na baki nan da kwana biyu ki canza sim kuma kar in sakejin kina waya da Abdul d'in kinji?"
"But Papi-"
"Ko baki jini ba? Har yaushe kike son ki cigaba da yaudarar sa? Kefa kikace kin amince zaki auri Afzal kodan ki biyasa alkhairin da yayi miki a baya yanzu kuma kice ba haka ba Baby?"
"Papi bawai dena waya da Ya Abdul d'inne bazan iya ba, naga tunda ba auran Yaya zanyi ba yanzu ai ba laifi idan muna gaisawa da Ya Abdul, Papi dan Allah karkace a'a."
"Kaman ya Baby? Ni da na d'au da jimawa ma kin canza layin naki? Ke bakisan alkhairi ne miki ba idan kika rabu da Abdul d'in tun wuri, kema zaki fi samun kwanciyan haka shima a hankali Allah ze yaye masa son da yake miki kuma gaisuwa ne kad'ai kuke ko hirar masoya?"
"But Papi-"
"Ya isa haka Baby baki cika sa6awa dokokin da nake kafa miki ba, kar kiyi hakan yanzu nan da kwana biyu bana son in sake jin kina waya da Abdul idan kuma ba haka ba zan yima iyayen Afzal magana dama su basu k'i ko a satin nan a d'aura auren ba, se suzo ayi magana asa rana."
"Papi dan Allah kar kayi mun haka."
"Toh kiyi kaman yadda nace." Kai ta gyd'a a hankali tana share hawayenta "Tashi ki fice Allah yayi miki albarka" ko amsawa batayi ba ruga d'akinta a guje ta baje kan katifarta ta shiga aikin kuka. Wayanta ta jawo had'e da shiga photos tana kallon pictures nasu tare da Ya Abdul yayinda kukan yaso yaci k'arfinta. Chan dare kaman yadda ya saba kiranta haka nan ya danna mata kira bata 6ata lokaci ba ta d'aga suka sha firarsu sam bata nun masa wai da akwai matsala a k'asa ba sede ko da yakeson yi mata seda safe tak'i amincewa ya katse wayan ita wai suyita hira kawai. Haka ya biye mata dukda cewan bacci yakeji, wayan suka yita yi har zuwa lokacinda ta zarce bacci se anan yayi mata goodnight yayi hanging call d'in. Washegari bayan ta taso daga school ta wuce Post office ta sai sabon sim sannan ta dawo gida. Video call ta dannawa Ya Abdul shi kansa beyi expecting ba dan tun tafiyansa sau d'aya da sukayi video call basu kuma ba. Haka nan tayita masa hirar shirme har seda kud'inta ya k'are sannan ya kirata suka cigaba har anan bata nuna masa cewan akwai wani abu ba. Da daren ranan ne bayan sun k'are wayan ta karya sim d'in ta sa sabuwa tana kuka haka ta zuba pieces d'in a bola. Ranan ko bacci batayi ba, kuka ta kwana tana yi washegari idanun nan sun kumbura tim ko school ta k'i fita. Dama normally kowani safiya da good morning text messages na Ya Abdul take tashi se gashi yau wayam ba komai. Ba yadda Mami batai da ita ta fito ta karya ba amman tak'i.
Shiko Abdul chan da yamma bayan ya dawo daga office yayi tunanin kiran Amal tunda shiru yau bata kirasa ba sede fa switched off layin nata ke ce masa. Be kawo wani tunanin a ransa ba yace ze gwada anjima, sede har zuwa dare Amal bata kirasa ba gashi ko ya kira switched off da wasa da wasa hankalinsa ya soma tashi. Sak'onni da dama ya tura mata amma ba response yau akeyinta! Danne zuciyarsa yayi yace bari ya bari zuwa gobe. Safe bim ya sake trying layin nata amma still baya shiga, hankalinsa idan yayi dubu be tashi ba shin meke faruwa? Wutansu ne ya 6aci kokuwa wayarta ta aka sace? Tunani de ba wanda beyi ba k'arshe da shirun yayi yawa ya yanke hukuncin kiran Maamah. Tana ganin call nasan tasan Amal ta canza sim ne kenan. Allah sarki Ya Abdul.
Sam bata so d'aga wayan ba amman gudun kar ya fahimci wani abun seta d'auka bayan sun gaisa yake tambayarta ko ta fita school yau. K'arya ta mai tace bata fita ba.
"Toh Amal fa kunyi waya da ita?"
"A'a wallahi tun shekaran jiya rabon mu da muyi waya."
"Ikon Allah I've been trying to reach her but it ain't going through."
"Toh kuma? Kasan wuta ya 6aci gabad'aya gari toh se a hankali nakega bata da chargi ne."
"Nima nayi tunanin hakan gobe zaki fita school ai ko?"
"Ka manta gobe Saturday ne? Besides bani da lecture ma."
"Toh bazaki je gidansu ki duba mun ita ba?"
"Ya Abdul ka kwantar da hankalinka mana ai Amal lafiyarta k'alau wuta ne ya lalace wayan nata ba chargi ka gane?"
"Maamah are you sure?"
"Dagaske amma sunce nan da sati ma zasu gyara."
"Anya kuwa zan iya jure sati banji muryan Amal ba? Ni kawai gobe kije gidansu ki had'amu."
"Allah sarki Ya Abdul zan raka Mama gidan biki fa kabari mana zuwa Monday."
"Mey zakiyi jibi da bazaki je ba?"
"Naji Allah kaimu."
"Yauwa good girl nagode ko?"
"Uhumm you're welcome" hira kad'an suka ta6a sannan sukayi sallama. Wayan ta ajiye had'e da sauk'e nauyayyar ajiyar zuciya gabad'aya ta rasa ya zata 6ullowa al'amarin. Mama taje ta samu ta irga mata halin da ake ciki inda take shawatarta da komin yaya karta kuskura ta basa sabon layin Amal.
Kamar yadda Abdul ya shiga tashin hankali haka Afzal ma, barin ma shi da bashida clue sam gameda rashin samunta a wayan ya rasa dalili, layin Mami ya kira itama unavailable yake cemata. Beso kiran na Papi ba akan zuwa gobe zeje ya duba ta yaji ko lafiya. Sosai Nazeefah ta warware, washegari bayan sallan La'asr Afzal ya zarce gidansu Amal.
Mami da Papi ya tarar a tsakar gidan bayan sun mishi sannu da zuwa ya k'arisa suka gaisa sannan yake tambayar ko lafiya jiya throughout yana neman Amal amma ya kasa samunta.
"Bade bata baka sabon lambar nata ba?" Papi ya furta a hankali sede Afzal ya jiyosa saboda nisan kunnensa.
"Na'am?" Ya tambaya.
"Bata kiraka da sabon layinta ba?"
"A'a" ya kad'a kai cike da rashin fahimta. "Sabon layi kuma?"
"Afzal nasan kana hak'uri amma ka k'ara, kasan Baby yarinya ce tunaninta kad'an ne, bayan nan kuma shi rabuwa da masoyi zafi gare shi, gabad'aya na kasa gane kan yarinyar nan gashi kuma idan akace ta rabu da kai ta koma ga Abdul d'in setace a'a ita bata son abinda ze sake samun lafiyanka ta fita harkan Abdul d'in kuma abun ya gagara. Afzal bazan 6oye maka ba amma idan kasa wasa kana sakaci toh wallahi da k'yar idan zaka iya maye gur6in Abdul a zuciyanta, ban san wani irin makahon so takeyi masa ba. Ka sani yanzu ne kake da daman shiga zuciyarta tunda Allah yayi ta canza layin nata zasu daina waya."
Sosai Afzal yaji wa Amal, ba k'aramin tausayi take basa ba, yasan yadda takeji sarai saboda shima he went through such. Tunanin ya ze iya karkato da hankalinta akansa yake amma gabad'aya ya gagara.
"Papi Amal ta riga ta tsaneni, tsana har a fuska tana nuna mun, wallahi ina iya k'ok'arina don ganin nayi straightening relationship namu but she's not willing to give me a chance I don't know what to do again."
"Abba a gani na idan ba aure akayi ma Baby da Afzal ba, yarinyan nan baza ta ta6a amincewa da cewa Abdul yayi mata nisa ba" Cewan Mami.
lBut Mami makarantar ta fa?l Afzal yayi saurin tambaya kafin Papi yayi magana "Bana son maganan aure ya raba mata hankali."
"Hakane Afzal amma kuma akwai abin dubawa acikin abinda Mamin Baby ta fad'a, idan ba wai har rana taga an sa muku ba bazata ta6a fita daga harkan yaron nan ba tasan yanzu ba ita ba shi."
"Tabbas hakane Papi toh zan gwada yimata maganan inji mey zatace duk abinda akwai zan sanar da ku."
"Toh shikenan hakan ma yayi amma kam kayi sake haka kana ji kana gani 'yar nan zatayi maka nisa."
"Toh zan wuce ko zan iya ganin Amal?"
"Bari inyi mata magana" cewan Mami.
"Toh zan jirata a waje nagode sosai se anjima."
"Ka gaida gida" Papi ya fad'a masa. Da haka ya mik'e ya fice. Koda Mami taje kiran Amal akan cewa Afzal yazo yana nemanta, shareta tayi k'arshe seda Papi ya sa baki. Fuskanta ta fito ta wanke sannan taje ta samesa lokacin har ya gaji da jirarta.
"Yaya ina yini?" Ta gaishesa daga chan nesa yayinda yake zaune kan benchin sa na kullum.
"Fa bazan amsa gaisuwan nan ba sekace wani bak'o Lily? K'ariso nan mu zauna kinji?" Bata mai gardama ba ta k'arisa ta zauna a gefensa.
"Meya faru fuskanki ya kumburo haka?"
"Babu" ta amsa tana tare fuskan nata.
"Dan ance se kin fito shine kike kukan nan Lily?"
"Yaya ba haka bane."
"Lily I'm sorry for making you hate me if you can't love me back please tell me."
"Yaya wani irin magana kuma kake? Har na isa ince bana sonka ne?"
"Gashi kuwa sede a bakin Papi zanji kin soya layinki you had zero intention of notifying me koba haka ba?"
"Jiya fa na canza layin ko Maamah ma ban bata ita ba, ba wanda na kira da ita."
"Toh shikenan dama magana nakeson miki."
"Ina jinka."
"Is it okay with you in turo su Abba for formal introduction?" Wani irin wawan fad'i gabanta yayi bade yanzu Afzal ke shirin auranta ba?
"Lily?"
"Yaya..." se kuma tayi shiru.
"Talk to me kinji? Ki fad'a mun ra'ayinki I'll do only as you wish Lily."
"Yaya Nazeefah fah? Yaya bana son shiga tsakaninka da matarka bana son tashin hankali."
"And who said by agreeing to marrying me zaki shiga tsakani na da Nazeefah? Ke daban ita daban karki damu da ita zata fahimci al'amarin namu in shaa Allah."
"Yaya what of my studies? Kaifa kace baka son abinda ze raba mun hankali dangane da karatu baka tunanin auran nan will be a great distraction to me? Yaya I'm sorry amma ban shirya da yin aure ba yanzu."
"Is this just how much you don't want to be with me Lily? Yanzu inda Abdul ne yace ze turo ai bazaki ce masa haka ba ko? Shikenan ba matsala dama ra'ayinki kawai nakeson ji saboda in sanar dasu Papi. Kina iya komawa ciki" yayi maganan yana sa hannunsa cikin aljihu, wata envelope ya zaro ya sa mata a hannu. Kafin tace zatayi masa godiya har ya k'arisa cikin motansa yana k'ok'arin tada ita. Seda taga ficewansa sannan ta k'arisa ciki. Ko mutum be tambaya ha yasan ransa ya 6aci, daga yadda yayi magana ma.
Kud'in ta mik'awa Mami akan gashi Afzal ya bata. Zaunar da ita Mami tayi "Baby?"
"Na'am?" Ta amsa.
"Yanzu kina ganin kina kyautawa Afzal kenan?"
"Mami ni kuma mey nayi?"
"Kisani wallahi koda ba don istikharan nan da kikayi ba, bawanda ya cancanci soyayyarki sama da Afzal ki tuna da kalan hidiman da yaron nan ya miki ba ke kad'ai ba harta ni da Papinki. Be sanmu ba, besan daga ina muke ba amma ya d'au nauyin karatunki, kud'in takardu da handouts tun kafin ki tambaya yana baki amma ace kike wulak'antasa haka Baby? Wallahi samun mutum kaman Afzal a zamanin yanzu se an tone. An sani rabuwa da masoyi da zafi amma yaci ace kin yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi be kamata ace har ki bari Afzal ya fahimci cewa bakiya sonsa ba."
"Mami ni yaushe nace bana son Yaya? Wallahi ban ta6a furta hakan wa kowa ba."
"Amma haka halayyanki suke nunawa abinda nake fad'a kenan. Kuka ne kawai be min ba ranan gabad'aya kin tada masa hankali har yake cewa shi ze hak'ura kawai a dawo maki da Abdul d'in haba mana Baby ki sani fa ba duk abinda mutum keso yake samu ba a duniyan nan. Yanzu gashi duk da kalan rashin mutuncin da kike masa hakan be hanasa baki kud'in k'arshen watan ki ba harda k'arin dubu ashirin akai."
"Zan kirasa inyi masa godiya."
"Da kin kyauta dan babu dad'i hakan kiyi hak'uri ki sani Abdul ya riga ya miki nisa ki bud'ewa Afzal zuciyarki sanin kanki ne Afzal baze ta6a cutar dake ba."
"Mami na sani."
"Toh kina iya tafiya Allah yayi maki albarka."
"Ameen" da haka ta wuce d'akinta. Wayarta ta d'auka ta kira Maamah se a karo na biyu ta d'aga kasancewar bata san layin ba.
"Halo Maamah? Amal ce."
"Amal? Ya kike."
"Lafiya k'alau ya kwana biyu?"
"K'alau ai na d'au nima baza a nemeni da sabon layin bane."
"Haba Maamah ya gida?"
"Lafiya k'alau jiya Ya Abdul ya kirani wai baya samun line naki."
"Allah sarki Ya Abdul I miss him already please komin ya za'ayi karki basa sabon layi na bana son in cigaba da zolayansa Maamah, ina tausayawa kaina but I pity Ya Abdul the most."
"Haka ma Mama tace."
"Maamah I'm so sorry for hurting your brother."
"Ba komai Amal ai yin Allah ne ba naki ba."
"Thank you so much for everything."
"You're welcome."
"Toh sekiyi saving numban nawa se mun had'u a school ran monday."
"Alright I'll" da haka sukayi sallama bata kaiga ajiye wayan ba sega call na Ya Abdul. Ko gaisawa be bari sunyi ba ya hau kurareta akan tabar duk abinda takeyi taje gidansu Amal taji ko lafiya haka kawai yana ji a jikinsa ba k'alau ba. Corner-corner tayita masa akan yau bazeyi ta fita ba seko gobe haka nan ma washegarin daya kirata tace ai taje gidan su Amal d'in Mami tace bata gida amma lafiyarta k'alau. Matuk'a hankalinsa ya d'an kwanta na jin lafiyanta k'alau amma rashin jin muryarta hankalinsa ya kasa kwanciya gabad'aya.
Amal ko sosai take kewansa sede gabad'aya ta rasa me take ciki, sosai maganan da Mami tayi mata keta yawo mata a kai tun jiya se tunanin magann take gashi har yau bata kira Afzal d'in ba seta d'au wayan zata kirasa se ta fasa. Haka tayita yi har tazo ta kirasa k'arshe. A lokacin suna tare da Nazeefah suna kallo, ya tashi ya amsa yana gudun kar ta fahimci wani abun, yayi rejecting call d'in kuma baze iya ba haka kawai ya rufe ido ya d'auka.
"Assalamu Alaikum" ta soma da cewa.
"Wa'alaikumus salam" ya amsa sa6anin yadda ya saba kiranta da Lily yau sallamar kad'ai ya amsa ita ko se ta d'au kodan abin da tayi masa ne yake fushi.
"Yaya I'm sorry" ta furta chan ciki-ciki.
"Ba komai karki damu."
"Dama na kira ne inyi maka godiya tun jiya ina trying numbanka baya shiga" tayi mai k'arya.
"Ayya bakomai."
"Wannan ne new line nawan se kayi saving."
"Alright I'll se anjima" nan ya katse, da mamaki Amal ta tsaya kallon wayanta yau har Yaya ne ya katse waya a kanta? Hmm
Nazeefah kuwa kallon sa ta tsaya yi tana nazari kode da budurwansa yayi wayan ne? Kud'i ya bata ne take godiya har yake cewa ba komai? Amma kuma ai idan budurwarsa ce baze bari ma ya amsa wayan a gabanta ba, toh ko business colleague tasa ce?
Kwana hud'u Maamah ta jera tana raina wa Ya Abdul wayo tun be d'auki abun da zafi ba har ya fara zaton wani abun daban. K'arshe da abun ya ishesa Mama ya kira yake ce mata gashi kwana biyu baya samun Amal yayi da Maamah da ta had'asu amma abun ya gagara inda hali please ko ma waye ne asamu a tura gidansu Amal d'in aji ko tana lafiya, Mama bata nuna masa komai ba tace washegari zata tura ayo bincike se anan hankalinsa ya d'an kwanta sede har gari ya waye rana ya sauk'a Mama bata kirasa ba duk yadda ya k'osa haka ya hak'ura ya bari se a jibi sannan ya sake kiranta itama wani hujjan ta nema ta sake basa. Haka suka yita waina sa, suna masa wasa da hankali ba wanda ya iya fitowa fili ya sanar dashi zahirin abinda ake ciki, ta fannin Amal kuwa duk yadda take missing d'insa hakan besa ta d'au waya ta kirasa ba dukda cewan bata k'i hakan ba. So dayawa takan zuba numbansa da niyyan zata kirasa amma idan ta tuna da fad'an Mami na ranan seta fasa. Sosai fad'an ya shigeta haka ko tana kewansa sede ta rufe kanta a d'aki ta sha kukanta amman bade ta kirasa ba. Hotunansu kuwa har yau ta kasa gogewa haka zata zauna tana kalla tana kuka.
Ta fannin Afzal kuma tun kan amsan da Amal ta basa ranan akan cewa ita bata shirya auransa ba gabad'aya ya rasa walwalansa ko kiranta be sakeyi ba, a gida kuwa ba yadda Nazeefah batayi da shi ba amman yak'i sanar da ita halin da yake ciki haka ya bari abin yayita chin sa har seda wani attack d'in yaso kamasa. Daga fitan Nazeefah d'auko masa ruwa dawowan da zatayi kawai ta tarar da shi zube a k'asa se birgima yake yayinda ya rik'e saitin zuciyansa inda yake masa k'una sosai, se wani sama-sama numfashinsa ke masa. Salati tasa yayin da yasar da goran ruwan a k'asa ta nufi kansa da gudu tana k'walla masa kira.
Kafin ta tashi tace zata nemi mai gadi dan yazo ya d'aukesa su kaisa asibiti ya rik'e hannunta. "Don't call Ummi.." ya furta da k'yar yayin da ya shiga yin tari.
"Afzal so kake ka mutu ne? Barin kira D'an ladi stay calm kaji?" Ta buk'acesa a rud'e "Don't call Abba too please" ya rok'eta kai tayi saurin gyad'a mai sannan ta kira D'anladi nan da nan ya cicci6esa suka yi mota. Akan cinyarta ta ajiye kansa yayinda take ta kuka ganin yadda yake wasu irin abubuwan wane wanda ake cire ma rai.
Sintiri ta rink'ayi bakin k'ofan nasa gabad'aya ta rasa me take ciki gashi yace mata karta kira su Ummi shin ta biye masa ne ko ta kira sun? Amma kuma tasan halinsa sarai ba k'aramin aikinsa bane idan ya farfad'o ya gansu akansa yayi mata fushi. Haka nan ta rasa me take ciki chan da likitan nasa ya fito ta nufi kansa tana tambayansa ya jikin nasa.
Ya buk'aceta ne da ta kwantar da hankalinta Allah yaso an samu an kawosa asibitin da wuri tun kafin heart d'in yayi failing, an kuma basa immediate treatment yanzu sauran a jira farfad'owansa nan da kaman minti ashirin haka. Hamdala ta saki yayin da ta shiga yi masa godiya. Bayan sa tabi ta shige d'akin Afzal inda ta tsince sa kwance kan gadon, wane wanda k'wai ya fashewa a ciki haka sid'ak-sid'ak ta k'arisa ta zauna kan kujerar dake gefen gadon nasa yayinda hawaye ya ciko mata dam a ido. Sunansa da tace zata kira kawai se hawaye. Kuka sosai ta sha wajen ta rasa me ke janyo masa bugawan zuciyan, komi da ta sani baya so tana iya k'ok'arin dainawa amma ace ciwo yak'i ci yak'i cijewa? Ita abu d'aya take gudu ranan da zuciyar nasa zata buga gabad'aya tak'i aiki tasan ko sama da k'asa zata had'a ba wanda ze ta6a amincewa akan ba ita ce sanadin ciwon nasa ba. Tana cikin kuka ba makawan ne Afzal ya shiga kyafta idanunsa har ya bud'e su gabad'aya. Da mamaki ya tsaya yana kallon yadda take kuka gabad'aya se ta basa tausayi.
"Afzal" ta kira sunansa a hankali ko amsata ya kasa. "Dan Allah idan wani abun nake maka wanda ka kasa furta mun please tell me I'm tired of seeing you collapsing everyday like this idan wani abun nakeyi maka wanda baka jin dad'insa please tell me."
"Nazeefah" ya kira sunanta cikin dashasshiyar murya.
"Please tell me Afzal I promise zan yi iya k'ok'ari na inga na kiyaye."
"Bar kukan haka kinji?" Yayi maganan yn neman share mata hawayen nata. Fuskan nata taja baya "Not until you tell me mey ke jawo maka attck haka please tell me idan nice."
"Bake bace bar kukan haka."
"How can I? Bazan iya ba Afzal so kake se idan ka mutu kowa yace nice na kashe ka? Dan Allah ka tausaya mun ka fad'a mun matsalar."
"Nazeefah nima han sani ba all I want is ki kwantar da hankalinki baki da alak'a da rashin lafiya na kuma ko a gaban waye me zanyi defending naki kinji? Stop bothering yourself like this."
"Then mey ke jawo maka?"
"Nazeefah I'm sorry but I can't tell you."
"Afzal nasan ba wani jituwan kirki bane a tsakaninku nasan nayi maka laifuka da dama I know I'm not the perfect girl for you, amma matarka nake kodan wannan matsayin please tell me."
"I can't Nazeefah" ya sanar da ita.
"Saboda ban kai inji damuwanka ba?"
"Sam, saboda nima ban san meke damuna ba, I have no idea why."
"Ban yarda da hakan ba Afzal tun ba yau ba nasan kana 6oye mun damuwanka zan cigaba da addu' har izuwa rananda zaka fara fad'amun damuwanka I believe mey hak'uri shi kan dafa dutse ya sha romo, I love you Afzal I'll do everything to stay by your side this's how much I love you."
"Thank you Nazeefah, come here" hannunsa ya bud'e mata a kasalance, a hankali ta shige jikinta dai-dai saitin k'irjinsa ta aza kanta yayinda ya rufeta da hannayensa yana mey shafa bayanta a hankali. "Forgive me for hurting you this much? I'm so sorry." Kai ta gyad'a masa a hankali yayinda ta sake shigewa jikinsa tana mey cigaba da kukan da takeyi. A nitse ya d'agota had'e da share mata hawayen ta "Kin kira su Ummi?"
Kai ta kad'a "Kace kar na kirasu."
"Very good thank you so much Nazeefah Allah miki albarka."
"Ameen" kafin tayi wani k'wak'k'waran motsi wayanta ya shiga ruri dubawan da azatayi taga Mummy ke kira. "Waye ne?" yayi saurin tambayarta.
"Mummy" ta amsa cike da fargaba.
"Ki d'auka."
"What if tana gida taje duba mu ne fah?"
"D'auka kice mata mun fita." Hakan ta d'aga Mummy take ce mata gata da Khhaleefah bakin gate sunata honk amma ba kowa. Kaman yadda Afzal ya buk'ata haka tayi tace mata sun fita ne D'anladi kuma yaje duban gida.
"Can I use your phone to call Sultan?" Ya tambayeta bayan da ta kammala wayan.
"Sure" tayi maganan tana mik'a masa "Amma banida numbansa."
"Don't worry I have it off hand." Numban Sultan d'in ya zuba ya kirasa.
"Halo Sultan?"
"Triple A?"
"Yes Sultan kana ina?"
"Office ina ka ajiye wayanka inata kiranka baka d'auka."
"Kazo TH please."
"Subhanallah bade jikin naka bane?"
"Yes but da sauk'i and please don't tell Umma banason su Ummi suji ina asibiti nima yanzu zance suyi discharging d'ina come quickly."
"Alright I'm on my way."
Be 6ata lokaci ba ya kar6i excuse a office ya kama hanyan TH saidai kafin nan ya kira Amal yasan sarai itace sanadin komai. Tana d'agawa yake sanar da ita ai Afzal ya sake samun wani attack d'in yanzu haka ma yana TH an rik'e shi. Sosai gabanta ya fad'i salati kawai ta shiga yi har Sultan ya ajiye wayan. Yanzu mey zatace wa su Ummi? A banza tana neman kashe musu d'a. Bata jira lectures d'in ya k'are ba ta tattara jakarta ta fice kasancewar university da TH ba nisa kusan a tare ita da Sultan suka isa tana sauk'a a napep se gashi yana k'ok'arin shiga shima. K'arisawa tayi cikin motan nasa suka shiga tare. A waiting room yace ta jirasa gudun kar kuma suna shiga suci karo da Nazeefah. Bayan ya k'arisa d'akin Afzal suka gaisa da Nazeefah sannan ta basu waje.
"Amal ce har yanzun?" Sultan ya soma da tambayansa.
"Sultan haka so yake?" Ya tambayesa a raunane. "Tunda nake ban ta6a son wani mahaluk'i sama da iyayena a duniyan nan ba, ban san haka so yake da sharri ba da nayi duk abinda zan iya na hana son Amal shigewa zuciyana."
"Triple A..."
"Sultan I'm tripping" ya katsesa, "Ban san ya zanyi da son Amal ba, ina sonta amma kona second d'aya bata sona, bata da niyyan bani daman in kasance masoyinta. she disperses me Sultan help me out please, ina jin idan ban samu Amal ba ina iya rasa rayuwana."
"Calm down Afzal, meya faru?"
"Komai ma ya faru ni yanzu nakega kawai zan hak'ura ne zan nemi transfer in d'au Nazeefah mu bar nan kawai maybe by doing so Allah ze rage mun sonta a zuciya, gar da gar ta nuna mun she can't marry me ya kake tsammanin zanji? I've tried my best to forget it but I can't, da kalamunta kullum nake tashi nake yini, I'm mad over her. And to be frank, I'm tired of seeing Nazeefah like this, gabad'aya ta d'au laifin komai ta d'aura wa kanta, na gaji I don't know what to do again."
"Mun taho tare da Amal" ya sanar dashi.
"You what?" Ya tambayesa cike da d'umbun mamaki.
"Yes tana waiting room, kana kirana itama na kirata se muka k'ariso tare."
"Why? Meyasa ka kirata? So kake su had'u da Nazeefah? Maza why?"
"Saboda tasani idan ta cigaba da abinda take yi maka tana iya jefa rayuwarka cikin matsala."
"And? Ba wai kaman ta sona bane bale idan rayuwan nawa ya shiga matsala hakan ya dameta."
"Taya zakace Amal bata sonka Triple A? Ai zuciya bata ta6a k'in me kyautata mata ya kamata ka gane cewa Amal na duk abinda takeyi ne saboda haushinka da takeji na shiga tsakaninta da Abdul amma bayan nan wallahi ko ita bata isa ta buga k'irji tace bata sonka ba."
"Wai kam bakaji me ta fad'a mun bane? Amal bata sona."
"Amal na sonka Afzal she's just too broken to realize that, gabad'aya soyayyar Abdul ne ya rufe mata ido aikinka ne ka maye gur6insa a zuciyarta idan ko kayi sakaci kana iya rasata har abada amma so kam akwai shi achan k'ark'ashin zuciyarta."
"Ko meyasa kace haka?"
"Da bata sonka da baza tabar duk abinda takeyi ta iso nan atake da na kirata ba, and you know the funniest part? Ta jirani a waiting room d'inma tak'i wai sam semun k'ariso tare, kallo d'aya mutum zeyi mata yasan tana cikin tashin hankali. Gabad'aya ta rasa natsuwarta a haka zaka ce bata sonka? Yanzu that aside, ya za'ayi in shigo da ita?"
"I don't know nide bana son su had'u da Nazeefah ban shirya ma wani masifan ba."
"Kasan ya za'ayi? I'll call Nazeefah se kace mata kana jin yunwa taje tayi maka girki kafin ta dawo de nasan Amal harta tafi."
"Sultan nifa bana son su had'u."
"Trust me" yana fad'in haka ya fice ya kira Nazeefah akan Afzal na nemanta.
K'arisowa tayi ta tsaya a kansa tana shafa kansa a hankali "Kana buk'atan wani abu ne?" Ta tambayeshi a maraice.
"I'm hungry" ya sanar da ita.
"Mey kakeson ci?" A farko yayi niyyan cewa stew tuna akwai stew a gida seyace spaghetti.
"Toh bari D'anladi ya zo ya kaini gida inyi sauri in had'a maka, shikenan ko kana buk'atan wani abu?"
"Shikenan."
"Alright I'll be right back."
"Thank you."
"Don't mention" murmushi kad'an ta sakar masa sannan tayi sallama da Sultan ta fice. Nan suka samu suka shigo da Amal.
Tana shiga ciki tayi kan gadon nasa a guje had'e da rushewa a gabansa tana kuka sosai sede ko kallonta Afzal beyi ba. Kukan tayita yi chan ta d'ago kanta ta shiga basa hak'uri. "Yaya I'm so sorry please kar ka mutu."
"Bakiya son ya mutu kuma kike wulak'antasa haka Amal? Afzal d'in? Bari in kira su Mami in sanar dasu halin da kika jefasa daga nan se asan nayi idan ma rabaku za'ayi toh don da shi zefi alkhairi ma because bazan iya jure ganinki kina destroying min life na amini ba, Amal baki san idan kika cigaba da hakan ba kija iya zamewa sanadin mutuwansa ba?"
Kuka take sosai tace, "Ya Sultan please don't call Mami wallahi tana iya kasheni da duka kuma ya kake magana haka? Sanin kanka ne Yaya yafi k'arfin in wulak'antasa."
"Kuma shine kike wulak'antasa hakan?"
"Ni ban wulak'anta Yaya ba, sanin kanka ne ina son Yaya, Yaya please say something." Sede ko kallonta Afzal be juya yayi ba.
"Toh ai ba haka ake so ba Amal kowa ya sani rabuwa da masoyi da ciwo amma ya zamo dole ki hak'ura tunda an riga an bada ke wa Afzal ko ba haka ba?" Kai ta gyad'a a hankali.
"Yanzu haka iyayensa basu da labarin yana asibiti saboda baya son ya had'a kanku amma still kina wulak'antasa haka? Sanin kanki ne Afzal na sonki I don't have to tell you."
"Ya Sultan I'm sorry dan Allah kayi hak'uri."
"Ni baki yi mun komai ba Amal, Afzal zaki bawa hak'uri let me excuse you two" daga fad'in haka ya mik'e ya fice tare da ja musu k'ofan. Shiru ne ya rufesu a d'akin Afzal yak'i yayi magana itama Amal tayi shiru bata sake cewa komai ba. Chan ta numfasa had'e da kiran sunansa.
"Yaya please ka juya ka kalleni kaji? Yaya I'm sorry please look at me" ganin har yanzu be juya yako kalleta ba ai seta rushe da kuka wajen. Kuka sosai take tun Afzal na iya jure sautin kukan nata har abun ya gagara, be san a lokacinda ya juyo yana kallonta ba don kukan Amal ba k'aramin tada masa hankali yake ba.
"Yaya I'm so sorry dan Allah kayi hak'uri please don't go and leave me, I'm here please don't go."
"You're not here Lily, you're never here. You don't love me, you don't even care about me baki damu dacna rayu ko na mutu ba. Lily nasan ni mey laifi ne but I'm sorry, bazan kuma gaji da baki hak'uri ba but please ki amince ki aureni, Lily bazan iya rayuwa ba ke ba you've become a part of who I am that I can't do without, you complete me, I feel so incomplete and lost without you. Lily idan baki kasance mallaki na ba ina iya rasa rayuwa na. I'm sorry but I love you, I love you morethan life itself, your love runs in my veins duk yadda naso 6oye soyayyarki hakan ya gagara, duk yadda na so cireki daga zuciyana nakasa, Lily I was created for you. Nazeefah might be my wife but you're my home, my soul, my happiness and life, please don't let me go astray."
By now kuka Amal take sosai. A hankali kalamun Afzal suke shigewa jikinta suke kuma tasiri, tabbas ba k'arya ko d'aya acikin kalamunsa tasani batada masoyi sama da shi abu d'aya yake hanata sakewa da shi idan ta tuna yadda ya rabata da Abdul sede kuma da ta zauna tayi tunani, seta gano komi na faruwa ne saboda dalili. Allah nada dalilin daya ya turo Abdul rayuwarta ya kuma ciresa a lokaci guda, dalilin kuwa itace ta sani cewa ba duk abinda mutum yakeso yake samu ba a rayuwa. Hawayenta ta shiga sharewa a hankali ta soma da cewa;
"Rana d'aya Allah ya kawo ka cikin rayuwana Yaya, acikin k'azanta da yarinta ka ganni ka kuma ce kana sona, baka sanni ba, baka san daga ina na fito ba, bakasan suwaye dangi na ba ka nuna min so da k'auna ka kuma ja ni jiki tamkar k'anwar ka ta jini ka k'ara bani daman kiranka Yayana. Rana d'aya bayan na cira ran zan sake komawa boko ka dawo mun da mafarki na ka nuna min everything is possible with you and God, ban ta6a neman abu na rasa a k'ark'ashinka ba Yaya. Damuwa na tun kafin in furta kake yaye minsu, baka wasa da sha'ani na komai nakeso shi kake mun taya bazan so ka ba Yaya? Idan nace bana sonka wallahi na zama mak'aryaciya but I love Ya Abdul too, ina sonshi amma bawai hakan na nufin ina shirin rasaka bane. Ina iya sadaukar da raina maka Yaya, batun maganan mu na ranan kuma ina sake neman gafararka kayi hak'uri na baka amsa bisa rashin tunani da shawara da nayi. Yaya idan har aurena ne ze farinta maka rai then I'm ready to be your wife, ko a yau kakeson in kasance matarka na amince zan aureka but please ka dena tada hankalinka a kaina haka bana son abinda ze ta6a lafiyanka bana son a sanadi na ka rasa rauwanka, dan Allah ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka sani I'm only yours and no one else's."
RANA D'AYA
#RD
Love... King Miemiebee👄✨
2 comments:
Awwwww😍😍😍thanks hun!
Nice pine
Post a Comment