Sunday, 24 June 2018

RANA D'AYA

  BY MIEMIEBEE
 PAGE 13


      Da mamaki ta k'arasa ciki ta watsa ruwa taci abinci, dab bayan sallan Maghrib ta gwada kiran Afzal sede kamar yadda ta k'udurta a ranta haka mutuminku yak'i d'aukan wayan, sau biyu take kiransa ta regular line nasa amman yak'i d'agawa, private line nasa ta kira next. nan ma yak'i d'agawa dagangan dan kuwa wayan na a gefensa yana mik'e kan gado sede ya kalla ya cigaba da zura wa ceiling ido. Sak'o ta tura masa ta text message tana basa hak'uri nan ma yak'i reply bayan ya karanta. Duk da haka bata kariya ba, ta bisa whatsapp ta tura masa messages bil adad tana basa hak'uri tana kuka duk seya karanta ya kuma k'i reply abinda yafi ci mata rai kenan. Taya har ze karanta amman baze bata reply ba? Yau ina zata sa kanta? Assignments nata data d'ibo zatayi ma taji baza ta iya ba tsan-tsan tashin hankali.

  Dab tazo kwanciya wajajen k'arfe goma na dare ta sake kiran lamban nasa sai da still Afzal yak'i d'agawa, ganin ba mahalicci se Allah kawai ta tofe addu'o'inta ta kwanta abinta duk da cewan ba baccin take ji ba, gabad'aya hankalinta yana kan halin da Afzal ke ciki. Ita da tasan hakan ze biyo baya wallahi da bata shiga motan Ya Abdul d'in bama tun farko.

  Washegari lectures nata na safe na k'arewa tama driver'nta waya ya dawo da ita gida. Aldeb da zo6o me dad'in gaske ta d'au lokacinta ta had'a ta zuba masa a silver flasks nasa sannan ta tanadar wa Papi da Mami nasu a gefe. Wanka ta sakeyi ta canza kaya tasa matching color hijab ta feffeshe da turare sannan driver ya sauk'eta a office nasu Afzal. Tun da ta ga motansa a fake hankalinta ya d'an kwanta. Tana isa bakin office nasan a sama tayi knocking inda ya amsa da "Come in" a hankali ta bud'e ta shiga. Sosai mutuminku yayi murna da kuma mamakin ganinta amman ya dake a gun yana wani mozewa, kansa ya kawar tamkar ba mutum neba ya shigo office d'in had'e da cigaba da aikin dake gabansa. Ajiyar zuciya ta sauk'e ta k'arisa ciki ta zauna kan kujerar da ta saba zama a kai kullum tare da yin shiru.

   Ganin be da niyyan yi mata magana na kusan tsawon minti biyu kawai se ta gaishesa "Yaya good afternoon" Yadda kuka san da kurma take magana haka yayi mata, ko kai be d'aga ba balle ya kalleta se rubuce-rubucen sa kawai yake.

    "Yaya gaisuwan nawa ma bazaka amsa ba?" Ta tambayesa cikin kamala a hankali tamkar wacce take shirin yin kuka. "Yaya so kake ne ciwon zuciya ya kamani in mutu? Dan Allah kayi hak'uri" har anan be ce mata komi ba.
  "Yaya I'm sorry, I'm so sorry" ta fad'a had'e da rik'e kunnuwanta yayinda idanunta suka soma cikowa da hawaye.

    "Yaya yanzu se nayi kukan zaka mun magana?" Yanzu kam har hawayen sun soma d'iga sede har anan Afzal yak'i koda d'aga kai ne ya kalleta.

   "Toh shikenan" tayi maganan tana share hawayenta "Bari in koma inda na fito tunda ko d'aga kai bazaka iyayi ba ka kalleni" ta ja hanci "Ga Aldeb da zo6o nan na kawo maka, I'm still saying sorry" tana kaiwa nan ta mik'e, bata kai ga taka k'afarta ba Afzal ya mik'a hannu ya rik'e hijabinta,  chak ta tsaya gun ba tare da tace komi ba se faman kukanta take a hankali.

  "Don't go" yace da ita a hankali dad'i sosai taji amman ta fake itama "Ni ka sake mun hijabi."

  "Nace ki tsaya" ya nanata cikin tattausar murya. Juyowa tayi tana kallonsa yayinda hawaye ke d'igowa sama-sama daga idanunta. "Bayan tun jiya ina baka hak'uri kak'i kulani bale ka hak'ura ni ka sakeni inyi tafiya ta dama tun ba yau ba na gano ba ka sona."

   "I'm sorry toh zauna kin ji?" Ya ce da ita a hankali.

  "Nifa tafiya ta zanyi ka sakeni kurum."

  "Lily nace ki zauna."

  "Toh haka akeyi ne?" Ta tambayesa had'e da turo d'an bakinta. "Ko baccin kirki na kasa yi jiya, I called and texted you severally sarai kana gani kak'i responding d'ina, Wallahi if only ka san yadda hankali na ya..." ba se kawai ta rushe mishi da kuka ba. Yana tayi shiru tayi shiru kar ta tara masa jama'a amman inaa tak'i jinsa, se kukarta take harda me sauti. A haka ne har PA'n Afzal ta lek'o take tambayan ko lafiya. "Lafiya Blessing don't mind her kukan banza take" yace da PA'n sannan ya samu ta ja musu k'ofan ta fice.

   "Yanzu Lily ni ke miki magana amman bakiya ji? In ce miki kiyi shiru kik'i yi? Se kin tara mun duka mutanen office d'in tukuna zaki ji dad'i?" Itama yadda kuka san bada ita yake ba, se aikin kukanta take harma tana k'ara sautin, gaban hijabinta ko lis ta jik'asa da hawaye. "Toh kiyi hak'uri, yi hak'uri kibar kukan haka" ya soma pampering nata yana bata hak'uri.

  "O'o ba tun jiya nake baka hak'uri ba kak'i ji na."

  "Toh ba ya wuce ba?"

  "Ni seka cemin ka hak'ura tukuna" ta fad'a tana zum6uro baki yayinda ta 6oye kusan rabin fuskarta k'ark'ashin hijabinta.

  "I'll think about it keep quiet first."

 "O'o ni seka ce ka hak'ura" ta sake sa wani kukan sanin sarai ya tsani hayaniya.

  "My Goodness!" Ya furta cike da tashin hankali yana susa temple nasa. "Da gan-gan kike ko?"

  "Ni se kace ka hak'ura" ta kuma sa wani kukan.

  "Fine! Naji na hak'ura shikenan kiyi shiru."

  "Ka hak'ura dagaske? Bazaka sake ignoring calls d'ina ba?" Se anan ta ciro fuskan nata gabad'ai tana kallonsa. Ba k'aramin dariya ba reaction na fuskarta yasanya sa da k'yar ya had'iye dariyan ya gyad'a mata kai "Bazan sake ba" ya sanar da ita.
  Se anan taji sanyi a ranta ta shiga share hawayenta, hannu ya cusa a  aljihunsa ya ciro hanky ya mik'a mata. Ba gardama ta amsa ta share hawayen nata dashi bayan da ta gama ta mayar mishi ya amsa ya mayar cikin aljihunsa.

  "Wato taurin kan nan namu na nan har yanzu ko?"

  "Wani taurin kai kuma Yaya?" Ta tambayesa tamkar bata fahimci abinda yake nufi ba.

  "Baki na nawa ina ce miki kiyi shiru amman ki k'i yi?"

  "Toh ba kaine ba, inata baka hak'uri amman kaki hak'ura."

  "Toh ai kece kika janyo."

  "Kawai don na shiga motan wan k'awata? Believe me da nasan hakan ze 6ata maka rai wallahi bazan soma ba."

   "Na ji and I'm sorry for making you worried and restless jiya but on a serious note bana son in sake jin kin shiga motan wani Lily, komin ya situation d'in yake kuwa, duk randa driver'n ki bashida lafiya call me up and let me know if I'm too busy to come pick you up zan tura driver'n office kona gida yaje ya d'auko ki banason in sake jin kin shiga motan wani, kinji?"

  "Na'am Yaya, in shaa Allah anyi na farko anyi na k'arshe."

  "Masha Allah that's my Lily."

 "Amma Yaya, Maamah is my very good friend bana tsammanin har zata iya cutar dani. I trust her."

  "Ni bance miki Maaman ne ban yarda da ita ba wan nata ne ban yarda dashi ba."

  "Toh amma-"

  "Lily enough, nide na fad'a miki in ba wai fad'a kikeso muyi ba toh karki sake shiga motanshi ko na wani banda nawa kinji?"

  "Naji Yaya" ta amsa tana mamakin iko irin na Afzal lallai wannan da ace yana da k'anne da sun taso da discipline don ba k'arya yayi kalan yayun dake jibgan k'annensu idan suka tafka rashin hankali.

  "Ya lectures toh?" Yayi maganan yana janyo cup a saman fridge nasa don tsiyaye Aldeb d'in. "Kawo in tsiyaya maka" tayi maganan tana k'ok'arin amsan cup d'in "Lectures Alhamdulillah amma ba dad'i mutun kullum 7 ya fita sekace d'an secondary school."

  "Lol toh me maraban ki da 'yan secondary school d'in?"

 "Yaya wallahi akwai difference."

  "Toh big girl naji" yayi maganan yana amsan cup d'in "Thank you" yace da ita.

  "You're welcome" chan tace, "Ba kace yayi dad'i ba" tare da had'e gira.

  "Ina santi ze bar ni in fad'a? Rabonki da ki kawo mun Aldeb har na manta."

  "Forgive me Yaya daga yanzu kam zanyi k'ok'ari koda once in a week ne ina kawo maka."

  "Keda kike school yanzu? Don't bother."

  "When it comes to my Yaya komin yaya ne se an mishi abinda yakeso so kar ka damu."

  "Hakane?" Ya tambaya yana me jin dad'in amsan data basa.

  "Sosai ma kuwa."

  "Toh shikenan thank you."

  "You're welcome, I guess I can go now, kaima ka samu ka kammala aikin dake gabanka, zani gida inje inci abinci yunwa nakeji."

   "Let's eat out it's almost lunch time" yayi maganan yana duban agogonsa. Ba musu ta jirasa ya d'an k'imtsa kan table nasan sannan suka wuce restor suka ci abinci, bayan sun gama ci ya sauk'eta a gida sannan ya komo office.

****
  A kwana a tashi be ragar da komi ba se gashi yau su Amal suna rubuta first semester exams nasu. A gida kuwa ta fannin Nazeefah da Afzal suna nan kaman kayan wanki ba cigaban komi, don koda tace wa Mummy kan zata fara yiwa Afzal girki koda wasa bata ta6ayi ba, ko tace zatayi se wata ra'ayin ta hanata ta hura mata kai kan cewa ai yanzu da zaran ta fara yi masa girki ze ga kaman sonsa take tana son su shirya kar tayi, itako seta biye wa ra'ayin. Amma se de bataji Afzal na waya da Amal ba, se zuciyarta tayi mata k'ona, zama take ta gabzi kukanta ta godewa Allah a hakan kuma ta tsaya tana cewa ita ba son Afzal take ba.

   ****
  Amal da Maamah ne ke zaune akan slabs suna karatun paper'nsu na gobe Maamah ta fara janta da hira.

   "Friendy?" Ta kirata.

  "Na'am" Amal ta amsa cike da fara'a.

  "Har yanzu fa baki bani amsa ba wallahi Ya Abdul ya tak'ura min."

  "Nikam kibar zancen can Maamah muyi karatu" Janye handout d'in Maamah tayi. "Ha'a! Ya da haka?" Amal ta tambaya tana k'ura mata ido.

  "Wallahi yau kam sekin bani amsa haba mana friendy yanzu kodan k'awancan dake tsakaninmu ma baza ki bawa Ya Abdul dama ba? Wallahi he's a very cool and gentleman if you get to know him, baida matsala sam."

  "Na sani Maamah bazaki gane bane."

  "Mey ne bazan gane d'inba? Kede kawai kice kin k'i min Ya Abdul kuma shikenan na gode ni kika k'i ba shi ba wallahi."

  "Wallahi ba haka bane don Allah karkiyi magana haka."

  "Ya kikeson inyi toh? Yaya na fa kikayi rejecting tun yaushe nake k'ok'arin shawo kanki amman ko lambarki kin hana in basa wallahi ko baccin arziki Ya Abdul bai samu kwana biyun nan as kullum tunanin ki yake tun kan ranan daya rage miki hanya har izuwa shekaran jiya da ya kaimu Unimaid garden."

  "Ji k'arya wai ko bacci baya iyayi a d'akinsa kike kwana ne da zaki san hakan?"

  "Eh yimin wayo ki canza topic d'in" Maamah ta fad'a tana juya mata ido.

  "Lol yi hak'uri toh."

  "Nide ba hak'urin da zanyi sekin amince in bawa Ya Abdul numbanki."

  "Ke dad'i na dake naci wallahi kibari mana mu gama karatun tukuna gobe ne fa exams d'in."

  "Friendy seconds nawa ne ze d'auke ki kice 'ki bashi' kawai? Wallahi rashin mutunci ba kyau."

  "Nikam kode biyanki Ya Abdul yayi ne? Dagewan naki fa yayi yawa."

  "Wallahi sam ba haka bane, you're just the perfect girl for him wallahi tun da nasan Ya Abdul 'yan mata biyu ya ta6a yi ta farkon har sun fara zancen aure Allah yayi mata rasuwa se kuma ta biyun sunyi nisa itama yazo ya gane tana son abokinsa se suka rabu daga baya tayi-tayi ta dawo mishi amman ina he's already heartbroken."

  "Allah sarki Allah ya jik'an ran musulmi."

  "Ameen" ta amsa, "Kuma kinga kusan wata shida kenan da faruwan hakan ban sake jin yana neman wata ba se daya kafa idanunsa akanki Wallahi he's intentions to you are clear."

  "Na ji kuma na gamsu Maamah kawai ina ganin this's not the right time for me to be in a relationship ne kiga part one fa kawai nake I have almost 5 years to go Ya Abdul baze iya jira na ba."

  "Wallahi ze iya, he is willing to wait till forever for you."

  "Hmm" ta numfasa.

  "Kode kam Yayan nawa be miki bane? Yayi muni dayawa ko?"

  "Haba ai kema kinsan yana da kyau wallahi gashi chocolate skinned, ga saje ga ido kaman naki a nan."

  "Yana da kyau kenan?"

  "Eh mana" ta amsa without knowing when "I mean ni ba ruwana ki rufa min asiri kiban handout d'ina" ta shiga canza zancen.

  "Amal pleasee ki amince pleasee wallahi ko na basa lamban naki baze kiraki ba se mun gama exams shi da bakinsa ya cemun haka."

  "Toh naji ba se kin cinye ni ba ki bashi shikenan?"

 "Yeyyyyy!!" tasa ihu had'e da hugging d'in Amal wane wacce ke neman suffocating nata.

  "Toh nikam sakeni haka mu k'arisa karatun nan kinga har Azahar ya doso." Handout natan ta mayar mata suka cigaba da karatu suna iddawa sukaje sukayi sallah sannan kowacce tayi hanyan gida. Kamar yadda Ya Abdul ya d'au alk'awari, seda su Amal suka kammala exams bayan kwana biyu ya buga mata waya, lokacin tana zaune tsakar gida tana bita wayan ya shigo. Ganin new number yasa bata d'aga da wuri ba seda ya kusan tsinkewa. Shiru tayi da ta d'agan chan daga d'ayan 6angaren taji bak'on murya nayi mata sallama. Cikin sark'ak'k'iyar muryarta me sanyi ta amsa da "Wa'alaikumus salam wa rahmatullah."

   "Amal ya kike?" Sama-sama suka gaisa dake har yanzu bata fahimci wake magana ba. "Baki gane muryan bako har yanzu?"

  "Eh wallahi I'm sorry."

  "Abdul Rahman ne" ya sanar da ita.

  "Abdul Rahman daga ina kenan?"

   Murmusawa yayi kad'an sannan yace, "Ya Abdul toh" se yanzu ta fahimta ashe de Abdul Rahman ne complete name nasa, wow. "Laa! Ya Abdul ina yini?"

  "Bayan wuyan da kika bani har kin manta dani ko?"

  "Haba Ya Abdul ina na isa."

  "Gashi kuwa."

  "A'a wallahi kullum da Ya Abdul Maamah ke addressing naka bata ta6a ambaton full name naka ba kaga ko bazeyi in gane wanene ba at first thought" ta mar bayani a hankali.

  "You're right so ya hutu?"

  "Hutu Alhamdulillah ya aiki?"

  "Lafiya k'alau kun gama exams ko?"

  "Eh wallahi."

  "Toh Allah ya bada sa'a."

  "Ameen thank you."

  "I thought I should call and check up on you."

  "Ayyah to nagode sosai a gaishe da gida."

  "Zasuji take care" a haka sukayi sallama. "Phew!" Ta numfasa had'e da ajiye wayan a gefe sannan ta cigaba da karatunta. Tun daga ranan Ya Abdul ke kiran Amal suna gaisawa, kar kuma kuyi tsammanin irin kira barkatai ba fasali d'innan ne, no a sati befi suyi waya sau biyu ba idan yayi yawa shine sau uku ko hud'u. A hankali shak'uwa ya fara shiga tsakaninsu ba abinda ke burge Amal a gun Ya Abdul kaman yadda yake yawan sanyata dariya, sede basuyi waya ba koda ranta a 6ace ne seya faranta mata da kalamun sanya dariyansa, he's so jovial Maamah batayi k'arya ba da tace bashida matsala. A satin da zasu koma makaranta ne yayi insisting se ya zo sun had'u mutumiyarku da shegen tsoro kam ba se ta shiga yi masa corner-corner ba.  Yau tace zata islamiyya, gobe tace zata raka Mami gidan suna ko makamancin haka daga k'arshe de ya gane tsoro take ta ke6e dashi shi kad'ai kuma bega laifinta ba hasali ma yaba mata yayi sosai hakan na nufin tasan abinda takeyi ne. Don haka ya tambayeta idan ze taho da Maamah zata amince ta fito? Tuni ta amince. Hakan ko suka shirya ranar Laraba da yamma se gashi da Maamah sun k'ariso gidansu, har ciki Maamah ta shiga suka gaisa dasu Mami sannan suka fito da Amal inda Amal ta zauna a gidan gaba ita kuma ta koma baya. Bayan gaisuwa suka sha hira sosai dukansu ukun cikin motan, se dariya Ya Abdul yake sanya su barin ma Amal dake dariya harda k'walla, kusan k'arfe shida Ya Abdul yace ya kamata su tafi, don dad'in hira Amal ji take kaman kada su tafi. Dab tazo sauk'a daga motan kenan ya mik'a mata wata leda, ta kar6a ita kuwa tak'i ba yadda beyi ba amman tak'i, daga k'arshe seda ya baiwa Maamah ta shigar mata dashi ciki har cikin d'akinta.

**** Bayan ta dawo ciki ta wuce d'akinta ta fito da ledar, zazzagewan da zatayi ta tarar da chocolates turum, ba wanda babu aciki da wanda Afzal ya koya mata ci da wanda se yau ma ta ta6a ganinsu, abu de yayi kyau. Haka nan ta 6oye abinta cikin akwati tana ci a hankali a hankali. Bayan sallan Isha ta kira Ya Abdul tayi masa godiya inda suka sake ta6a hira kad'an sannan sukayi sallama. Ganin goma be cika ba ta yi tunanin kiran Afzal da alama aiki yayi zafi ne ko nemanta bayya yi kwana biyu, daman yayi tafiya zuwa Lagos for a meeting, yau k'imanin kwana biyu zuwa uku kenan. Tana kiransa on the first ring ya d'aga, "Yaya kayi wuyan gani" ta soma cewa.

  "Wallahi Lily, I've been so busy ko time na wayan ma bani dashi."

  "Allah sarki ya kake ya aikin?"

  "Alhamdulillah ya gida dasu Mami?"

  "Lafiyansu k'alau d'azu take cewa kwana biyu bata ji motsinka ba nace ai kayi tafiya, she's sending her warm greetings so as Papi."

  "Toh ayya ina amsawa."

  "Yaya I miss you yaushe zaka dawo?"

  "Saturday in shaa Allah."

  "Toh Allah kaimu barin barka haka nasan a gaje kake."

  "Alright Lily thank you have a peaceful night rest."

  "You too, seda safe" da haka sukayi sallama.

****
  Nazeefah ce zaune gaban Tv ta sa channel na Zee world tana kallon wata indian series se faman buga tsaki take, ga takaicin rainin wayon da ake tayi a series d'in ga na rashin Afzal kwana biyun da tayi bata sanyasa a ido ba bata kuma ji muryansa ba, ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, se a yanzun take sake jaddada cewa lallai-lallai ta fad'a kogin sonsa. Seta d'au wayarta zata kirasa seta kashe ta fasa, tayi hakan sau fiye da a k'irga. Daga k'arshe de ta dage ta kira har ya shiga yana ringing, se cewa kanta take ai don ya sanar dani zeyi tafiya ne yasa zan kirasa, da ace tafiyansa kawai ya kama yayi wallahi ko ta kansa bazan yi ba bale har in kirasa.

  Ya kusan tsinkewa ya d'aga kasancewar har ya fara bacci. Shiru tayi bayan da ya d'agan kaman yadda shima yayi shiru yana jiran ta soma magana dukda cewan yayi mamakin ganin kirarta amman dake yasan halin matar nasa, tunaninsa gabad'aya yayi kan ko so take ta sanar dashi kud'inta ya k'are ne ya hankad'o mata wasu.

  Ganin ba mahalicci se Allah mutumiyarku tayi gyaran murya had'e da cewa "Halo?"

  "Yes?" Ya amsa cikin sleepy husky like voice nasa. Rasa na cewa ma tayi, tace ya isa lafiya ne? Toh ai tun shekaran jiya yayi tafiyar chan de ta gaishe sa kawai "Ina yini?"

   "Lafiya" ya amsa casually, "Ya kike?"

  "Lafiya k'alau ya aiki?"

  "Alhamdulillah."

  "Dama nace in ji ko kana lafiya."

  "Toh thank you I'm good ba wata matsala dai ko?"

  "Babu."

  "Toh yayi kyau."

  "Nace gobe zan fita gidan k'awata, ina neman uzuri."

  "Kikace?" Afzal da mamaki ya rufesa ya tambaya tun yana a mik'e akan gadon nasa har ya tashi ya zauna besani ba, kode gizo kunnensa ke masa ne? Har Nazeefah ce zata kira waya ta gaishesa musamman don ta tambayesa izini? Lallai yau za ayi ruwan mutane.

  "Nace zani gidan k'awata gobe, am I permitted?"

  "Sure you're, kikaje ki gaisheta."

  "Toh seda safe."

  "Yauwa Allah tashe mu" da haka sukayi sallama. "Phewww!" Ta sauk'e ajiyar zuciya yayinda shima yayi haka ta d'ayan 6angaren. Afzal yana mey mamakin anya kuwa wannan Nazeefah ce yayin da ita kanta take tambayar kanta anya kuwa itace??

   Ranan da Afzal ze dawo ne Nazeefah ta fad'a cikin kan zata mai girki sede da zaran ta motsa d'auko tukunya se wata ra'ayin ta hanata kan cewa har na me zata masa girki? Ai seya d'au sonsa take, yayinda wata ra'ayin ke ce mata mey aciki don tayiwa mijijta girki, besides ma ai ya sanar da ita ranan da ze dawo. Haka dey tayi nan tayi chan daga k'arshe girkin da ba azo anyi ba kenan. Haka nan ya dawo gidan dry ta nad'e k'afa a kan kujera tana kallo. Sannu da zuwa kad'ai ta masa ya amsa ya wuce d'akinsa. Yana watsa ruwa ya canza kaya ya fito se buga k'amshi yake, ko bata tambaya ba tasan gidansu Amal ze wuce. Wani irin zazzafan kishi ne ya tokareta ji take kaman ta rik'o k'afarsa ta hanasa fitan.

  Da ta zauna tayi nazari kuma se taga ai duk laifinta ne da ace ta dafa masa abinci da sede tace yaje dining yaci hakan baze ma samu daman fita ba. Holy sh*t.

  Kaman Nazeefah ta sani gidansu Amal  direct Afzal ya wuce inda aka shirya masa abinci kala-kala ga smoothies d'innan ba wanda Amal bata had'a ba su Ginger ne, zo6o da kuma Aldeb nasa. Sosai ya ji dad'i, dalilin da ya hanasa cin abinci kenan through out yau saboda yasan Amal bazata taresa da dry hannu ba. Zama yayi ya gabza abincin sosai har ya buk'aci a sa masa ragowar a kula ya tafi dashi gida. Amal se dariya take tana neman tsokanansa tana kiransa glutton. Da yazo tafiya ne ya ciro masu tsarabar laces daya musu ita da Mami.

****
   Haka nan tafiya ta cigaba har hutun su Amal ya k'are suka shiga second semester. Ita da Ya Abdul fa se abinda yayi gaba shi de har yanzu be furta mata kalamun so ba, but with the way he's being so extra ita kanta Amal tasan relationship nasu ya tashi daga friendship ya koma wani abun daban. A rana se suyi waya sau biyu zuwa uku, har Mami ta fara sa mata ido tana zata k'wace wayan idan batayi hankali ba. Ana nan ana nan kwatsam rana d'aya Ya Abdul ya fad'awa Amal abinda ya juma yake son sanar da ita kan yana sonta, so kuma na aure. A wannan lokaci itama Amal ba k'arya ta fad'a kogin sonsa, saboda ko be kirata a waya ba, ita zata d'au wayarta ta kirasa. Tunda ya furta mata wannan kalamu ta daina d'aga wayansa ko message ya mata bata responding, ba k'aramin tashin hankali ta sanya sa ciki ba gabad'aya ya rasa meke masa dad'i. Gun k'anwarsa Maamah ya nufa yayi mata bayanin abinda ke faruwa kan dan Allah ta taimaka masa. Kwantar mai da hankali tayi ta kuma tabbatar masa da cewa in shaa Allah Amal ta sa ce saboda ita ta riga ta gane Amal na sonsa. Washegari ko school Amal tak'i fita sanin the moment ta fita zasu had'u da Maamah itako zata kira Ya Abdul ta had'asu don haka ta fake a gida da cewan cikinta na ciwo.

  Da misalin k'arfe goma Afzal ya kirata bayan sun gaisa yake tambayarta lectures take ce mai bata ji dad'i ba yau tana gida amman da sauk'i yanzu haka. "Se yau za'a same ki kenan Lily" yace da ita afterwards.

  "Kamar ya Yaya?" Ta tambayesa cike da rashin fahimta.

  "Throughout last week koda na kiraki kullum line busy nakeji wa muka samu haka?"

  "Kai Yaya ba kowa fa idan ka kira kaji line busy to da da Maamah nake waya."

  "Anya kuwa Lily?"

  "Dagaske Yaya."

  "Toh shikenan Allah k'ara sauk'i."

  "Ameen thank you." Da haka sukayi sallama bata kaiga ajiye wayan ba se ga call na Ya Abdul kaman wacce bazata d'aga ba seda call d'in ya kusa tsinkewa ta d'aga had'e da yin shiru.

   "Alhamdulillah" ta ji ya furta "Amal?" Shiru tayi "Amal kuma bazaki amsa ba?"

  "Ina kwana?" Ta gaishesa a hankali.

  LAmal mey nayi da zan fuskanci wannan hukunci daga gareki? Don't you think hukuncin nan naki yamin tsauri dayawa?"

  "I'm sorry."

  "Amal in sona ne bazaki iya yi ba you could have simply told me, I was worried sick about you gashi yau ko school kin k'i fita duk don gudun karki had'u da ni ne?"

   "Nifa ba haka bane, cikina ne yake ciwo."

  "Why do I feel like you're lying?"

  "I'm sorry" haka kawai ta tsinci kanta tana basa hak'uri ba gaira ba dalili ko de don ita kanta tasan abinda tayi masa bata kyauta masa bane?

  "Look I take back what I said to you kinji? Na gane you can't love me back but please karki 6ata friendship dake tsakanin mu I cherish our friendship alot Amal."

  "Ya Abdul ka dena magana haka."

  "Toh ya kikeson inyi Amal? Haka kawai kika dena recieving calls d'ina kina ignoring d'ina anyhow."

  "I'm sorry."

  "It's okay abu d'aya nakeson tambayanki Amal please give me a sincere answer."

  "What is it?"

  "Who's the lucky guy da ya rigani sace zuciyarki? I'm sure this's all about him."

  "Wallahi ba kowa Ya Abdul I just need some space."

  "You mean I still have hope?"

  "In zaka iya jira" ta amsa bayan tsawon lokacin da ta d'auka.

  "Amal I'm ready to wait for eternity for you, Amal ba zaki gane irin soyayyan da nake miki ba, it's been long since I felt this. Amal out of the blue kika sace min zuciya, I love and adore everything about you and I'm willing to wait for you for as how long it takes until you're ready. Amal I love you."

  "Ya Abdul..." se kuma tayi shiru.

  Yes Amal I love you and am not ashamed of it ko a gaban waye zan fad'a, I love you Amal."

  "Thank you Ya Abdul."

  "Gobe ki fita school kinji?"

  "Ni banida lafiya" ta fad'a stubbornly.

  "Haba beautiful? Duk don gudun kar inzo d'aukan Maamah mu had'u ne? Ki kwantar da hankalinki ni gobe ma zanyi tafiya."

  "Tafiya kuma Ya Abdul?" Alokaci d'aya se taji kuma tana missing nasa.

  "Ba abinda kikeso ba kenan."

   "A'a fa ni bance ba."

  "Toh zaki fita school gobe inzo in kun tashi?"

  "Eh kazo."

  Does this means you missed me too?"

  "Ya Abdul yes, I missed you" ta amsa cuke da kunya ita kad'ai ce a d'akin amman tana kare fuskarta da pillow.

  "Wow!" Yayi exclaiming cike da murna da farin ciki "That's my girl, I miss you even more, so se na zo ko?"

  "Toh Allah kaimu"

 "Ameen, you take care okay? I love you."

  You take care too" da haka ta karse wayar tare da rungume ta. Haka kawai ta tsinci kanta tana murmushi ita kad'anta there's no denying itama tana son Ya Abdul halan fiye da yadda yake jin yana sonta ma kawai de as a lady her ego comes before her feelings.

*****
   Mu kwana mu tashi be ragar da komi ba, haka tun Amal tana 6oyewa Ya Abdul soyayyarta ta shiga nunawa, haka zata la6e a d'aki kaman tana bacci amman waya take. A school kuwa yawancin in sun fita break shima Ya Abdul seya kar6i excuse a office ya fito su had'u su sha firarsu. Afzal kuwa kasancewar ya samu cigaba a office, daga Assistant manager ya koma manager sam baya samun zama kullum cikin aiki yake da tafiye-tafiye hakan ya bawa Amal da Ya Abdul daman sake shak'uwa sosai.

  Yau bayan juma'a Amal na karanta suratu Kahf wayarta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira, wai wata sabon gani. D'agawa tayi take had'e da cewa, "Yau Yaya ya tuna dani kenan."

  "In ban tuna dake ba ai ke bakida niyyan kira na."

  "Inji wa Yaya? Wallahi kullum kana raina banason tak'ura maka da kira ne saboda naga kaman aiki na maka yawa yanzu."

  "Toh ya kike?"

  "I'm fine just that am missing you."

  "I miss you too Lily ya school?"

  "School lafiya k'alau."

  "Ki fito ina bakin k'ofa." Dum taji zuciyarta ta buga a tunaninta gabad'aya Afzal baya gari ne, dan kuwa yanzun sukayi waya da Ya Abdul yace mata yana tahowa ya zatayi idan yazo ya iskesu da Afzal? Yau nata ya k'are me hana afzal kurara ta se Allah motan wani kawai ta shiga seda ya kusan cinyeta bale ace har ta kawo saurayi gida?
  "Halo Lily? Fitowan ne baza kiyi ba sena k'ariso ciki da kaina?"

  "A'a Yaya gani nan fitowa" daga nan ta ajiye wayan. Zagin kanta ta shiga yi, meyasa bata ce masa bata gida ba? Sede sarai tasan halinsa yana iya cewa bari ya k'ariso su gaisa da Mami, daga nan kuma Mami ta fallasheta. Numban Ya Abdul ta kira take don sanar dashi kar yazo yanzu ya bari se anjima zata fita sede kash two missed calls ta masa amman bai kusa. Yau akeyinta! Ta furta a ranta.

  Qur'anin ta mayar mazauninsa ta d'an shafa powder da jan baki taja hijabinta ta sanya ta d'an feffeshe da turare sannan ta fice. Tun da ta fito Afzal dake zaune cikin motansa yake binta da kallo yayinda ya tsinci kansa cikin wani irin walwala da farin ciki maras misaltuwa. Se gani yake kaman yau ya fara sanya ta a idanunsa, tana k'arisawa cikin motan k'amshin turarenta ya mamaye ciki. "Kyau kenan Lily?" Ya ce da ita yana murmushi sosai.

  "Kai Yaya" ta amsa tana kare fuskanta da hijabin nata "Dan Allah ka dena sani jin kunyanka."

   "Ai kuwa sede ki dunga cin kunyan nawa don bazan fasa fad'a miki kinyi kyau ba Lily."

  "Toh ai kaima kayi kyau in fact kullum ma cikin baza kyau kake."

  "Hakane?"

  "Sosai ma Yaya."

  "Toh tsaya in d'aukeki hoto."

  "Yaya wai kai se mutum yayi muni zaka ce zaka mai hoto?"

  "Kika sake cewa kinyi muni zamuyi fad'a."

 "Toh na dena amman d-" flash na cameran daya haskata ne y rufa mata baki. "Haba mana Yaya!"

  "Tsaya mana kiga kinyi kyau" tsayawan tayi ya nuna mata se kuma taga batayi muni ba "See? I told you tsaya mu k'ara miki d'aya." Daidaita zamanta tayi daram tayi posing yayin da ya haska mata flash ras ta fito ta kuma yi bala'in kyau.

  "Toh saura kai, kaima ka tsaya a d'aukeka."

  "Ce miki akayi maza suna hoto?"

  "Yimin yanga de Yaya" ta kai ga d'aukan wayanta a inda ta ajiye kenan sega Ya Abdul na kira kafin tace zata janye inaa har idon Afzal sun karance mishi sunan wanda ke kira as
  "LOML❤️🔐" meaning 'Love Of My Life' danqaree! Ba zuciyan Amal kad'ai bane ya buga harta na Afzal, infact nasa ma yafi nata tsinkewa take wajen yaji jikinsa yayi sanyi lissss. A hankali ta janye wayan, yadda ta kasa d'agawa haka ta kasa katsewa ta bari se ringing yake, yana tsinkewa Ya Abdul ya shiga kira again se a karo na biyu ne ta katse.

  "Mey na katsewa kuma?" Afzal ya tambayeta yana me k'ok'arin 6oye kishi, k'unci da bak'in cikin da ya fad'a aciki.

  "Ba important call bane" ta fad'a a hankali, gabad'aya kunya yabi ya mamayeta ba haka taso sanar da Afzal batun Ya Abdul ba.

  "Love of our live yana kira kice ba important call ba Lily?"

  "Yaya please-" tana cikin maganan ne Ya Abdul ya shiga kira again bata kaiga katsewa ba Afzal yace, "You're excused, jeki amsa ina jiranki."

  "Yaya I can call him back later."

  "Ni nace ai kije Lily kar ki damu" kallonsa tayi one last time sannan ta sauk'a daga motan ta ke6e gefe guda. Afzal da yake ji tamkar na lahira ma yafisa jin dad'i besan lokacinda ya tada motan ba ya fice a guje ji kawai Amal tayi iska ya wuceta, juyawan da zatayi taga motan Afzal ne bata san lokacinda ta bawa Ya Abdul hak'uri akan anjima zasuyi magana ba ta katse wayar.

   Yau kashinta ya bushe!


RANA D'AYA
#RD

Love... King Miemiebee👄✨

5 comments:

Unknown said...

Masha Allah. More updates pls

Unknown said...

tanks sis

Unknown said...

Jazakallah khairan plz more

Unknown said...

Thank you sis allah kara basira pls more update you keep us witing

Unknown said...

Ure doing a NYC job, keep it up dear