Friday, 6 April 2018

RANA D'AYA

BY MIEMIEBEE

  PAGE 02


    Seda ya d'auki tsawon lokacin da ya wuce tsammanin mutum sannan yace, "Ga magunan naki, ina kyautata zaton kin iya karatu za kuma ki iya gane dosage d-" bata basa dama ya k'arisa fad'in abinda yake da niyya ba ta katse shi "Mallam ba seka zageni ba am not an illiterate."

   "Serve you well" ya fad'a ba tare da nuna damuwa ba "Then kina iya tashi in kaiki gida."

  "Nagode kar ka damu I can bring myself home" taga alaman d'an rainin wayo ne shi to ya kwantar da bokatin hankalinsa, kar yace don ya ganta a haka zey raina mata wayo dan kuwa ita ba jahila bace saboda tayi karatun ta na secondary ba kuma a kowani gajan government school ba. No private school ne me kyau wanda ake kira da Ruby springfield college wanda ya kasance one of the best schools in Maiduguri.

  "What gibberish are you saying?" Ya tambayeta a takaice. "See kar ki 6ata min lokaci, kar kiga don tun d'azun ina danne zuciya na ina binki a hankali ki d'au hakan ba a bakin komi ba. Ina da muhimman abubuwa a gaba na wanda sukafi tsayuwa anan ina rok'anki to take you home, now get up" ya buk'aceta cike da tsiwa sede ko motsawa Amal batayi ba. "Are you deaf?"

   "I said to leave me alone!" Ta buga mai tsawan itama "Ka kama ka jawo min asara ina zaman zama na zaka wani kama kace min in tashi ka kaini gida? Me kakeson in cewa Mami bayan duk cafanin dana yo mata ka ta6ar6arar min dasu kabarni da babu? Don Allah ka barni kayi tafiyanka."

   "In ke baki san abunda ya kamata ba toh ni na sani a cewarki bazan biya ki asaran dana janyo miki bane? I'm aware of all that and zan mayar miki da komi kawai ni ki tashi in kaiki gida na bawa iyayenki hak'uri na fita hak'k'inki, I have other important things to attend to" ya sanar da ita. Kaman wacce bazata motsa ba se kuma ta shiga miqewa a hankali wanda a garin hakan ta kusa fad'i kasancewar k'afar nata da ta kasa takashi. Da sauri Afzal ya tarota, ganin bey saketa ba har yanzun kuma baida niyyan yin hakan ta shiga jan hannunta sai dai ta kasa.

   "Don't fight it" yace da ita "Muje" bata sake yunk'urin k'watan kanta ba har suka kai haraban asibitin inda yayi parking motarsa. Sanyata yayi a kujeran gaba sannan ya zagaya ya shiga shima tare da tada motar. A circular road inda ya kad'etan suka koma inda ya buk'ace ta da ta rubuta masa list na abubuwan datayi rashin nasu. Ba gardama ta amshi paper da biron ta lisafo komi harda kud'ad'e da amount nasu. Abu d'ad'd'aiku ne be samu ba wanda yamata alk'awarin bata kud'in idan ya kaita gida. A farko yaso su jesu kasuwan domin ta siyo amman tuna besan kan kasuwan ba sabida bai ta6a shiga ba seya fasa. A karo na biyu kuwa yayi tunanin ko zasu shiga su biyu tayi leading nasu but referring to her wounded leg yaga wuya kawai hakan zai bata so se yayi sticking to first decision d'in kawai: na miyar mata da kud'in. Kwatancen gidansu ya buk'ace ta da tayi mar wanda tayi ba tare da gardama ba. Chan cikin Jiddari suka shige. Tunda Afzal yake be ta6a shiga kwamacalan unguwa ba kaman wannan se yau, yasan war haka motansa ya fita daga kamanninsa ya dawo wani abun na daban saboda potholes da kwatamin daya rink'a shiga. Sun kai wani junction ta buk'ace sa daya tsaya.

   "Ina ne gidan naku?" Abinda ya fara tambayarta kenan.

   "Mota baya iya shiga layin zan k'arisa daga nan nagode."

 "Acewarki kawo ki kawai nayi saboda inada ra'ayin hakan? Am here to apologize to your parents and tsaya ba sekin karya min handle na mota ba" ya buk'ace ta ganin tun d'azun take k'ok'arin bud'ewa amman ta kasa. Fitowa yayi ya zagaya sannan ya bud'e mata k'ofar tare da miqa mata hannunsa.  A cewarta gabad'aya nufi yake da ta sanya nata aciki saboda ya taimaka ya fito da ita daga motan sede wani hanzari ba gudu ba tana gwada yunk'urin sa hannunta cikin nasa kawai taga yaja hannun nasa baya da sauri yana me kad'a mata kai "Tray d'in zaki miqa min" ya sanar da ita. Wani irin kunya kaman ta tone k'asa tasa kanta aciki ta jiyo amman wallahi seta rama ba shakka da gangan ya mata hakan don ya kunyatar da ita. "Kar ka damu ina da hannu I can manage" ta fad'a rai a murtik'e tare da murgud'a mai baki. Murmusawa yayi yaja gefe tare da crossing arms nasa a faffad'ar k'irjinsa yana me kallonta. Yasani sarai bazata iya fitowa ba harta sai ya taimaka mata toh why don't he enjoy the moment?

   Amal tafi minti biyu tana k'ok'arin fitowa amman ta gagara, ko kad'an k'afan nata baison nauyi ai kawai ta rushe da kuka har anan Afzal be motsa ba seda yabari ta sha wahala ta shiga neman taimako da kanta. Ganin ba mahalicci se Allah ta kewayo da kallonta a garesa, dagangan shiko ya shiga duban lokaci a agogon dake d'aure a hannunsa pretending as if beda masaniya game da abinda takeyi tun d'azu.

   "Bawan Allah don Allah ka taimaka min bazan iya fita ba." Dariya ne ya k'eto mar sosai amman ya dage ya danne tare da matsowa kusa da ita. "So kin iya magana da ladabi haka dama?" Ya tambayeta yana me k'are mata kallo.

  "Ni ba abinda na buk'ata ba kenan" ta amsa tana me kawar da kanta haka kawai bata jin dad'in had'a ido dashi, "Ni ka taimaka min in samu in fita daga wannan motar nakan please!"

  "Ohh! Rashin kunya kuma zakiyi min? Kinsan kad'an ne daga cin aiki na in barki har sekinyi tsami cikin motan nan ko? Don't you dare me young lady."

   "A'a kayi hak'uri don Allah." Cike da rashin mutunci ya taimaka mata ta samu ta fito daga motan suka shiga takawa zuwa gidan nasu wanda baida nisa daga inda Afzal yayi parking. Sede duk wani angle da suka wuce se sun zama topic and side of attraction. Surutu babu wanda basu ji ba amman duk haka suka manna musu har suka k'arisa gidansu Amal d'in.

   Gida ne dai-dai da d'an talaka bawan Allah wanda za'a iya cewa be rasa ci da sha ba da kuma tufafi. D'akuna biyu ne gabad'aya a gidan a jere seda toilet d'aya daga other end d'in sekuma kitchen a opposite nashi, suna da famfo a tsakar gidan wanda ba sai anje ibo ruwa daga waje ba. Dai-dai Mami ta fito daga kitchen kenan su Amal suke k'arisowa tsakar gidan da Afzal riqe da ita, ai ba shiri tayi baya ta b'oye kanta cikin kitchen d'in tana me leqensu ta window. Salati kawai ta shiga yi ganin yadda mutumin dake sanye da suits ya riqo mata 'ya a cewarta gabad'aya wani masifa Amal taje ta kwaso musu sanin sharpness na bakin 'yar nata kaman razor. Tun farko dama bata goyi bayan zuwa aiken nan ba don de ba yadda ta iya ne Amal tafi k'arfinta gashi Papi (kakan Amal) da take d'an jin maganansa ma bai gida balle ya mata. Yau ina zata sa kanta Amal ta ibo musu abinda yafi k'arfinsu. Tunani kala-kala ba wanda ba tayi ba. Tunda suka shigo Afzal ke bin gidan da kallo, tabbas talakawa ne amman hakan be maida su k'azamai ba. Ko leather d'aya  be gani a k'asa ba ko ina an share tsaf ga kuma k'amshin turaren wutan dake tashi. Suna k'arisowa dai-dai tsakar gidan suka tsaya, se anan ya saketa tare da jan baya kad'an hakan ya bawa Amal daman sauk'e nauyayyiyar ajiyar zuciya.

   "Ina Mamin naki?" Ya tambayeta ai take zuciyan Mami yawani har6a shikenan nata ya k'are yau ga Papi bayi nan yayi tafiya.

   "Dake fa nake" Afzal ya kuma fad'i jin bata bashi amsa ba. Tsaida kewaye-kewayen da takeyi don neman Mami tayi tana me dawo da kallonta a garesa "Gani nayi tare muka shigo gidan taya kake tsammanin zan san inda take?" Ta tambayesa cike da rashin kunya. Cike da d'ambun mamaki Afzal ya tsaya yana kallonta shin wannan wacce irin fitsararriyar yarinya ce? Ace ko kunyan idonsa batayi ta rage wani abun? Sai dai ya daina mamakin hakan tuna 'yan qauye da masifaffen rashin kunya ga kuma shaidan dayayi mata na 'yar gudun hijira, tama daina basa mamakin. On the other side kuwa cikin Mami ya gama d'iban ruwa ji take kaman ta cafko Amal ta nad'a mata na jaki upon all the trouble data janyo masu still tana da bakin yima wannan security (as yadda ta ma Afzal shaida ganin sa sanye da suits) rashin kunya? Lallai kuwa tayi hak'uri ta rufa musu asiri.

   "Mami!" Amal ta k'walla wa mahaifiyar nata kira, shiru kukeji ba amsa. "Mami don Allah ki fito daga b'uyan nan ni bance miki bala'i na kawo ba wannan mutumin gefe nan ne yazo baki hak'uri ya kad'e miki 'ya" ta sanar a fili. Se anan Mami tad'an ji sukuni but even still ta kasa fitowa gani take kamar k'arya Amal keyi saboda sau dayawa takan yi mata hakan, ta d'ibo bala'i daga waje  sannan ta fake tazo tace alkhairi ta kawo.

    "Mami wallahi zan k'ariso in janyo ki daga kitchen d'innan" tafad'a tana kallon setin windon da Mami ke leqe daga gun ai tuni ta miyar da fuskarta ciki, ashe de Amal ta ganta. Numfasa tayi sannan ta fito alokacin kuwa Afzal ji yake idan be saki wannan dariyan daya k'eto mar ba ze iya mutuwa. Wannan wacce erin matsoraciyar uwa ce? Ai kam dole Amal tayi rashin kunya haka daga ganin mahaifiyar natan batayi kalan me tsiwa ba bale har ace zatayi discipline Amal.

   Da k'yar d'in k'yar ya samu ya maida dariyan ciki ahaka ma seda yayi kad'an a waje wanda a sanadin haka Amal ta juya ta galla mai harara sede be ganta ba dake hankalinsa gabad'aya ya duk'ufa akan Mami yana mey mamakin yadda akayi basu kama sekace ba mahaifiyarta ba. Ashe bashi kad'ai ne bayi kama da Umminsa ba (mahaifiyar shi.)

  "Sannu da zuwa bawan Allah" Mami ta fad'a tana nufo su cike da tsoro da fargaba.

   "Yauwa Mami" Afzal ya amsa. "Ina yini?" Ya gaisheta cike da ladabi had'e da durk'usawa kad'an. Ai gaisuwan da Mami bata amsa ba kenan ta shiga basa hak'uri.

  "Don Allah idan wani abun Baby tayi ma kayi hak'uri bawan Allah wallahi banida abun da zan iya baka banda hak'uri" tace ba alaman kwanciyan hankali a tattare da ita. Ido Amal ta juya cike da takaicin abinda Mami keyi gaban wannan maras mutuncin bawan Allah'n, taya zata tsaya tana basa hak'uri while shi ya kamata yayi hakan?

   Afzal ya bud'e baki zeyi magana kenan Amal ta riga sa "Wai ni Mami yaushe nace miki nayi mar laifi? Dubi fa, dubi k'afa nafa" tayi maganan tana miqar da k'afanta a hankula so Mami could see "Karya min k'afa yayi."

    "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Baby!" Mami tayi exclaiming tare da yin kan 'yar nata tana me zaunar da ita a hankali bisa wani benchin dake kusa tana mata sannu in the process.

   "Look Mami ni ban karya wa 'yarki k'afa ba don't listen to her" Cewar Afzal.

   "Wallahi ya karya" Amal tayi saurin fad'i tana katse Mami "Idan ba karya min k'afa yayi ba toh seya fad'i dalilin daya sa ban iya taka k'afan."

   "Yi shiru Baby na sannu ai ko baki fad'a ba gashi kumburin k'afarki ta nuna kin karye saidai kariya nawa ne?"

   "Kaman biyu ne inji likitan" ta fad'a bayan tasan sarai k'arya take. Se wani zum6uro baki take cike da shagwa6a a yayinda Mami ke ta mata sannu tana shafa k'afan a hankali.
   Shi de Afzal ya rasa nayi, ya rasa menene yayi yau Allah ya had'a sa da dramatic people kallan wad'annan, ace ba babba ba yaro? Hmm shide gado ba gwaninta ba. Da kalan uwa me d'aura wa k'arya gindi haka ai ko hannu Amal ta d'aga ta zagi mutum a kan layi baza'a ga laifin ta ba tunda gashi ba tare da bincike ba mahaifiyar nata ta hau ta zauna akan k'aryan da 'yar nata ta shirya na cewa an karya mata k'afa.

   "Sannu ko Baby bari Papinki ya dawo a yanka miki d'aya daga cikin kajin kiwon nan. A kariya biyun har kika iya kike taka k'afan? Sannu." Har anan bata yi ta kan Afzal dake tsaye duk mamaki yabi ya mamayesa ba.

   "Mami?" Ya kirata ganin wannan draman nasu bana k'arewa bane gashi kuma yana da k'arancin lokaci.

   "Tsaya tukuna bawan Allah in gama da 'yar tawa ita kad'ai Allah ya bani-"

  "Mami!" ya katse ta cike da rashin hak'uri, shi kansa besan lokacinda ya fusata har ya kira ta da tsiwa haka ba. Da mamaki both Mami da Amal suka juyo suna kallonsa, a yayinda zuciyan Amal ke raya mata itama ta miyar masa da masifan.

   "Kinga na farko ni ban karya wa 'yarki k'afa ba I admit I wasn't watching the road attentively na gauce akan hannuna na yo kanta na kuma bugeta and am dearly sorry" ya fayyace mata. "Amman ban karya mata k'afa ba" ya k'arisa.

  "Baka karya mata k'afa bafa kace? Ban gane ba, yo ko nufi kake kawai don ado likitan ya d'aure mata k'afar da bandeji?" Ta tambaya cike da mamaki tana kallon kumburarren k'afan Amal tare da kewayo da kallonta a gareshi, ba shakka akwai rainin hankali anan.

   "Ni ba abinda nake nufi ba kenan amman de kam ban karya wa 'yarki k'afa ba, targad'e ne ta samu tun achan kuma Dr'n ya sanar da ita hakan bansan dalilin da yasa tace miki kariya ne ba."

  "Hakane Baby?" Ta tambaya tana maido da kallonta akan Amal dake faman raba ido.

   "Mami har sekin tambayeta ne? Da girma na ne zan tsaya ina miki wasa da hankali? Kuma idan da har banida niyyan admitting laifin da nayi do you think zan bar duk abinda nakeyi in nemi har gidanku domin in baku hak'uri akan hak'urin dana ba ita Amal d'in? Har kuma in kaita asibiti, think please" Daga yadda yake magana za a san ransa ya soma 6aci kuma bako k'arya acikin duk abinda ya fad'a.

  "Hak'uri? Ni de baka ban hak'uri ba" cewar Amal tana murgud'a baki. "Allah ya karya min k'afa kar ki jisa Mami."

  "Baby kallen shin bawan Allahn nan karya miki k'afa yayi ko kuwa targad'en ce kamar yadda ya fad'i?"

   Ganin fa an ganota ta soma kame-kame "Toh ni ina zan sani ko had'a baki sukayi da likitan don ya rufa mai asiri-" bugi Mami ta kai mata a cinya interrupting her, wanda a sanadin hakan ta sa ihu.

   "Yanzu haka kawai kima bawan Allah sharri ya karya miki k'afa Baby? Shin yaushe zakiyi hankali?" Baki ta zumb'uro tana kukan munafirci a yayinda Mami ta juyo kan Afzal da yayi jugum yana kallon ikon Allah.

   "Bawan Allah don Allah kayi hak'uri wallahi haka take gagara da rashin ji toh wane akanta akayi wahayinsa."

   "Ba sekin fad'a ba naga hakan a tattare da ita" ya fad'a yana meyi wa Amal kallon rainin hankalin dayasa ta murgud'a mai baki. "So am here to say sorry and take full responsibility" ya numfasa "Ga magunanta nan" anan ya miqa wa Mami leathern inda ta amsa "Dr yace karku tada hankalinku she's going to be alright kuma gobe idan Allah ya kaimu zan dawo in maida ta asibitin don a sake dressing ankle natan kaman yadda likitan ya buk'ata. Za a cigaba da yin hakan na sati daga nan in shaa Allah k'afan zai warware." Kafin Mami da akayi ma bayani tayi magana Amal ta hau k'orafi.

   "Ni wallahi ban komawa asibitin" ta fad'a tana buga d'ayan k'afanta a k'asa stubbornly.

  "Rufa min baki do Allah!" Mami ta ce da ita amman still se gunguni takeyi dake sam bata tsoron idon Mami. "Allah sarki bawan Allah lallai ka cika d'an halas mun kuma gode sosai, ina me sake baka hak'uri kuma."

   "Ba komai Mami ya wuce nine da godiya."

   "Allah yima albarka Babana."

   "Ameen" ya amsa da murmushi kad'an.

   "Nace ba kar ka damu ba seka kuma dawowa bama anan tsallake gun wanzami zan kaita a sake duba k'afan nata gobe in shaa Allahu."

   "No Mami, I promised to take full responsibility so karki damu and here" ya fad'a yana ajiye ledojon a k'asa "Sakamakon hatsarin abubuwan da kika aiketa siya suka tarwatse so gasu I'm able to get some wad'anda ban samu ba kuma zan baku kud'in seku siya in kuka samu lokaci, I'm sorry" hannu ya zira a aljihun sa don ciro wallet nasa inda yaji wayam holy sh*t ashe ya baro sa acikin mota. "Excuse me please let me get my wallet."

    "Haba bawan Allah ai da ka bari, hakan ma mun gode wallahi ni na yafe sauran" fad'in Mami.

  "Ni ban yafe ba" cewar Amal wane da ita aka kasa, ko ta kanta Afzal beyi ba yayi saurin katse Mami dake shirin yima Amal fad'a "No Mami please I insist, ai hak'k'in kune."

   "Toh shikenan tunda kace haka mun gode" ta fad'a tare da kewayo da kallonta akan Amal "Ke tashi ki bi bayansa ba seya sake shigowa nan inba yayi sahu biyu tunda duk ke kika jawo komi" cewar Mami.

   "Taya ni na jawo? Ni na kaisa kad'eni?" Ta tambaya cike da rashin kunya.

   "Da bance kibar aiken ba se da yamma kika k'i?" Zata kuma magana Mami tayi yunk'urin gwa6e bakinta nan take tayi shiru. Afzal da yayi shiru yana kallon su ne ya nisanta yace, "Karki damu Mami, let her be."

   "A'a don Allah kar muyi haka da kai. "

  "Mami-"

   "Don Allah fa nace" hakan yasa yayi shiru.

  "Toh shikenan" ya fad'a a hankali.

  "Yauwa bari Baby ta bika seta amso kud'in tashi mana Baby" ta fad'a tana dawo da kallonta akan Baby dake faman zumbure-zumbure ko yunk'urin miqewa batayi ba. "Ko baki ji ni bane?"

   "Toh ai bazan iya tashi ba."

  "Uhn uhn fa Baby kin san ni."

  "Don kinga Papi bai nan ba? Allah ze dawo dashi kuma wallahi sena k'irga mai komi" ba don tana so ba ta shiga miqewa wanda k'arshe saida Mami ta taimaka mata, k'ingishi ta shigayi tana takawa a hankali. Murmushi Afzal yayi sannan ya shiga bin bayanta.

  "Toh gashi bawan Allah zaka tafi ban san sunanka ba." Kewayo wa yayi cike da ladabi sannan yace "Afzal."

  "Afzal" ta nanata "Sunan larabawa ga me k'iran su, masha Allah" ta fad'a acikin wasa. Murmusawa yayi sannan yayi mata sallama ya fice alokacin har Amal ta isa bakin k'ofa tana tsaye tana kallon yaran dake wasa akan layi.
   "Excuse me" yace da ita ganin tayi tsaye bakin k'ofan ba chance da ze wuce. Seda tayi muttering wasu kalamu chan k'asa iya jinta sannan taja gefe ya samu ya wuce. Bayan sa ta shiga bi sannan ta tsaya daga jikin wani bango a yayinda ya k'arisa gun motan nasa. Wallet d'in ya d'auko, dai-dai yazo bud'ewa kenan don sallamarta wayarsa dake inner aljihun suits jacket nasa ya shiga ringing. Ba tare da 6ata lokaci ba ya zaro, ganin Abba ke kira zuciyansa ya mugun har6awa yau ya shiga uku. Cike da fargaba ya d'aga sede kafin ya samu daman magana Abba ya riga sa.

   "Yanzu Afzal in kiraka sau biyu in ce maka ina neman ka as a matter of urgency shine har yanzu ban ganka ba? Ai ko bangon duniya kake yaci ace ka dawo war haka" daga yadda yake magana mutum zaisan ransa ya 6aci matuk'a ba shakka Abban nan nashi mutum ne mai gajan hak'uri.

   "Abba I'm so sorry-" katse sa Abba ya kuma yi  "Wallahi ban san ka da halin nan ba, bansan kuma meyasa kake hakan ba amman karka damu ba seka zo d'inba domin shi wanda yake neman ma maganan ma ya gaji da jiran ka ya tafi" daga fad'in haka ya katse wayan ba tare da ya basa daman magana ba. Hankalin Afzal ya mugun tashi, rabon shi da ya 6atawa Abba rai irin na yau ya juma, probably tunda yake yaro lokacin da bai gama gano darajan iyaye ba. Yau ina zaisa kansa? A kullum shi me ladabi ne game da umarnin Abba, a kullum Abba na alfahari dashi se gashi yau all because of wannan fitsararriya 'yar gudun hijirar ya 6atawa Abbansa rai to the extent da har Abba ya kashe waya a kansa abinda be ta6a yi ba. Yasani kafin Abba ya sauk'o ya soma mishi magana kuma se ranan da Allah ya nufa.

   Ranshi a murtuk'e ya bud'e wallet d'in be ma san iya adadin kud'in daya d'iba ba tsabaragen all he wanted at that moment was yaga kansa a gida ya samu daman bawa Abba hak'uri tun kafin lokaci ya k'ure.

  "Ke!" Ya daka mata tsawa wanda sanadin haka ta firgita. Tun da tasan kanta bayan wani PHE teacher'n su tun a JSS 3 ba wanda ya ta6a mata tsawa yakuma razana ta irin na yau. "Kinyi tsaye achan nine zan k'ariso miki da kud'in?" Ya jefa mata tambayar cike da tsiwa.

    "Malam dakata fa!" ta tsorata iya tsoro amman dogon bakinta baze barta tayi shiru ba "Haka kawai bazaka sauk'e min haushin da kakeji a ka ba, a dalilin meh? Don wani ya kiraka ya 6ata maka rai se ka hau huce zafin ka a kaina kana min masifa? Da ni nace ka kad'eni kokuwa ni nace ka kawo ni gida? Ra'ayin da ya saka yin all of that shi zai sa ka tako har nan ka bani kud'in da kace zaka baiwa Mami in kai mata" ta fad'a kai a tsaye ko tsoron yadda yake kallonta cike da haushi da tsana batayi. Duban time a wrist watch dake d'aure a hannunsa yayi ganin he is running out of time yasa shi fasa aikata abinda yayi niyyan mata in ba haka ba belt nasa yayi niyyan zara ya nad'a mata na jaki a gurin tunda a gidansu ba meyi mata hakan. K'arisawa spot da take tsayen yayi sede yarinyan naku ko motsawa batayi ba dukda chan k'asan zuciyarta kuwa ta gama tsorata. A duk tunaninta mari ze kai mata setaji ya damqo hannunta, damqan da tana iya rantsewa ba a ta6a mata irin sa ba ai bata san lokacin da ta shiga ihu ba. Ji tayi k'asusuwan ta suna k'ara, wannan wani irin k'arfi yake da shi? Toh ita kam ya agaza ya rufa mata asiri kafin ya karya mata d'an hannu, ace ga kariya ga targad'e? Bazata iya ba.

   "Naga alaman Allah ya had'aki da iyaye masu sanyin da ko tsawata miki basu iya yi as ko mey kikayi dai-dai ne a idansu kisani I'll not let you disrespect me and get away with it, bazan bar k'aramar k'waron da bata kai inyi immediate sibling da ita ba ta raina ni, ko ki iya bakinki ko na koya miki yin hakan, maras kunya kawai."

 Sosai idonta ya cika da k'walla don azaba, "Ni ka sake min hannu kuma kar ka sake sa min sunan iyaye cikin zancenka, musamman na Abba na saboda ya rasu" ta fad'a cike da k'arfin hali. Ganin fa baida niyyan sake ta tasa ihu "Mami!" A lokacin har hawayen na neman gangarowa. Se anan ya saketa cike da wulak'anci regardless of her condition, wanda da ace ba bango a kusa da ita data fad'i a k'asa. Hannunta yaja out of nowhere tare da tusa mata kud'in aciki sannan ya juya ya kama tafiya. Kafin ya isa gun mota har Amal ta zaro kud'in ta k'irga, dubu hud'u ta gani "Hey!" Ta danna mai kira amman yayi banza da ita se a karo na biyu, nan ma ba juyawa yayi ba tsayuwa kawai yayi, "Ce ma akayi Papi na ya rasa na ciyar damu ne ko na sha da zaka wani kama ka bada dubu hud'u na abinda be taka kara ya karya ba?" Se anan ya juyo yana kallonta ashe de dubu hud'u ya zara "Zan d'au dubu d'aya, ban sani ba ko canji ze rage amman idan har ya kasance hakan, I'll return your change for you ga sauran kud'in ka" nan ta zare dubu daga ciki tare da yin watsi da sauran a k'asa ta juya da k'ingishinta ta wuce layin gidansu leaving Afzal da baki wangalau a bud'e cike da mamaki, don shock k'wak'walwarsa tama kasa fahimtar dashi abinda wannan 'yar gudun hijirar ta masa. Ji yake as if ya cafko ta ya nad'a mata na jaki shin wannan ya iyayenta suka girmar da ita? Fitsara sekace 6era, besan na gida ba balle bak'o. Lallai ta guji had'uwansu, yanzu baiwa Abba hak'uri ne ke gabansa dako seta gommaci kid'a da karatu.




*~*~*~*~*~*~*~*~*~*
    So how was the chapter? One word for Amal?😂
  In shaa Allahu bayan sallan azumi kuma semu d'aura daga inda muka tsaya. Na sako pages biyun nan ne domin mutane irinsu Meela da Sumayyah masu shegen maita da tak'uri 😜 se kuma don wasu fans d'ina da suka d'au cewa na daina rubutun hausa gabad'aya. Wishing you all a faithful Ramadan ahead xoxo.

    RANA D'AYA
  #RD
   Love... miemiebee👄✨

No comments:

Post a Comment