Wednesday, 18 April 2018

RANA D'AYA

Post zena zuwa ne alhamis zuwa juma'ah in shaa Allah.

  BY MIEMIEBEE
  PAGE 08


   Haka kwanaki suka ta shud'ewa a yayyinda Afzal da Amal suke sake shak'uwa wane asalin 'yan uwan jini. Traditional smoothies d'innan ba wanda Amal bata yi mishi, yau ayi Aldeb, gobe Ginger, next day Zo6o. Shima sau dayawa yakan kaita gidan madara ko Sidis su sai mata chocolates, ice creams da makamancin hakan.

  Ta fannin Nazeefah kuwa Daddy be fasa da abinda ya d'aura ta akai ba, kafin azumi ya fita seda ta kaiwa Afzal abinci kusan sau hud'u ko biyar don haka itama Ummi tayi tunanin ya kamata Afzal yayi wa Nazeefah kayan sallah shima as a token of appreciation saidai ta fanninsa bayida niyyan hakan ko kad'an, Amal tasa kad'ai zai saiwa kayan Sallah ba wata fand'ararriyar Nazeefah ba. Yana cikin shirin zuwa gidansu Amal don kai mata kayakin da yayi niyya ne sega kwatsam Ummi ta fad'a cikin d'akin ko sallama yau babu.

  "Haba Ummi!" Yayi saurin fad'i "Taya zaki na shigo min d'aki ba sallama idan da kuma ban sanye da kaya fah?"

  "Seka godewa Allah uwarka ce ta shigo ba su Juliet ko Esther ba, speaking of ina shigo maka d'aki ba sallama wani abun kake 6oyewa?" Ta k'arisa tare da tsayawa ta gefen gadonsa.

  "Me kuma zan 6oye?" Ya amsa yana bin jikinsa da body spray.

  "Meye acikin leather'n chan?" Sauri yayi ze ja sede dake tafisa kusa da gadon ta rigasa d'agawa tare da zazzagewa akan gadon. Zani ta tarar wanda take da tabbacin super wax ne exclusive ma kuwa, da wata voil lace.

  "Iyyeehh!" taja numfashi tana binsa da kallo cike da k'in yarda wanda Afzal ya manna mata hasali yima yayi wane be san dashi takeyi ba.

  "Prince wannan kuma se ina?"

  "Wai kam Ummi ina ruwanki? Haa'a! Ni ki miyar min su cikin leather'n."

  "Lallai Prince ka girma tunda ka soma 6oye min al'amuranka wato kayi wata sabuwa awaje shine ko a sanar dani ita ko? Da kyau."

  "Kaman ya sabuwa a waje kuma?" Ya tambaya nan take.

  "Ai sarai kasan mey nake nufi wannan d'in ina zaka kai?"

  "Gidansu k'anwata" ya bata takaicaccen amsa.

  "K'anwa?" Ta nanata da mamaki "Kanwa fa kace Prince? Yaushe na haihu ban sani ba?"

  "God help me" ya furta can k'asa-k'asa. "Wai kam se wanda kuka fito ciki d'aya dashi ne ze zamo k'aninka?" Ya tambayeta.

  "Ni ba abinda nake nufi ba kenan" ta amsa had'e da kare kanta. "Amm-" katseta yayi a hankali "Kinga na farko Amal ba budurwata bace, ina yarinyan nan da na ta6a bigewa days back?"

   "Wacce tayi targad'en nan?"

  "Eh ita she's the one am referring to my sister" ya fayyace mata.

   "Ahhh ahhh!" Ta fad'a cike da neman tsokana "Kace tun daga nan ta sace maka zuciya!"

  "Ya Subhanallahi!" Yayi exclaiming a rud'e "When did I ever say that?"

    "Yo gashi alamu sun nuna da de 6oye-6oyen nan ka dena ka rok'eni in tayaka da addu'a."
       
   "Ummi please! Ni ba abinda yake tsakani na da Amal banda dangartakan ya da k'anwa so please kar maganan nan ya isa kunnen Abba."

  "Hmm Allah sa gaskiya de kake fad'i."

  "Ya ma riga ya sa don am telling you nothing but the truth" ya amsa ta yana mey manne bakin cuff links na rigansa.

  "Nide nace Allah ya sa don kuwa gashi har an sai mata kayan sallah ni uwar taka gabad'aya ko d'an kunne ba a sai mi ba."

  "Oh Ummin tawa akwai kishi, a tunanin ki har zan sai ma wata zani ban saya miki bane?" Wardrobe nasa ya bud'e ya ciro wata leather tare da miqa mata "Gashi open up" Da murmushi kwance fal a fuskanta cike da hanzari ta amsa tare da since bakin, super biyu ta tarar ciki wanda sukafi na Amal ma kyau seda wata had'ad'd'iyar purple lace me torches na white and black.

   "Awwn Prince duka nawa?"

  "Eh mana you deserve even more."

  "Gasu duk da torches na purple a jiki my favorite color."

   "Ummi ai duk wanda yace besan purple ne best color naki ba toh besanki bane."

   "Thank you so very much Prince Allah yayi maka albarka ya k'ara bud'i ya kuma sa albarka acikin al'amuranka sakallahu bil jannah."

  "Ameen your prayers keep me moving."

   "Suna tare da kai a kullum Babana."

  "I'm grateful bari inyi sauri yamma nayi."

  "Uhmm Prince nace Nazeefah fah?" Ta tambaya cike da gudun 6ata masa rai.

  "Ohhhh!" Yayi exclaiming tare da buga k'afansa a k'asa "Ummi please kibar zancen yarinyan chan she's not yet my responsibility kibari bayan na aureta ban yi mata kayan sallah ba seki min fad'a ki tilasta ni but not now please."

  "Ayyah Prince ai ko yanzun ma ba tilasta ka nake ba, har na kai insa Prince d'ina aikata abinda beyi niyyah bane? Naga kaman abune da ya kamata kuma ma ai yima kai ne, kana sane de da yadda take kawo maka abinci ba fashi ya kamata kai ma kayi mata wani abun in return kodan iyayenta ma" ta mai bayani a hankali yadda ransa baze 6aci ba.

   "Toh Ummi ni na aiketa? Ko ni nace lalle-lalle se ta kawo min abinci? Abincin da ba ci ma nake ba" ya fad'a ba tare da yasan yaushe ba.

  "Ba ci kake ba?? Innalillahi Prince!"

  "Ni ba abinda nake nufi ba kenan I mean" nan ya shiga kame-kame. "I mean ni inba girkin kiba ban k'oshiwa ko naci natan sena k'ara da naki a kai."

   "Da Allah chan! Ni zaka ma zak'in baki? Wato zubar da abincin kakeyi kullum ko?"

  "Itama lace da atamfan kikeso a sai mata kokuwa?" Ya tambayeta deliberately da niyyan canza topic of discussion d'in.

   "Kasan mey za'ayi ne? Tunda zaka fita yanzu kuma gashi yamma tayi why not ka kai mata nawan yaso seka sake siyo min wani ko zuwa gobe? Bana son a samu akasi."

  "Like seriously?" Ya tambayeta cike da mamaki "Abinda na sai wa mahaifiyata kike son in kai wa wata?"

  "Ai ni nace kayi karka damu all shall be well."

  "A'a nikam tunda ba firewa zatayi ba gobe idan na fita sena saya mata in tura akai mata."

  "Prince wai yaushe muka fara jayayya da kai ne? Nifa ban san ka da halin nan ba."

  "I'm sorry" yayi saurin bata hak'uri.

    "Ai Prince baya laifi nide alfarma nikeso kayi hak'uri ka kai wa yarinyan kayakin nan."

  "Duka ukun Ummi? Wallahi lace d'innan ba lalle ne asamu exact irinsa ba kuma ko da za'a samun ma ba exact color d'inba saboda wannan d'inma a online na gani na baiwa me kayan kud'i ya siyo min da ze tafi Dubai."

  "Ai ko daga ido ma ansan ba k'aramar lace bace wannan kuma nima banda niyyan baida wannan d'in dama atamfofin nike nufi."

  "Alright keep them aside bari in kira Juliet tazo ta kai mata."

  "Haba Juliet kuma Prince kai baka ga kullum ita da kanta take kawo maka kayan bud'a bakin ba?"

   "Ohhh! Ummi please."

  "Yi hak'uri d'an albarka d'an autan Abbansa kuma d'an gaban goshin Umminsa yi hak'uri" shiru yayi bece komi ba "Yau zan yi maka pepper soup na kifin nan da kakeso fah ko kar ayi?"

  "Ni bance ba" yayi saurin amsata "Naji zan kai mata."

  "Yauwa my charming Prince nagode ko? And please karka manta kace zaka tambaya min yarinyan nan da ta had'a maka aldeb na jiya."

  "Don't worry I'll ask her of it gidansu ma zani ai yanzu."

  "Laaa! karde itace Amal d'in?"

  "Toh da waye? She's the only sister I have."

  "Iyyeh!" Nan ta shiga yi mai wani irin kallo cike da neman tsokana da magana, shide be ce mata ko k'ala ba hasali bema damu da abinda take tunani akanta tsakaninsa da Amal ba saboda yasan a matsayin k'anwarsa ya d'auketa kamar yadda itama ta d'aukesa a matsayin yayanta. Dressing mirror ya nufa inda ya daidaita hulansa tsab sannan ya shiga feshe varieties na designer turarukan dake jere gaban mirron.

****

  Daga gefen gate na gidan Alhj Abdallah Afzal yayi parking motarsa inda yasa masu gadi suyi ma Nazeefah sallama, yana zaune cikin motarsa yana going through twitter feeds nasa yaji murya kaman na Daddy na kiransa. D'aga kan da zeyi suka yi ido hud'u. Fitowa yayi daga motar nasa take ya k'arisa inda na Daddy yake, nan Daddy ya bud'e k'ofa suka gaisa. Bayan gaisuwa yake tambayar Afzal dalilin dayasa be shiga ciki ba ya tsaya nan waje sekace wani bak'o.

   "Wallahi sauri nake ne shiyasa I'm sorry."

  "Allah sarki ba komai, gun Nazeefah kazo ne?"

  "Eh Daddy saqo nakeson in bata." Wani dad'i ne ya ziyarci zuciyan Daddy a tunaninsa gabad'aya abubuwa sun soma daidaita ne tsakanin Nazeefah da Afzal not knowing the actual situation.

  "Kuma shine take 6ata ma lokaci bayan gashi kace da akwai inda zaka zarce?"

  "Eh Daddy amman ba damuwa nima ban dad'e da zuwan ba."

  "Barin tura d'ayan me gadin ya kirat- yauwa gata nan ma." Ya sanar da Afzal sanda Nazeefah ke fitowa daga gate d'in tana sanye da bak'in hijab three quarter. "Ke haka akeyi ne Nazeefah seki ajiye bak'onki shiru haka?"

  "Daddy ina taya Mummy aiki ne a kitchen" tayi explaining cike da ladabi kaman ba ita ba. "Sannu da dawowa."

  "Yauwa sannu ki k'ariso Afzal yana son miki magana" ba musu ta nufi wajen motan Afzal daga baya-baya ta tsaya, ba don tanaso ba sedon idon Daddy data gani a kanta ta gaishe da Afzal harda d'an durk'usawa shima ganin idon Daddy yasanya sa amsa gaisuwan cike da walwala da murmushi seda yaga shigewan Daddy ciki sannan ya azo asalin fuskarsa. Motan nasa ya koma ciki ya fito da ledar "Gashi ki d'au d'aya ki bawa Mummy d'aya" ya sanar da ita ba tare da ya nuna damuwa ba. Mamaki ne ya mamaye zuciyan Nazeefah har ma ta mance yadda ake amsan abu gun mutum. Shiko ganin tana 6ata mar lokaci ya ajiye ledar kan bonnet na motan.

   Wai Afzal ne ze siya mata kayan sallah? Ta tsaya tana tambayar kanta. Hannu ta mik'a ta janye ledan izuwa 6angarenta tana mey shawaran yi masa godiya kokuwa.

  "Dont think twice about it" fad'in Afzal yana mey tsamota daga cikin duniyan tunanin data fad'a. "Ummi ne tace lalle-lalle sena kawo miki wani abun kodan bautan kawo min abincin da ban rok'a ba da kikeyi gudun kar ki tashi a tutan babu if not banida ra'ayin hakan sam."

  Hamdala ta saki na k'in masa godiyan da tayi, dan kuwa da tayi da taji kunya. Numfashi taja tace, "Kaman ka sani there is absolutely nothing in this world daze sani sanya wani abinda ka siyo da hannunka kokuwa kud'inka" ta fad'a cike da gadara da rashin kunya.

  Murmusawa yayi ta gefe sannan lokaci guda ya tamk'e fuskan nan "Then that makes us even saboda ko wuta da aljannah aka bani bazan iya cin abinda kika girka ba, hannun da sama da maza goma sun rik'e sunyi gadamansu dashi. So idan ma shirin kawo wani tarkacen kike yau I'd better make your work easier for you tun a bakin gate ki tsaya ki rabawa securities because it'll be more of a westage idan suka shigo site d'ina cause tsab a toilet zan juye kamar yadda na saba inyi flushing." Duk yadda Nazeefah taso 6oye mamakinta ta kasa, lallai ya cika d'an halas.

  "You can close back your mouth gudun kar flies su shiga my warmest regards to Khaleefah and Mummy" yana kaiwa nan ya bud'e motansa ya ja yabar gun da d'ankaren gudu har yana neman kad'a mata k'ura.

  Gidansu Amal ya wuce inda ya tarar da ita da Papi dake shirin fita shima. Taburma Amal ta shimfid'a masa inda duk suka zauna suka gaisa, bayan gaisuwa Afzal ya mik'a wa Papi ledan dake hannunsa. Cike da jin dad'i Papi ya bud'e ledar se ganin kayaki yayi ba adadi, "Wai wai wai Baba na da wahala haka?" Ya tambayi Afzal cike da k'in yarda a yayinda yake fito da kayakin d'aya bayan d'aya. Ashe gogan naku zannuwa biyu ya sai wa Amal sannan da lace nata har ma da takalmi da jaka, d'ankunne dasu sark'a bugu da k'ari harma da d'inkekken hijabin da ze shiga da zannuwan nata. Se kuma atamfa super exclusive wa Mami da babban gezna wa Papi amman ya 6oye wa Ummi saboda yasani da tagani zata hau fassara masa niyya while actually shi bada wata manufar yayi ba illa don k'anwarsa ce.

  "Kai Afzal mun gode mun gode k'warai wallahi bansan ta ina zamu fara ma godiya ba" Fad'in Papi da se d'aga zannuwan yake yana bi da kallo. Amal kam don yadda mamaki ya mamayeta tama kasa magana banda zuba ma kayakin ido da tayi tana mey mamakin anya kuwa ita zata sa kayakin nan? "Baby bakiga kayaki bane da baza ki bud'e baki ba kiyi godiya?" Papi ya tambayeta.

   Kai ta kad'a tana mey dawo da kanta asalin rayuwa daga duniyar tunanin data fad'a.
 "Yaya?! Duka wannan namu?" ta tambaya tana mey nuna kayakin.

  "Ji Amal" ya fad'a had'e da murtuk'e gira "Kin ta6a jin inda babban yaya yasai wa kansa kayan sallah be yi wa k'anwarsa ba?"

  Cike da kunya ta kad'a kanta "Yaya mun gode sosai Allah k'ara bud'i ya kuma miyar maka da gidan aljannah."

  "Ameen" Papi ya amsa a fili a yayinda Afzal ya amsa a zuciya.

   "Gaskiya Afzal ba muda bakin yima godiya sai dai muce Allah ya biya ya k'ara bud'i godiya ba adadi Allah ya sak'a ya shige maka gaba aduk abinda kake ciki kake kuma nema."

  "Ameen Papi please godiyan ya isa haka ana tare ai."

  "Toh masha Allah, Baby mai da kayakin ciki kinji kar k'ura ya 6ata" ya sanar da ita a yayinda yake k'ok'arin mik'ewa "Zan fita zani kasuwa sena dawo" ya sanar da Afzal.

  "Papi idan ba sauri kake ba daman inaso muyi wata magana da kai ne" Afzal yayi saurin tanka shi.

  "A'a ko kad'an Babana bismillah" nan ya koma ya zauna.

  "Thank you, dama batun Amal ne munyi magana da ita kuma tace tana son ta koma makarantar boko idan har kaga hakan ba matsala I am willing to provide for her education se tayi sitting jamb muyi mata applying jami'a nan Unimaid."

  "Jami'ah! Allah sarki babana nauyin baze zo yayi maka yawa ba kuwa? Dan Allah karka damu nima ina kan tara mata kud'i ne ko nan Ramat ta shiga don Allah karka tada hankalinka."

  "Papi ni izinin ka kawai nake nema karka damu da komai."

 "Baby zaki deyi karatu baza kisa Yayan ki asaran kud'in makaranta bako?" Ya juyo yana kallon Amal data had'e gira. Lalle ma Papi sekace besan k'ok'arinta ba yake fad'a mata haka gaban Afzal, ai se Afzal ya d'au ita d'in doluwa ce.

   Daga bisani tace, "Papi da gan-gan ka fad'i hakan donka kunyatani idon Yaya ko? Allah se in d'auko report sheets d'ina tun daga JSS1 in nuna mishi kaima kasan bana wasa da karatu."

  "Ah ah mamana na kaina yi hak'uri maida wuk'an wasa nike." Murmushi Afzal ya saki yana mey sha'awan relationship dake tsakanin Amal da Papinta.

  "Toh Afzal nide ba abinda zance sede muyi ma addu'a Allah ya biyaka. Rashin shiganta babbar makaranta ba k'aramin damuna yake ba a matsayina na mey kula da ita barin ma yadda take da son karatu, tun tana damuna da cewa tanason ta shiga jami'a har tagaji ta dena saboda rashin samu, ba yabon kai ba amman uwata akwai ja inada tabbacin cewa bazata baka kunya ba, kuma nima zan sa ido sosai akanta inga ta cika maka burin ka nason ganin tayi karatun nan, Allah sak'a maka da alheri."

  "Ameen Papi nine da godiya daka amince da wannan k'udiri nawa zan d'anyi tambayoyi kad'an in shaa Allahu duk abinda akwai zan sanar dakai."

  "Toh toh Babana mungode mungode sosai Allah kad'ai ze biyaka shikenan ko akwai wata maganar kuma?"

  "A'a Papi kana iya tafiya nagode da ka bani lokacin ka."

  "Toh madallah madallah" ya fad'a yana mik'ewa.

  "Toh a dawo lafiya" cewan Afzal.

  "Allah tsare Papi" inji Amal.

  "Ameen Afzal ameen uwata, mungode sosai sosai ka gaishe da gida idan ka koma."

  "In shaa Allah" Da haka ya fice ya rage Amal da Afzal kad'ai kasancewar Mami ta shiga mak'ota.

  "Yaya wanne ne nawa?" Ta tambayesa cike da jin dad'i tana mey zazzago da kayakin. Murmusawa yayi ganin yadda ta kasa 6oye farin cikinta. Atamfan Mami yaja gefe da kuma shaddan Papi sannan yace, "Duka wannan naki ne."

  "Dagaske Yaya? Da wannan da wannan da wannan duka?" Ta tambaya cike da k'in yarda tana mey bin kayakin da yatsarta tana nunawa.

  "Sosai ma."

  "Yaya you're truly an angel thank you so much."

  "You're welcome Lily" ya amsa yana mey miyar mata da murmushin da take masa.

  "Toh ni da irin abubuwan nan da kake min dasu Papi me muke dashi da zamu iya baka in return?"

  "Addu'o'in ku kad'ai ya isheni Lily."

  "Are you sure Yaya?"

  "Absolutely sure Lily."

  "Toh shikenan Yaya ga addu'o'ina na yau da kullum a gareka; Allah sak'a maka da alheri, ya k'ara maka bud'i yasa ka cimma duk wani burinka a doron k'asa, Allah ya baka mace ta gari da 'ya'ya nagari ba masu rashin kunya da taurin kai kaman ni ba fa" Dariya sosai Afzal ya tsaya yi a yayinda ta cigaba "Allah sa ka gama da duniya lafiya, ya baka gidan aljannah kuma, kai Allah ya baka duk wani abinda kakeso tun a zuci ba seka furta shi waje ba." Shiru ta yi don jin yadda Afzal keta dariya tun zamansu dashi bata ta6a ganinsa yana dariya haka ba, ashe de haka dariya yake kar6ansa shine baya yi? Cankwad'i! aikuwa ta rik'a sashi dariya kenan kullum yanayi.

  "Ka gama dariyar baka amsa da ameen ba."

  "LOL ameen Lily kema Allah ya miyar miki da duka addu'o'in da kikayi min."

  "Hmm ameen da babban murya kaga barin surfa waken nan kafin Mami ta shigo ta balbale ni tun d'azun tace inyi na tsaya ina shirme."

  "Kafin nan Ummi tace tanason ki koya mata yadda akeyin aldeb d'innan Lily na rage mata na jiya bakiga yadda tayita santinsa ba."

  "Kai Yaya dagaske?" Gira ya d'age mata "Wai yayi dad'i tace?" Ta tambaya zealously.

  "Sosai ma."

  "Ai dama nasan na iya girki Mami ce kullum ke kusheni."

  "LOL that is because tanaso ki k'ara himma ne don't blame her it's what mothers do."

  "Hmm toh kasan me za'ayi? Barinje in kira Mami nan mak'ota tayi hak'uri tayi sirfen waken sena had'a wa Ummi da kai aldeb d'in ai idan nayi a gabanka zaka gane procedures d'in idan ka koma gida se kayi mata bayani ba?" Shiru Afzal yayi yana nazari shi banda dafa indomie, tafasa ruwa, farar shinkafa ko spaghetti da macroni anya akwai wani abinda ya iya?

  "Kode Yayana be iya girki bane sam?" Ta tambayesa cike da neman tsokana.

  "Waya fad'a miki?" Ya wani 6ata rai yana cin fuska.

  "Toh naji kayi shiru."

  "Of course, how do you expect me inje in fara yima Ummi bayanin yadda ake had'a aldeb mace ne ni? Kede yanzu ki bani number'n Mami in naje gida sena had'aku kiyi mata bayanin ta waya."

   "Haha nide na gane Yaya ajebo ne be iya komi a harkan kitchen ba."

  "Na yarda fad'i koma mey ba shi zey sa in amince da k'udirinki ba."

  "Toh shikenan Yayana na kaina ai ni duk abinda ka fad'a ya zauna se ayi hakan." Bece da ita komi ba yayin da ta shiga ciro ingredients da zata buk'ata tsakar gidan, tana cikin taran ruwa daga famfo sega Mami ta shigo. Sosai tayi murnan ganin Afzal, bayan sun gaisa Amal ta fito mata da kayakin da Afzal ya kawo musu ta nuna mata, da godiya na kisa kam daya kashe Afzal a wajen saboda kalan godiyan da Mami tayita masa.

   Bayan ta mai da kayakin ciki ta fito ta tarar da Amal na aiki daban maimakon sarrafa musu waken da zatayi. Ta soma k'orafi kenan Afzal ya shiga bata hak'uri had'e dayi mata bayanin lamarin cewa Ummi ce keson aldeb d'in. Ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga surfen da kanta yayinda Amal ta cigaba da had'a aldeb d'in. Ido Afzal ya k'ura mata yana mey sa hankalinsa sosai game da duk wani abinda takeyi ko da ze iya fahimta yayi ma Ummi bayani ko dan kar Amal tayi underestimating nasa.

   Abu d'aya daya karanchi tattare da Amal shine kominta tsaf-tsaf take yinsa ba dotti bale k'azanta hakan ba k'aramin burgesa yayi ba, a rayuwa ya washi mutum me shegen daud'a da k'azanta kasancewar acikin tsafta ya girma, mutane har suna cewa tsaftan Ummi yayi yawa, shara idan batayi atleast sau biyu ko uku a rana ba bata jin dad'i.

   A haka har Amal ta samu ta gama ta d'ura masa cikin manya-manyan silver flasks guda biyu d'aya nasa wai d'aya na Ummi.

   Kud'i ya k'irga yasa a hannun Mami cewa suyi d'inkin kayakin nasu dashi. Wayyo Mami ta ma rasa ina zata sa kanta, albarka tayita sa masa sannan suka rakasa har inda yayi parking motarsa, bayan ta mishi asha ruwa lafiya ta koma ciki ta barsa shi kad'ai da Amal.

 "Here press Mami's number bayan ansha ruwa zan had'aku da Ummi se kiyi mata bayani" ya fad'a yana mey mik'a wa Amal wayansa da ta amsa da 'Toh.' Hannu na 6ari ta mik'a ta amsa tana mey fatan Allah ya kawo mata ranar da zatayi wayar kanta me k'aton screen kaman wannan ko shegiyar Bintun ajinsu na islamiyya zata shiga hankalinta ta daina yi musu yanga da wata k'aramar infinix nata da bai iya zama cikin jaka ba sede akan table don a nunawa 'yan aji ana da waya. Bayan ta zuba ta miyar masa da wayan inda yayi saving.

  "Toh Lily ba-bye."

  "Mungode Yaya asha ruwa lafiya."

  Murmushi kad'ai ya saki mata yayinda ya bud'e murfin motan ya shiga, se da taga ficewansa sannan tabi lungun gidansu ta koma.

****
BAYAN SHAN RUWA, GIDAN ALHJ AHMAD AMIN.

   "Ni fa ban yarda ba kuma bazan yarda ba in zaka kira min yarinya kawai ka kira tayi min bayani da kanta dududu banda tafasa ruwa mey ka iya da zaka wani cemin ka iya had'a aldeb me dad'i irin na Amal in yarda" Fad'in Ummi dake zaune a gefen Afzal akan kujera a parlourn site nasa.

  "Am serious Ummi a ido na ta had'a and I did observed her closely."

  "Oho nide kiramun ita se naji daga bakinta zan amince, ba ka amshi lambarta kona mahaifiyarta ba? Call her up for me."

  "Fine!" Ya fad'a aggressively tare da dannawa lamban Mami kira saida ya kusan tsinkewa aka d'aga. "Assalamu alaikum" yaji siririyar muryar data d'aga ta fad'a. For a moment ya shiga duhu yade san muryan Mami ba haka yake ba, na Amal shigen hakan ne seda kuma wannan d'in har yana son fin natan zak'i.

  "Yaya?" Ta kirasa wanda hakan ya tabbatar masa da kokonton da yake.

  "Na'am Lily" ya amsa yayinda Ummi ta zura masa.

  "Ina yini? An sha ruwa lafiya?"

  "Lafiya Alhamdulillah ya gida?"

  "Lafiya k'alau ya Ummi?"

  "She's okay ita ma ke son miki magana kafin nan Lily aldeb d'innan bada tsamiya, sugar, ruwa..." nan ya shiga irgo duka ingredients d'in sannan kuma da procedures d'in, sosai Amal ta sha mamakin yadda ya rik'e komi dai-dai dukda fad'in sau d'aya aka ta6a had'awa a gabansa.

    "Wow! Impressive kai Yaya na akwai k'ok'ari ai kuwa ka bada procedures din dai-dai sede tsamiyan da ruwan zafi ake jik'a sa kuma sugar'n ma ba raw one ake sawa direct a ciki ba se an narkar dashi."

  "Ai na fad'a seda na fad'a maka narkar da sugar'n nan ake kak'i yarda Pff" nan Ummi ta shiga yi masa gwalo.

  "Whatever ai nayi k'ok'ari for goodness sake yau fa na fara ganin yadda akeyi."

  "Eh sugar'n ma ana iya sa shi direct amman narkekken yafi fita ne" Amal dataji Ummi sama-sama ta waya ta amsa. Gwalo ya shiga yima Ummi shima "Pff to you! Kin deji da kunnen ki a hakan ma ana iya sawa."

  "Kai Yaya bade gwalo kake yima Ummin namu ba?" Ta tambayesa "D'an bata mu gaisa."

  "Barshi Amal 'yata gwalo yake min" Ummi ta amsa tana matsowa kusa da wayan.

  "Toh bata mu gaisa."

  "Nak'i, ke bakiji sanda take min gwalon ba itama?"

  "Yi hak'uri toh ka bata" ba gardama ya mik'awa Ummi wayan inda suka gaisa take ta yaba aldeb na Amal wanda har ahakan yasata kunya sosai.

  "Ai da na bi procedures na Prince da nayi kwa6a" For a moment kan Amal ya d'aure karde sunan da ake kiran Yaya dashi kenan a gida Prince? Ta tambayi kanta, lallai kuwa d'an gata ne. "Kai Ummi ai yayi k'ok'ari" ta amsa cike da wasa.

  "Bani waya na Ummi bani!" Ya fad'a trying to sound serious. Da sauri ta tare hannunsa "Kinsan kuwa banda tafasa ruwan zafi ba abinda ya iya? Taya mutumin da ko jollof be iya dafawa ba ze ce min ya iya had'a aldeb kuma in yarda, 'yata is it possible?" Dariya sosai Amal tasa har tana sark'ewa Afzal da ya kai har maqora se harara yake dannawa Ummi yayinda take tayi masa gwalo. Taya zata fad'awa Amal bai iya girki ba? So take ta raina sa?

  "Ai fa ba laifinki bane nine nan na had'aku ai" yace da ita yana girgiza kai.

  "Kinji Yayanki yamun fushi ko ki basa hak'uri" Ummi tace da Amal dake ta faman yi musu dariya tun d'azu.

  "Laaa yayi mana hak'uri don Allah ai bamu iyawa da fushin Yaya, Yaya?"

  "Gashi amshi k'anwarka na son yi maka magana."

   "Nak'i" ya amsa ba walwala "Ni d'agani in mik'e idan kun gama wayan naku ki kawo min wayana ciki ko ki kirani inzo in kar6a." Kafin ya kaiga mik'ewa Ummi ta danneshi "Haba Prince yi hak'uri mana."

  "Toh Ummi seda safe, ki sake yiwa Yaya godiya sosai dan Allah munga kaya mun gode Mami tac-" wabce wayan yayi daga gun Ummi da sauri kafin Amal ta k'arisa zancenta had'e da katsewa yana mamakin dogon baki irin na Amal se kace bata san halin Ummi ba.

  "Ya haka Prince?"

 "Babu d'agani nikam."

 "Tsaya ma tukun wato ba wa ita kad'ai ka sai wa kayan sallan ba harda iyayenta ko?" Shiru yayi tamkar be jita ba, "Hmm su Prince an fad'a kogin soyayya."

   "God help me! Ni wallahi saboda irin suratan nan naki nak'i nuna miki kayakin duka baga irinta ba" ya fad'a a tak'ure.

  "Aww ashe da gaske ne ka sai wa iyayenta kayan."

  "Eh na sai musu shikenan kin huta?"

  "Prince jokes aside kode son yarinyan nan kake ne amman ka kasa ganewa har yanzu?"

  "Haba Ummi! Taya zan so Amal please? Ai banyi adalci ba kenan."

   "Kamar ya bakayi adalci ba?"

  "For goodness sake a matsayin yayanta ta d'auke ni, ta na gani na da k'ima da daraja tana girmama ni kawai don ni na kawo rashin halacci da kunya duniya se in hau sonta? It's not possible."

  "Kana nufin in ba don wannan dalilin ba zaka iya sonta kenan?"

  "God help me!" Ya furta unbelievably "No that is not my point you know what? Let's just drop this topic" ya fad'a ransa na soma 6aci.

  "Hmm tayi tsami maji."

  "Ummi please kidena blabbing d'innan haka Amal is just my sister there is no any other feeling attatched to it" ya fad'a cikin tattausar murya. Shiru Ummi tayi bata kuma cewa komi ba ganin yadda ransa ke 6aci.


  ~•. .•~        ~•. .•~        ~•. .•~      ~•. .•~

     Bayan Sallah da k'imanin wata biyu dai-dai da lokacin watan Zul~Hijjah ta kama kenan Afzal da Ummi suka wuce Saudi wanda tafiyansu yazo dai-dai da na Nazeefah, Mummy da Khaleefah. A hotel d'aya duk suka sauk'a inda Khaleefah da Afzal suka had'a d'aki, Mummy, Ummi da Nazeefah ma haka. Kusan kullum tare suke fita suyi Ibadunsu har Allah ya kawo su k'arshen aikin Hajji. Ana jibi zasu juya ne Ummi tayita insisting cewa se Afzal ya kai Nazeefah shopping kar Mummy tayi zaton lallai-lallai tilasta masa akayi batun auren. Seda suka kusan haurawa sama Afzal ya amince. Bayan ya fito daga wanka, ya shafa lotions nasa sannan ya zira d'aya daga cikin expensive jallabiyan daya sissiya ya feffeshe jikinsa jak'ab da turare sannan ya tattara wayoyinsa.

  "Khaleefah kace bazaka bimu ba? Da Nazeefah zamu fita fa" ya sanar da Khaleefah dake mik'e akan gado se faman buga game na world tip yake.

  "Friend d'ina zezo za muje muyi playing video game kuje sekun dawo."

  "Alright make sure you lock the door idan zaka fita."

  "Toh Uncle Afzal Allah ya kare." Da haka ya fice ya sauk'a reception a k'asa. Numban Nazeefah da Ummi tayi masa saving about last two weeks yayi scrolling yakai kai amman bai jin ze iya kiranta. Bayan tsawon lokacin daya d'auka yana nazari k'arshe ya yanke hukuncin kiran Mummy. Bayan ta d'aga sun gaisa yake sanar da ita cewa yana reception yana jiran Nazeefah yana son su d'an fita yau, yayita trying layinta amman bai shiga.

   "Allah sarki halan network ne don gata ma a gefe na bari yanzun nan zata sauk'o sannu ko Babana."

   "Yauwa Mummy thank you" da haka ya katse.

  "Nazeefah maza tashi ki shirya Afzal na jiranki a reception."

  "Mey zey min?" Tayi saurin tambaya had'e da d'ago kanta.

   "Jimin tambaya yace yana son ku fita go meet him downstairs."

  "Mummy ni wallahi da kince mishi na fita bana nan."

  "Dalili? Yanzu har yaro yayi creating time miki ki tsaya kina batun banza?" Itade Nazeefah bata kuma cewa komi ba amman tasan tabbas inma Ummi ce tasa sa na dole kokuwa yana shirin yi mata wani mumunan abun. "Ba zaki mik'e bane?"

  "Ba naji ba" ta amsa a tak'ure. Da haka ta kimtsa ta fice inda ta tarar da shi da wasu yaran larabawa se faman wasa sukeyi. Sallama tayi masa wanda se da ya gama 6ata mata lokacin duniya sannan ya amsa. Maimakon ya sallami yaran su tafi inda zasu, no wasan suka cigaba dayi yabar Nazeefah tsaye gun kaman ta6arya, seda ya tabbata ta gaji sannan ya sallami yaran ya mik'e. Don kanta ta shiga bin bayansa dan kuwa beyi niyyan yi mata magana ba.

   A mall suka tsaya inda ya d'au trolley tare da ce mata "Pick whatever it is you want I'm doing this because of Ummi so karki kawo tunanin wani abun a ranki." Daga fad'in haka yaja nasa ya fice ya shiga shopping. Tafi minti biyu tsaye wajen sannan daga bisani taja trolley'n ta shiga kwasan duk abinda yazo hanyarta da abinda zatayi amfani da shi da wanda bata ma san meye shi ba komi kawai d'auka takeyi har Afzal ya gama kwasan abinda ze kwasa Nazeefah bata gama ba se chan ana cikin billing masa abubuwan da ya siya se gata nan cike da trolley tazo ta tsaya bayansa. Murmusawa yayi ba tare da yace da ita komi ba.

  Kayakin nasa ta leqa ciki sede da mamaki taga yawancin kayan 'yan mata ya kwasa wanda ta nada tabbacin bana Ummi bane gashi bawai k'anwa ko ya yake dashi ba bale ace nasu ne, toh na waye ne? Kode budurwa yake dashi?? Toh ma ina ruwanta? Kanta ta kawar ta maido da kallonta akan wayarta har izuwa lokacin da billing ya iso kanta. Kud'in abubuwan data siya yayi ninkin na Afzal biyu, da gangan tayi hakan dama, fatanta kawai ace kud'insa ya kasa ta biya wa kanta tasasa jin kunya cikin mutane sede kash! Credit card nasa kawai taga ya zaro ya mik'a wa mutumin inda yayi debiting nasa suka miyar masa da abunsa, har maqora abin ya kai Nazeefah sam ba haka ta so ba. Acikin manya-manyan shopping bags aka sanya musu kayakin nasu suka fito. A bakin k'ofar Nazeefah ta tarar da beggers masu rok'o d'innan tsaye suna neman taimako, ledojin nata gabad'aya ta dank'a musu lokacinda taga Afzal ya kewayo yana kallonta.

  Ya sha mamaki sosai amman yayi k'ok'arin 6oyewa, taxi d'in ya bud'e ya shiga tare da cewa driver'n su tafi, sa6anin tahowansu a rarrabe suka koma. Ko a babu itama tasan tayi mishi ba dad'i yau, a cigaba a hakan aga wa ze yi surrender.

   ***
   Afzal ne mik'e kan gadon d'akinsu da Khaleefah se tunanin abinda Nazeefah tayi masa yake yana mey nazarin mey zeyi mata wanda zataji zafinsa haka itama a yayinda wata zuciyar ke cey masa kawai ya barta yaci girma sede yana ganin da k'yar idan ze iya. Ana cikin haka ne wayansa dake kife akan cikinsa ya shiga ruri, duban wa da zeyi ya tarar da Nigerian number, be kawo wani tunanin ba a ransa ya d'aga a tunaninsa gabad'aya ma Sultan ne sede ya tarar da muryar mace, macen ma Amal.
  Yau akeyinta, bema san ta ina ze fara yi mata bayani ba saboda ko sanar da ita cewa zasa aikin Hajj beyi ba rabonsu tun kafin ya taho Saudi yau kusan sati uku kenan. Ma ya akayi ta samu numbansa? Katse wayar yayi gudun kar kud'inta ya k'are sannan ya kirata back.

   "Lily?"

  "Na'am Yaya ka kyauta min kenan? Ai kam yanzu na tabbata ni ba Lilir ka bace kamar yadda kake fad'a tunda har zaka aikin Hajji amman baka sanar dani ba."

   "Lily ba haka bane."

  "Toh yaya ne Yaya? Kawai sena dena jinka ga layinka kullum switched off hankalina du yabi ya tashi haka su Papi ma gashi ban san gidanku ba, last week naje office naka nake tambayarka sukace kayi tafiya se yau kawai Allah ya had'a ni da Ya Sultan yake fad'a min wai Hajj ka tafi sannan ya bani numbanka truly am very disappointed."

  "Yi hak'uri kinji Lily? I know I've offended you ni kaina bansan meya hanani sanar dake ba but I'm sorry."

  "Saboda baka damu dani bane mana inda kayi ai da ka sanar dani."

  "Kema kinsan that's not true I do care about you Lily."

"Uhmm" tace kad'ai.

   "Baki hak'ura ba?"

  "Ai Yaya baya laifi" ta fad'a tana murmushi.

  "Masha Allah that's my Lily ya kike toh?"

  "Lafiya Alhamdulillah ya Ibada kun kammala ko? Allah yasa kar6e66iya ce."

  "Eh Lily ameen, jibi ma in shaa Allah zamu juyo, anyi sallah lafiya?"

  "Lafiya k'alau though I miss having you around."

  "I miss you even more Lily yasu Mami da Papi?"

  "Duk lafiyansu suna gaisheka."

  "Ina amsawa my regards, ya karatu?"

  "Gashi muna ta fama da tilawa."

  "Allah ya taimaka guess what?"

  "Ameen, tell me Yaya I'm a bad guesser."

  "Alright digital Qur'an na sai miki na k'ira'a Al~Sudais complete."

   "Kai Yaya! Dagaske!" Tayi exclaiming yayinda ta tsinci kanta cikin farin ciki maras misaltuwa. "Kaman kuwa kasan k'ira'an Sudais nake bi nake kuma son koya."

   "Ai kin riga ma kin iya Lily sede kice kina son sake k'warewa."

  "Kai Yaya! Har yaushe ka sani?"

 "Am serious, there was a day naje gida na tarar dake kina karatu so I stayed back and listened to you as you recite."

  "Kai Yaya har kasa naji kunya."

  "Sosai fah Lily nan na gano k'ira'ar Sudais kike bi and masha Allah kin iya sosai."

  "Thank you Yaya."

  "You're welcome karatun boko fa kina d'an tab'awa ko?"

  "Eh wai February zamuyi Jamb ko?"

  "Eh in Allah ya yarda."

  "Ina d'an ta6awa amman akwai wasu abubuwan dana d'an manta a physics da chemistry kasan it's been long banbi ta kansu ba."

  "Don't worry idan na dawo I'll help you out."
 
  "Toh Allah ya dawo mana da ku lafiya."

  "Aameen."
 
  "Amman Yaya dama ba commercial class kayi ba?"

  "Waya fad'a miki? I was once a science student."

  "Shine kuma kake aikin banki?"

  "Ai kowa ma zey iya aikin banki Lily ba se lalle wanda ya karanta accouting ko economics ba kuma kinga ni da bank of agriculture nake aiki."
 
  "Agric ka karanta kenan?"

  "Yes se nayi specializing a Horticulture and Agronomy."

  "Wow! I'm impressed" hira sosai suka tayi se kusan k'arfe goma wanda yake dai-dai da k'arfe sha biyu a k'asar Nigeria Afzal yayi tunanin suyi sallama kodan Amal ta samu tayi bacci, bayan seda safen da tayi masa ya jira tayi hanging sannan ya ajiye wayan a kan side drawer. Daidaita wa Khaleefah dake ta faman bacci blanket yayi sannan ya mik'e ya shiga bayi ya watsa ruwa had'e da d'auro alwalan bacci ya dawo ya kwanta a gefensa.


 ~•. .•~       ~•. .•~       ~•. .•~      ~•. .•~

    Da dawowansu Afzal da sati biyu kayakin su na Cago suka iso nan yayi sorting out tsaraban da yayi ma mutanen hannun damansa ciki harda na Amal dasu Mami. Na Sultan ya soma kaiwa sannan na colleagues nasa a office. Daga can ya zarce gidansu Amal har ya soma sabawa da 'yan unguwa saboda yawan shiga da fitan da yakeyi. Parking yayi suka gaisa da 'yan bakin shago inda suke tambayarsa ko lafiya kwana biyu shiru yake sanar dasu cewa tafiya yayi.

    Da kansa ya fito da ledojin har zuwa bakin k'ofar gidansu Amal inda ya shiga had'e da yin sallama saidai tun daga bakin k'ofar yake jin hayaniya, kasa kunnen da zeyi ya jiyo muryan Mami da ihun Amal da hanzari ya k'arisa ciki ya tarar dasu se kuje-kuje suke yayinda Mami ke rik'e da tsumagiya tana bin Amal da keta zagaya tsakar gidan. Mami ce ta soma yin tozali da idon Afzal don haka tayi saurin dakatar da abinda takeyi wanda hakan yasa Amal daina ihun da take ta faman yi.

   "Afzal??" Mami ta kira sunansa cike da k'in yarda.

  "Na'am Mami" ya amsa. Amal kam don mamaki da kunya tama kasa magana banda raba idon da takeyi.

  "Wai! Wai! Lale lale mutanen Saudiya sannu da zuwa sannu da zuwa, Baby d'auko tabarma ki shimfid'a masa sannu da zuwa Baba na, sannu da zuwa" Tafiya take wane wanda k'wai ya fashe mata a ciki har ta isa bayan k'ofan d'akin Papi ta d'auko tabaramar.

   "Zo ki shimfid'a a nan" cewar Mami tana mey mata nuni da inda take tsaye. K'arisawa tayi ta shimfid'a ta kai ga d'agowa kenan Mami dake fakonta ta sauk'e mata tsumagiyan zuwat a baya da iya k'arfin ta, wani irin rkicaccen ihu Amal ta saki yayinda ta shiga susa bayan nata take tana kuka.

    "Subhanallahi!" Afzal daya zame shedan yadda tsumagiyar ta sauk'a da k'arfi akan bayan Amal yayi saurin furtawa "Dan Allah Mami kiyi hak'uri" be san lokacin da ya sake ledojin dake hannayensa ba a k'asa tare da shiga tsakanin Mami dake shirin sake kaiwa Amal wani zanan yayinda Amal ke ta faman kuka.

   "Ba zaki rufa ma mutane k'aton bakin nan bako?" Mami ta tambayeta tana neman bin ta gefen Afzal don kuma sauk'e wa Amal wani zanan wanda da sauri Afzal yasa hannu ya k'wace bulalan yana mey bawa Mami hak'uri.

  "Afzal don Allah ka barni da yarinyan nan yau seta fad'amun waya haifi wani tsakani na da ita a gidan nan."

  "Kiyi hak'uri Mami beyi zafi haka ba yi hak'uri."

  "Haba! Wace erin 'ya ce bata jin magana haka? Ba sa'anninki bane suke aure a k'auye amman don an barki anan kina girman jaki kina abinda kika ga dama zaki soma wuce gona da iri? Wancan ma a gefe amman ace kullum sekin k'ona min miya idan nace ki kula da shi? Kinada kud'in sake min wata cafanin ne?" Shiru Amal dake la6e bayan Afzal tayi se faman share hawayen dake ta faman zubo mata take da hannunta.

   "Ba dake nake bane?" Nan Mami tayi kaman zata ture Afzal don ta jawo Amal daga bayansa ta gaggaura mata mari saidai Afzal be bar aukuwan hakan ba as da sauri ya janye Amal sukayi baya yana kareta. "Kice mata tayi hak'uri" ya juyo yana kallon Amal saidai ko d'ago kai ta kallesa batayi ba bale tayi yadda yace se faman kukan zucin da takeyi tana hawaye. "Lily ki bawa Mami hak'uri nace" ya sake fad'a mata.

  "Kiyi hak'uri" ta furta a hankali.

  "Ni da kene a gidan nan ai ba Papinki yayi tafiya ba? Zan koya miki hankali ma tukunna maza jeki ki tattaro duka novels d'innan ki kawo su nan in cinna musu wuta ba shakka suke d'auke miki hankali 'yar iska kawai."

  "Ya isa Mami please kiyi hak'uri bazata sake ba in shaa Allah kiyi hak'uri" Hak'uri Afzal ya cigaba da baiwa Mami yayinda take ta huci, kunde san yadda fad'an itayenmu mata yake idan suka kama basu san suyi shiru ba, da k'yar ya samu ta hak'ura tayi shiru ta janyo hijabi daga kan igiyan shanya tare da d'aukan purse nata akan benchi ta fice don zuwa bus stop ta sake yin wata cafanin. Tana fita Amal ta ruga cikin d'akinta a guje had'e da jan sakata inda ta fad'a kan katifarta tana kuka. Afzal dake tsaye totally out of what to do daga bisani yabi bayanta, k'ofan ya gwada bud'ewa yaji a rufe don haka ya kira sunanta a nitse.

   "Lily?" Shiru tayi bata amsa ba se k'aran shesshek'an da takeyi yake ji.

  "Yi hak'uri ki taso ki bud'e wa Yaya kinji?" Nan ma shiru. "Yaya na miki magana bazaki tashi ba Lily? Yi hak'uri kinji? Ina nan ba inda zani sekin bud'e k'ofar nan" Seda yayi dagaske sannan ya samu ta taso ta bud'e masa, ta kai ga juyawa ta koma ciki kenan ya rik'e k'asan rigarta stopping her. Idanunta da sunka kad'a sukayi ja ta d'ago tana kallonsa a maraice.

 "Come with me" ba musu tabi bayansa inda suka zauna akan benchi. K'aramar gelen abayan daya tsinta a k'asa wanda yake da tabbacin a garin guje-gujen da suka ta6a da Mami ne ta yasar ya d'ago had'e da mik'a mata. "Gashi cover your hair" nan ma batayi musu ba ta amsa ta rufe bak'in gashinta me uban shek'i.

   "What happened Lily? Kin manta alk'awarin da kika d'au mun na cewa bazaki sake sa Mami surutu ba? Mey kika mata yau kika fusatar da ita haka har ta ta6amin lafiyar jikinki?" Shiru tayi ta kasa cewa komi gudun kar da ta soma magana ta shiga yin kuka.

  "Talk to me kinji?"

   "Yaya.." ta furta bayan tsawon lokacin data d'auka kafin ta iya furta wata kalman kuka yaci k'arfinta. Tausayi na hak'ik'a ta basa saboda be ta6a ganinta tana kuka me tsuma zuciya kaman na yau ba toh shin meya faru? A kan k'ona girki zalla de Amal baza tayi kuka haka ba kamar yadda itama Mami bazata tayin surutu yadda tayi ba, mey take nufi data kwatanta Amal da 'yar iska? shin meya faru?

  Be sake cewa da ita komi ba saboda yasan how badly she needed to cry, ya sani kukan nan da takeyi ne kad'ai ze iya rage mata k'unar da zuciyarta keyi mata don haka ya zauna yana saurronta tanayi badon yanaso ba sedon ba shida wata mafitar. A hankali ta shiga yin shiru, handkerchief nasa ya ciro daga aljihun wandonsa ya shiga share mata hawayen nata a hankali har ya samu tayi shiru.

   "Yaya-"

  "Shhh" ya katse ta a hankali "Don't speak."

  "Yaya but I need to let you know what's really happening ko Allah zeyi kai zaka yarda da ni kuma bazaka yimin kallon 'yar iskan da Mami keyi min ba."

  "Subhanallah Lily! Meya faru?"

  "Yaya Mami tak'i ta yarda dani dan Allah help me out" ta kuma fashewa da wata kukan. "Wallahi ni ba 'yar iska bace."

   "Shhh it's okay I'm here, yi shiru ki fad'a min meya faru."

  Hanci taja ta share hawayenta sannan ta fara kamar haka; "Ina yaron nan dana ta6a maka hirarsa ranan a office?"

  "Wanne d'aya? Yaron me markad'en bakin hanyan nan?"

  "Shi" ta amsa tana gyad'a kai.

  "Meya faru?"

  Hawayenta ta share da hanky'n da Afzal ya bata ta cigaba "Yaya sharri yayi mun gun Mami wai kullum ba aikina idan ta tura ni markad'e saidai inyi ta mishi hirar banza ina tatta6ashi."

  "Subhanallah!" yayi exclaiming cike da k'in yarda.

  "Yaya ko kai na ta6a shafa koda hannunka ne? Yaya ka yarda zan iya aikata abinda yake tuhumata da shi?" Ta tambayesa cikin kuka sosai.

  "Ko kad'an Amal you'll never do such a thing kibar kukan haka kinji? Your Yaya is here."

  "Thank you Yaya but Mami tak'i yarda dani wai sam ni 'yar iska ce idona a bushe yake ni munafuka ce, bata sanar da Papi ba tukun amman ta rantse se tayi hakan, shekaran jiya data aikeni markad'e ashe yace mata tabi bayana yanada abinda ze nuna mata bayan ya k'arisa markad'en yace in k'arisa in d'auka, dai-dai na kai inda yake tsaye sauran in d'aga roban kenan na zame na fad'a jikinsa ba tare da na sani ba ashe 6awon ayaba yasa mun don in zame. A sanadiyyar ture ni da yayi naji wannan ciwo" nan ta d'aga bakin skirt nata zuwa idon sahu sega wani babban k'warzani, fatan gun gabad'aya ya d'aye don azaba.

  "Subhanallah" Afzal Yayi exclaiming cike da tausayin Lilirsa. "Me kikayi masa ya za6i yayi framing naki haka Amal?"

  "Wallahi Yaya ba abinda nayi masa."

  "Tell me the truth Amal bakiyi masa komi ba?"

  "Wallahi Yaya banda cewa da yayi yana sona na nuna masa ko wuta da aljannah ze bani bazanso mutum irinsa ba bakuma abinda ya sake had'amu shine yace min wai zan gani sena lahira ya fini sukuni." Shiru Afzal yayi ko nazarin me yake se Allah. "Yaya kaima baka yarda dani ba?" Ta tambayesa sabin hawaye na ambaliya a fuskarta "Wallahi ni ban aikata abinda yake tuhumata dashi ba, Yaya please believe me."

   "Shhh!" ya katse ta "I believe you Lily nasan bazaki ta6a aikata abu haka ba, I'm here bazan tsaya ba se inda k'arfi na ya k'are in shaa Allah yaron nan da kansa zaizo har nan gida ya baki hak'uri ya kuma yiwa Mami bayanin gaskiyan al'amarin da bakinsa."

  "Yaya how is that even possible?"

  "Trust me okay?" Kai tayi saurin gyad'awa had'e da yi masa godiya. "Girkin da take cewa kullum kina k'ona mata shi kuma fa, haka ne?"





 RANA D'AYA
#RD
Love... king Miemiebee👄✨

4 comments:

Unknown said...

OMG! I can't wait 4 the next update
Miemiebee Allah ya kara basira please we're waiting 4 BWMH

Unknown said...

Thank you miemiebee😘 in luv with rana daya😓😫

Unknown said...

Aww you're welcome love

Unknown said...

Ameen ya Allah ❤️ i'll in shaa allah update within next week