(Like Mother Like Daughter)
⚜⚜⚜♠♠⚜⚜⚜🌟
written by miemie👄
9⃣2⃣
Washgary kuwa tunda safe suka shirya sukaje suka ma daddy sallama ya musu nasiha sosai sosai sannan suka fice se gdansu Saalihah nanma haka umma da abba suka musu nasiha Saaly tasha kuka sam batasan abinda ze rabata da ummanta dakyar Fudail yajata suka bar gdan suna isa airport jirginsu na sauk'a Habeeba kam se murna. Nan danan suka gama all processes akayi boarding jirgi ya tashi. Habeeba harda kuka ita a sauketa tafasa zuwa Abujan se dariya Fudail da Saaly suka mata, tafiyan 'yan mintoci sukayi suka iso garin abuja.
Acan new driver'n Fudail ya daukesu se sabon gdansu. Gdan ya casa na Bauchi a kyau harda fountain a ciki. Kai tsayuwa dan describing gdan b'ata lokaci ne wuyan Habeeba kam se da yakusan b'allewa dan juye juye. Komin gdan a kimtse yake kayakinsu daya iso jiya da daddare duk an shirya masu anyi shara anyi mopping an kunna turaren wuta gda de shi ake kira da aljannan duniya. Fudail yace, "sweery do u like ur new home? Zo mujw kga d'akin twins namu" "I like it? Infact I love it." Ta fad'a tana mai miurmushi.
Dad'i sosai yaji yadda Saaly take appreciating each and every single effort dayayi, wannan na d'aya daga cikin abubuwan dayasa yakeson ta kamar ze mutu.
Erin rayuwar da Fudail da Saaly suke living shi ake kira da rayuwar aljannar duniya. Ko musu bai had'asu as in tace abu black ne koda fari ne agreeing mata yake yace eh black dinne sede tunda tashiga month of na haihuwarta (due month) nata ta koyi wani sabon hali. Ba aikinta se masifa har tsoronta Fudail da Habeeba suka somayi abu kad'an seta tsigale mutum ynzu kam Fudail ya rage zama a gda kullum a office yake ko randa ba office k'arya yake mata yce akoo dan gudun masifarta. Habeeba baiwar Allah kam se yadda Allh yayi da ita masifa take sha gun Saaly kan ba gobe.
Flight to Dubai Fudail ya musu booking dukansu, harda Habeeba anje anyi su passport da komai sauran tafya, visa is ready. Saaly ba k'aramin dad'i taji ba da wrin suprise da Fudail yamata nan ta kikkira su Phaary take sanar dasu zata Dubai can zata haihu nan duk suka mata murna. Bint tace ai muma yau muke da niyan kiranki aurenmu nxt month in gaya miki, tare zamui aure nida Phaary. Saaly ta mugun jin dad'i wa frnds natan sede taji haushi she cant make it to their wedding sunsha hira sosai sannan sukayi sallama nan ma data kira umma haka suka ta shan hira shide Fudail wayan Saaly mamaki yake basa se tafi awa biyu tana waya shida Habeeba tsayawa kawai suke suna kallonta in yabasu dariya se su kyalkyale da dariya. Kallo kawai take watsa musu suyi shiru.
Ana gbe zasu tafi Dubai, Habeeba tagama shirya musu kap kayakinsu ba abinda suka manta daman basuyi sayyanan babies ba kan se sunje Dubai suyi. Ana gobe zasu tafi Saaly da Fudail da Habeeba duk suna zaune a parlour suna kallo. Habeeba na nan tamkar 'yar gdan inba wai ance me aiki bane za'a d'au sister'su ce. Saaly na kwance a jikin Fudail nata suna cin pop corn wayarta tasoma ringing. Tana kai dubanta taga new number dakamar barata d'aga ba sekuma tacanza mind nata tayi picking. Muryan Ikleema tajiyo ba k'aramin mamaki tasha ba nan tasa a handsfree Fudail ya rage vol na TV'n. Bayan sun gaisa da Saalihah ta rok'i gafararta take Saalihah ta yafe mata wanda ya mugun bawa Fudail haushi shi har yau inya tuna da abinda ta masa ji yake kamar ya shak'ureta ta mutu.
Bayan da Saaly tagama yafematan ne Ikleema ta tambaya "ina Fudail?" Saaly tace, "yana gefena in basa ne?" "Eh dan Allah kibasa inhar ze yarda." Nan ta mik'a masa Fudail ya matse kafad'a yace bare amsa ba, ba yadda batayi dashi ba yak'i sanda tayi kmar zatayi kuka sannan ya amsa nan ma bece mata komi ba. Haka Ikleema ta riga rok'onsa tana basa hkr tana kuka da k'yar ya yrda ya yafe mata from the buttom of his heart.
Ba karamin dadi taji ba Saalihah ta amsa wayar Ikleema se gdy take mata. Saaly take gaya mata ai yanzu ma sun dawo Abuja da zama kuma a gbe zasu tafi Dubai acan zata haihu. Ikleema taji mata dad'i sosai tamusu fatan alheri sannan tace tamata sendn numban umma takirata itama tanemi gafararta nan danan Saaly tamata sendn.
Ikleema ta kira Umma tata neman gafararta. Umma taji dad'in shiryiwan da Ikleema tayi take ta yafe mata a daren ranan suka k'ull k'awance da umma. Su Saaly kuwa washegary around 10:00AM jirginsu ya tashy. Wannan karan Habeeba bataji tsoro sosai ba musamman ma data samu emirates airline tabaje haka sui bacci su tashi har suka iso DUBAI. Bayan sunyi retrieving luggages nasu Fudail ya tsara musu taxi Habeeba na gaba sukuma suna baya kafafun Saaly sun kumbura sosai dukda cewar a first class sukayi tafiyan amman still sanda suka kumbura a *Jumeirah Beach Hotel* suka sauk'a nan ma Habeeba anzuba k'auyenci. Dan kud'i yama Fudail yawa harda kama ma Habeeba d'aki itama ita kad'ai dan kamar k'aramar kanwarsu suka d'au Habeeba badan komi ba dan yadda take reapecting nasu dakuma sansu gata marainiya ba mama ba baba.
A ranan de a gajiye suka kwanta. Washegary through out basu fita ba suka huta se nxt day ne suka fita shak'atawa wajaje da dama sukayi visiting a Dubai daga k'arshe sukaje city mall nasu inda Fudail ya ringa cika trollies da kayan babies. Ba abinda be saya ba. Bayan sun gama Fudail na wajen biya Saaly kuma suna zaunw da Habeeba dan yadda tagaji d'aga idan da zatayi ta hango wani me kamada Suleiman data tab'a mai rashin mutunci. Bata wani damu ba acewarta kama ne kawai dan me ze kawo Suleiman Dubai? Can fa tasake ganinsa yanzu kam hakurinta ya k'are tashi tayi taje tasamesa tareda masa sallama yana ganinta ya gane ta ya amsa da fara'arsa.
Kallonsa take dan wani kyan daya k'ara gashi ya k'ara kauri yanzu gonin sha'awa. Ganinta da ciki ya tabbatara masa dacewa tayi aure. Gaisuwa sukayi coldly sannan ta gaya masa abinda yakawo ta.
Ko kad'an shi yama manta da abinda ya faru tsakninsu dan ko ya yafe mata da jimawa. "To me kakeyi anan suleiman?" "Oh wai ni" ya murmusa "karatu." Tace, "wow na maka murna wani course?" yace, "civil engineering" atakaice. Kunya ne ya rufe Saalihah tana tuna time data ce masa;
"*kana iya karanta civil engineering*"
Murmushi ta k'irk'iro "gaskia na maka murna Allah taimaka. Daman ba komai bane ya kawoni dan na baka hkr gameda abinda na tab'a maka da dan Allah ka yafemin." "Haba anty Saalihah koh?" Ta giad'a masa kai "baki min komaiba hasali ma abinda kka min ma seya zamo kamar inspiration agareni bakiga yanzu ina karatu ba? Allah yafemana gabad'ai" dadi taji sosai "nagde matuk'a Suleiman zan tafi kar mijina yasoma nemana" ahaka sukayi sallama.
Nan da nan suka dawo htl nasu. Yanzude Saaly hankalinta yad'an kwanta mutum d'aya take nema har ynzu alhj me credit card. Ta samesa shknan she will now be able to live freely and peacefully liko others.
Hakade yawancin kullum suna fita strolling kasancewar takusa haihuwa, haihuwa nan da sati d'aya in shaa Allah. Yawancin kullum kuwa se sunyi yawa da umma da mummy. Tundaga lokacin tashiga tsoro daga ta tuna da wahalan da ake sha a labour room seta fara kuka Fudail ko yata lalashinta yana kwantar mata da hnkl.
No comments:
Post a Comment