Sunday, 5 March 2017

‘YAR GATA CE!

   *BY MIEMIEBEE *
Page 58
FEBRUARY, 2017



Daga baya dabara ce ta fad'owa Adeel inda ya bari seda Ruky bata gida ya kawo me gyara ya canza mai lock na k'ofofin duka, musamman ya tanada gun ajiye keys nasa inda hankalin Ruky baze ta6a bata ba. Da daren ranan Ruky na zaune a dining table tana had'a golden morn taga fitowan Adeel tsaf yasha supras nasa ready to party. Dariya ta qyalyalqe da "wanga wanka se muga ina zakaje" tayi stating confidently tare da shigewa kitchen dan d'auko abu. Fitowan da zatayi taga k'ofa wangale a bud'e. "Bade na mance ban sa key ba?" First abinda ta soma tambayar kanta kenan."Kode ya binciko inda nake ajiye keys d'inne?" Ajiye saucer'n dake hannunta tayi ta nufi d'akinta kamar yadda ta ajiye ta tanadar da keys d'in nufin be ta6a ba "to how?" Ta sake tambayar kanta. D'aukan keys d'in tayi taje ta gwada a jikin k'ofan, sede yayi k'ara kaman ya kullu amman ba kulluwan zahiri yayi ba ma'ana Adeel ya canza lock kenan. Lallai kuwa Allah yayi tana da mai gyara itama. Ko kwana a gida Adeel beyi ba ranan akuyan d'aure ya samu saki, washegari kawai da safe ya dawo yayi wanka ya wuce office. Anan ne Ruky ta kira me gyaranta ya canza mata lock d'in itama zuwa na da. "You wanna play the game? Then let's pray it" tayi maganan tana 6oye makullin nata. Yau dagangan ta fito parlour ta zauna tana zaman jiran fitan Adeel. Bada jima ba kuwa ya fito cikin shirin party like se k'amshi yakeyi. Magestically ya nufi k'ofan tare da gwada sa key nasa sede yayita wainawa amman k'ofa bai bud'uwa. Abu kaman fa wasa but his key aiint working, "what could be the problem?" Ya tambayi kansa. Juyawan da zeyi yaga Ruky na shirin dariya, wani dogon tsuka yaja.
   "Allah yaso tsaka ake yiwa tsaki, zaka gaji ka bari, the earlier the better gomma kaje ka kwanta kanada office gobe." Bata jira jin me zece ba takai plate nata kitchen tazo wucewa d'akinta kenan ya danna mata kira da "Ke!"
  "Ba suna na ba kenan."
   "Whatever me kike nufi?"
  "Me kuwa? Abinda kayi nima shi nayi."
  "Kina nufin kin canza min lock na k'ofan gidana?"
  "Sosai ma kuwa, kaima ba haka kayi ba?"
  "Amman yarinyan nan bakida hankali wallahi."

   "Hankalin ne ya jawo hakan ai seda safe."
  "Wallahi Ruky bana wasa dake, kizo ki bud'en k'ofan nan."
  "Saboda kaje ka samu mata a waje kana shafasu? Inaaa Adeel I won't let that happen." Da wuri ta shige d'akinta tare dasa lock. Tsaye yayi wajen totally out of it, wai shin meya auro wa kansa ne? Ba yadda ya iya ranan dole yayi cancelling fitan nasa. Washegari kuma da safe taje ta bud'e mai k'ofan, kaman shekaran jiya yau ma ya kirawo mai gyara ya sake canza mishi lock yadda da daddare ya samu ya fita party abinsa. The next day itama Ruky ta kirawo mai gyaranta ya sake canza mata lock d'in haka fa suka cigaba da wasan yara. Shi Adeel seya biya kud'i ake canza mai lock d'in. Itako Ruky a kyauta me gyaran yake mata saboda na gida ne shi. Ganin kud'insa na iya k'arewa a hakan ya hak'ura kawai ya barta. Ya zammana yanzu ba kullum yake zuwa party ba randa zasa tun safe idan ze wuce office se ya d'au kayan da zesa ya fita dashi sekace dole. Daga office ya wuce gidansu Xarah ya d'auketa outting byan Maghrib ya wuce gidan Mami yaci abinci ya watsa ruwa ya wuce party abinsa.

  Ruky de tashiga damuwa dan kuwa ba abinda yafi ci mata rai kaman taji Adeel na zuwa party. Time suka sa ita da Safiyya suka shirya tsaf suka jesu gidan su Safiyya bayan dogon binciken da sukayi har suka gano gidan nasu. Kaman abinda suka yima Nusee haka sukayi ma Xarah ma sede ita Xarah idanunta a bud'e suke, kaca-kaca sukayi da Ruky wanda daga k'arshe seda Ruky ta rufe ta da d'ankaren duka a idon mahaifiyarta da Safiyya tayi mata rik'on da bata iya k'watan kanta. Lik'is ta daka Xarah dake nan 'yar pirit. Sannan ta koma mota ta fito da gallon na ruwan da take cutan mutane tace acid ne. Ita sam seta watsa wa Zarah. Nan fa Xarah da Mom nata suka kid'ime wannan wace erin mahaukaciya ce. Xarah bata son abinda ze ta6a mata fuska don haka tayita rok'on Ruky tana had'ata da Allah kan bazata sake shiga mata harkan miji ba. Seda Safiyya tasa baki kaman dagaske sannan Ruky ta hak'ura suka fice. Tun fa daga wannan rana Xarah bata sake picking call na Adeel ba ita tasan me ta gani. Daga bakin 'yan unguwa Adeel yaji abinda Ruky ta sake yimai, gida ya koma ya kwakkwad'eta inda take threatening nasa kan idan har ya sake ta6ata wallahi seta k'ona Xaran shi kuma tayi zaune kan ruwan cikinsa.
 
  ***
   Life loved on, duk girlfriend da Adeel yayi Ruky na sane da ita, seta bari relationship nasun yayi k'arfi sannan tajeta da gallon nata ta tada bori ta tsoratar da bayin Allah. Haka Adeel ya kasa yin gaba, bayan nan kuma ga k'ananu-k'ananun d'auke-d'auke da take yimai. Saboda ba kud'i yake bata ba yanzu gashi har yanzu ita ta kasa samun aiki, sena lecturing ita kuwa wai bata so its stressful. Daga yau ta sata mar dubu biyunsa, se gobe dubu d'aya kai atimes har biyar. A dalilin haka yabar ajiye ko k'wandala a gida, gabad'aya rayuwarsa ta gama hargitsewa da kalan tashin hankalin Ruky, he can't explain just how much he is missing Zeezee. Divrocing Zeezee is the biggest mistake he has ever done, haka kawai bata mishi komi ba ya d'au karan tsana ya aza mata ya riga maltreating nata, why? He can't answer.

    Cikin ikon Allah Ruky ta sake samun wani cikin, wanda yana 5 weeks again ta sake miscarrying baby'n. Abun ba k'aramin damun Adeel yake ba, ba shida burin daya fiye mai yaga jininsa yanzu. Ya dawo daga rakiyan neman mata saboda ko yayi ba riba se ma asara, yayi ta kashe musu kud'i daga k'arshe Ruky ta kora masa su. Gashi nan ne kawai da Ruky suna maneji.


     ^*^*^_ZEEZEE_*^*^*
  Da rasuwan Baba watanni da d'an dama kenan yanzu, getting to 5 months. Zeezee has finally moved on lokaci-lokaci take zubar da hawaye idan ta tuna da rauswan sa, amman kusan a kullum kam setayi tunaninshi. Ta fannin heartbreak nata ma yanzu ba laifi saboda gabad'aya ta manta da Adeel on occasional purposes kawai take tunawa dashi, sede wani hanzari ba gudu ba, a day never goes by batayi tunanin Ya Al'ameen ba bata da mafarkin daya fiye mata ta sake kasancewa matarsa again saboda ta farinta mishi and show him just how much she loves him.
   Manyan mutane da dama sun leqo kai don neman hand d'in Zeezee in marriage amman gabad'aya sede tayita raina musu hankali ita she believe one day she'll be MARRIED AGAIN to Ya Al'ameen. Fateemah matar Ibraheem ma ta sake haihuwa inda ta samu 'yar ta again wanda shi Ibraheem da ita Fateemah suka yima Zeezee takwara kasancewar situation nata na rashin haihuwa. Mama tayi-tayi da ita suje asibiti a duba ta don sake tabbatar da komi da kuma duban ko da akwai taimakon da za'a iya mata a gyara mahaifar amman tak'i saboda batason abinda ze sake jefa mata ryuwarta cikin k'unci.
   Zeezee ta d'au son duniya ta d'aurawa 'yar Ibraheem me sunanta. Ko a mafarki bata ta6a kawowa a ranta Ibraheem zeyi mata takwara ba, d'aya daga cikin alkhairin daya fito daga tafiyan Baba shine jituwa dakuma so tare da had'in kan daya sake yad'uwa a tsakanin yaran shi. Kowa yayi mata farin cikin wannan takwara data samu, atimes idan ta rik'e mini Zeezee se kawai ta fara kuka tuna ita fa yanzu shikenan bazata ta6a ganin jininta ba, Adeel ya cuceta na har abada. Ko bayan suna ma Zeezee tak'i dawowa gida seda ta k'ara musu wani sati biyun sannan ta dawo ta. Unlike before wannan karan Fateemah taji dad'in zama da Zeezee, komai Zeezee keyi mata wanka wa Maamah, shirya ta school, dafa abinci. Wanke-wanke da shara ne kawai me aiki keyi. Ibraheem couldn't ask for more, shiri sosai suke yi da Zeezee yanzu saboda tadena yimai rashin kunya. Har atimes yake neman tsokanarta wai tad'an yi mai rashin kunyan nan nata mana he misses beating and kicking her around. Kafin Zeezee ta baro Abj seda wani friend na Ibraheem ya ganta ya kuma yaba mata da tayi mai sosai and yana sonta da aure. Unlike before da idan friend nasa yace yana son Zeezee yake jin haushi wannan karan murna yake yazo ya sanar da Zeezee sede sam ta nuna mai she is not interested tare da yimai k'aryan wai ita bata son danginsa suzo suna goranta mata akan rashin haihuwarta but deep inside don tana son tazo ta komawa Al'ameen ne take avoiding d'in kowa.

^*^*^
   Zeezee tayi nisa sosai ba laifi ta fannin haddanta, tana neman izu goma sha bakwai kenan, hadda ras a kanta. Wani jin wak'a duk ta dena se jifa jifa. Ana cikin haka ne rana d'aya over the weekends bayan Zeezee ta d'auko yaran Mariam ta kawosu nan gida, suka jiyo ana knocking daga bakin gate. Alokacin ma abinci take baiwa Ummie, Ramlah na gefe tana cin nata. Ramlah na jin knocking tamiqe a guje zata je ta bud'e. Haka take ita mayyar bud'e k'ofa ce, kuma bata tanbayan ko waye kawai ita bud'ewa take which is not good.
   "Ramlah dawo nan" Zeezee tayi maganan tana k'ok'arin tashi daga zaune. Sanye take da wata purple lace me torches na black and white, kanta a bud'e ta kama gashinta gu d'aya tare sa lank'washe jelar.
  "O'o ni zan bud'e Aunty Zeezee."
  "Kidawo nace zan bud'e." Ai ko sauraronta Ramlah batayi ba ta k'arisa da gudu ta bud'e se gani kawai tayi kan bindiga na mata sallama. Da gudu ta koma bayan Zeezee tana la6ewa "ahtoh! Maganin wanda bai jin magana kenan, keba wai bakiya jin magana ba wataran d'aukeki zasuyi su tafi da-" bata k'arisa maganan ba taga the most breathtakingly gorgeous soldier ever which is non other than *Maj-gen Al'ameen.* Sanye yake da killer uniform nasa me sake k'ayata shi, d'ayan hannunsa na d'auke da wayoyinsa while kuma the other hulansa, gefensa da kuma bayansa sojojinsa ne suna guarding nasa. Wani k'war jini ya sake yimata, dama Ya Al'ameen nada kyau haka? Ta tambayi kanta a zuciya. Ita da ta d'au kyan farintaka ne kawai dashi ashe ba haka abin yake ba, Ya Al'ameen koda za'a fenta sa bak'i kyan na nan yadda yake sede farin na k'ara mai ne kawai. Wow! Kawai take ta furtawa a zuciyarta ta kasa keeping eyes nata off him gashi wani fresh daya k'ara gaskiya ba k'arya time da suke tare yad'an fad'a all due to abubuwan da take yimasa.

   Shima kallon nata yake long time no see, dukda Zeezee tad'an k'ara weight da haske compared to lokacin da ta fito daga gidan Adeel, amman har a yanzun bata kai kauri dakuma hasken da take da shi ba time da take gidan Ya Al'ameen. Anytime ya kalle ta banda kyau datake k'ara yi masa theres nothing more. He stared at her for about 2 minutes sannan ya kawar da kansa itako har anan ta kasa dena kallon nasa tama manta ba d'ankwali bale hijabi a jikinta.
  "Uhm-uhm" yayi clearing throat nasa ganin kallon nata bana k'arewa bane. Shi tambayan kansa ma yake me Zeezee keyi a gida? Instead of her matrimonial home dan bashida labarin ta rabu da Adeel at all. Toh kode tazo yini ne? He can't judge. Baki na 6ari guiwa suna shaking tace, "Yya... Ya Al'ameen?" Still not believing her eyes ashe Allah ze sake kawo mata rananda zata sa masoyinta acikin idanunta, addu'a d'aya take yi a ranta a yanzu haka. Allah yasa miji na garin da Baba yayi mata fata kafin ya rasu shine Ya Al'ameen.
   "Na'am Zainab" ya amsa cikin OMG voice nasa me sake tafiyar wa mutum da imaninsa. Nan fa heart na Zeezee yayi skyrocketing daga earth zuwa pluto (Lubna🀣) bata san tayi missing Ya Al'ameen ba seda tajiyo wannan zazzak'ar muryan nasa.
  "Aunty Zeezee kinsan wannan me bindigan ne? Wayyahi mu gudu kafin ya mana dush-dush mu mutu." Cewar Ramlah tana 6oye still a bayan Zeezee. Dariya ta bawa Al'ameen wanda hakan yasa ya murmusa sosai revealing his two sided pointed dimples and making him worth more looking, Zeezee couldn't stop staring and falling in love all together.
    "Inji wa Baby? Ba Wanda ze har6eki kinji? Zo abinki" ya nuna mata hannunsa. Shima Al'ameen gwana ne when it comes to son yara, kafad'a ta buga "o'o zaka min dush-dush in mutu." Widening dariyan nasa yayi tare da cewa men nasa "excuse me, ku jirani a waje." Se anan Ramlah ta d'an ji iska, "zo yanzu toh kinga sun tafi."
  "Inje Aunty Zeezee?"
  "Kije Ramlah, this is your Uncle ba abinda ze miki." Ba gardama tajeta ya d'agata sama ya shiga jero mata questions se hira suke wane tun da sun san juna.
     Kasa dena kallonsu Zeezee tayi tana me sake tsanar kanta, da bata biyewa Adeel ba ta rungumi k'addara tayi wa iyayenta biyayya da yanzu haka sede Al'ameen farin cikinta yad'au baby'nsu yana cuddling mata ko masa.
   Chan Al'ameen ya dawo da kallonsa kan Zeezee data kasa dena kallonsa tun d'azu, bata bari idansu ya had'u ba tayi sauri ta kawar da idonta akansa tare da maidosu kan Ummie tana wasa da hannunta. Shi kam ma ya d'au Ummie 'yarta ce saboda Ummie na nan sekace wacce batayi two years ba sam bata da tsawo Ramlah ta fita girmah.
 
   "Ramlah wace wancan? Baby'n Aunty Zeezee ce?"
  "Wacce Uncle Soldier?" Dan sunan data sa mai kenan. Murmushi ya mata sannan ya nuna Ummie.  
    "Ohh Sunanta Ummie."
   "Ummie" ya nanata "Yar Aunty Zainab ce?"
  "Laaaa!" Tayi covering mouth nata with both of her palms "Aunty Zeezee fa batada baby, k'anwa nane."
  "Aww haba ashe shiyasa naga kuna kama, Ummie Baby zo kinji?" Aiko ta buga kafad'a tare da kama k'afafun Zeezee gagam. Question nasa na "wancan 'yar Aunty Zainab ce?" ya tsaya wa Zeezee a wuya, bata hankara ba tajiyo idanunta na neman cikewa da hawaye da k'yar ta samu ta had'iye kukan sannan tayi womaning up tace "ka shigo ciki Ya Al'ameen bari inyi wa Mama magana."
   "Okay tana cike ne?" Ya tambaya yana bata full concentration nasa cike da dignity.
  "Eh bismillah." Bayan ta yabi yana wasa da Ramlah dake ta faman shafa sajen fuskarsa tana cewa irin na Daddy na. A parlour tace ya zauna ita kuma tayo d'akinta inda ta d'au gyale ta yafa, har anan kaman jela Ummie keta binta. Kitchen ta nufa tare da d'auko masa ruwa da 5 alive ta kawo har gabansa ta ajiye. "Ai da kin bari Zainab."
  "A'a Ya Al'ameen koban tambaya ba nasan daga tafiya kake" tayi maganan tana tsiyayar masa da juice d'in a cup.
   "Toh nagode."
  "Bari inyi wa Mama magana." Tana miqewa Ummie ma ta shiga bin bayanta, "Ummie bazaki bar Aunty Zainab ba kizo mu gaisa?"
   "Ai Uncle Soldier kabal Ummie nima haka take min wataran kaman bata sanni ba nima sena shareta kawai, kaima ka shareta, ni kad'ai ma na isheka wasa." Kai kawai Zeezee ta kad'a sannan ta shiga ciki ta sanar da Mama dake fitowa daga bayi bayan tayi wanka.
   "Allah sarki Maj-Gen. kice mai gani nan zuwa, kun gaisa ne ke?"
  "A'a yanzu zanje mu gaisa."
  "Yauwa jeki nima gani fitowa."
  Back in the parlour ta tarar dashi da Ramlah se game take bugawa a wayansa tana zaune bisa cinyansa. Daga can nesa adjacent to him ta zauna tare da zaunar da Ummie a gefenta.

   "Ina yini Ya Al'ameen?"
  "Lafiya Zainab" ya d'ago kai yana kallonta. "Mun yini lafiya?"
  "Lafiya k'alau ya gajiyan hanya da kuma aiki?"
  "Alhamdulillah, ya mukaji da hak'uri Baba lokaci yayi."
  "Alhamdulillah Baba Lokaci yayi."
  "Toh Allah ya jik'anshi ya gafar ta mishi ya kuma kai rahma kabarinsa, our prayers are with him."
  "Ameen ameen nagode Ya Al'ameen."
  "What for? Sannun mu da hak'uri ko? Tun tuni nakeson shigowa wallahi but Allah be nufa ba, an kai mu Maiduguri saboda state of emergency shiyasa kuka jini shiru aiki yamin yawa. Da akayi rasuwan kuma I called you but bana samun ki, Mama tace bakida lafiya."
   "Ayyah ba komai Ya Al'ameen ko yanzu da kazo ai bakayi latti ba, zuwan shine babba ai, da rasuwan nima banji dad'i bakam shiyasa."
   "Ayya ya jikin toh yanzu?"
  "Alhamdulillah da sauk'i sosai."
  "Toh Masha All-" be gama maganan ba Mama tayi sallama tare da shigowa nan ya shiga neman sauk'owa daga kan kujerar don bata girma inda tayi saurin hanasa.
    Gaisawa sukayi sosai inda yayi mata ta'aziyya itama yake kuma bata hak'uri na jinkirta zuwa ta'aziyyan da yayin, su Hajiya Mama duk suna gaishesu. Bayan gaisuwa yayi wa Baba addu'a sosai, seda Zeezee ta zubda k'walla se gani take kaman jiya-jiya Baba ya rasu.
  "Mungode sosai Maj-Gen. Allah shi biya."
  "Ameen Mama" d'ayan wayansa ya d'aga ya kira men nasan kan su shigo da drinks d'in. Carton na malts da other canned drinks ne har guda biyar ya kawo musu, sosai Mama tayi appreciating tayi kuma masa godiya haka Zeezee ma.
  "Toh ni zan tafi Mama dawowa na kenan daga tafiya zuwa jibi haka nakega zan koma."
  "Toh, toh a huta gajiya Maj-Gen mungode fa sosai ina zuwa." Nan ta koma ciki. Tun tun d'azu kallonsa Zeezee take ko kyafta ido bata iyawa tana ganin ze juya seta kawar da kanta haka ma yanzu, kallon Ummie dake zaune akan cinyarta yayi sannan yana murmushi yace "anya kuwa wannan ba 'yar Aunty Zainab bace Ramlah?" Murmushin dole ta k'irk'iro sannan
tace, "ba 'yata bace Ya Al'ameen."
  "Kai ban yarda ba dan kin dace ki zama Maminta kyanku d'aya."
   "Kai Ya Al'ameen 'yar sister na ne Mariam, dukansu biyu da Ramlah."
  "Ayyah toh Allah ya raya mana su, ina namu toh?"
  "Allah be kawo ba tukuna" ta amsa tana forcing out a smile.
  "Toh Allah kawo rayayyu masu albarka."
   "Ameen ameen."
  "Ya mai gidan naki da kowa?"
  "Alhamdulillah" kaman da tayi mai k'arya tace yana lafiya seta ga kuma ba amfani. "Na dawo gida ai yanzu." Sam be fahimci me take nufi da ta dawo gida ba yanzu, "baza a iya rabaki da gida ba Zainab, kin dawo yima Mama weekends kenan."
   "A'a" ta kad'a kai "actually mun rabu dashi tun kafin rasuwan Baba ma." Ido ya kwararo waje da kyau yana sauraronta amman Adeel be kyauta mata ba, shi bayi ma tunanin kalan rashin kyautatawan da tayi masa, rashin kyautatawan da Adeel yayi wa Zeezee ne ke damunsa (see true love.)

  "Subhanallah!"  Sam beji dad'in hakan ba, she's of too tender age ace aurenta biyu duk babu no wonder ashe yaga tad'an zube not as before. "Allah rufa mana asiri toh."
   "Ameen nagode." Tayi forcing out a smile "ya Madam kuma? From all seeing tana kula mana da kai."
  "Haha" yad'an murmusa "toh gamu nan de, har yanzu ban sake..." sekuma yayi shiru da kaman yace mata yana shirye-shiryen sake aure se kuma ya fasa. Dukda be k'arisa zancen nasa ba Zeezee ta gane be sake aure ba yake nufi. Only this thought is driving her crazy.




*MIEMIEBEE.         Team #YGC!πŸŽ€*
 Beeenovels.blogspot.com
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

No comments: